Showing 171001 words to 174000 words out of 190738 words

Chapter 58 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17316

amma kin kasa dawo da shi gida, bakwa tsoron haƙƙina rabona da shi tun ina amarya tun kafin na samu ciki?"


"Kamarya kenan kafin ki samu ciki kuma? Ko dai bayan kin samu ciki?" Cikin inda-inda Mardiyya ta ce "A'a ina nufin kafin nasan da cikin a wajena" murmushi Umma ta yi ta ce "To albishirin ki wannan kuɗin shi ne ya turo da su ya ce a ba ki kuma yana nan kan hanya soon" cikin farinciki Diyya ta ce


"Da gaske ko dai ƙarya kike mini Umma?" Da wani mamaki Umma ta ce "Ƙarya kuma Mardiyya?"


"Opps sorry na ruɗe ne, bedside kin jima ai kina ce mini yana hanya, amma dai kafin na haihuwa zai dawo" Umma ta jinjina kai cikin ya yi laushi ta ce "In sha Allah" daga haka ta juya cikin sauri Mardiyya ta kira ƙawarta ta sanar mata komai ta cikin waya ta ce "Saura ki ƙara jakanta irin na baya, tunda brain ɗinki a tushe yake kamar na kifi bayan maganinsu sha'awa ki saka masa wanda zai zama kamar na maye, sai ki yi bidiyo shi zai zama hujja ni kuma zan bayar a yi editing na bidiyon a cire cikin jikinki shi kuma a ɗan rage masa ƙiba, don na lura ya ƙara tumbi da kyau da haske wallahi irin yana cikin kwanciyar hankalin nan" Diyya ta haɗe fuska ta ce "Ban gane ba, mijina ne fa kuma kike yabon ƙyan shi"


"Dilla to mene? Ai kyakkyawa ne"


"Kambu saurara akan shi zan iya rabuwa dake tuni wallahi aikin banza daman haka ku ƴan'matan da kukai kwantai a gida kuke, guzuma" ta ce "Ni kikewa gorin aure Mardiyya? To shikenan kya zauna da Ustaz ɗin na gani" tana faɗin hakan ta kashe wayarta. Baba ƙarami ya dinga ladamar aibata Ustaz da ya yi daman a lokacin ya kasa fahimtar meke faruwa da shi har ya yarda, ya samu nutsuwa ya kuma tambaye shi ya jikin Ridayya da yanayinta ya sanar masa tana lafiya.


Baba ƙarami ya ce "Babban mutum ya kama ka dawo gida haka nan domin asan kana tare da matarka" Ustaz ya sauke ajjiyar zuciya yana janye idanunsa da lumshe su hannunsa ɗaya yana shafa sumar Ridayya dake bacci akan cinyarsa hankali kwance ta zama wata ƙatuwa da ita jikinta ya buɗe sosai kamar an hura ta, ta fresh da ita laɓɓanta jajur dasu ya kasa cewa Baba ƙarami komai.


"Muhammad yaushe haka zata ci-gaba da kasancewa ne? Akwai rikici mai yawa muna buƙatar ka, hakƙin matarka dana mahaifiyarka ga matsalar kuma ta cikin Mardiyya, gashi kai kaɗan zaka iya tanƙwara surukinka ya saka a saki mahaifiyarsu Junaid ai abin kunya ne"


"Cikin Mardiyya?"


"E, ai tama kusa sauka" Ustaz ya taɓe baki yana murza lips ɗin Ridayya can ya ce


"Oh, cikin gaske ne ashe?"


"Baka da labari ne? Bayan jininka zata haifa"


"Ina da shi, amma Ridayya ce kawai ta amshi budurcina Abba, ita kawai ta san baɗini na, kuma Mardiyya ta sake ta furta haka a kan idanuna zan watsa mata yatsuna biyar a kuncinta, kawai ina addu'ar Allah ya yafe mata zunubanta da kurakuranta ne Abba"


Baba ƙarami ya ce "Ikon Allah, to Allah ya yafewa Babban mutum da sakin bakin sai anjima"


Ustaz ya dinga tunani mai ya ce wanda bana daidai ba? A hankali ta juya suka haɗa idanu ya ɗaga mata gira ta yi murmushi ta ce "Ba ka yi bacci ba?"


Ya sake jinjina mata kai ta miƙe tare da jingina a jikinsa a sanyaye ta ce "Abbiey" ya yi shiru ta sake cewa "Abbiey?"


"Kina buƙata ta ne jaririya?" Ta girgiza masa kai ya lumshe idanu.


"I am sorry, ni kaina na kasa yafewa kaina tsananin ruɗewa ne ya saka na aikata abinda na aikata, amma bawai don ina son murgayi bane, na faɗa ne da tunanin ko kalamai na za su saka ya dawo hayyacinsa amma wallahi ba kowa a raina kuma....," bakin dake ta juyawa ya kame ta yi saurin yin tsit bisa tilat some minutes ya sake ta yana jan numfashi.


Ta zare idanu ta ce "Yawon bacci fa Abbiey" ya juya ya harareta ba tare da ya ce komai ba, fuskarsa a haɗe dai ta yi ta magana ya yi banza da ita can ta fara masa cakulkuli ya juyo gabaɗaya ya ce


"Wa'auzubillah yake Ustaza wasan banza ne wannan ai" ci-gaba ta yi ya fara murmushi tun yana daurewa ya fara dariya sosai wacce bata taɓa ganin ya yi ba, ya jata ya rungume sosai yana shafa cikin jikinta dake gab da zuwa duniya.


"Tab Mimi kalli hancinki ya yi kamar funkaso wlh"


Ta haɗe rai ya girgiza kai ya ce "Serious wannan cikin ya saka ki zama Mama boss kin fi ƙarfin bayana" bata kula shi ba ta miƙe tana juya masa mazaunai ya girgiza kai kawai ya san tsokana ce.


Zameer ya shiga tashin hankali cikin bacci zai farka a gigice yana kiran sunan Ridayya ya azabtu ya rame ya fita hayyacinsa da kamaninsa wanka da gayun tuni babu daman ya tattara ya koma Batsari, ba sana'a sai dai ya ɗauki fatanya da magirbi zuwa gona ga yara har uku har tsora tashi suke cikin dare sai ya gansu kamar yaran aljanu. Idan azabar kasancewa da Ridayya ta tasu masa yaje wajan Hanne haka zata raraka shi ya kwana yana birgima yana son komawa Kano ko Ridayya ta dawo ya san zata ji tausayinsa ta dawo gare shi amma yana tsoran Tajj da kuma ƴan'sanda ya susuce.


Sosai yake saffa da marwa a harabar wajan ya kasa zaune balle tsaye yana cikin halin Dr ya fito da sauri ya ce "Sir dole sai dai ka saka hannu mu yi mata c.s ba zata iya haihuwa ba"


Ya ja wani irin numfashi da ƙyar da ya ji ya tukare masa maƙoshi a hankali ya ce "Ok" ya amsa ya saka hannu har Dr ya tafi sai kuma ya ce


"I love my wife dr please...,.," ya kasa ci-gaba likitan ya ce "Idan baka nutsu ba, zaka iya shigowa ka kasance da ita lokacin aikin"


Ya jinjina kai. Cikin ƙaƙanin lokaci aka shirya aiki kasancewar babban asibiti ne kuma na kuɗi komai nasu daban yake. BM USTAZ na zaune saman kujera ya damƙe hannayenta biyun idanunsu maƙale da juna, yayinda aka saka labule ya raba tsakanin cikin Ridayya na wajan likitocin ƙirjinta da kanta yana wajan Ustaz.


"Abbiey"


Ya ware idanunsa har lokacin bakinsa ɗauke yake da addu'a ta ce "Me ake mini ne? Na ji ƙafana ya sake kamar ba nawa ba"


Ya shafa kanta yana murmushi can ya ce "Za ki zama Big Maama jaririyata Little zai samu sister" ta ɗan yi murmushi ta ce "To bani labari"


Ya ɗan yi jim a taushashe ya ce "Me zan ce wanda ya shige labarta miki yadda nake son ki tun kina zanin goyo ina goyaki a bayana? Ridayya da gaske ban taɓa shan a zaba wacce ta shige ta soyayyarki ba, har mamaki nake da zuciyata bata buga ba, ke wata irin macace da duk wanda ya kasance dake zai ji kin fiye masa mata da dama, ba kowa ke bawa ni'imar daya ba ki ba. Ina tsananin son ki da ƙaunarki akan ki nasan cewa ni mutum ne lafiyayye, sanda kika zaɓi wanina da tunanin ya fini qualities I just hate myself, na fara ƙoƙarin ganin na sauya na zama yadda zaki iya sona amma it's too late to cry, kin wahalar dani da zuciyata da gangar jikina. A hankali na fara fahimtar hakƙin Muwaheeb ke bibiyata ta so ni sosai amma na yi kamar ban sani ba, ta sha tara ta tana kuka akan na taimaka mata na kunnen uwar shegu...."


Ridayya ta sauya fuska kishinta ya fito sosai Ustaz ya kashe mata idanu kana ya sumbaci goshinta ya ce


"Da ne not now, you're the only one i love you Miftaahu qalbiy"


Sosai ya zage yana faɗawa Ridayya abinda ita kanta bata sani ba, ya buɗe zuciyarsa a haka suka wanzu suna kallon juna bata cewa komai sai shirunta ya yi yawa ta lumshe idanu ya ɗan bugi kumatunta ya ce "What?" Ta girgiza masa kai yana lura da yadda fuskarta ke ɗan sauyawa ta yatsuna fuska ko ta marairaice ce a hankali ya ce "Repeat after me"


Yana addu'a tana maimaita hannunta har lokacin yana cikin nasa fuskarsa a kan tata. Basu ankara ba Dr ya ɗorawa Ridayya baby a ƙirjinta sai kuka yake, ta dinga kallon babyn shi kansa Ustaz kallon babyn yake, zai magana Dr ya sake ɗora wani babyn suka buɗe idanu lokaci guda"Dr.....," maganar ta tsaya ganin na ukun Dr ya ce "Wannan kuma kai na bawa ka riƙe" bai damu da jinin ba ya amshi yaron ya riƙe a ƙirjinsa Ridayya idanun take ta rarrabwa suna ta hira ashe abinda ake ciro mata kenan? Abinda suka rayu a coming kenan ashe wani irin hawaye ta ji ya zubu mata ya fahimci rabo masifa ne musamman idan ya rantse, ta dinga kallon yaren shi kansa Ustaz girman zatin Ubangiji yake girmamawa likitan ya ce "Madam yara nawa kika haifa?"


"Uku" ta furta hawaye na bin fuskarta sosai ya ce "Mata ko maza?"


"Ban sani ba" ya girgiza kai ya ce "A'a duba da kyau" Ta juya ta kalli Ustaz ta ce "Abbiey"


Ya yi mata tattausan murmushi ya ce "Gabaɗaya boys ne Mimi" Ta jinjina masa kai. Ya ajjiye jaririn Norses suka ɗauke su aka fara shirya su. Ustaz ji yake kamar ya gama samun komai a rayuwarsa ya dinga sawa Ridayya albarka da addu'a ya rungume ta sosai ya dinga sumbatar fuskarta ta yi shiru a jikinsa.


Labarin haihuwar ƴan ukun masu matsanancin kama ɗaya ya wanzu a asibitin sai labari ake wasu na zuwa ganinsu sosai kuma Ustaz ya musu addu'a da huɗu ba. Ɗaya ya amsa sunan Baffa ɗaya kuma Baba ƙarami na ƙarshe ya amsa sunan Hamza Sadauki. Da sauri Ridayya ta kalli Ustaz jin ya ce Sadauki ta kasa furta komai sai gdy take a ranta.


A can gida Nijeriya fitowar Umma kenna daga ɗakin Mardiyya sbd har ta shige Edd nata amma shiru. Turus ta yi ganin wani abin mamaki makeken photo ta gani an saka shi a Frame yara har uku jere farare tas jajur tasu suma har gaban goshi kamar su guda baka iya bambance ɗaya a ciki. Nan take son yaran ya kamata ta sake kallon frame ɗin da manyan baƙi aka saka “WELCOME TO THE RANO'S FAMILY, TAHIR, MANSOOR, HAMZA” Baba ƙarami ya yi kamar bai san me take ba, ta sake juya can da sauri ta ce "Yaran waye waɗannan?.....




More comments more update
08164069385
Na'ima Sulaiman Sarauta
*MUNAFUKIN MIJI*


Nimcyluv......
46


*Follow my account AREWABOOKS* https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv


Jaririn shima ya zubawa idanu ya ce "Sun miki kama da wani ne?" Umma ta girgiza kai ta ce "Bana jin kaf RANO'S FAMILY akwai mai kyawun halittar jariran nan, Ustaz ne kyakkyawan ciki kuma sun ninka shi a kyau da komai yana jariri bai samu kyansu ba wallahi wannan girmansu abin kallo ne" Baba ƙarami ya jinjina kai ya ce


"They're blessed, Allah ya yi musu albarka ya ƙare haɗa kan iyayensu ya kau da idanun maƙiya akan su"


"Amin, yaran waye?" Umma ta tambaya cike da zaƙuwa saboda kyawun yaren ya gigita ta ainun ya sake murmushi ya ce


"Ki fara saka musu albarka tukunna tunda kin yaba" Umma da take jin wani irin matsananci daɗi ga wani farinciki daya saukar mata lokaci ɗaya wanda hakan ya faru ne sanadin ganin zuƙa-zuƙan jaririn guda uku sanye da kaya iri guda kuma kamanni guda ta ce "Wallahi tun kafin na furta komai na sanya musu addu'a tare da addu'ar Allah ya tsone idon maƙiya ya yi musu albarka, ya ƙara so da ƙauna a tsakanin iyayen su, ma sha Allah tubarakallah har cikin zuciyata nake jin ƙaunar yaren" yadda take nuna farinciki a fili zai nunawa mutum zahirin gaskiyar da take faɗa tsakani da Allah take son yaran kamar yadda ta furta.


Baba ƙarami ya sauke numfashi idanuna akan matarsa yana jinjina girman rabo, kuma duk inda jininka yake sai jikinka ya baka ya kasa furta komai deep down na zuciyarsa addu'a yake Allah yasa haihuwar yaran nan ya kawo daidaito tsakanin uwar yaran da kakarsu ya zama silar kwanciyar hankalin duka familyn bakiɗaya. Ya nemi waje tare da zama saman kujera yana girgiza ƙafa shi kansa yaran Ridayya da Ustaz sun jijjiga shi kyan yaran ya bashi mamaki dukda ba'a mamaki da ƙudirar Allah.


"Baka faɗa mini yaran waye ba? Ni dai na gama tunani daga dangina har naka babu mai haifar kyawawan yara kamar su" Baba ƙarami ya juya ya sake kallon yaran a hankali ya ce "Ko?" Ta ce "Wallahi fa, Mardiyya kawai nake saka ran zata haifawa Muhammad kyakkyawan yaro kamar shi ko fiye da shi"


"Me ya sa kike tunanin namiji zata haifa kuma kyakkyawa kamar gwarzon ɗana" ta matsa kusa da shi ta ce "To ai haka ne kuma juma'ar da za ta yi kyau Hausawa suka ce tun daga Laraba ake gane ta, Mardiyya nada kyau haka Babban mutum kuma an ce abin cikin ƙwai yafi ƙwan daɗi kaga dole ɗan za su haifa shi da Mardiyya ya zama kyakkyawa" Baba ƙarami ya jinjina kai cike da gamsuwa ya ce "Haka ne kam, kina da taki gaskiyar"


"Ni sai naga kamar baka ƙaunar yarinyar nan baka mayar da hankali akan lamuranta karka manta daughter-in-law ɗinka ce fa" Cikin sauri ya juya ya kalleta yana waro idanunsa waje ya ce "A'a karki mini sharri matar, ai jinin ka wuya za shi you're just like a drive mu duka passengers ne a tafiyar nan sai inda kika ajjiye mu, nina isa naƙi zaɓin uwar gidan Tahir" ita dai duk bata gane me yake son cewa ba, don haka ta tattara maganar ta ajjye waje guda. "Ki mini wata alfarma ɗaya mana Hadiza"


"Wacce alfarma?" Ya fito da A.t.m guda biyu ya ajjiye mata kana ya nuna mata jariran ya ce "Haɗaɗɗun kayan barka nake so ki haɗu na Triplets masu kyau na gani na faɗa, komai da kika sani na yara ki haɗu" Umma ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Wannan kam ai ba alfarma bace ko su waye waɗannan na san suna da muhimmanci a rayuwarka sosai. Zan wa wata friend ɗina magana da take kawo kaya irin wannan daga waje sai na yi mata list na duka abinda muke buƙata, sana'arta kenan ai" "To madallah ba damuwa a yi hakan"


"Uwar yaran fa?" Ya ce "Me fa?" Ta ce "Ina nufin me za a siya mata?" Baba ƙarami ya yi shiru can ya girgiza kai ya ce "Iya yaran dai kawai"


"A'a ba za a yi haka ba, uwar kam ai ta cancanci a yi mata ni zan haɗawa uwar da kuɗina kaga sai na kai daga nan naga yaran so ma sha Allah"


Yana miƙewa saboda kiran sallah ya ce "Lallai to muna godiya" har zai tafi ta ce "Don Allah yaushe ɗana zai dawo gare ni ne? Idan fushi yake wallahi hukuncin daya ɗauka ya yi yawa ina jiye masa fushin uwa Baba ƙarami, yana da kyau ya dawo kafin matarsa ta sauka ga kuma hakƙin matarsa" A hankali ya ce "Zai ba ki mamaki ne soon zai dawo ki shirya tarɓa ta musamman domin ya yi aure a inda yake"


Da wani irin tashin hankali Umma ta ce "Aure kuma? Shi babban mutum ne ya yi aure ba tare da mun sani ba, a wani gari? Waya aura? Ƴar waye?" Duk hankalinta a tashe yake wani gefen kuma tana jin hakan ba komai bane idan har ba Ridayya bace kuma daman tuni ta raba shi da ita, tana mace tana raye wama ya sani ne? "Zan je sallah zan miki bayani idan na dawo ki haɗa mini tuwon nan ki saka man shanu" jiki a sanyaye ta ce "Tom"


Baba ƙarami na fitowa Main parlor ya ci karo da Junaid ya fito yana gyara hannun riga alamar ya yi alwala ya ce "A'a Junaidu dawowar yaushe?" Yana murmushi ya ce "Yanzu ne Abba"


"Lalle kaga ina son magana da kai kowa idan mun idar da sallah" Junaid ya jinjina kansa suka jera tare da nufar masallaci sosai Junaid da Khaliperh sukai mamakin ganin Burhan a masallacin kusa da Baffa sahun farko har aka idar kuma basu ce komai ba. Baffa ya gai da yayansa yaran suka gaida shi Burhan dake ɗan janye jiki ya ce "Barka Abba"


"Yawwa Burhan" Burhan bai kalli inda su Junaid suke ba ya yi shigewar shi cikin gidan da mamaki Abdallah ya ce "Baffa me wannan yake a gidanmu kuma?"


Cikin ko in kula Baffa ya ce "Nina kira shi?" Ya faɗa fuska a kame ba alamar wasa suna shigowa parlour suka samu Zainura tsaye ita da Mami suna kallon tafkeken frame ɗin ƴan ukun wanda aka maƙala a main parlour gabaɗaya bata lura da Burhan dake zaune saman kujera ya zubawa bayanta idanu hatta Mami bata lura dashi ba Zainura ta ce "Mami yaran waye waɗannan don Allah i love them wallahi" Mami ta zubawa yaran idanu musamman na tsakiya ta juya ta kalli little Bilal ta ce "Waya saka frame ɗin nan?" Zainura ta ce "Ni ma a haka na gani kuma akwai a ƙaramin parlonki ma akwai ana Baffa" Kafin Mami ta yi magana sun ji sallamar Baba ƙarami cikin sauri Mami ta shiga part ɗinta domin babu ko mayafi jikinta Zainura ce ta uzzura mata ta fito. Baffa ya dubi ƴar rigar dake jikin Zainura iya qwwia cikin sauri ya ce "Zainura wanne shirme ne nan za ki fito haka?" Ta yi narai narai da idanu ta ce "Baffa naga dama haka nake zama" ya lura dai ba zata fahimta ya nuna mata hanyar part ɗin babarta ya ce "Leave" wajan ta bari cikin sauri Burhan daman tuni ya ɗauke ya fara danna wayarsa da bai jima da siya ba sbd zaman shagon kati da yake yi yanzu.


_You look so beautiful Zinu, and please save ur dress for me...... I love you_


Tsaki ta yi sanda taga saƙon ta rufe idanu da sauri ta buɗe jin tsigar jikinta na tashi da kuma tunanin Burhan data fara. Mami ta ce "Lafiya?" A hankali ta ce "Ba komai" sai kuma ta miƙe ta ce "Mami nifa babyn nan na tsakiya yana mini kama da little

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login