Showing 138001 words to 141000 words out of 190738 words

Chapter 47 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17312

hannun Ridayya ta ce "So na gaskiya yana tare da mutanen ƙwarai ne kawai. Shi yasa duk yadda za ayi just be with the right person in sha Allah za a dace, ba wai following soyayya ko sharholiya ba"


"Kina ganin Sadauki zai haƙura?"


"Yeah but not really. Saboda if one of them got another man or lady and the other is such a jealousy he can't absorb it. Dole zuciya ta tsaya a iya ɗaya na san Ustaz yana da kishi kuma soyayya ba zata rufe masa ido ya kasa hukunta ki ba.
Mafi girman dace ko kuskure shine na zaɓar aboki/abokiyar rayuwa. Shi yasa a irin wannan lokacin ga samari da ƴan mata yake da matuƙar haɗari musanman a zamanin nan, ki tsayar da zuciyarki ga Ustaz"


Idanunta ta lumshe ƙofofin zuciyarta ya buɗe maganganun Anuty Kaltum suka shige ta sosai ta ji Abbiey ɗinta take son gani. Wayarta ce ta fara ringing ganin sabuwar number ya sa ta ɗaga ta cikin wayar aka rangaɗa buɗa nan da nan hankalin Ridayya ta sha can kuma ta ji saukar muryar Mardiyya ta ce


"Yadda kika aure mini miji da sunan aure da haɗi na iyaye bayan mijin ba son ki yake ba, to yau an sake ki uwar da ta yi nishin haihuwarsa ta ji zafin naƙudar shi ta saka ya miki saki har uku. Bashi da mata sai ni don haka stay away from my husband idan ba haka ba zan miki abinda ba ki yi tunani ba. Banza baƙa mummuna mai auren mijin wata kuma bazawara a karo na biyu"


Ƙitt ta kashe wayar Anuty Kaltum ta ji komai Ridayya ta kasa kuka wani abu ya tsaya mata a wuya zuwa ƙirji she needs a shoulder to cry on wanda zai fahimci kukanta. Miƙewa kawai Anuty Kaltum ta yi ita kanta jikinta ya yi sanyi. Ridayya ta zama so silent ashe sakinta ya yi shi ya sa baya nemanta.


Washegari suna zaune a parlourn an gama yi wa Ridayya kitso wasu manya kamar doka jelar ta sauka har hannu aka saka mata stone yatsunta sun sha zanen lalle da ƙafa. Kamar daga sama suka ji sallamar mutum kasa ɗago kanta ta yi jikinta ya ɗauki rawa ta gane muryar Abbiey ce. Wata riga ce a jikinta iya qwiwa gashi a ranar ta sha gyara ta kasa motsi tana ji ana ga gaida shi bata sani ba ko ya amsa tunda bata jin muryarsa.


"Ashe kana tafe?"


Ya ɗan kalli Anuty Kaltum ta gefen ido sai ya jinjina kai kawai kafin wani lokaci an jere masa abinci kala-kala Anuty Kaltum ta ce "To bari idan ka gama ma gaisa da kyau ko?"


"No, zan ɗan je unguwa da ita ne yanzu ta shirya ina waje" Ya miƙe ya nufi waje har zai fita sai ya tsaya ya ce


"Ta ɗakko wayarta,abu mai muhimmanci banda kaya"


Ajjiyar zuciya Ridayya ta sauke shi kansa ya ji bai dai kula ta bane bashi da lokacin shirmanta. Da ƙyar ta shirya cikin wata lafaya mai kyau da taushi zanen kitson ya fito Yamara ta yi mata wani turare ta mata wasu magani ta sha kana ta yi waje tana tafe tana harɗewa da lafaya ɗin.


Tsaye ta same shi jingine da mota shi da Khamis ɗan gidan Yamara tana ƙara sawa Ustaz ya yi shiru sai kuma ya buɗe manya mata ganin ta tsaya ya saka ya zuba mata narkakkun idanunsa da sauri ta shiga shi ma ya shiga, Khamis ya ja su zuwa airport. Kwanan BM USTAZ biyu a garin bai zo sai da komai na tafiyarsu ya zama ready daman yana da komai nata suna zuwa airport minti ashirin sukai suka shiga jirgi shi ya ɗaura mata igiya duk a tsorace take shi kuma ko tari bai mata ba, sanda jirgi zai tashi ya kama hannayenta biyu ya damƙe cikin nasa dukda haka bata nutsu ba sai ya ɗora kanta a ƙirjinsa ya ɗora nasa kan saman kafaɗarta ya ɗan riƙe ta da kyau a jikinsa jirgi na sama ta ƙanƙame shi tana rufe fuskarta a ƙirjinsa Ustaz rufe idanunsa ya yi a ƙasan zuciyarsa yake furta "Ya subuhanallahi banda kisa Ustaz"


Bata san wacce ƙasa suka ta fi ba, ta farka dai ta ganta still kwance a jikinsa ya rungumeta very tight hannunsa riƙe da nata yana kallon red henna ɗin ta kasa kallonsa ganin ta motsa ya saka Ustaz ɗago ta ya kalli fuskarta idanunta rufe a hankali ƙamshin bakinsa na sauka a hancinta ya ce.
"Kin danne mini ƙirji" Ta ɗan turo baki a ransa yana Maman rufe idanun a hankali ya ce "Baccin za ki koma?" Ta girgiza kai a nutse ya ce


"Za ki ci abinci Baby?"


Jin sunan Baby ya saka Ridayya saurin buɗe idanu kunya ta sake rufe ta, sunan babyn ya yi mata wani iri a ranta tana mamaki Abbiey da zai ce mata baby sai taga babu Ustaancin a fuskarsa yau.


Kafin ta yi magana ta ji saukar hannunsa a flat tummy ɗinta daya shafe a daidai kunnenta ya ɗora bakinsa ya ce


"U need a food Baby"


Ya ce shortly yana kiss ƙasan wajan very lightly da lips ɗinsa da suke softly. Ridayya ji ta yi komai na shirin ƙwace mata mene ya damu Abbiey yau?.
Kayan fruits ya jawo ta fara ƙoƙarin zame wa daga jikinsa ya hana ta ya ɗakko kankana ya kai bakinta ta girgiza baki ta buɗe za ta yi magana ya ɗora yatsarsa ya ce


"Shhhh, buɗe bakin" a hankali ya fara bata fruits cikin nutsuwa jirginsu na ta yawo saman gajimare.


Sosai hankalin Mami ya tashi jin batun sakin Ridayya nan da nan Baffa ya haɗa meeting ɗin gaggawa kowa ya hallara bayan addu'a Alhji Mansur ya cec


"Yaya yaushe aka saki ƴar wajan Babban mutum bani da labari?"


"Alhaji Mansur ai baka gari ne ina son a samu daidaito....,"


"Ba wani daidaito Allah ya ƙara rusa wannan auren na ƙaddara"


Baba ƙarami ya kalli Umma bai ce komai ba. Baffa ya ce "Ikon Allah to saki nawa ne?" Baba ƙarami ya zaro takarda ya miƙawa Baffa.


A hankali Baffa ya fara ware takardar abinda idanunsa ya sauka a kai ya bashi mamaki ya sake dubawa yaga an saka


_“Ba zan iya rabuwa da jaririyata ba, yin hakan kamar mutuwa ce bayan ina numfashi, ba kuma zan saki Mardiyya ba domin babu saki a rayuwata zan je ba zan dawo ba sai Ridayya nada turtsetsen cikin da na yi mata in sha Allah. I love my wife ina son jaririyata Umma ki yi haƙuri bye daga Mijin Ridayya Muhammad-Bilal Tahir Rano na Ridayya”_




More comment more update
A yi haƙuri da errors
Ramadan mubarak
*MUNAFUKIN MIJI 38*
Mikiya Writers Ass...




Bright pens free batch
Nimcyluv




Follow my tiktok Account
https://www.tiktok.com/@nimcyluv?_t=8lxgsAjuU0z&_r=1


Allahamdulillah Channel ɗina ya je 2k followers keep following my people❤‍🔥🥰






“Yau nake ganin ɓatan nono a ƙirjin budurwa? Wai da gaske babban mutum ya saki Ridayya? Ku karanta mana takardar a fili mana" caraf Ammi ta karɓe zancen da faɗin "Wallahi Hajiya kema kya faɗa, su kawo takardar na karanta a fili kowa ya ji, ai saki ba kan Ridayya farau ba, ba kuma za a ƙare a kanta ba. Allah ya ƙaddara ita ɗin matar Burhan ce"


"Burhan kuma?"


Junaid ya furta da mamaki kwance a fuskarsa ita nata allon sai ya haska mata Burhan matsayin mijin Ridayya? Ai kowa da ƙaddara sam ba ta yi wa Ridha adalci ba, duk lalacewarta ta fi ƙarfin mashayi.


Ammi ta zarewa Junaid Idanu ta ce "To uwar mece da Burhan ɗin har kake maimaita sunansa, ai daman ya jima yana son ta, kawai babu yadda zai yi ne ni ce nake tanƙwara shi"


Kowa kallon Ammi yake banda Baffa da Mami, wacce ta yi kamar ruwa ya cinye ta wani irin zafi zuciyarta ke yi mata yaushe ne Ridayya za ta yi farinciki? Yaushe ne damuwarta za ta zo ƙarshe? Mene laifinta? Wani abu ya tukare maƙoshinta nan da nan abinda ke kwance a mararta ya motsa tare da tabbatar da lafiyarsa ras.


Baffa ya sauke numfashi bayan kammala karanta abin da takardar ta ƙunsa ya yi shiru domin bashi da wani abin cewa tsananin kunyar abinda ke zane a takardar shi ya addabi ransa ya kuma jin daɗin kalaman Ustaz har ransa, tantama da mamaki suka mamaye zuciyarsa at the same time kuna ya hasko irin zuri'ar da Ridayya da Ustaz za su samawa Rano families. Ya ɗaga kansa yana kallon Hajiya ya ce "To daman ba wani abu bane face.....,'


Abba ya yi saurin tarar numfashin Baffa yana me riƙe hannunsa ya ce


"Saki ne kamar yadda kowa ya ji sai fatan Allah ya daidai tsakani. Aure daman rai gare shi na wasu ya ɗore na wasu akasin hakan ƙaddara kuma yaɗo take idan an san farko babu wanda ya san ƙarshen ta, wata ƙarshen ya zo me kyau wata ba yadda muka yi tsammani ba, idan akwai rabo tsakanin Muhammmmd da Ridayya babu shakka wanda ke da tawaye da auren rabo zai yi ajalinsa kowa ya sassauta buri" saurin yin shiru ya yi jin Umma ta rangaɗa uwar buɗa da faɗin.


"Ayy yiri-yiriri. Na gode Allah na kuma ji daɗin wannan rana don murna kamar na zuba ruwa a ƙasa na sha haka nake ji, ina roƙan Allah ya ɗorawa muguwar ƴarku son ɗana wanda zai kwantar da ita har gadon asibiti ta ji irin abinda ya ji, kuma tsakaninta da shi sai kallo daga nesa Mardiyya ita ce matarsa ta nan gidan duniya da kuma lahira, na tsaneta bana ko ƙaunar buɗe idanu na ganta ina fata idan rabon ya tashi kisa ya kasheta ita" ta sake sakin dariya.


"Ahhayeee cas raina fari tas idan ma mata biyu yake so ni zan nema masa wata in sha Allah ko a cikin yaran ƴan'uwana ne na Zamfara, kuma Muhammmmd dole ya dawo gida ya kuma bi umarnin uwarsa"


"To bari mu gani umarni uwa zai bi ko na mata? Ko kuma soyayya" Abba ya faɗa a fili ta ce "Me ka ce?"


"Cewa na yi ki saurin nema masa matar auren nima zan fi son hakan, kuma ki dinga sara kina duban gatari ki buɗe kunne da idanun zuciyarki kuma ki tuna cewa ɗanki nakasashe ne banga lafiyayyiyar yarinyar da zata zauna da shi baya amfana mata da komai ba, musamman yaran zamani da idanunsu yake a buɗe. Babban dalili babu iyayen da za su amince su bawa Muhammmmd auren ƴarsu bayan sun san ba zai taɓa haihuwa ba. Itama Mardiyya zan nemi makusanta na labarta musu komai"


Yana faɗin hakan ya miƙe tsaye tare da barin parlourn ransa babu daɗi, ana zaton wuta a maƙera sai gata a masaƙa bai yi zaton Hajiya Hadiza zata kawo masa tsaiko ba. Mami ma miƙewa ta yi ta nufi part ɗinta zuciyarta tuni ta raunata ainun.


Hajiya ta ce "Allah shi daidaita al'amarin nan duk auren da ake tsiya haka fa ya fi tsayin rai, mutane suyi ta ƙoƙarin kashe aure kamar sune suka halacce shi, Ubangiji ya kawo musu da sauƙi"


"Amin" Anty Zuhura ta ce Ammi ta watsa mata muguwar harara tana ƙwafa.


Baffa ya miƙe Ammi ta yi saurin cewa "Baffa idan ba damuwa ina son magana da kai" ya dube ta can ya ce "Ina ji"


"Kamarya kana ji nemi waje ka zauna" da wani irin expression Baffa ya juya gabaɗaya yana kallon Ammi a kasashe ya ce "Maryama kin haife ni ne? Yaushe muka saba haka dake? Ko Junaid kya faɗawa haka balle ni ubansa kuma mijinki?" Ta yi shiru domin ta kwafsa wai tana gwada aikin sabon malamin data samu ne sai dai taga har yanzu da saura. Rai ɓace ya juya ya nufi ɓangaren Mami dukda cewa girkin Ammi ne.


"Uhm ka yi lokacinki na, ka mure shi ina nan zuwa daga kai har Fatima za ku gane shayi ruwa ne" Junaid ya kalli Ammi ya ce "Ammi wai meke faruwa ne?" A tsawa ce ta ce "Ubanka da uwarka sune suke faruwa, ka fita daga sabgata Junaid kuma wallahi ko ka fito da matar aure ko na zaɓa maka duk wacce ta yi mini"


Ya miƙe zai fice ta ce "Ina magana kana mini banza? Do i look like an idiot to you?"


Ya girgiza kai ya ce
"Me zan ce Ammi? Kin san matsalata genotype ɗina AS ne duk wacce na gani ina so da zarar mun je gwaji sai itama aga AS ne dole aure ba zai yiwu ba" tausayin Junaid ya kama anty Zuhura amma Ammi ta saka ƙafa ta shure ta ce "Duk fa ƙarya ce kawai irin ta likitoci ba wani ciwon sikila da sanda ake auren uwar wa ya samu mutane? Sai yanzu to ni zan nema maka mata kuma dole ka aura tunda kai baka ganin me nake faɗa maka, bari su Aliyu, Abubakar, da Khaliperh su shigo suma"


Junaid dai bai ce komai yana fice daga gidan bakiɗaya.


Baffa ya samu Mami tsaye a baƙin ƙofa ta yi shiru ya shiga yana murmushi ya ce "Waya ɓata mini ran Sahiba? Shi ma yanzu nasa ya ɓaci" Ta juya gabaɗaya hakan ya bawa hawayen idanunta damar sakkowa zuwa saman kumatunta. Muryarta na rawa ta ce "Baffa da gaske ne Babban mutum ya saki Ridayya?"


Ya yi shiru yana kallonta sai kuma ya saki dariya ta kwaɓe fuska tana dire ƙafa ta ce "Ba maganar wasa bace hankalina duk ya tashi, tsoran sanin gaskiyar abin ya addabi zuciyata"


"Yaushe na yi miki ciki Batool? Ciki nake gani a jikinki fa?" Gabaɗaya hankalinsa yana kan cikin ta yi saurin juyawa ya kamota ya saka hannu a cikin muryarsa na fidda sauti na farinciki ya ce


"This is serious, please when?"


"I have no idea, ni ba maganar ciki nake yi ba"


"Ni kuma ita nake so mu yi Zarana ɗa za ki haifa mini wannan karan. Allahamdulillah" gabaɗaya ya kamota jikinsa ta yi shiru can ta ce "ina son Ridayya ta rayu da Ustaz Baffa ina son haka shi kaɗai na aminta da shi, bana son ta sake shan wahala a rayuwarta"


"In sha Allah,ki kwantar da hankali ba wani saki fa? Bai sake ta ba kawai muna pretending ne zuwa sanda ƙaddara zata sauya komai, ya isa kin ji?" Ta jinjina kai... Yana shafa cikin ya ce "Mu je ki ji akwai batu fa ƴar nan" ya ce yana raɗa mata a kunne.


*****
Numfashi ya sauke a karo na biyu yana sake ware idanunsa da nutsa su cikin photon da kyau "why? You have been far away from me and you have tortured my heart a lot?" Ya cije bakinsa tare datse bottom lip yana jiwa kansa ciwo, zafin da zuciyarsa ke masa tamkar ciwon daya ruski mace mai ciki.


“Ban taɓa ganin inda so ya zama aibu ba, I love you, i just loves you kina yi kamar ba ki san komai ba, kina wasa da feelings ɗina, I don't care what will happen, I don't care what you will say, I only know myself and my heart, dole na raba ki da ko wanne namiji na kasance dake, ba zan yafe miki ba muddin kika saka bakin almakashi wajan datse alƙawarin zuciyoyinmu, dole; tabbas ne hakan"


"Sadauki what is this? Mene haka Sadauki kana cikin nutsuwarka kowa?"


Ya juya da jajayen idanunsa ya kalli Mother laɓɓansa sai rawa suke ya kasa furta komai har ƙanƙance Idanu yake, ganin yanayinsa ya saka Mother juyawa zuwa wajan fridge ta ɗauki ruwan gora mai sanyi tare da tsiyayawa a farin cup ta ƙarasa kusa da Sadauki tana cewa


"Drink, sha Sadauki"


Bai yi magana ba sai tsare Mother da kallo da ya yi, a hankali ta kama hannunsa tare da saka masa glasses cup ɗin hannu, ya amsa still he looks at into her eyes ya matse hannunsa cup ɗin ya yi ƙara tare da fashewa a hannunsa jini ya fara zuba hankali tashe Mother ta ce "A kan mace kake neman kashe kan ka Hamza? Baka tunanin ni da kuma Prof?"


Murmushi kawai ya yi mata idanunsa na ƙara rinewa a hankali kuma underneath his breath ya maimaita sunan “Prof.....”
Irin bai gane ɗin nan ba can ta ce "Baka tunanin halin da za mu shiga ni da mahaifinka? Kai kaɗai muke da shi fa" ya yi baya yana tura hannunsa cikin suma har yanzu jikinsa rawa yake musamman tsokar ƙirjinsa ta cikin zuciyarsa


"Oh your husband?"


"What?" Sai kawai ya girgiza kai ya juya baya yana ɗaga kansa sama tare da ƙurawa waje guda kallo. Tsoro ya kama Mother kar wani abu ya taɓa tunanin Sadauki ta sakko daga upstairs da sauri tare da ɗaukan wayarta.


3 miss calls ta yi Prof amma ba a ɗagawa ana huɗu ta samu aka yi picking muryar da ta ji ya saka ta yin baya tare da neman waje ta zauna bisa tilas, wani irin bugawa ƙirjinta ke yi ta kasa furta komai sai da aka ce.


"Hello who is on the line?"


Hajiya Azizat ta haɗiye yawo mai yauƙi daya tsaya mata can ciki ta ce "Matar me wayar ce, You can give the phone owner his phone?"


"Baya kusa yana kan......,"


"Hiiii stop this nonsense, mijina nake nema bake ba, and lemme warn you first; idan na sake kira kika ɗaga mini waya I'll show you the other side of me, har ina ki bani mijina kina tsayawa yi mini rubbish? Who are you? How dare you eh?"


Faɗa sosai Hajiya Azizat ke yi daman mai haƙuri bai iya nuna ɓacin rai ba, ƙitt ta ji an kashe wayar. Tunani ya shiga kanta who is she? Mene haɗin ta da Professor? Har take ɗaukan wayarsa kai tsaye wacce ko ita bata da damar hakan?.


Ta miƙe tsaye ta fara kai kawo can wayarta ya fara ringing line ɗinsa ta gani ta ɗauki wayar tun kafin ta yi magana ta ji ya sauke ajjiyar zuciya mai nauyin gaske ya ce.


"Sorry wife wallahi wata....," Hajiya Azizat ta katse shi ta cewa "It's okay. I trust you ban taɓa saka zargi a aurenmu ba tsayin shekaru"


"But wife at least ki tsaya na miki explanation who is she to me?"


"Sweetheart bana buƙata ko wace na san bata da wani important a wajanka, kuma duk lalacewar abu matarka ai matarka ce" Ya sauke numfashi ta wayar ya ce "Haka ne that's why i always Madam, ya akai?"


"Ni da ɗanka Sadauki muna buƙatarka don Allah don Annabi don darajar iyayenka ka bamu lokacinka professor, muna da damuwa muna da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login