Showing 108001 words to 111000 words out of 190738 words

Chapter 37 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17309

naki rabon ki saka albarka"


Ta kalli abinda ya bata ya ce "all this for?"


"Idon matambayi ki yi addu'a na ce"


Fita ya yi ya bawa Ammi itama da Junaid ya ce duk su yi addu'a abin farin ciki ne Ammi ta yi, ta yi ya faɗa mata ya yi shiru


Junaid ya ce "Ki yi addu'a kawai Ammi"


Baba ƙarami yana zaune fuskarsa ɗauke da farinciki Umma ta ce "Wai wannan tulin alawar ta mece?"


"Ta abin alheri ce mana sai da kika shanye za ki tambaya?"


Ta share ta ce "Ina buƙatar ɗana kusa dani na fara gajiya da wannan tsarin a gaskiya zan je wajansa, ni ina kan ƙudirina wallahi tallahi bana ƙaunar a haɗa mini yaro da wannan yarinyar tunda bata da halacci gabaɗaya na tsane ta a nemo ko wace a bashi da ita wallahi idan kaga an yi auren sai dai idan bana numfashi"


Bai kulata ba yana ta murmushi "Ina magana ka mayar dani sauna?"


"Bani da lokacinki ne Hadiza"


Farin cikin da Hajiya ta yi na ganin Ridayya ya ɓaci ta rasa inda zata saka kanta don farinciki ashe zata sake ganin wani nata? Jikinta kai Allahamdulillah komai ta ce jikata Mai ran ƙarfe ya dinga murna. Ridayya ta yi farin ciki sosai bayan ta huta ta ce "Granny ɗan bani aron wayarki"


"Riƙe ƴar'nan na baki ita duka ma" number Sadauki ta kira yana ɗagawa ta miki a hankali ta ce


"Sahibi"


Ya sauke ajjiyar zuciya ya ce "Na azabtu Shanshan don Allah kar ki sake mini haka karki hukuntani ta wannan hanyar"


"Ka yi haƙuri"


"Uhm kina ina?" Ta faɗa masa sosai ya yi mamaki "ki tura mini address via email, zan zo gobe"


"A'a mu yi waya ba sai ka zo ba" cikin zafin rai ya ce "Yakike so na yi? Har yanzu ba ki amsa mini ba, kina so na ko a'a kin guje mini kuma yanzu ki ce kar na zo what do you mean by that eh?"


"Shikenan zan tura maka" Ya sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya a hankali ya ce "I'll call you later"


"To" cikin wata kalar murya yana sauke mata numfashi ya ce "I love you Shanshan, i love You till the end of my life, i love You to square of infinity mu'aaah"


Da sauri ta kashe wayar jikinta na amsawa tana rufe Idanu.


Duk suna zaune a parlour tun bayan dawowarsa bai fito ba sai yini cikin bedroom da ƙyar ya samu ya fito ya zauna saman kujera ya rufe Idanu abubuwa sun masa yawa Hajiya ta ce


"Ango ango kaga ango mijin amarya" Ya yi saurin buɗe idanu. Kafin ya yi magana Mardiyya ta fito daga wani part sanye da lemon ɗin lace sai baza ƙamshi take ta kafa ɗauri tana taku ɗaiɗai. Lokaci guda Ustaz ya haɗe rai ƙasa-ƙasa kuma yake kallon Mardiyya ɗin


"Barka da gida Hajiya"


"Yawwa Mardiyya kin fito ya gajiyar hanya?" Ta yi murmushi kawai ta nemi waje kusa da Ustaz ta zauna cikin iyayi ta ce


"Na shiga dubaka kana baccin gajiya, ya hanya Yallaɓai?"


Ganin wani irin kallo da Ridayya ke yi masa shi da Mardiyya ya saka shi daurewa ya ce


"Lou"


Wata irin zufa ke yanko masa ta ciki tashin hankali ya bayyana daga ta cikin zuciyarsa me Hajiya ke nufi? Me ya kawo Mardiyya gidan nan?. Ridayya kuma cike da mamaki take kallon Mardiyya daman ita Abbiey ya aura ya rasa wacce zai aura sai aminiyarta? Ita Mardiyya za ta ci amana kenan don ta ce ta je ta auri Abbiey ɗin shi ne ta aure shi? Wani irin ɗaci ta ji a ranta har wani duhu take gani a idanunta.


"Barka da hanya ƙawata aminiyyata kuma ƴata ya rayuwarki kuma?"


Miƙewa Ridayya ta yi daidai nan suka haɗa Idanu da Ustaz ta auna masa wata harara idanunta cike da ƙwalla ta yi cikin ɗaki. Tana barin wajan ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa, Hajiya ta bishi ta wassafa masa komai da yake faruwa.


"Ba ki kyauta mini ba, kin haɗa ni da aiki duk abinda na yi wallahi zunubi a kan ki"


Ta riƙe baki ta ce naga kana ƙifta Idanu kana girgiza kai "Ohho maka aure dai an ɗaura nan da wata tara na ji kukan jariri ai nasan ƙarya kake lafiya lou kake"


"Sai ki je ki yi mata cikin ai"


Ya shige toilet abinsa. Washegari da safe Hajiya ta ce Ridayya ta je ta kira Ustaz ya yi breakfast. Gudun faɗa yasa ta miƙe ta nufi ɓangarensa tana shiga ta ganshi tsaye a gaban madubi ga Mardiyya a gefe. Ganin Ridayya ya saka Mardiyya saurin rungume Ustaz ta ce "Abbiey ka bari na zaɓa maka kayan sawa"


Ai gabaɗaya maganar Ridayya ta maƙale jikinta ya ɗauki rawa ta yi saurin juyawa Ustaz ya kalli Mardiyya ta yi saurin sakinsa wani irin kallo mai kama da “Last warning”


Bayan ya gama shiryawa tsaf ya nufi bedroom ɗin Ridayya da niyyar tambayarta abubuwan da suka faru da yadda akai ta haɗu da Tajj. Yana shiga ya ganta tamkar mahaukaciya tana zaune a saman gado gashinta ya sauka har baya ta ci kuka son ranta ga Little nata kuka taƙi kula shi.


Ya kasa magana sai tsayawa da ya yi kawai a kanta ƙamshinsa da ta ji ya saka ta ɗago idanunta, ganinsa ya saka ta ji wani irin abu yarr a jikinta ta miƙe tsaye zata shige parlour ya ɗan sha gabanta


"Ina kwana?"


Bai amsa ba ya saka hannu ya tallafo haɓarta yana ƙare mata kallo sosai kafin ya ce "Kukan na mene?" Ta kasa magana sai kawai ta rushe da raunataccen kuka gabaɗaya ta nufi kan Ustaz shi kuma ya ɗan yi baya tana zuwa ta faɗa jikinsa kamar yadda ta saba a baya ta ƙanƙame shi tana wani irin kuka kamar ranta zai fita kuka take da dukkan zuciyarta da ƙarfinta wani irin kuka take wanda bata taɓa yinsa ba a rayuwarta, kuka take wanda ko sanda aka ce su Baffa sun mutu ba ta yi irinsa ba, har wani irin shiɗewa take jikinta na rawa da karkarwa babban tashin hankalinta bai shige zunubin data aikata ba ko rufe Idanu ta yi tana hango ranar data bawa Zameer kanta.


"Abbi..... Abbiey" Ta kasa magana tana neman zubewa a ƙasa saboda yadda jikinta ke rawa magana take son yi ta kasa ta haɗa zufa shi kansa Ustaz sai da ya ji tausayinta.


"Ka yafe mini Abbiey don girman Allah ka ya....," Maganar ta tsaya sanda ta sake fashewa da kuka gabaɗaya ta ɓata masa farar shaddarsa he could feel yadda hawayenta ke sauka a jikinsa.
Ya riƙe ta da kyau bashi da wani zaɓi dole ya bata damar kukan ko hakan zai sanya ta ji sauƙi


"Abbiey an ce ni mayya ce an ce bani da gata" Ustaz bai san lokacin daya rungumeta a jikinsa ba idanunsa ya yi wata kala ƙirjinsa na buga ta yi luff tana kuka sosai "Da gaske mayya ce ni Abbiey?"


"Shhhh" ya faɗa daidai kunnenta yana ɗan bubbuga bayanta, Ridayya ta juya fuskarta tsakiyar ƙirjinsa da sauri Ustaz ya ce "Ya Rasulullahi Manzon Allah.....






Karku yanke hukunci sai an sauke littafi
*MUNAFUKIN MIJI 32*
Mikiya Writers Ass..


Bright pens free batch
Nimcyluv




Ustaz ya girgiza kai ya kama hannunta suka zauna bakin gado, har lokacin kuka take ta ɗora kanta a ƙafarsa tare da zamewa zuwa ƙasan carpet, sosai take kukan ta riƙe ƙafafuwansa gani take kamar zai gudu ya sake barinta rashin gatan ya tabbata a gare ta.


Sai da ta yi mai isarta ta fara sauke ajjiyar zuciya nan da nan kanta ya fara ciwo ta ɗaga kai ta kalli Ustaz shi ma ita yake kawai yake kallo.


"Kin gama?"


"E, ina jin kamar na yi ta kuka" ya miƙe tsaye ya nufi wajan fridge ruwa mai sanyi ya ɗakko ya ɓalle murfin gorar ya dawo ya miƙa mata yana mai sake zama inda ya tashi.


Ta tsare shi da idanu dukda gefen fuskarsa kawai take kallo. Ruwan ta sha sosai kana ta ajjiye tana sauke ajjiyar zuciya mai nauyi.


"Ki kwanta, bacci ko za ki ji daidai"


Ta girgiza kai tana ƙoƙarin sake ɗora kanta a ƙafarsa ya zame yana kame fuska ya san tuni ta saba, ko bacci wani lokacin a kan ƙafafuwansa take yi, ta ɗauke shi uba, aboki, uwa, amini bata shakkar faɗa masa komai da zama a duk yadda ta so idan yana wajan.


"Abbiey magana zan yi maka"


"Ki kwanta"


"Ko na kwanta ba zan iya bacci ba, ka bari na faɗa maka ka ji" ta ƙare maganar tana marairaice fuska ta ɗan tura bakinta gaba. Jinjina mata kai ya yi ta sauke kan ta a ƙasa


"Abbiey don Allah yau ɗaya ka faɗa mini me ya sa Baffa da Mami basa so na? Me ya sa Mami take son Zainura ni bata so na, me ya sa Baffa yake son kowa ni ban dani, me ya sa nake amfani da sunanka a makaranta maimakon na Baffa? Me ya sa kuma kowa na gidanmu fari ne ni kuma baƙa mummuna? Me ya sa ko a makaranta kowa ke guduna? Me ya sa mutane suke cewa ba zan taɓa samun mijin aure ba saboda ni mummuna ce ina da manyan idanu, da babban leɓe kuma ina da jiki da gashi me ya sa fatata take maiƙo kamar an shafa mai? Me ya sa kowa baya sona kowa yake guduna kai kuma kake so na Abbiey?"


Ustaz ya yi shiru ta ce "Ka faɗa mini mana kamar na so na gane"


"Ustaza ba za ki gane bane, ki na ta harbo tambayoyi"


Ya miƙe ya nufi gaban madubin ɗakin da hannu ya nuna mata ta zo, tana zuwa ta yi ƙoƙarin jingina da jikinsa ya yi saurin zamewa kan hakan ya faru ya yi baya ya nuna ta tsaya gaban madubin a hankali ya saka hannu ya yaye labulen gabaɗaya suka fito a cikin madubin tana gaba yana baya da ta zara


"Bani za ki kalla ba, dubi kan ki sosai"


Ta ƙura wa kanta Idanu dan baƙi da gaske ita ɗin asalin baƙar fata ce, asalin Bahaushiya ƴar'hausawa cikakkiya kuma. Idanunta farare tas sai dugwayen gashin Idanu har kwanciya suke, girarta a haɗe suke sai yalwar gashi gaban goshinta ma haka, lips ɗinta su ba jaa ba kuma ba pink ba sun yi wani colour yirrr da su ɗaya ƙarami ɗaya mai ɗan faɗi ya bada wani shap tana da Oval face kawai tsananin baƙi da duhun fatarta ya saka ake ganin muninta.


Ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Na gani ni dai ban gane ba"


"Ki gode Allah ki gode Annabi irin ku, ku ne ya yi yin zamani. Farin mutum har abada ba zai iya komawa kalar fatarki ba, ke kuma kina iya komawa fara idan ba ki gode Allah da irin zubin halittar da ya yi miki ba...," Ya sauke numfashi yana ɗan hutawa.


"Idan kowa baya son ki ai ni ina son ki ko?" Ta yi shiru ya ce "Idan Allah da kansa daya halicce ki ya samar dake a duniya yana son ki kuma ya amince da ke to babu damuwa kowa ma yaƙi ki, mutanen ƙwarai Ubangiji yafi jarraba imaninsu Ustaza ki kasance mai haƙuri da gode Allah da ni'imar da ya yi miki. Mutane da yawa sun lalace da yi wa mutum ba'a na daga halittar da Ubangiji ya yi masa, amma tunda kike kin taɓa ganin mutum ya yi halitta?"


Ta girgiza kai ya kalleta ta madubin ta yi saurin cewa "A'a"


"To bai kamata ki yi fushi ba, yin hakan kamar kina nuna rainuwa ga Allah da nuna masa bai iya halitta ba, ki saka a ranki ke mutum ce kamar kowa mai tarin marudai wanda kike shirin cimma, ki yi ƙoƙarin bawa masu faɗar hakan kunya, ki zama mai ƙwatarwa kan ki ƴanci a ko'ina kar ki bari a wulaƙantaki kuma kar ki wulaƙanta kowa, Allah da kansa ya ce wáakaramna bânii adama"


"To idan mutane sun guje ni me ya sa su Baffa za su yi mini haka?"


"Ki manta da abinda ya shige, mutanen kuma da basa raye wanne ƙorafi Ustaza? Ki yi addu'a ki yafe musu ki zama mai uzuri"


A sanyaye idanunta na cika da sabbin hawaye ta ce "Allah ya jiƙansu da rahma na so ko sau ɗaya Baffa ya kira ni da sunan ƴa, ya saka mini albarka kamar su Zainura su Yaya Khaliperh"


Ustaz bai sake kallonta ba ya fara shirin barin wajan ta ce


"To baka faɗa mini me ya sa kai kake so na?"


"Ban sani ba"


"Ina son sani Abbiey


Dole ya kai Ridayya a duba lafiyar tunaninta da kyau domin yana kokwanto ta marairaice sosai "Ka faɗa mini"


"Saboda you're lovely ke bar so ce"


"To ni da matarka wa ka fi so? Kuma me ya sa ka aureta maimakon wata? Abbiey ka taɓa ce mini aure ba dole bane daka haƙura"


"To ni dai ina son matata"


Sai kawai yaga ta fashe da kuka sosai tana cewa "Amma ba zata haihu ba ko?"


"Ke za ki haifa mini idan ita bata haihu ba? Idan kin yarda duk shekara za ki bani baƙaƙen yara kamar ki to"


"Ga Little na baka kyauta, kuma me ya sa Little yake fari kyakkawa kamarka?"


"Saboda abin cikin ƙwan ya fi ƙwan daɗi, Little ya mini kaɗan zuri'a nake so mai yawa kinga da gani sai ke muka rage sai ki yi ta haihuwa, idan kuma ba zaki haifa ba nan da wata tara za ki ga Mardiyya ta haifa mini"


Wani abu ta ji ya tukare mata zuciya kanta a ƙasa ƙirjinta na ɗagawa, shi ɗin babanta ne taya zata iya haifa masa yaro wannan ai iskanci ne kawai. "Ustaza ban yi zaton zan sake ganinki ba, bana faɗar abinda ya shige a baya amma kaɗuwar ganinki gidan Mahmah ya kasa barin tunanina, gani nake kamar a mafarki na fita daga gidan saboda tashin hankali da mamaki kuma zan iya abinda bai dace ba, yanzu haka ina ganin kamar idan na rufe idanu na buɗe ba zan sake ganinki ba, ke ɗin ƙaddarata ce tamkar inuwata haka kike ban iya guje miki, ba zan iya zama hankali kwance ban san ya rayuwarki take ke ɗin amana ce. Ban taɓa nunawa Tajuddeen photonki ba balle na ce yana sane ya ajjiyeki a gidansu, a labari dai ya sanki banda kamanni ya akai kika je? Ina mijinki?"


Wani irin miki ne ya taso mata bata ƙaunar tuna Giɗaɗo gabanta faɗuwa yake tana yawan manta abubuwa amma ba zata manta rayuwarta gidan Zameer ba.
"Abbiey shi ɗin MUNAFUKIN MIJI ne, ba don Allah ya aure ni ba, ashe ba ɗan kano bane a Katsina yake ya zo Kano Almajiranci sunansa Giɗaɗo. Baya bani abinci, baya yi mini ɗinki babu magani ba sabulun wanka babu man shafawa, ya kwashe kayana ya siyar ya ce aiki ya samu da yake buƙatar kuɗi, ashe caca yake yi komai nawa ya siyar ya sace wayata ya siyar ya sace atamfofina ya siyar, na yini na kwana banci abinci ba baya barin kowa zuwa gidana baya barina fita, lefen da ya yi mini ashe na haya ne ranar da aka kai ni ya saka aka sace su, na fara yin ƴar'tsala mutane suna siya da kuɗin nake cin abinci na siyi omo na kwanka da kuɗin kuma shima yake amfani, duk kuɗin da kake tura mini tura mini shi yake amfani da su. Na yi faskare na dafa masa ruwan wanka na yi masa wanki da guga ya ƙona mini fuska da iron ya karya mini hannu, kuma ya dinga shaƙe ni a wuya idan zai....,"
Ta kasa faɗa haka kurum ta ji nauyin faɗawa Ustaz abinda Zameer yake mata a gado, kuma ta kasa faɗa masa zaman Khairy a gidan tana ganin kamar sirrin aurenta ne wannan ko dan ɗanta Little ba zata tunawa ubansa asiri a wannan ɓangaren ba.


Ustaz ya kasa cewa komai kallonta yake yana jiran jin me zata ce kuma?? Yadda zufa ke yanko masa da yadda jijiyoyin kansa suka tashi kaɗai zai saka mutum yasan ran Ustaz ya ɓaci zafin zuciyarsa ya motsa.


"Abbiey ka yafe mini don Allah kar ka ce na koma gidan Giɗaɗo kashe ni zai yi kuma ya ƙwace takardun da Baffa ya bani please forgive me Abbiey"


Ustaz ya taka zuwa gabanta yana riƙe numfashi ya jima sosai sai kuma ya ce "Ya zama kukanki na ƙarshe, ban taɓa fushi dake ba ya isa haka nan, fatan za ki nutsu ki gane kuskurenki ki buɗe zuciyarki kin san wanda ya dace dake a rayuwa a matsayin miji....,"


"Sadauki Abbiey"


A sama Ustaz ya ji sunan Sadauki shi har ya mance ma, da wani irin expression na mamaki yake binta da kallo gabaɗaya naman jikinsa rawa yake ya kasa cewa komai ya juya tare da ficewa tabi bayansa to me ya sa ya yi shiru kuma?


Fasa fita ya yi ya koma bedroom ɗinsa ya kwanta yana kallon sama tunaninsa ya tsaya cak bakiɗaya ma ya rasa wanne Irin tunani ya kamata ya yi wanne kuma irin tunani ne da Ridayya? Har akai zhur yana kwance Hajiya ta shigo ta ganshi zaune saman ladduma ta ce


"Wai daman kana gidan nan? Babban mutum sallah a ɗaki ban taɓa gani ba"


Ya kalleta bai ce komai ba ta zauna kusa da shi ta ce "Lafiya dai? Meke damunka Babban mutum?"


"Hajiya bani da Nagarta da za a so ni ne? Ko ni ba mijin ƙwarai bane ko ba zan iya kula da mace bane?"


Ta sauke numfashi jikinta a sanyaye ta ce "Injiwa? Wane ya faɗa maka hakan Muhammmmd wallahi kwaɗayin halinka ya saka na karfafa aurenka da Mardiyya, kai ɗin mutum ne mai ƙoƙarin kyautatawa mutane da neman na kansa kuma hakal da zuciyar neman addini riƙon amana da gaskiya, na saba cancanta gaka kyakkawa son kowa ƙin wanda ya rasa ma macen da zaka tunkara ta yi fatali da soyayyarka ka bawa Mardiyya dama ban sani ba ko akwai wacce kake so ka yi haƙuri ka yafe mini na yi kutse a rayuwarka da tunanin na isa na yi hakan ba dan na baƙan ta maka rai ba, tausayin halin da kake ciki nake, ka rungumi Mardiyya hannu bibbiyu"


Daidai nan Mai ran ƙarfe ya shigo.


Ustaz ya riƙe hannun Hajiya da kyau ya ce "I was depressed, ƙofar da kuka saka a ɗakina bai wa ɗakin kyau ba, ba haka na tsara ba kada ku saka na zama mai karya alƙawarin zuciya"


Hajiya da Mai ran ƙarfe suka saka Ustaz tsakiya domin suma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login