Showing 87001 words to 90000 words out of 190738 words
Chapter 30 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt
daidaito ɗin dake tsakanin Baffa da Fatima, kuma muddin ina raye wallahi tallahi ko Ridayya na duniya ba zata taɓa zama wata a duniya ba kuma dole ne mu mallaki wannan kadarorin da aka bata gabaɗaya haihuwarsa yarinyar nan masifa ta zame mini"
Zuhura ta cika ta yi fam ta ce "wannan mayyar mijin kike tunanin zata iya rabuwa da shi? Kila ta tattara ta mallaka masa dukiyar" "da kowa na yi ɗaiɗai da rayuwarta wallahi Ridayya ba zata taɓa zama wata a duniya ba, ai daman sai dai shi Zameer ɗin duk yadda naso kashe auren Burhan ya aureta abu ya gagara ni addu'a nake ma plan ɗin Alhji ya yi daidai dukda yaƙi faɗa mini komai ta dawo ta auri Burhan ai daman shi ne ya zama dole a yadda take uban wanne namijin ne zai aure ta ko shela akai matsayin kyauta babu mai amsar ta yin"
Miƙewa Zuhura ta yi ta ja hannun yaranta a ƙalla ta yi ya ji sama da biyar gashi igiyar auren nata saura ɗaya tal da take lilo.
"Kee Zuhura" Baffa ya kira sunanta ta tsaya ta ce "Na'am Baffa ina yini?"
Bai amsa ba ya ce "Me ya kawo ki gidan nan? Asiri kike son tuna mana? Bana gaya miki bana son a san wani daga cikin ahlinmu na raye ba? Shi ne kike ta mini zurga zurga?"
"Baffa ka yi haƙuri wallahi daman Nura.......," Caraf Ammi ta ce
"Nuran ne baya gari ya ce ta zo gida kafin ya dawo"
Baffa ya juya ko Ammi bai kalla ba ya ce "To ki kiyaye zan yi magana ta Nuran idan ba zai iya haƙuri har mu kammala ba kawai ya barki a gidan nan har zuwa sanda komai zai zo daidai" Yana faɗa ya yi sashin Mami.
Ammi ta cije bakinta ta ce "Kin gani ko Zuhura ko inuwata Baffa baya son gani? Na zama mujiya to ni me na yi masa duk yadda na riƙe yarinyar nan tsakani da Allah?"
"Ammi kin fiya mita shi Baffa kin taɓa ji ya miki maganar Ridayya ne? Duk kin damu kan ki"
Miƙewa ta yi ta nufi ɗaki number Biba ta kira tana ɗagawa ta ce "Biba ko ba za ki dawo ƙasar nan ba ki turo mini kuɗina na wajanki ko miliyan biyar ne" daga cikin wayar Biba ta ce
"Maryam babu kuɗin nan fa wallahi an sace" Wata uwar ashar Ammi ta ja ta ce "Kan uba ni za ki cewa ba kuɗi last kuɗin dana tura miki a ƙalla ya yi miliyan huɗu da rabi kuɗina a wajanki ban san adadi ba shi ne ki ce mini an sace na bi sata da gudu ba wando....,"
Ƙittt! Biba ta kashe wayar nan take kuma ta saka number Ammi a Black list.
Satin Ridayya biyu cikin asibitin ta warke sosai aka sallame ta Tajj ya dawo da ita gidansu saboda ita yaƙi komawa wajan aiki dukda yana son zuwa wajan Ustaz can leges ɗin rabonsa da shi tunda aka ɗauki jininsa ko wayarsa ya kira a kashe yake jinta. Kulawa sosai yake bawa Ridayya Mahmah da kanta ta saka aka kawowa Ridayya sabbin abayas masu kyau da tsari wando da riga su english wears mayuka wanda aka rubuta mata a asibitin Bela bana saka fari bane amma nan da nan fatarta ta yi fresh daga tattarewar da ta yi ƙashin wuyan ya fara cikowa ta fara miƙewa sosai a kan ƙafafuwanta daga ɗan ranƙwafawar da ta yi hips ɗinta ya fara buɗewa zuwa asalin yadda yake. Tajj yana ƙoƙarin janta a jiki da son jin muryarta amma ko daga bedroom bata fitowa gaisuwa ce kawai ke haɗata da shi kullum cikin tunani take ko ta shagala da kallon Little Bilal. Gashi abinci mai kyau da gina jiki ake bata bisa tsarin likitoci ba a bata mai ya ji saboda bata son ya ji Kwata-kwata.
Wajan watanta guda kenan sati biyu da tafiyar Tajj tana zaune a gaban madubi Little Bilal ya maƙale bayanta sai rigima yake mata ya hanata sakat kamar mai zazzaɓi dai kokawa take da gashinta da take son ɗaurewa take gashi wata ƴar ƙaramar riga ce a jikinta sai wani wando iya qwiwa tunda tasan daga ita sai Mahma ta saki gashin ta kalli kanta a madubi gabaɗaya babu tabon ƙonar fuskarta ta yi fresh asalin baƙinta mai kama da chocolate ya bayyana ashe duk wahala ce ta dafar da ita da rashin kula gashi yanzu data samu hutu da abinci mai kyau ga gado da a.c ga mayuka bisa yardar likita sai baƙin wahalar ya kai fatar sai glowing take baƙin gwanin sha'awa ga gargasar a saman fatar da sukai kwance luff gashin girarta kamar su haɗa dana juna, laɓɓanta yirrr jajur da su idanunta farare tas kamar tana ɗiga musu wani abu. Idan ka kalli fatar ta a time ɗin ba za ka yi sha'awar farar fata ba domin irin skin ɗinsu ke wahala a wannan zamanin. Sumarta har gaban goshi ta langwaɓe kai cikin siririyar muryarta ta ce
"Abbiey me kake so ne?" Ta faɗa tana ɗaukar shi ta ɗora saman mirror sai ya fashe da kuka ta taɓa jikinsa ta ji zafi nan da nan idanunta ya cika da hawaye
"Ka daina kuka please" Idan duk bata san me za ta yi wa yaron ba daman Tajj ke rarrashinsa idan yana rigima sai kawai ta fashe da kuka tana kifa kanta. Mamaki ya hana Tajj dake tsaye bakin ƙofa magana mene na kuka ita sam shagwaɓa baya yi mata wahala ne? Kodayake ai yarinya ce babu mai cewa ta haifi Little Bilal jikinta ya dawo ɗanye shi kansa ya san yana kashe kuɗi a kan ta. Ya ƙarasa kusa da madubin ya ce
"Like mother like son, mrs crying"
Ta kasa ɗago kan ta saboda kunyar kayan jikinta Tajj ya ɗauki Little ya rungume shi ya zauna bakin gado ya ce
"Ka saka Mimi kuka ko? Mimi a taimaka a yi haƙuri kar a saka Daddyn Bilal kuka" Kamar ya ce ta ƙara sautin kukan nata ta sake fashewa da kuka Tajj ya miƙe ya nufi inda take ya zauna saman mirror ya ce "Mimi wannan kukan fa" ta yi shiru ya ce
"Ɗago kan ki muga" Kasancewar ta ɗauke shi matsayin yayan data rasa a baya ya saka ta ɗago kanta ta kalle shi fuskarta jage jage da hawaye ya ce
"Tsakani da Allah Mimi wannan kukan na shagwaɓa ne wannan ai ni za ki illata" Ta marairaice fuska a hankali cikin sanyin murya ta ce
"Abbiey ke ta kuka shine na yi nima" Tajj ya yi saurin ɗauke abinda ke zuciyarsa a taushashe ya ce "Saboda ke ƙaramar yarinya ce ko? Waye zai rarrashi wani?" Ta yi shiru
Ya sake rage murya ya ce "Ki daina ban so kukan nan, akwai sanda za ki yi na shagwaɓar ba yanzu ba" Ya ɗago wani magani ya bata ya ce
"Kullum da daddare kina shafawa a lips ɗinki na ƙasa, wannan kuma Dynewell safe da rana za kina sha saboda na lura baki son cin abinci"
"Na gode Yaya" Ya ta zaune ya yi yi wa Little Bilal pictures wani mai masifar kyau ya ɗora a status tare da emojin na love. Tun kafin ya fita yaga Ustaz ya yi viewing can yaga ya yi masa reply da.
"Ɗan waye?"
"Ɗa na ne mana, bani kaga na saka shi a status ba?"
A taƙaice Ustaz ya ce
"Bana son wasa ɗan waye wannan? Ka cire shi a status"
Tajj ya ce "Me ya sa kake son jin ɗan waye?"
"I just seen my photocopy, we look alike" Ustaz ya bashi amsa Tajj a fili ya ce "Ikon Allah"
Kiran wayar Ustaz ya shigo wayar Tajj ya ɗauka ya ce "Wai ya naga duk ka damu ne tunda ka buɗe WhatsApp baka taɓa mini magana ba, sai yanzu? Abinda baka sani ba takwaranka ne wallahi sunansa Bilal"
Tsit Ustaz ya yi can ya ce "His mother please? Kirani vedio call ka bani yaron mu gaisa" Tajj ya ce "Ba zan nuna maka ɗan mutane ba kuma.....,"
"Yaya Yaya Yaya" Ya ji ana kwaɗa masa kira ya ajjiye wayar saman mirror ɗin ya fita tsaye ya ganshi hannunsa riƙe da jita ya ce "Wannan kiran fa?"
"To ka je ka wani shige ɗaki tun ɗazo na zo ni bana son jiran gaskiya ka sani ni sai naga me kake a ɗakin" kafin Tajj ya yi magana Sadauki ya shige cikin bedroom ɗin lokacin Ridayya na tsaye tana ta kallon wayar Tajj da ake kira a jiki an rubuta friend haka kurum ta ji tana son ɗaga kiran hannunta na rawa ta ɗaga tana kai kunnenta tare da yin shiru tana jiran a yi magana. A hankali Sadauki da yake tsaye riƙe da ƙugu ya ce "You?"
"Sadauki zo ka fita" cewar Tajj ya faɗa idanunsa sun yi jajur Sadauki ya juya ya kalli Tajj fuskarsa a haɗe shima baya son Ridayya ta san yana ɗakin don sai ya rama yadda ta yi masa ya damƙi hannun Tajj kamar za su fita tare yana zuwa baƙin ƙofa ta tura Tajj waje ya rufe ƙofar tare da sanya mata key ya cilla makullin cikin Aljihu ya nufi inda take tsaye tana jin sautin bugun zuciyar Ustaz ta cikin wayar.....
Share and share and share as so much as you can! Saboda masu tambaya
sulaimanshuaibunaima@gmail.com
08164069385
*MUNAFIKIN MIJI 27*
Mikiya Writers Ass
Bright pens free batch
Nimcyluv
Sosai numfashinsa ke sauka a kunnenta ta cikin wayar dukda bata san waye ba amma tsigar jikinta ce ta shiga mimmiƙewa tare da tsastsafo mata da wasu zufa daga ƙofofin gargasar. Ta zame wayar a hankali ta tunanin ko an kashe kiran? But his still on the line, ta sake bin jerin haɗaɗɗun 11 digits ɗin da kallo ta mayar da idanunta kan sunan da aka sanya wa.
“Friend”
A sanyaye ta sake mayar da wayar tana tunanin ko za a yi magana amma har lokacin shiru yanayin sautin da take ji kamar mai wayar ya sauya muhalli na asalin inda yake ta ɗan marairaice fuska sai ta ajjiye wayar ba tare data kashe ba ta ƙara zubawa kan ta idanu ta cikin madubin. Tarin sauyin data samu daga barinta Batsari take kallo sai dai har yanzu babu farin ciki a fuskarsa ta zuciyarta kawai ƙoƙarin danne komai take kar ta nuna musu gazawarta dole akwai abinda take buƙata mai matuƙar amfani at least ko ba ta yi farin ciki ba a rayuwa a ce zuciyarta ta kusanta da wannan abun.
Ta yi rolling fararen idanunta manya da su wanda suka sake yin sheƙe saboda kwantaccen ruwan hawayen daya cika su. Kamar daga sama ta ji an ce
"So you're here all this time?" Duk wannan lokacin kina nan?
Da sauri ta juya tana mai ƙoƙarin ɗaukar hijabi domin kai tsaye ta san ba muryar Tajj ba ce ya yi saurin ƙara sawa inda take tsaye ya riƙe hijab ɗin yana zuba mata rikitattun idanunsa a saman fuskarta. Ridayya ta sauya fuska domin sarai ta gane shi ta sakar masa hijab ɗin kunya duk ta gama cikata ita bada burin kowa ya ga jikinta ta juya zata shige bathroom ya saki hijab ɗin ya sha gabanta.
"Ka bari" Muryarta can ƙasa ta yi maganar Sadauki ya haɗe duka girarsa guda biyun ya haɗe su waje guda tun daga sama har ƙasa yake kallonta zai iya cewa ba ita bace ganin yadda ta sauya lokaci guda jikinta ya buɗe fatarta ta yi fresh tana ɗaukar Idanu ga sumar kanta kamar ta Aljanu har ta yi mata yawa lips ɗinta ya rage girma.
Muryarta da manyan fararen idanunta sune suka tabbatar wa Sadauki cewa ita ce babban dalili kuma shi baya mantuwa. Ya jima yana kallonta bai ce komai a hankali ya matsa gefe ya bata hanya ta shige bathroom ɗin da sauri kamar ta tashi sama.
Ya zube gefen gado yana riƙe da kansa idanunsa rufe kamar yanzu ne ta shigo ɗakinsa tana tambayar wani yanzu kuma shi ne a ɗakinta ya kasa rama duk abubuwan daya shirya ya ƙudurcin niyyar yi mata ɗin bai san lokacin daya shafe yana zaune ba sai da ya ji muryar Mahmah a bakin ƙofa tana cewa
"Hamza buɗe ƙofar nan ka ji ko?" Ya miƙe tare da nufar wajan ƙofar ya ciro key ya buɗe.
Mahmah ta kalle sauyi ta gani sosai a tattare da shi, ya shigo da karsashi fuskarsa wasai yanzu kuma jikinsa ya yi weak fuskarsa a haɗe ya yi kicin-kicin. Ya shige Mahmah ya nemi waje ya zauna ita kuma ta shige cikin bedroom ɗin Ridayya.
Tajj ya jujjuya cup ɗin hannunsa kawai yake yana jiran ya ki Sadauki ya yi magana ya ci ubansa ko ya juye duka abinda yake ji a ransa a kan Sadauki ɗin sai ya lura yaron ko inda yake bai kalla ba sai zama da ya yi ya manne jikin kujera yana rufe idanunsa. Tajj ya kasa jurewa ya ajjiye cup ɗin ya ce
"Me ka shiga yi cikin ɗakin? Me ka yi mata"
Sosai Sadauki ya ji tambayar sai kawai ya basar ya zaro wayarsa ya fara dannawa a ƙufule ya miƙe ya ce
"Wai Sadauki ba da kai nake magana bane raini ko?"
Ya ɗaga manyan idanunsa yana gyara zaman rigarsa da take a ɗan buɗe kallon Tajj yake bai ce komai ba. "Ina magana kana tsare ni da Idanu yaushe na zama abokin wasanka?"
Ya girgiza kai ya ce "Ko mother bata mini faɗa mara dalili to a kan me kamar ka haifan daga shiga ɗaki za ka hau ni?"
"Ni kake faɗawa haka?" Sadauki ya haɗe fuska bai ce komai shifa shiyasa bai damu da zuwa ba idan yana nan, saboda Mahmah kawai yake zuwa gidan.
"Kadai san ko babu komai na girmeka kuma ni uba ne dole ka girmama shekaruna ko tashen girma kake ji sai na yi maka duka a nan wajan bama iya nan ba har gidan mother ɗin sai na je idan kuma Prof ke ɗaure maka gindi to"
Sadauki ya miƙe tsaye saman ƙafafuwansa ya ajjiye wayarsa a saman kujera ya matsa kusa da Tajj ya ce
"To bari kawai na zo ka dake ni mu gani" Har hucin juna suna juyowa daidai nan Mahmah ta fito tana rafka salati ta ce
"Mene haka ne zan gani kuma ni Hajjara? Faɗa kamar wasu sa'annin juna ko abokan gaba" Sadauki ya juya idanunsa tuni sun sauya wani irin numfashi yake fesarwa dan dai ba zai iya taɓa Tajj bane amma da tuni ya watsa masa yatsu biyar a fuska.
Har wani rawa jikinsa yake saboda ɓacin rai ya ce "Ya ce zai iya dukana ba tunda shi ya haife ni, bar shi ya dake ni"
Mahmah ta yi salati ta ce "Wanne irin duka kuma Hamza? Shi Tajuddeen ɗin ya ce" Tama rasa me zata ce dalilin wannan rikicin take son ji amma babu alamar za su faɗa. "Nemi waje ka zauna Sadauki maganar ya shige bana son ji ai Tajuddeen gaba yake da kai" Ya cije lips ɗinsa ya tsune da alamar yana huce zafin zuciyarsa a kan su a hankali ya juya ya hango wani zare ya je ya ɗauka ya nufi Tajj ya ce
"Ba ka ce Daddy yana ɗaure mini gindi ba ko? To gashi kai ma ɗaure ka ɗaure na ce"
"Sadauki wai ba nace a bar maganar hakan nan ba? Ta shige" Ya runtse idanunsa ya buɗe ya tura hannunsa cikin sumar kansa ya girgiza kai ya ce
"Ba zan samu nutsuwa ba sai ya ɗaure mini shi ma, idan kuma gadarar ka haifi Nadra ne ka zuba Idanu wallahi ni ma yarana sun kusa zuwa duniya" Bala'i kawai yake zubawa idanunsa na yin wani ruwa ruwa idan ya yi kamar zai daki Tajj sai ya yi saurin dunƙule hannunsa.
Tajj kallon ikon Allah kawai yake shi ne mai laifi kuma shi yake yi wa wani faɗa yama kasa cewa Sadauki komai don takaici a ransa ya ɗauki niyyar dole ya yi amfani da uniform ɗinsa wajan tanƙwara Hamza ɗin. Kamar ɗaukewar ruwan sama haka muryar Sadauki ta ɗauke daga parlourn ya yi kicin-kicin don bai yi zaton za ta fito ɗin ba cikin ikon Allah kuma Ridayya bata ji ko kalma ɗaya ba ta ƙarasa shigowa cikin parlourn.
A hankali ya nemi waje saman kujerar ya zauna yana harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya ya fara buga game a waya, ko inda Ridayya take bai kalla ba.
Mahmah tana murmushi ta ce "Yawwa Mimi ai gwara kina fitowa sai ki yini a ɗaki kamar matar mamaci" Ridayya dai ba ta yi magana ba kanta a ƙasa Tajj ya kalli Sadauki ganin yadda ya yi ya sanya ya sauke ajjiyar zuciya ko babu komai ya san ba lallai Ridayya ta zama daidai da ra'ayin Sadauki ba domin zai iya shaidar Sadaukin duk abinsa mata basa gabansa sai dai su ɗinne suke liƙe masa.
"Ridayya nikam mijinka ba zai neme ki ba kar hankalinsu ya tashi kina zama a gidan nan da auren wani a kan ki tunda kin ji sauƙi ko number mijin naki ne ki bayar sai a faɗa masa halin da kike ciki" gaban Ridayya ya faɗi domin ita bata ƙaunar koda wasa ta tuna da wani Zameer balle ta tuna zaman ƙuncin da ta yi a cikin gidansa da wahala da tuzarcin data fuskanta a tattare da jama'ar ƙauyen Batsari nan da nan idanunta ya cika da hawaye sosai Mahmah ta ce
"Duk sanda na yi miki maganar mijinki sai ki fara kuka ko mutuwa ya yi ne akwai alamar tambaya a tattare dake, waye mijin naki"
"Mtwsss" Sadauki ya ja siririn tsaki shi kansa bai san ya yi ba maganar damunsa take. Maganar Ridayya ta share abinda yake tunani faɗuwar gaba ta ruske shi inda take cewa
"Mahmah ki mini alfarma a bar maganar zuciyata bugawa take"
Muryarta ita kanta rawa take sosai kamar yadda jikinta ya ɗauki rawa tsoro take kar su ce za su mayar da ita Batsari ta ci-gaba da rayuwa da Zameer.
Mahmah ta miƙe ta dawo kusa da Ridayya ta riƙe ta ta ce "Ridayya what are afraid of? Ki faɗa mini matsalar in sha Allah maganar zata zama confidentiality tsakaninmu"
"Mahmah ki barta"
Ya faɗa a taushashe ta ce "Sadauki an barta, amma ta faɗa mini ina mijinta"
"Mun rabu, wata guda kenan" Ridayya ta ce tana runtse idanunta ta na jin hakan kamar