Showing 48001 words to 51000 words out of 190738 words
Chapter 17 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt
ta ce "Ayya" kamar an cillo Baffa ya fito daga bedroom ɗinsa zai nufi ɗaya ɗakin idanunsa ya sauka a kan Mami data kafe shi da idanunta sai ta yi murmushi ta ce "Ikon Allah kaga kamar Aljani, yanzu Ammi ke cewa baka ciki, da alama kamar babban aiki ka gama?" Baffa yana inda-inda ya ce "E....eh...eh haka ne ina ciki, ina nufin ina bayan gado kamo ɓera.....
(Wata kishiyar Alheri ce wata kuma sharri mata a dinga jin tsoran Allah, bana son labarin nan ya ja ni da tsayi amma yanayin comment da supporting naku shi ne ƙarfin qwiwata. Bright pens na matuƙar godiya).
Domin gyara ko sharhi
sulaimanshuaibunaima@gmail.com
Ko WhatsApp
08164069385
*✿ MUNAFUKIN MIJI 17 ✿*
Mikiya Writers Ass.....
BRIGHT PENS🤙🏼 free batch
Mami ta tsare Baffa da kallo zuciyarta na yi mata soya, ta girgiza kai tare da miƙewa zata fice. Baffa ya tare ta faɗin "Yawwa na ce ki tattara dukkan furnitures ɗin dana siya miki, na bar wa Ammi su" Maganar ta doki zuciyar Mami ta juya a sanyaye ta ce "Ban gane na tattara kayan ɗakina na bar wa kishiyata su ba, explanation please?" Cike da faɗa Baffa ya ce
"Ba wani explanation Hausa ce dai na san kina ji ko Fatima?" Ta jinjina kai alamar E, kafin ta ce
"Bana tunanin akwai wani yare da ka iya wanda ban iya shi ba, ma'ana da hujjar tattara furnitures ɗina na bawa wata ne ban wani ba Alhji Mansur, cikakken bayani"
Kamar zai make ta haka ya tunzura ya ce"Maryam ɗin ce wata? Abokiyar zaman ki ce fa. Ok fine zan maimaita ki tattara komai na ki na bar wa Maryam su ina nufin Ammi, kawai yanzu nake ganin ita ta cancanta da kayan bake ba, kuskure na yi wajan siya miki su wallahi tallahi" Mami ta dinga kallon Baffa ta kasa cewa komai ta fice idanunta na cika da hawayen baƙin ciki.
Mami na komawa bedroom ɗinta ta fashe da matsanancin kuka mai cin rai, damuwar zuciyarta gabaɗaya ta addabe ta, duk yadda tasu ta yi sharing ɗinta ta wani ta gagara, gashi babbar damuwarta a duk sanda ta buɗe baki da nufin yin addu'a wajan faɗawa Ubangiji halin da take ciki, sai ta ji kamar an rufe mata baki ta kasa ambaton sunan Allah da nufin neman taimako. Ga wani irin masifaffen yanayi da cikin ya saka ta, na buƙatar mace zuwa ga mijinta babu abinda take so irin kasancewa da Alhji Mansur da shaƙar ƙamshin turaren shi. Ta share hawayenta komai yaƙi ƙare wa kamar cin ƙwan makauniyya.
Washegari da sassafe ta kwashe komai nata, ta ce a zo a kwashe Alhji Mansur Rano wato Baffa da kansa ya kira yara suka kwashe tas, ya ce ita kuma a mayar mata da furnitures ɗin Ammi ta ce ta gode. Kwana biyu da yin haka aka shigo da sabbin kaya ƴan Turkiyya masu masifar kyau lokacin suna zaune a parlour Umma ta shigo.
Ammi ta dinga kallon zubin kayan da tunanin ko Baffa ne ya siya masa sabo fil tana girgiza ƙafa cike da taƙama ta ce "Kayan ne?" Wani matashin saurayi ne ya ce "E, Hajiya sune ina za a saka" Ya ce yana danne dariyar data kama shi
"Ok ku haura da su upstairs" cewar Ammi. Mami ta dinga murmushi kafin ta juya ta ce "Hilal har kun ƙarasu?" Ya ce "E Mami, Mimi na gaishe ki ma" Mami ta miƙe tana murmushi har lokacin ta ce
"Zan kira ta kam, amma kayan sun yi ma sha Allah". "Mami a wajan fa kaf babu irin su kin san kuɗin da Grandfather ya tura? Ai arziƙi ya yi idan kana da kuɗi ka shige duk wani raini da wulaƙanci wlh Mami"
Murmushi kawai Mami ta yi Hilal ya ce "Talk Mami, ai gaskiya ce duk wata mugunta a wajan ɗan talaka aka santa musamman idan ka samu gidan miji ba fus ba ass sai dai a shimfiɗa dugwayen ƙafafuwan na cin banza da damfara, ga mugun abu kamar haihuwar Katsinawa"
"Wallahi Allah ya shirya ka Hilal Yaya A'isha bata gasa maka baki ba halan?" Ya ɗan kashe murya ya ce "Surprise....."
"What?" Ya mirgina kai ya ce "Na ba ki gari" Ta girgiza kai ta ce "I'm not good da cankar Surprise but i like surprises, just giss me" Hilal ya ce
"Aure zan yi" sai ya ɓata fuska ya ce "Mimi ta ce na yi ƙanƙanta don Allah mene abin ƙanƙanta a nan? Shi aure ai raya sunan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ne, kinga haihuwar fari sai na saka sunan Mamina" Mami ta ce "Kuma kana da gaskiya, amma auren RUƊIN ƘURUCIYA ne"
"Mami Ridayya fa?" A wannan lokacin ita kan ta Umma mahaifiyar Ustaz kallon Mami ta yi tana jira ta ji me za ta ce? Amma ta haɗe rai kamar bata taɓa dariya ba, ganin hakan yasa Hilal yin shiru.
Ammi kunya ta kama ta ganin yadda ya kwafsa, a ranta tana mamakin kuɗi irin na mahaifin Hajja Fatima wato Mami.
Hilal suka fara gyara kaya, Mami kuma ta haɗa musu lunch. Hira suke sosai da Umma tana mata murnar kayan data siya ta ce "Hajja Fatima yaushe aka zuba miki kaya har kika sauya wasu?" Caraf Ammi ta ce "Lallai fa, cewa ta yi bata so tunda kinga ai haihuwa za ta yi shi ne Baffa ya ce ta bar mini su, da gudu na karɓa ina godiya" Girgiza kai kawai Mami ta yi tana jinjina munafurcin Alhji Mansur Rano. A ranta tana mamakin yadda Ammi ta gane tana da ciki domin kullum cikin hijab take a gidan, kamar wacce take duba?
Ustaz Bilal sai raba Idanu yake a harabar makarantar su Ridayya, a hankali ya dubi a gogon hannunsa ganin ai tuni lokacin tashi ya yi wasu sun jima a gida ma. Ya miƙe daga jinginen da yake a hankali cikin nutsuwa da kamala, tare da zallar haiba da nagartar dake siffanta ainahin Ustazancin shi, ya nufi office ɗin Headmaster a ransa yana ayyana rashin dacewar haɗa mata da maza a makaranta. Da fara'a Headmaster ɗin ya tarbi Ustaz Bilal.
"Irin wannan zuwan bazata haka? Fatan lafiya" Ustaz ya yi shiru yana haɗa kalaman da zai faɗa a gajarce. "Kamar kullum karatun Ridayya sai addu'a, domin tafi gane naka karatun fiye da na mu, babbar damuwar ma kullum cikin bacci take a aji, bata wasa da yara she feels uncomfortable" Ya fiddo da duka littafan ta na makaranta wanda ya amsa wajan class teacher ɗin su, ya nuna wa Ustaz kana ya ce
"Za a Iya magance matsalar ta, ta hanyar cire mata tsoran dake addabar zuciyarta a saka son karatu da nuna mata itama ƴar ce kamar kowa mai gata da ƴan cin zama duk abinda take da buri a duniya, a nuna mata watarana ita uwa ce a nuna mata cewa Ubangiji ke yin halitta ba kuɗi ake bayar wa a kasuwa a siyi mutum ba, buwaya da ƙudirar Allah da girman zati da kaɗaitar shi ce, a nuna mata Ubangiji yana son duka bayinsa kuma babu mummuna a cikin halittun daya halitta, a saka mata ya ƙini da hope na cimma buri, a nuna mata cewa ko wanne mutum yana da nasa raunin cikakken mutum mai asalin kyau shi ne wanda ya yarda da Ubangiji ya kuma yar da ƙaddara. Dukda ba lallai ta gane yanzu ba, amma ya zama na wannan shi ne nata karatun kafin mu ga mai zai faru next"
"Yaa Rabb"
Ustaz ya furta a taushashe yana lumshe idanunsa, Headmaster baya iya tantance yanayin sauyin fuskar Ustaz Bilal don haka bai fahimci damuwa ko akasarin hakan ba ya ce "Karka damu fa, ina ji a jikina Ridayya zata zama wata a nan gidan duniya, yawanci yara irin wannan suna da baiwa ta musamman" Jinjina kai kawai Ustaz ya yi da ƙyar ya iya buɗe bakinsa ya ce "Ta na ina?" Da mamaki ya ce "Ai mun tashi, ka duba za ka ga babu students a compound" hankalinsu ya tashi a ka shiga neman Ridayya babu ita babu mai kama da ita, har class teacher ɗin su sai da aka kira.
A ɓangaren Ridayya sai rarraba manyan fararen idanunta take yi tana jin me suke faɗa.
"To ko dai Aljana ce ke ko kuma babanki kika gado a muni ko?" Ridayya ta kalli Nimra wacce ta kasance class mate ɗinta a makarantar masu kuɗin dake nan unguwar Darmanawa.
Ɗaya daga cikin students ta fashe da dariya ta ce
"Help me as Nimra, oh oh muni ko wahala?" Nimra ta yi fari da idanu tana riƙe maƙalallen ƙugu idanunta kamar ya fado cike da azaba ta ce
"Yapp, ga idanu kamar na mujiya gata daƙiƙiya sai tsinanen bacci kamar kasa, kullum sai ta yi mana fitsari a class"
"Ohh Goodness! Fitsari?"
Jidda ta faɗa a ruɗe. "Ai yawan sai na ci uwar ta wallahi, baƙa mummuna mai baƙin zunubi ji Idanu kila mayya ce" A sanyaye Ridayya ta ce "Ai dai ɗakin Allah ma baƙi ne"
Da sauri Nimra ta doke bakin Ridayya ta ce"Uban me kika sani? Ke ina kika taɓa ganin ɗakin Allah ɗin? Wannan dama gidan zoo aka kai ma da ita da sallah mu je mu ga daƙiƙiya" Idanun Ridayya ya yi rau rau sai ya fidda wani shiny.
"Ai dabbobi ake sawa a zoo road" Jidda tana dariya sosai ta ce
"To ke ɗin me ce? Wallahi dabba ce ki je ki tambayi Babanki ki ce a dabbobi da wacce kike kama zai faɗa miki" Suka haɗu sukai mata dukan tsiya da bulala wai ba za su saka hannu ba kar su shafi baƙin zunubi. Haka kurum suka tsane ta. Ridayya na son wasa da zarar ta nufe su idan an fita break sai kowa ya daka mata tsawa ya ce ta tafi, daga nan sai ta fi wajan bishiyoyin makarantar ta dinga wasa Ita ɗaya, a lokacin kuma sai ta dinga karatu ita ɗaya ita bata iya gani ta karanta muddin zaka takura mata ta yi karatu to ba zata iyi ba ko a exam ne. Idan ita kaɗai ce kuma sai ta dinga yi tiryen-tiryen a nutse take komai nata.
"Shalele" Da sauri ta ɗaga kai tana kallonsa dukda hawayen dake idanunta bai hana Ridayya sauke ajjiyar zuciya ba, ta nufi wajansa da gudu kafin ta ƙarasa ya ware hannayensa tana zuwa ya ɗauketa ya cira ta sama yana furta "Shalelen Abbiye, You scread me" Ta yi shiru. Jikinta ya ji zafi sosai yana ɗaga rigarta ya ga shatin bulala duka jikinta, ya kalleta tambayar duniya taƙi faɗa masa waɗanda suka dake ta.
Kamar kullum yau ma Ustaz da kansa ya yi wa Ridayya wanka bayan ya naɗe ta da towel ya shirya ta cif cikin wasu sabbin kaya ƴan kanti daya siya mata, ya ɗaure tulin sumar da ribbon yana hakki, yana gamawa ya yi baya tare da kwanciya ta haye ruwan cikinsa tana dariya ta ce "Abbiye gajiya" Idanunsa rufe domin yanzu Ridayya ta zama ƴar lukuta saboda kulawar da yake bata. Ya yi murmushi ta ƙura masa ido, ganin kumatunsa ya loɓa _Beauty points_ ta danna yatsa a wajan ya ce "Shhhh, Shalale mu je ki yi bacci ko?" Ta maƙale kafaɗa ya rufe ido tana zaune bacci ya ɗauke shi da sauri ta fice ta nufi part ɗin iyayenta.
Lokacin data shiga ba kowa a parlour sai Mami wacce cikinta ya girma kawo yanzu kuma kowa ya san da zamansa hatta shi mai gayya da aiki Alhji Mansur Rano. Jin motsi ya saka Mami juyawa idanunta ya sauka akan Ridayya itama Mamin ta ke kallo. "Lafiya ke kuma?" Ridayya ta girgiza kai sai kuma ta juya zata fita aka ce "Daughter come back" Ammi ta faɗa cike da fara'a da sauri Ridayya ta juya tana murmushi don yanzu ta daina jin tsoran Ammi tunda ta fara nuna mata kulawa da soyayya.
"Yawwa ƴar baba mai iyaye maza biyu ta gaban goshin Abbiey ɗinta Muhammad-Bilal Ustaz" Ridayya ta yi murmushi ta ce "Zauna na baki abin daɗi daughter na"
Mami dai ko motsi ba ta yi ba, Kwata-kwata bata damu da Ridayya ɗin ba, bata taɓa ɗaukar ta ba, tunda take a duniya bata taɓa hira da ita ba ki na seconds ba, sai magana sama-sama. Farfesun nama ta zubo mata hakan ya yi wa Ridayya daɗi tana son nama kuma gashi yanzu Ustaz ya saba mata kullum sai ya siya mata balango ko tsire ko kaza.
Ta cinye tas kana Ammi ta ce "To zo mu je na baki ɗaya abin daɗin"
Hannunta ta kama suka nufi cikin bedroom ɗinta, a zuciyarta tana tsinewa Ridayya tana kuma jin daɗin yadda Mami ke nuna rashin kulawa a kan Ridayya ɗin. Maganin mayen da take bata a kullum, yanzu ma shi ta ɗauka. "Yawwa ungu wannan shanye tas kin ji ko?" Ridayya ta jinjina kai kana ta amsa ta shanye tas kusan cikin kwalba ɗin, kama hannunta ta yi ta ce "Kinga yadda nake son ki ko? Ko me kika ce ina miki haka ne? To Mami da kike gani ba ƙaunar ki take ba, cillar dake ta yi ta ce bata son ki ni kuma na ɗauke ki, ki daina ko gaishe ta kina ji?" Ridayya ta jinjina kai ta ce "Ai shi ne take mini haka...,"
Ta yi maganar tana yin harara da taɓe baki ta ce "Yaya sunan wannan abin Ammi?"Ammi ta ce "Yana nufin na tsane ki, kuma sai na kashe ki"
"Ta kashe ni na bar ganin Abbiey?" Ammi ta ɓata fuska ta ce "Abbiey kawai bani?" Ta yi shiru kan ta a ƙasa can ta ce "Ni ma na tsane ta, zan ɗauki wuƙa na caka mata"
BATSARI /KATSINA.
Yanayin duhun samaniyya da yadda daddaɗar iska ke kaɗawa, gari ya yi shiru sai kukan tsuntsaye da tashin ledoji zuwa sama zai tabbatar maka a tsakiyar watan Agusta ake. Yau ruwa gobe ruwa, hakan ya yi dab da shigowar watan azumin Ramadan. Yau ma kamar kullum garin ya yi baƙiƙƙirin gajimare sai gudu yake, ana wata kalar walƙiyya da iska mai ƙarfi dake tashi tana yaye gutsirarrun rufin saman wani gidan mai ƙarar kwana. Hankulan jama'ar ƙauyen Nahuta dake yankin ƙaramar hukumar Batsari, ya fara tashi ganin hadarin yau na musamman ne, wanda suke gonaki suka fara shirin dawowa gida, wanda suka fita bara suka fara tattaro tarkacansu suna ɗaukar hanyar gida, matan da suka fita garuwa suma duk suka yo hanyar gida, aka dinga kama awakai da shanu ana ɗaure su.
Kamar yadda Hausawa ke yin lakabi da sunan “Katsinawan Dikko, kunya gare ku ba dai tsoro ba” Gefe guda kuma wasu su ce “Ta Dikko ɗakin kara" Hakan ɗin ce ta kasance a cikin wani fafakeken gida, wanda zubi da tsarin shi bashi da mara da gidan gandu. Gida ne mai rangwamen ƙarfi, ga tarin yara manya da ƙanana kasancewar mata huɗu ne a gidan, idan ka ɗauke surukansu da duk suke tare waje guda. A daidai sanda ruwan saman ya fara sauka a sannan ne ya fito daga ɗan ƙaramin ɗakin da take ciki mai kama da Bukkar Fulani mita take kamar ta ari baki
"Ni wannan masifa da bala'in na cikin gidan nan ya ishe ni, masifa kamar ana tuttula mata man fetir, hoɗijam!" Ta faɗa tana yin turken awakai tare da kama gudu wacce ta kifo mata da ƙazon data shanya,sai ta yi wa akuyar dokan kawo wuƙa kana ta ɗaure. Ta kalli sama ganin yadda cita ke ta gudu ta ce
"Ko a ina Gaaji ta samu gindin zama?" Kafin ta shige ɗaki yariyar ta shigo da gudu tana haki saboda ruwan daya fara dukan ta. Kallon tsaf ta yi mata kafin ta ce "Hala kin kwana turo? Hakin ga na lafiya?" Gaaji ta ce "Iya don ki ji Gidaɗo ya zo, ya dawo daga birni" A guje sauran yaran suka fito daga ɗaki suna murna yau za su ci abu mai daɗi da kyau. Iya ta ce "Ke ƙarya, Gidaɗo nawa? Yaushe ya zo babu labari"
"Yana bisa hanya" Rufe bakin Gaaji kenan ya faɗo gidan yana cin magani sai taɓe baki yake yana kakkabe jikinsa. Jikin Gaaji na rawa ta ce "Ina taimaka maka kawo jakar tafiyar" Tana zuwa ya saka hannu ya sakar mata ranƙwashi ya ce "Kina ƙara taɓa mini kaya sai na ci ubanki, ƴar ƙauyen banza" Da sauri ta matsa tana sosa kan ta. Iya ta ce "Sannu lale me ka zo mana da shi? Kawo jakar naga?" Ya haɗe fuska tamau ya ce "Ke Iya nan kamar kin bani ajjiya, wai karatu na je yi ne ko neman kuɗi?" Ta riƙe baki
"Kake faɗa mini haka Gidaɗo?" Ya ce "Gaskiya ce ai, ba ki ce Gidaɗo ya karatu ba sai me na zo da shi, ko tunanin na mutu a can bakwa yi kun kai ni gari kun zube babu mai zuwa, sai ni nima daga sallah sai sallah ko idan na yi wata ƙaryar"
"To zage ni ka huta Gidaɗo, ni dai bani burodi" Ya ƙara yin kicin-kicin da rai ya ce "Point of correction, biredi ake cewa Iya"
"Bari na je na faɗawa Hanne ka zo" Iya ta ce "Maza ki faɗa mata, a zo a yi maganar aurenku" Gidaɗo ya kalli Gaaji ya ce "Wallahi kika fita kika gaya mata sai na yi miki shegen duka ƴar banza da baki kamar na aku" Haka daga shigowarsa suka fara yi da baki daman babu kowa namiji a gidan sai Jafar shekarar shi Bakwai shirin kai shi Maiduguri ake wajan sauran yayyensu da suke can.
"Ka je gona, lokacin girbi ya kusa za mu samu albakar noma na hatsi sosai" Gidaɗo ya miƙe ya ce "Ku za ku iya cin hantsi ni na yi hannun riga da shi, noma kuma a yanzu gaskiya Iya sai dai ku yi haƙuri na fi ƙarfinta" Kafin Iya ta yi magana an tsuge da ruwan saman, da gudu Gaaji ta fice daga cikin gidan ta nufi gidan su Hanne ta shaida mata Gidaɗo ya dawo.
Gidaɗo na zaune a ƙofar gidansu ya ci wani uban yadi yellow ful da shi, da ƙaton takalmi ga wani irin glasses daya saka a fuskarsa ya haɗe rai, kasancewar fari ne jajur da shi irin