Showing 93001 words to 96000 words out of 190738 words

Chapter 32 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17327

ma kallonsa yake yana ɗago masa hannu yana tsalle kallon yaron kawai Ustaz yake da wani irin firgitaccen yanayi ya kasa furta komai kamar yadda ya kasa daina kallon Little kamar daga sama suka fara jiyo tari daga kitchen ga hayaƙi na tashi a gigice Mahmah ta ce "Nadra ce a kitchen" Jin haka ya saka Ustaz ajjiye wayarsa ya miƙe tsaye babbar rigar jikinsa na ƙara saboda sabbinta dukda dokawar da ƙirjinsa yake na rashin dalili bai hana Ustaz nufar kitchen ɗin ba kai tsaye....






Share and share as so much as you can! Sorry Ustaz🥰 Shanshan tana wajan Sahibi




Na'ima Sulaiman Sarauta
Nimcyluv
08164069385
*MUNAFUKIN MIJI 28*
Mikiya Writers Ass...




Bright pens free batch
Nimcyluv




Duk yadda zuciyarsa ke bugawa bai hana Ustaz nufar kitchen ɗin kai tsaye ba, ga wani irin hayaƙi da yake fitowa ya turnuƙe cikin kitchen ɗin gabaɗaya, hakan bai dame shi ba sai na zuciyarsa data ƙarfafe shi ta hanyar ƙara masa ƙwarin qiwwar shiga ciki ɗakko Nadra kamar yadda tunaninsu ya wanzar musu ita ce a ciki.


Yana ƙoƙarin ɗaga ƙafarsa da nufin shiga ya ji an riƙe masa babbar riga ana faɗin "Uncle ƙani na kuka ƙani yana kuka" cak Ustaz ya tsaya ƙafar daya shigar cikin kitchen ɗin a nutse ya zaro ta, tare da mayar da ita baya yana juya idanunsa sosai da suke zube a kan yarinyar ba tare da ya ce komai ba.


Mahmah ta ce "Babban mutum dawo ka zauna ashe Nadra na bedroom ɗina tana mini wasa da bagaruwa, nasan baka son hayaƙi saboda ciwon kan ka, Sadauki shiga ka duba mene ya haddasa wannan hayaƙin idan dai gas ne sai dai mu fita daga gidan don sharrin shi yawa ne da shi"


Ustaz ya dawo da baya jarumta kawai ya nuna amma zuciyarsa ba ƙaramin tsalle take masa ba tana matsewa waje guda a ƙirjinsa tuni jijiyoyin kansa sun fara bayyana ya zauna saman kujera, ya kasa yin alkunyar ɗauke ganinsa daga kan Little Bilal.


"Mun same ku lafiya?
Yara gida da ayyuka?"


Ya faɗa a rarrabe bayan ya gama samun daidaito da tafiyar numfashinsa. A hankali ya saka hannayensa biyu ya ɗauki Little Bilal.


Mahmah ta murmusa cikin jin daɗin yadda ya ɗauki Little ta ce "Lafiya lou Babban mutum, kwana biyu zuwa kano baya yi maka wahala"


Ya lumshe idanunsa ya buɗe bai ce komai ba, sai nutsuwa da sanyin da yake samu deep down na zuciyarsa yana mamakin baiwa da ƙudirar Allah dake samar da mutane masu kamanni iri guda kuma ma bambanta jini, toshe da ƙwayar halittar haihuwa. Sosai ƙaunar Little ta zauna daram a zuciyarsa.


Mahmah ta ce "Sadauki ta shi mana, kana ganin baƙo babu gaisuwa?"


Baya son nuna halinsa da yi wa Mahmah gardama ya kalli Ustaz ya ce "Ina yini?" Tamkar Ustaz bai jima, haka ya yi shiru kai bama zaka ɗauka da shi Sadauki yake ba, can ya nisa ba tare daya ɗago kai ba ya ce


"Sannu"


Wani baƙin ciki Sadauki ya ji zuciyarsa kawai ya miƙe ya nufi kitchen ɗin a ransa yana mamakin waye shi a wajan Mahmah? Mene ya sanya yake yawan haɗuwa da shi? Kuma shi ne wanda yaje gidansu yana neman Ridayya kuma ga Ridayya ga shi what's going on?


Bayan tashin Sadauki Mahmah ta kalli Ustaz ta ce "Muhammad-Bilal ya kamata ka yi haƙuri da dukkan abubuwan da suka faru ka ɗauki ƙaddara, Ubangiji shi ke rayawa kuma shi ke kashewa, shi ke samar wa kuma shi ne ke kwacewa, shi ke tadawa kuma shi ne sarkin dake kashewa. Ka ɗauka Ubangiji ya fi ƙaunar su Baffa da iyalanka shi ne yasa ya amshe su, suka koma gare shi dole ka yi haƙuri ka ɗauki ƙaddara ka sakawa ranka cewa kaima ranarka na zuwa. Ka yi amfani da damarka ka ribaci lokacinka..."


Ta ɗan yi shiru, ta ɗora da faɗin "Aure! Ka yi aure Ustaz don Allah ka raya sunnar ma'aiki sallahu Alaihissalam, ka tara zuri'a yadda Ubangiji zai yi alfahari da kai wannan zaman da kake babu mace a gefenka is not good rashin aure ga baligi babban mutum irinka babbar matsala ce, shi aure ni'ima ce yana ƙarawa mutum nutsuwar zuciya da ɗauke damuwa rashin yinsa kuma yana taɓa kwakwalwa da gurɓata tunanin mutumin daya isa yin shi. Don Allah don Annabi Muhammad-Bilal ka yi aure kar ka tsufa a gida ƴan'matan su dinga gudunka nasan ba rasa matar aure ka yi ba, a taimaka a daure"


Ya kalli Mahmah sai kawai ya jinjina mata kai alamar “In sha Allah” don baya jin zai iya magana ya miƙe da Little Bilal a jikinsa wanda ya rungume Ustaz ya kwanta jikinsa tamkar jikin babansa, ya kama hannun Nadra yana ta tsaye bai ce komai ba. Fahimtar hakan yasa Mahmah cewa.


"Za ku fita kenan? Allah ya tsare Nadra banda ƙiriniya domin nasan halinki" nan ma jinjina kai kawai ya yi kana ya nufi waje da yaran a ransa yana ayyana inama yaran shi ne. Mahmah ta raka Ustaz da idanu ta ce


"Ikon Allah Ubangiji ka kawowa wannan bawa naka sauƙin rayuwa, a yi mutum magana ma wahala take masa? Sai ya ƙaraci zaman shi tari bai yi ba?"


Da sauri Sadauki ya saka ƙafa ya daki ƙofar ta buɗe ya kutsa kai ciki. Kwance ya ganta yashe a ƙasa jikinta nata rawa sai kakkarwa take ga abinda ya ɗora yana kamawa.


Ya kashe gas ɗin ya sauke tukunyar ƙasa zuciyarsa sai harbawa take ya tsuguna gabanta muryarsa a harɗe yake faɗin


"Shanshan lafiya? Me ya sameki?" Shiru bata amsa ba. Ya tattare bakin hannun rigarsa yana ƙoƙarin ɗaukarta yaga ta saki fitsari ya fara gangarawa zuwa bakin kitchen ɗin. Sadauki ya tsaya yana kallon ikon Allah domin bai taɓa ganin mutum kuma mace rana tsaka da fitsarin kwance ba.


"Hamza wai lafiya ne na jika shiru?"


"Mahmah"
Shi kawai Sadauki ya iya cewa Mahmah ta leƙo ta kalli Ridayya da tunda ta yi fitsarin ta dawo hayyacinta, tsananin kunya ne ya saka ta kasa motsawa tunani take mai ya saka ciwon ya motsa mata a gidan da bata iko da shi? Me ya sa ta yi fitsarin a gaban wanda ba muharraminta ba? Ta ƙara cure wa waje guda tana jan wani irin numfashi.


"Mimi fitsari? Sadauki jeka ko? Sai mun yi waya da Hajja Azizat"


Ya yi tsaye jikin sink hannunsa harɗe a ƙirjinsa abubuwa da yawa suna wanzuwa a zuciyarsa can ya juya tare da ficewa daga cikin
kitchen ɗin.


Yana fita ya shiga motarsa ya nufi gida zuciyarsa cike da tunani kala-kala. Ridayya kasa cewa Mahmah komai ta yi ta miƙe ta nufi bedroom ta wanke jikinta tare da sauya kaya, kuka ta yi sosai mai isarta wani irin kewar dangi da son ganin Abbiey ɗinta ya addabi zuciyarta, shi kaɗai ya san yadda zai kula da ita idan ciwon ya tashi shi kaɗai ya san hanyar yayewar damuwarta shi ne kawai baya damuwa data amsa shi ko ta yi shiru. Ta dawowa a lokacin da komai ya ƙare.


Ta miƙe ta nufi gaban mirror ta zubawa kanta idanu, hawaye ya cika mata Idanu sumar kanta duk ta dameta daman Abbiey ke kula mata da ita ji take tamkar ta aske ta wuta bata son gashin ya dameta duk wani abu da zai saka tana tunawa da Abbiey ɗinta bata ƙaunar ganinsa.


Ta fashe da wani irin raunataccen kuka kamar yarinya ta saka bayan hannunta ta share idanunta "Shikenan ka yi nisa da duniyata? Shikenan ba zan ƙara ganinka ba Abbiey, ba zan nemi yafiyarka ba, ko bamu dawo daidai ba ka yafe mini nasan abu ne mai wahala ka yi mini uzuri ka amshi ƙaddarata matsayin kuskure irin na kowanne bawa. Me ya sa kai ma ka mutu Abbiey kai ne kaɗai kake so na, me ya sa za ka bisu zuwa inda suka je don Allah ko a mafarki ne ka zo Abbiey ka tafi na rayu"


Jikinta ya ɗauki rawa ta durƙushe a wajan tana wani irin kuka


"Zan yi karatun yanzu zan zama abinda kake so na zama, babu ruwana da maza hasalima na tsani namiji ba zan sake yarda da kowa ba, zan tsaya tsayin daka wajan karatu da yi maka biyayya ko da za a kira ni da _Feminist_. Abbiey soyayya guba ce na sha ta kusa illata ni, Abbiey namiji ba ɗan goyo bane, na goya shi ya nakasta baya na, Abbiey namiji ɗan kunama ne wallahi tallahi Abbiey na tsani maza, kai ne ubana kai ne yayana you still be...."


"Ridayya"


Ta yi saurin goge hawayen idanunta, duk kukan da ta yi amma idanunta tar suke babu ja sai ruwan daya kwanta a cikinsu wanda ya ƙara musu haske sosai.


Mahmah ta ce "Tun ɗazo nake buga ƙofa shiru are you okay?"


"Eh" Ta furta a hankali kanta a ƙasa zuciyarta babu daɗi


"Ki fito ku gaisa da Uncle ɗin Nadra zai tafi, ai ya shigo kina kitchen ma"


"Ba zan iya ba"


Mahmah ta kalleta sosai sai ta jinjina kai ta ce "Babu matsala ki kwanta ki yi bacci idan kin farka za ki samu nutsuwa, daman naga Little ya maƙale masa ne yana kuka gashi hadda ɗawainiyya ya yi musu shatara ta arziƙi"


"Ayya Allah ya ƙara arziƙi ki ce masa an gode"


"La ba'asa"


Mahmah ta fita, Ridayya ta kwanta kan gado ta rufe jikinta har fuska kanta da ƙirjinta na yi mata ciwo sosai tana jin Mahmah tana magana ita ɗaya a parlour a haka har bacci ya ɗauketa.


A can parlour Mahmah ce kawai ke hira Ustaz yana zaune saman kujera ya harɗe ƙafafuwansa, mamakin yadda gudun zuciyarsa ke ƙara hauhawa idan ya shigo cikin gidan yake.


"Ai Tajuddeen baya garin ya koma can Katsina saboda abubuwan da suke faruwa, kasan ƙasar nan ta mu sai dai kawai aja mata li'ilafi cin kashin da ake mata ya yi yawa. Can kwanaki an sace ɗaliban makarantar kwana har yanzu shiru kake ji shawo ya saci shirwa, yanzu haka fa an ce an lalata ƴan'mata da yawa wasu ciki nema da su yanzu don girman Allah Ustaz wa kake ganin zai auri yarinya ba budurwa ba?"


Ustaz ya girgiza kai a ransa yake cewa


"Idan har yana son ta, to budurci ba wani abu ba ne, so na gaskiya bashi da dalili Mahmah ki gagauta tuma da neman yafiyar Ubangiji allahumma yahdiki Mahmah zancen ya yi girma"


"Abun ya yi wani iri ko ki ba lallai na bari ba zamani na ciwoka annoba kala-kala"


Ustaz ya miƙe yana gyara zaman rigarsa domin hirar a saman kan shi yake jinta. Nan da nan Little Bilal ya saka kuka da rigima yana miƙa wa Ustaz hannu a dole sai ya ɗauke shi.
"Wannan yaron ba dai son gantali ba, uwarka na can tana kuka kamar ƴar yaye". Ustaz ya rungume Little yana ɗan jijjiga shi a kafaɗa kamar yadda ya yi wa babarsa har bacci ya ɗauke shi ya ɗan faki idanun Mahmah ya sunbaci goshinsa kana ya miƙa mata shi.


"Zaka tafi kenan?"


"Uhm" ya ce yana nufar waje ko ruwa yaƙi yarda ya sha ta bisa da idanu tana "Miskilin mutum ko ƙaddara, Allah ya baka mace daidai kai amma wannan shirun ni kai na ya kusa kassara ni"


Ko da Ridayya ta farka ta ji ƙamshin da ko a mafarki ba zata manta ba, bawai ƙamshin turare bane ƙamshin Abbiey na musamman ne daban yake ta dinga kallon Little Bilal sai ta marairaice fuskarta a hankali tana tura baki ta ce


"Haba Abbiey komai sai ka ɗauke mini na uba?" Shi kuma yaron ya washe mata baki yana lumshe idanu ta cire masa rigar ta ɓoye ta saka masa wata ta yi shiru tana kallonsa ya zama tamkar t.v a gare ta.


Duk yadda Ridayya take ƙoƙarin gujewa buƙatar Sadauki abin ya gagara, ya san duk hanyar da zai bi ya rutsa ta kuma bata da wani dalili mai ƙarfi ita babu kalamai ma a bakinta. Yanayin yadda yake gudanar da abubuwan shi mamaki abin ke bata, yana ƙaunar yin sadaƙa yana son kayan kwaɗayi ta dinga mamakin inda yake samun kuɗi har yanzu kuma bai yi mata magana a kan fitsarin da ta yi ba, ya yi burus da batun ko a chat daya buɗe mata bata fiya magana ba sai kawai ya ce ta yi masa voice kuma kawai ya kirata kafin ta yi magana ya zai ce Shanshan shhhh numfashinki na kira na saurara yana gama ji zai kashe kiran. Abubuwan Sadauki hadda almara ta ɗan saki jiki da shi har ta yi masa murmushi ko dariya a kwana na biyar ke zancen ya sauya ya ɗauketa zuwa wani waje suna tsaye wata ta zo ta rungume Sadauki.


"Wow ashe da gaske Sadauki ne baby Idanunka kenan?" Sadauki ya juya ya kalli Ridayya yaga ta juya baya tana danna waya kamar mai sanin me take amma dannawa kawai take.


"Zubby ya kike?"


"I'm good, ina ka ɓoye ne ko'ina na duba ka baka nan ka bani number ka"


"No, ina tare da matata ne" Zubby ta zare Idanu ta ce


"Mata fa ka ce? Sadauki aure ka yi babu labari? Shi ya sa ka sauya number" bai kulata ba.


"Wace matar?" Da hannu ya nuna mata Ridayya bai ce komai ba.


"Hi" Ridayya ta juya ta kalli Zubby sau ɗaya ta ɗauke kai. Zubby ta zare Idanu tana kallon Sadauki ta ce


"Goodness! Sadauki wannan abar zaka aura? Kuma a gida za a barka wannan halittar? Yaaakkkk"
Ya gyara tsaiwa sai kuma ya ce "Wakike da suna?"


"Sunan nawa ka manta?" Ya ɗage gira ya ce "Sunan na uwata n da ba zan manta ba? Ke fara ita baƙa ko? Na yi rejecting ɗinki na yi accepting nata shi ne ya ba ki ƙarfin qiwwar cewa haka"


Ya juya ya damƙo hannun Ridayya wacce tuni idanunta ya cika da hawaye ta kalli Sadauki ya yi saurin matse hannunta ya ce


"Wallahi kika bari hawaye ya sauka a gaban kowa zan share su da bakina Ridayya, na tsani kuka mara dalili"


Ta sunkuyar da kanta ƙasa. Zubby dariya kamar me ta ce "Yanzu duk wayewarka da zagaye-zagayen da ka yi a nan ka yar da zango Sadauki? Wallahi kai ka yi abin ni ce kuma da kunya wanna baƙar da kayan idanun za ka kwasa village girl domin babu alamar hawaye a tattare da ita"


Sadauki ya ce "Ridayya ki rama abinda take faɗa miki i can't take it anymore, wallahi idan ki ka yi kuka ni na san me zan miki" gabaɗaya jikinta rawa yake domin bata saba da wannan tashin hankalin ba. Ya jata fuuuu zuwa mota ya buɗe ya dannata ciki ya saka key ya rufe ya dawo wajan zubby idanunsa jajur.


"Kin ci sa a Sadauki baya taɓa jikin ƙazamai kuma baya dukan mata, ita waccan ƴar ƙauyen ita ce zuciyar Hamza Sadauki gabaɗaya ita ce numfashina, abinda baki sani ba irin colour ɗinta nake buƙata mai wahalar samu domin yanzu baƙaƙen mata wahala da tsada suke sadakinsu daban suke, kalar kulawar da za a basu ta musamman ce. Idan za a biya sadakinki da naira na Shanshan da dallors za a biya, ki duba komai na jikinta natural ne halitta da Ubangiji al'arshi ita maza ma tsoro suke bata, ba ke da kika mayar da kan ki ƙaryar kowa ba, ita tana ƙaunar fatarta bake da kike shafa na kan ti ba. I love her the way she is, i love her so much i love her to the square of infinity💕 mother of my childrens"


"Ban yarda za ka aure ta ba" Zubby ta faɗa idanunta na sauya dauriya kawai take na cin mutuncin da Sadauki yake mata.


"Idan ban auri Ridayya ba ki ƙaddara Sadauki baya duniya, ni na san saboda ita ne har yanzu ban taɓa budurwa ba, babu macen data isa ta yaudare ni ba a haifeta ba, Sadauki bai yarda da asara ba baya kuma give up zan aureta kuma zan tabbatar miki da haka, useless"


Bayan ya shiga motar ya kasa driving ya cije laɓɓansa cikin zafin nama ya daki kan motar jin kansa yake yana yi masa wani irin hayaƙi, zuciyarsa na tafarfasa bai san dalilinsa na zuwa wajan nan da Shanshan ba, yasan ƙaddara ce wacce ya riga fata ya rasa wanne kalar love words masu taushi da zai yi amfani da su wajan rarrashinta, shi kansa zuciyarsa wata kalar rawa take masa ya buɗe baki zai yi magana ya kasa ya sake buɗewa da nufin magana ya kasa maimakon hakan wani irin sauti ne mai ƙarfi ya maye gurbin maganar da zai yi hakan ya tabbatarwa da Ridayya Sadauki ya fita shiga cikin tashin hankali ainu ta ɗago idanunta daya gama jiƙewa da hawaye ta kalle shi a tsorace yanayin rinewar da idanunsa ya yi shi kaɗai ya bata tsoro ya janye idanunsa murya a daƙushe ya ce


"Can you help me with drive?"


"Ban iya ba" Bai ce komai ya kifa kansa ya ɗauki lokaci kafin ya ja motar suka bar wajan.


Ita ce farkon fita ta yi gida da gudu bai bita ba domin yanayin da yake ciki ba nata bane ya nufi gida kawai. Ridayya har dare kalaman Sadauki na yi mata yawa ashe haka soyayyar take? Ashe haka ake faɗawa masoyi? Mai yasa ita sam bata taɓa jin daɗinsu ba, ta rufe idanu ta mirigna she wish a ce ita Sadauki zai mallakawa wannan kalaman domin bata hango ƙarya cikin idanunsa ba, bata da kowa a yanzu har a zuciyarta take gasgata cewa Ustaz ya rasu da yana raye dole zai neme ta. Ta samu kanta da lissafin kwanakin da suka rage da game ɗin soyayyarta da Sadauki.


"Kina yin hawaye zan share su da bakina?" Gabaɗaya tsigar jikinta ta mimmiƙe wani yarrr ita tunda take a duniya ko kiss bai taɓa haɗata da Zameer ba balle irin romantic abun nan, ko idan aka yi kiss ya mutum yake ji?.




Da sallama ya shigo parlourn idanunsa maƙale cikin glasses fitowarsa kenan daga Library yana research a kan wani abu. Jallabiyya ce a jikinsa mai taushi, laushi, santsi kasancewar weekend ne yana gida. Yana ƙoƙarin shigewa ya ji an ce


"Muhammmmd!"


Cak ya tsaya domin Hajiya bata taɓa yi masa irin wannan kiran ba, irin kiran yaran nan. "Dawo ka zauna"


Ya nemi waje ya zauna ya ajjiye wayar hannunsa da diary ɗinsa da yake ajjiye muhimman abubuwa. Babu wasa a fuskarta ta ce


"Wacece ni? Mene matsayina a wajan mahaifinka dama kai kan ka?"


Ya dinga kallonta "Ba kallona za ka tsaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login