Showing 54001 words to 57000 words out of 190738 words
Chapter 19 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt
ce "Ina fa? Nasan dai watarana zaka ci ubanka ka kuma koma Nahutun Batsari"
"Shikenan daga na faɗa maka sirrina sai ya zama abin gori Mujahid? Mene ya kawo maganar Batsari kuma?" Mujahid ya ce "Babu laifi a tunawa mutum asalinsa, ai arziƙi ne ka yi baƙo ya kashe ka" Mujahid ya sake yin dariya ya ce "Wallahi ka ji tsoron Allah ka daina rayuwar ƙarya"
"Idan ban ji tsoron Allah ba, Mujahid kai zan ji tsoro duk abinda nake yi bashi ne zan biya ka dana amsa sunan mijin Hajiya" Mujahid ya riƙe guntun gemunsa ya ce
"Ba shakka, wannan shi ake kira da kunne ya girmi kaka, duniyar rawar ƴan'mata na gaba ya koma baya, kai a ɗan iska ba labar farko ne"
"Ka rufa mini asiri"
Mujahid ya ce "Allah ya rufa mana, ai duk duniya babu mai jin wannan zancen ka huta ka sarara" Ya yi murmushi yana ƙanƙance idanunsa cike da iskanci wanda suke fusgar ƴan'mata ya ce "To ya Opay na zo yi, ka bani wannan shaddar awa ɗaya zan yi kawai ka haɗa mini da hula zanna bukar ka bani aron air-pies ɗinka na Iphone or bluetooth ake ce masa ko? Sai kuma takalmi"
"Duk a nawa? Domin masu kayan anjima za su zo amsa karka bar ni a ruwa don ubanka zan ci" Yana jingina da jikin bango hannunsa ɗaya a cikin aljihu ɗaya yana shafa sajensa ya ce
"1hour ya yi yawa zan dawo, wani get-together zani ne a group ɗinmu na Kano celebrities". "Yaushe Bakatsine ya dawo Bakano? A gaskiya idan ajeboters suka ji abin ba zai yi kyau ba" Tattara harɗaɗɗiyar shaddar ya yi, ya ba shi yana karta masa warning sosai ya ce "Dubu biyu za ka bani" Ya ce "Na ƙara maka da ɗari ɗaya"
Mujahid ya girgiza kai ya ce "Ɗan iskan Almajiri"
Kamar yadda a rayuwa baka san mene zai faru da goben ka tunda al'amarin na kasancewa kamar karatun littafi, abinda ka karanta a wannan shafi ba shi ne zaka ruska a shafin gaba ba, haka kuma bangon littafi bashi zai fasalta yadda labarin ya gunsa ba. Yau fari ne gobe baƙi, yau dariya gobe kuka, yau zuma gobe maɗaci. Rana ta juya zuwa kwanaki, sannu a hankali kwanaki ke mirgina wa suna rikiɗe wa zuwa satutttuka, sati ya zama watanni daga sai a yi maganar cikar shekara. Tafiyar Ustaz zuwa Lagos ya dawo da rayuwar Ridayya sabuwar fil, ta koma ruwa. Damuwa da ƙunci sune abokan hirar ta, bata jin daɗin zaman gidan domin hatta Umma bata wani damu da ita ba, hakan baya rasa na saba da sabon Malamin da Ammi ta sauya, asiri gaskiya ne sai dai ya zo maka da sauƙi idan kana da kariyar Ubangiji.
Bayan rubuta Jam ta samu maki na ban mamaki wanda ya yi daidai da kalar makarantar da Ustaz yake muradin sanya ta ciki wato B.U.K _Bayero University Kano_ A baya basa ɗaukan under 18 amma dake abu na manya ne an shiga an fita aka samar mata da Admission ta samu gurbin shiga a shekarunta daya kasance 16 amma jikinta ya ƙaryata ƙanƙantar shekarun.
"Ridayya tun ɗazo kikai shiru, wai a hakan bama ki fara attending lectures ba?" Ridayya ta yi shiru zuciyarta na bugawa da abinda zata ruska yau a gida, Baba ƙarami baya garin ya je Rano gashi Hajiya Grandmother ɗinta ta je Umra tunda suna cikin watan Ramadan ne. Tsaki wacce suke tare ta yi ta ce "Matsala ta dake wulaƙanci da raini"
"Haba mana Mardiyya"
Ridayya ta furta a sanyaye idanunta na cikowa da hawaye. Mardiyya ta ce "Mtwsss mene na kuka to? You looks so doll mene?"
"Nothing, babu" Ta faɗa tana share hawayen idanunta daya kasa tsaya mata. Diyya ta ce "Ni bana son irin haka, sai na faɗa miki damuwata amma ni kiƙi faɗa mini meke damunki ko Abbiey ne?" Jin sunan Abbiey ya saka Ridayya ɗan lumshe idanunta tana kokawa da numfashinta daya gama tsaya mata a maƙo shi
"A'a" A fusace Diyya ta ce
"To banga amfanin zama ƙawa a wajanki ba, daman nike tuttura kai na ina miki shisshigi a rayuwa, na yi hakan ne saboda conditions ɗinki"
Ridayya ta marairaice ta ce "Kema na ishe ki?" Sai kawai ta fashe da kuka har da shassheƙa ta ce
"Don Allah na dawo gidanku da zama kafin Abbiey ya dawo Mardiyya?" Tausayin Ridayya ya ƙara kama Diyya ta ce
"Komai ya zafi maganinsa Allah, ita ƙaddara tana da nata lokacin ki rubuta ki ajjiye watarana zai zama tarihi" Ridayya tunani take a zuciyarta yaushe za ta yi murmushi irin na Zainura? Irin na su Junaid yaushe zata zama cikakkiyar ƴa kamar kowa a gidansu? Ita da gidan ubanta amma ya fi ƙarfinta? _How long_ zata kasance haka? Sai yaushe komai zai zama daidai a rayuwarta? "Don Allah na tambaye ki Mar"
"Allah ya bani iko" Ridayya ta ce "Da gaske ba zan taɓa yin aure ba wai? Ba zan taɓa samun wanda zai ce yana so na ba? Wai zan ƙare a gidanmu har abada kamar baiwa" Diyya ta ce
"Ki daina faɗar haka, shi aure ai lokaci ne da shi da mutuwa ba a saka musu rana, da shi da haihuwa ba a yin gorin su babu maki ki yi auren ki bar ni, ki manta ki saka karatu a gaba ki yi achieving abubuwan da kike da buri" Ridayya ta yi shiru tana sauke ajjiyar zuciya hawaye yaƙi tsaya mata gashi idan tana kuka leɓen ƙasa ya yi sharɓeɓe ya sakko ƙasa hancinta ya bubbuɗe. Ganin tana sauri ya saka Diyya riƙe ta sosai
"Wannan saurin fa? Kar ki faɗi fa" Gabaɗaya ta tsangwami kan ta ji take ko'ina a makarantar gulmarta ake gashi ta hango wasu matasa tsaye a jikin mota sai kallonta suke kamar ta kurma ihu ita kam idan haka ne bata jin zata iya karatun. A haka suka gilma ta gaban samarin suka shige wani ya yi saurin toshe hanci ya ce
"Smell wannan kill me oh gosh!" Wani matashin saurayi ya faɗa yana rufe hanci da hanky. Moo Ya ce "Ban son sharri kana nufin mun yi tusa ne?" Khalil ya ce "No, I don't mean that, that black girl data shige ita ke yin warin" Duk suka juya suna kallon bayan Ridayya abaya ce a jikinta mai ɗan faɗi ta ɗaure igiya a ƙugunta, yadda abayar take baƙa ƙirin haka jikin Ridayya suka yi anko haƙonta ne kawai da idanunta masu haske a jikinta. Haɗa baki sukai wajan furta
"Rabbi ya yi halitta, halitta, halitta...," Shaba ya ce "Asnanic ya yi basira wajan yin waƙar nan, wlh ban taɓa cin karo da baƙar mace irin wannan ba, tab kwalta"
"Ga leɓe ina ruwan Dandamali" Moo ya ce "But she's arrogant, i like the way she's act"
Tunda suke surutun su, bai ɗago ba bai ma san a kan wa suke magana ba, saboda ba kowa ya sani a school ɗin ba. Sai baza ƙamshi yake mai ɗaukan hankali kaf cikin haɗaɗɗun matasan babu wanda ya kama yatsarsa a kyau da haɗuwa Ubangiji ya yi halitta, fari tas har ɗan yellow yake ga sajensa daya gewaye fuskarsa ya yi daidai da gemunsa mai kyau. Wagambari ne a jikinsa brown colour ya ɗora hula zanna bukar ya bluetooth a kunnensa ya riƙe waya iphone a hannunsa yana dannawa. Kan shi ya ɗaga ya kalleta idanunsa a sauka a faffaɗan ƙugunta dake juyawa ta cikin abayar, ya jima kana ya ɗan taɓe baki ya juya. Khalil ya ce
"Meer ka san ta ne?"
Ya ɗaga shoulder duka biyun alamar "No"
"Bama zata kula ka ba, ba hannunka ba ce?"
"A saboda bani da qualities da zata kula ni? Mu ai sai dai mu saka mace kuka mu ɗora mata hawan jini, har yanzu banga kala ta ba" Moo ya ce "Na santa fa" Duk suka juya suna kallonsa da alamar ƙarin bayani ya ce "Ridayya Muhammad-Bilal Rano is her name, babanta a yanzu mai arziƙi ne sosai da sosai yana da kantuna a katin kwari da sabon gari, gashi yana kwangila kala-kala business yake na ban mamaki, sai babban yayenta mai suna Muhammad-Bilal Tahir Rano ana ce masa Ustaz shi ne Md a fidelity bank dake Lagos yana mugun son ta, hatta aikin da ya ke yi domin ita ne. Babban mutum ake ce masa a familyn saboda ya girmi kowa kasancewar basu da wani yawan ƙwarai duk abinda ya mallaka sunan Ridayya ne a jiki, sai dai ita kuma kaf dangin basa son ta hatta babanta wai ya ce ba ƴarsa ba ce shi ne shi kuma Ustaz ya raineta tun tana ƙarama, yarinyar nan da kake gani ba hannun kowa ba ce dukka da muninta kamar a yanka a ɓoye wuƙar ko a haɗata da su Dila a kejin zoo road"
Meer ya ce "Wow interesting, kawai ka ce kadara ce" Moo ya ce "Meer kai me za ka yi da ita ai Daddynka ba zai bari ka auri ugly ba" Meer ya jinjina kai ya ce "Zai bari mana, matsalar na tsani abu mai muni gaskiya bana ƙaunar baƙar mace yadda nake fari na samu fara mu dinga haifar farare"
"Ba zata taɓa sauraran ka ba" Cewar Moo. Da sauri Meer ya ce "Hujja?"
Kai tsaye ya ce "Ta yi sati tana shigowa School fa, kuma ina bibiyarta duk wasu gulma na ƴan mata ni nake kawo muku, to ko mata bata magana da su balle namiji, kullum cikin kuka take sai dai tana da diri fa idan ka nutsu ka kalleta wallahi"
"Ko soyayyar minti ce sai na rinjaye ta mun yi, na ci moriyar ganga na yar da ƙwallon mangoro na huta da ƙuda kuma" Khalil da babansa ya fi na kowa kuɗi a wajan ya ce
"Caca" Gabaɗaya sukai shiru Meer ya ce "Ina ciki" Khalil ya ce "Idan ka nemi soyayyar yarinyar nan, kuma ka sami abinda kake so kana da 5 Million kassh" "Are you sure?" Khalil ya ce "Ai idan maganar caca ne ba a wasa, idan kuma bata amince maka ba zaka bani wani abu dana jima ina buƙata a wajanka, na baka nan da wata biyu" Duk sukai ihu Meer ya dinga tunanin miliyan biyar ko dubu ɗari ta kansa bai taɓa riƙe wa ba, hatta yadin jikinsa wajan Mujahid mai guga ya yi opay ɗin su, wayar ma ta Mujahid ce amma kaf cikin abokan nasa babu wanda ya san asalin Meer ganinsu yake kamar duka masu kuɗi shi ne kawai ɗan gidan Malam Ɗan'lami ya ji a ransa dole ya bi salo mai kyau na burge Ridayya kafin furta soyayyar.
Ridayya na komawa gida ganin Umma bata nan ita kuma ba zata iya yin girki ba saboda ciwon cikin dake damunta, gashi ko azumin ma bata yi, ya saka ta cire hijab ɗin kanta daga ita sai duguwar rigar da ta bi jikinta ta yi luf ita na maiƙo rigar na maiƙo. Ita ko powder bata taɓa shafawa ba bata kwalliya bata san yadda ake ba karatu kawai ta saka a gaba don tana da buri mai girma da take son cimma, dake ɓangaren Mefa take son karanta Medicine, daga ta zama Medical Doctor sai ta nufi Gynea. Bachelor of Medicine (MB) of Surgery (BCh) and of Obstetrics (BAO).
Idanunta rufe take son buɗe cooler ɗin ta ji an ce "Wallahi kina taɓa wa zan faɗawa Mami" Ridayya ta kalli Zainura tunu idanunta ya sauya ta ce "Yunwa nake ji"
"To cinye ni, ko me kika taɓa a gidan nan najasa ce wallahi" Ridayya ta kalli Zainura bata kula ta ba ta fara ƙoƙarin ɗora tukunya zata dafa Indomie "Wannan kuma ki ɗauki mai kama dake Allah ya sauwaƙe ki zama yayata kila ke fa shegiya ce zina aka yi aka haife ki"
"Zainura!" Ta ji Mami ta daka mata tsawa tana juyawa ta ce "Mami wallahi na tsane ta ai ƴar tsintuwa ce kuma mummuna duk gidan nan ita ce baƙa" Ammi na zaune ba ta yi magana ba Mami ta ɗaga hannu ta zabgawa Zainura mari idanunta na sauya kala har ƙasan zuciyarta ta ji zafin maganar amma koda wasa ba za ta yi kusantar kan ta da Ridayya ba. Kafin ta ɗauke hannunta Mami ta ji an zabga mata mari da sauri ta ɗaga idanu kallonta ya sauka a kan Baffa ashe tun jiya ya dawo bata da labari dukda cewa girkinta ne
"She is right, Zainura nada gaskiya wallahi kika ƙara taɓa mini ƴa a kan wannan shegiyar mujiya sai na yi maganinki Fatima, kuma waye ya hanata yin azumi ma?"
Kuka Ridayya ta fashe da shi sosai ta kalli Baffa ta kalli Mami ta ce "Baffa, Mami yau ɗaya ina neman alfarma don Allah don girman Allah ku nuna mini iyayena na gaskiya na koma wajan su, idan ni tsintata a ka yi a faɗa mini gaskiya ko gidan marayu ne na koma, idan kuma da gaske ni ƴar ku ce don Allah ku faɗa mini shin da aure kuka haifeni? Ko kuma zina ta samar dani, shin ni na yi kai, Ubangiji daya baku Zainura shi ne ya halicce ni don.....,"
Kau! Mami ta sauke wa Ridayya mari kalmar zina ta gigita Mami sai kawai ta fashe da kuka tana yin bedroom ɗinta. Baffa ya ce "Ni kik faɗawa haka?"
"Ka yi haƙuri Baffa, wallahi zuciyata bugawa za ta yi na kasa jurewa" Cafko tufkar kanta ya yi ya shiga jaa tana ihun a zaba tana kiran sunan Abbiey da Ammi Baffa ya shiga dukanta kamar jaka ya saka ƙafa ya murje mata yatsun hannu azaba ta saka ta saki fitsari. Addu'a take inama a wannan dukan Ubangiji ya amshi ran ta? Inama mutuwa zata ruske ta? Sai da ta gama dakuwa Ammi ta miƙe ta ce "Ya isa haka Baffa"
Cak kamar cirar ƙaya ya daina dukan Ridayya da sauri ta miƙe ta faɗa jikin Ammi tana kuka jikinta sai ɓari yake ko'ina ciwi yake mata. Baffa ya haura sama Ammi ta saki murmushi kana ta ce "Jeki Ki kwanta Ridayya ki yi shiru haka nan" Da ƙyar ta nufi waje. Ammi ta yi murmushi ta ce "Allahamdulillah, sannu hankali ku yi ajalin ƴar ku da kan ku daga nan na dawo kan Zainura ai ba zan taɓa ƙaunar kishiya kuma na ƙaunaci ƴaƴanta ba"
Kuka sosai Mami take ta rufe kan ta a ɗaki a lokacin na farko da ta ji bakinta ya buɗe ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Rabbi inni lima anzalta min khairin faƙir" Ta ji tana son kaiwa Ubangiji kukan ta. Zainura ta dinga dukan ƙofar tana kiran sunan Mami ta ji kuma tausayin Ridayya sosai a karo na farko na dukan da Baffa ya yi mata.
Kuka sosai take a corridor har lokacin kiran shan ruwa ya yi ta ji dama kawai azumin ta yi ta huta anya ba zata gudu tabar gidan ba? Ai ta san inda ake kai marayu kuma ta san gidan karuwai ba dai sabon gari bane bata taɓa zuwa ba amma zata tambaya tana da raguwar kuɗin da Abbiey ya bata. Hijab ta saka da slippers ta goge hawayen fuskarta tas ta nufi hanyar fita da Usman sukai karo ya kalle ta ya shige abinsa tana ƙoƙarin buɗe gate ne Junaid ya shigo ya ce "Ke ina zaki?" Da ƙyar tana rarraba Idanu ta ce "Wajan Diyya zani"
"Ba ki ji ana kiran magariba ba? Za ki shige ko sai na yi ƙwllo dake" Ta juya ganin ta koma ya nufi cikin gida yana shigewa ta fito daga bayan corridor da gudu har tana yin tuttuɓe ta fice daga gidan kai tsaye titin Darmanawa ta nufa inda zata samu napep.....
Na'ima Sulaiman Sarauta
Nimcyluv
sulaimanshuaibunaima@gmail.com
08164069385
Whatsapp Only
*BRIGHT PENS...* _suna mara ba da masu buƙatar a tallata musu kasuwancinsu, masu siyar da turarruka, kayan sawa, magani komai da komai, cikin sauƙi za a tallata musu a cikin duka littafan guda uku🤙🏼 *CUTARWA, MUNAFUKIN MIJI, YI WA KAI*_
Tsari👯🏻♀️
Duk page ɗaya 200
Duka littafin kuma 600
Shafi biyar a littafi ɗaya 1000
A littafai uku kuma 3000
Domin ƙarfin bayani sai a yi wa wannan number magana 08164069385🤙🏼👯🏻♀️🫶🫶🏼
*✿ MUNAFUKIN MIJI 19 ✿*
Mikiya Writers Ass.....
BRIGHT PENS🤙🏼 free batch
Nimcyluv
Masu tambayar ina advert a book Yes ina yin tallah a book if you're Interesting just chat me...... 08164069385
Tunda ta fara tafiya bata waiwaya ba, cikin kasalar da take tunanin sauri take yi haka ta nufi titi ba tare data san inda take cillar ƙafafuwanta ba. Tana tafe tana share hawayen da yaƙi tsaya mata, ga wani masifar ciwo da jikinta yake yi mata, hannunta jinsa take tamkar ba a jikinta ba saboda karayar data samu lokacin da Baffa yake haɗa mata na jaki.
"Ɗitt, ɗitt, ɗitt"
Haka wata dakakkiyar mota ke danna mata horn amma ina, Ridayya babu abinda take ji da matukin motar zai mata adalci da ya bi ta kan ta, kilan farinciki da jindadinta yana Aljannar firdaus. Tana ƙoƙarin shiga tsakiyar titin ta ji an saka hannu tare da fincikota zuwa baya rai ɓace mutumin ke magana idanunsa rufe
"Ke wacce kalar yarinya ce? Kurma ce ke da ana horn bakya ji? Who do you think you are? Eh? Salon ku jawa mutum bala'i a wannan rayuwar da ta tsada kuɗin diyya ma da ɗuwawun shi yake zaune, banda azumi sittin" Kasa cewa komai ta yi kanta ƙasa jikinta duk rawa yake don fargaba ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, musamman da ya ga taƙi kallonsa. Inda take fuskanta ya koma Ridayya ta yi saurin sauya direction ita bata so ya kalli fuskarta don bata san da wacce kalar dabbar zai haɗata shi kuma.
"Kurma ce ke da ina magana za ki yi ignoring nawa? Wace ke?" Ya faɗa yana sake kai hannu zai fusgota ta yi saurin juyawa tana haɗe hannunta biyu idanunta har yanzu hawaye yake fiddawa muryarta na rawa ta ce "Ka yi haƙuri don Allah" Zaka ɗauka iyayi ta yi wajan maganar saboda a sanyaye muryar ke fita, ga kukan da ya zama abokinta kodayaushe. "Goodness!"
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Wa'innahu Sulaimanu wa'innahu Bismillahir.....," Da sauri ta buɗe dara-daran idanunta farare tas ta ƙura masa ido irin me kake nufi ɗin nan? Shi kam murya na rawa ya ce "Oh.... Shi.... Shikenan it's