Showing 117001 words to 120000 words out of 190738 words
Chapter 40 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt
daku idan na tuna ina son rayuwarku ta yi kyau sai na dage wajan aiki" Ya ƙare yana shafa hannun Asabe reza.
"Ka yi haƙuri Prof na san kana ƙoƙari shi ya sa bana damuwa da rashin kwananka gida ka shiga maganar" ya rausayar da murya ya ce
"Oh ni ke haukana bama ki damu dani ba Hajja Azizat? Kin san yadda na yi kewarki kowa? Sadauki yau zai dawo babu abinda zai same shi"
Wani sanyi ta ji ta saki jiki ta fara masa ƴar shagwaɓa ya ga ji ya fara hura iska "Hello Hello wifey network problem zan kira ki"
Ya kashe wayar yana jan Asabe reza ya mance da batun Sadauki. Hajja Azizat ta yi murmushi ta ce "Allah sarki My man neman na kai akwai wahala Ubangiji ya dafa maka ya baka wannan kujerar ta Ɗan'majalissa"
Cikin dare Sadauki ya shigo da wani irin mugun ciwon kai yana shiga ya nufi wajan Mother tana ganinsa gabanta ya faɗi kafin ta yi magana ya zube gabanta "Mother ina buƙatar Shanshan ku nema mini aurarta kafin zuciyata ta samu matsala"
"Subuhanallahi wacce irin matsala ni ƴar nan, bari Prof ya dawo in sha Allah za a je a nema maka aurenta ai mahaifinka ba ɓoyayye bane suna yin bincike na tabbatar za su baka aurenta" Ya sauke ajjiyar zuciya "Yaushe zai shigo? Yana wanne office ɗin?"
"Ban san wanne office ɗin yake ba, tunda secretary ya tura masa pictures ɗin sabbin kayan da aka kawo musu ya fita amma na tabbatar a gida zai kwana. Ai yarinyar na son ka ko?"
"Tana so na sosai, zan jira har ya shigo"
Sadauki ya kasa bacci kansa a cinyar mother ko ruwa yaƙi sha tun yana duba lokaci har bacci ya ɗauke shi a ƙasan carpet wajan ƙarfe 3 na dare.
Ustaz ya kasa yarda iyayensa ne a gabansa wani irin daɗi da sanyi ya ratsa zuciyarsa da yana da ikon tashi da tuni ya yi hakan ya dinga kallon Baba ƙarami da Umma ya dawo ya kalli Baffa da Mami da Junaid da sauran yaran amma ko inda Ammi take bai kalla ba ya runtse idanunsa da sauri kuma ya mayar da abinda yake ji suna taruwa a idanunsa "Allahamdulillah!"
"Allah shi ne abin godiya Babban mutum ai ba zaka taɓa mutuwa ba muga zuri'arka ba"
"In sha Allah akan wata ba zai taɓa mutuwa ba, sai naga jikokina sai naga yaransa shi da Mardiyya kyakkawar yarinya kuma budurwa"
Mardiyya ta yi murmushi tana sake gyara zamanta a gadon da Ustaz yake, rigar asibiti ce a jikinsa ƙafarsa biyun duk a ware an saka masa abu a tsakiya. So yake ya tambayi Ustaz amma ya kasa a yaransa yana tunanin ko haka kurum taƙi zuwa wajansa.
"Yadda Babban mutum ya farko Allah ya sa Ridayya ta farka abu kwana uku? Shiru" zuciyar Ustaz ta buga ya kasa cewa komai. Bayan ganin jikin Ustaz ya buƙaci a bashi waje zai gana da likitan da ya yi Ridayya gwaji.
Dr ya numfasa ya ce "Bari na fara yi maka bayani. Neurology: wannan ɗaya daga cikin ɓangaren likitanci ne wanda ya keɓanta da cututtuka kaɗai. Ita kuma Nervous system wata hanyar sadarwa ce wanda take kula da aiwatar da aikin jiki na motsi da ji (Sensation) da tunani (Thought & emotion). Nervous system ta ƙunshi kwakwalwa da ɓargon ƙashin baya (Spinal cord) da kuma dukkanin sauran jijiyoyin da suka haɗa da sauran jiki da kwakwalwa ko ɓargon ƙashin baya. Ga kaɗan daga cikin ire-iren cututtukan da ya shafi Neurology"
Buɗe system Dr ya yi Ustaz na binsa da idanu yana jin tsoron abinda zai ji na game da binciken. Dr ya ce "Ciwon kai mai tsanani (Migraines & headaches) farfaɗiyya (Epilepsy & Seizures) da kuma rashin iya sarrafa gaɓɓai yadda ya kamata (Cerebral palsy). Yawan karkaɗuwar hannu, ko ƙafa ko kai (Parkinson's disease). Ciwon tsufa wanda yake sabbaba ko na ce haddasa mantuwa da ruɗani tare da rikicewa (Dementia ko Alzheimer's disease). Shanyewar wani gaɓa (Stroke) Jin tsananin zafi a hannu ko ƙafa tare da sauran cututtukan jijiyoyi (Neuropathy and nerve damage)......,"
Dr ya yi shiru yana kallon Ustaz ganin ya rufe idanu a hankali ya ce "Continue"
"Naga ai kamar bacci kake ne" Ya girgizawa Dr kai alamar “A'a” Dr ya ɗora da faɗin.
Cututtukan da suka shafi kwakwalwa kamar zubar jini a kwakwalwa (Brain hemorrhage) ko kuma dajin kwakwalwa (Brain tumor) waɗannan cututtukan ana kiran su da “_NEUROLOGICAL DISCORDERS_” sannan kuma waɗanda suka shafi kwakwalwa kawai a kira su da BRAIN DISORDERS. A wasu lokuta likitan daya ƙware akan yin fiɗa a ɓangaren Neurology Neurology wato Neuro-surgeon ya kan yi tiyata wato ya buɗe kwakwalwar mara lafiya domin magance matsalar dake damun sh. Daga bayanin da na yi maka zaka fahimci Neurologist shi ne asalin likitan kwakwalwa da ɓargon ƙashin baya da kuma jijiyoyi. Shi kuma Psychiatrist shi ne likiyany ciwon halayya da ɗabi'un Ɗan Adam (Mental Discorder). Sauran sunayen da za a iya kiran Mental Discorder sun haɗa da Mental Illness, Psychiatric Disorder da Psychological Disorder. Yanzu zan maka bayanin menene Mental Health da Mental Discorders Yadda za kafi fahimtar matsalar ƴar taka"
Dr ya sauke numfashi domin bayani ne mai wahalar ganewa kuma sai ka jima da mai irin halayyar baka san yana da matsalar kwakwalwa ba ya ce "Mental Discorder yana nufin tattarawar wasu alamomi waɗanda suke iya jirkitarda yanayin da mutum yake tsinkayan abubuwa da kuma yadda yake tunani da mu'amala da mutane. Irin waɗannan alamomin suna saka mutum ya shiga cikin matsanancin damuwa (Subjective distress) Sannan kuma suna janyo matsala ko nakasa (Impairment) a game da yadda mutum yake mu'amala da iyalin shi ko ƴan'uwansa a gida da abokan aiki ko kuma abokan karatunsa (Pervasive) Irin waɗannan alamomin za su iya jimawa mutum yana fuskantar su (Persistent) ko kuma a wani lokaci sai su zo gadan-gadan kamar saukar ruwan sama (Relapse) daga baya kuma sai su yi likimo kamar an yi ruwa an ɗauke (Remission) a wani lokacin ma su tsaya cak (Single episode)"
Dr ya yi shiru ya ce
"Manyan abubuwan da suke kawo Mental Discorders sun haɗa da Gado (Genetics) yanayin muhallin da mutum ya taso (Environment) ɗabi'un yau da kullum da aka ɗora ko gina mutum akai (Daily habits) da kuma yanayin halittar mutum (Biology) ko kuma yawan ƙarancin sinadarin kwakwalwa (Neurotransmitters) da kuma yadda suke aiki (Brain Chemistry) da kuma Shaye-shaye (Drugs) irin waɗannan Neurotransmitters ɗin sun haɗa da Serotonin (OCD) Dopamine (Schizophrenia, ADHD) da kuma Norepinephrine (Anxiety Disorders) da kuma sauran Brain Disorders ba waɗanda ake iya gano su ta hanyar yin gwaje-gwaje a asibiti kamar MRI ko CT scan har ila yau babu tabbatacciyar gwajin asibiti da ake iya yi domin gano Mental Discorders. Waɗanda suke da alhakin gano hakan sune Psychiatrist, Psychologist da kuma Clinical social worker amma an fi so Psychiatrist ya ja ragamar binciken duk wani Mental Discorders ciwon kuma shi ake kira da Mental Health Professionals"
Ya rufe system ya ce "Kai kake tare da mara lafiyan yana da kyau ka gaggauta zuwa wani likita domin a tattauna da ita da iyayenta da yin sabon gwaji amma nawa binciken tabbas ta jima tana shan kayan maye kuma ta rasa sinadarin kwakwalwa tun tana jaririya maybe ta hanyar jijjiga ko wani abu, dole zata dinga ganin abu somehow abinda yake daidai a rashin daidai zata ganshi na kuskure kuma a daidai zata ganshi zata dinga yawan mantuwa musamman abu mai muhimmanci, kuma kwakwalwarta ta samu shock na ganin wani mummunan abu ko ana tilasta ta yin abinda bata so wannan shi ne nawa binciken"
Ya miƙe Ustaz ya miƙa hannunsa mara ƙarin ruwa ya ce "Thank you Dr na gode da zuwa da kuma bayani zan kira ka"
"My responsibility Allah ya bata lafiya kai ma haka"
Dr na fita Ustaz ya sauke numfashi mai zafi ko Ridayya bola yake bi shi kam zan iya rayuwa da ita dukda yanzu wani irin zafinta ya ke ji rai amma dole ya yi mata uzuri ya buɗe mata dukkan zuciyarsa ya bayyana mata abun a fili ya kuma shayar da ita abinda ta rasa kuma take buƙata.
Da sauri Baba ƙarami ya shigo ya ce "Babban mutum maza ta so Ridayya ke kiranka ta yi suma babu adadi sai buga kanta take tana kiran Abbiey" ba zai iya tashi ba saboda aikin da akai masa a mara amma haka ya fisge ya tashi nan da nan jini ya fara bin ƙafafuwansa
"Wallahi ko ƙofar waje ka fita ni da kai ne ta mutu mana wallahi ka fita domin ganin wata Ridayya sai na yi maka Allah ya isa" Umma ta faɗa tana kumfar baki Mardiyya ta shigo haka Dr ta Junaid da Baffa hankali tashe domin yanzu likitan ya gama yi musu bayanin matsalar Ustaz
"To a kan me yaro da matarsa a tsiri liƙa masa bazawara kuma baƙa ban shirya ganin munanan cikoki ba"
Baba ƙarami ya ce "Ba kuma za ki taɓa ganin jikokin ba har abada"
"Wallahi gani kamar na gansu domin ina zargin Mardiyya ciki gare ta, idan kaga Muhammmmd ya auri wannan yarinyar sai dai idan mutuwa na yi kuma ko mutuwa na yi bashi da matar data shige Mardiyya"
Baba ƙarami ya ce "Ko? Bari mu gani idan soyayyar gaskiya take masa ita Mardiyyan domin har abada Ustaz ba zai iya tarayya da ko wacce mace ba a duniya kuma ba zai haihu ba, sakamakon faɗuwar da ya yi mararsa ta sauka akan dutse wannan jinin da kika gani yana bin ƙafarsa to aiki akai masa amma ba a yi nasara ba shi da mace dai dai kallo, kuma abinda baki sani ba Muhammmmd and Ridayya they're couples husband and wife suke kamar dai ni dake, tun a Kano kika sha alawar ɗaurin auren Muhammad-Bilal Tahir Rano da Ridayya Muhammad-Bilal Tahir Rano yanzu Ridayya matarsa ce hallaka ɗinsa halinsa ce....
Idan an karanta ayi comment a kuma danna sharing🤓🧚🏻♀️
Na'ima Sulaiman Sarauta
Nimcyluv
08164069385
*SARAUTA CHARITY FOUNDATION*
TAIMAKO DOMIN ALLAH
Allhamdulillah! Kamar yadda mu kaga azumin daya shige lafiya gashi muna ƙoƙarin ganin wani da izinin Allah. Mun saba yin taimako domin Allah ga mabuƙata musamman Almajirai, nakasassu da wasu bashi da shi. Duk azumi muna yi musu abinci, ƙosai, kunu da ruwan sha mai sanyi. Yanayin rayuwa ya sauya jama'a sun ƙaru gari kuma ya yi zafi abinda muke da shi a Account ba zai isa mu yi abinda muka saba.
*KIRA GA JAMA'A*
Akwai wanda suke da halin bada ko dubu ɗari, wasu kuma ƙarfin hali, akwai ƴan'kasuwa da ma'aikta maimakon ƙarawa mai ƙarfi ƙarfi, mai zai hana ba zaka taimaki mara shi ba. *SARAUTA CHARITY FOUNDATION* Na neman taimakon Al'ummar musulmi mai 500, 1000 har 200 zuwa abinda Allah ya baka su bayar domin a ciyar da mutane a cikin watan Ramadan. Ana saka alheri da alheri wannan alherin ranar ƙiyama za kaga samakonsa muna buƙatar yin abincin mutum 100 a kullum dole sai jama'a sun saka mana hannu😰🥰
Target: Target ɗinmu 200k ne yanzu muna da 20k da wani bawan Allah ya tura jiya ga wanda ya shirya taimako domin Allah ga Account number
6850917335
Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank
Ko kuma
8164069385
Na'ima Sulaiman Shu'aibu Opay
Ku yi zuwa ga ƴan'uwa da al'ummar Musulmi🥰🥰🥰 Allah ya haɗamu a ladan ya biyawa dukkan wanda ya taimaka bukatunsa na alheri.
*MUNAFUKIN MIJI 34*
Mikiya Writers Ass..
Bright pens free batch
Nimcyluv
Jikin Ustaz ne ya ɗan fara rawa, ya yi baya kamar zai faɗi Junaid ya tare shi jin maganar ya yi kamar tatsuniya, ta sauka a tsakiyar kansa baya son gasgata abinda ba haka bane, abinda kuma ya fid da rai da samun shi. Ko shakka babu an faɗa ne kawai domin ganin matakin da Umma zata ɗauka. Zuciyarsa ce ta ci-gaba da matsewa a ƙirjinsa komai nasa na ƙoƙarin tsayawa zafin da ƙirjinsa yake masa ya danne wanda yake ji a mararsa dukda jinin dake bin ƙafafuwansa saboda miƙewar da ya yi tsaye.
"Ka samu nutsuwa Babban mutum, take heart please"
Junaid ya faɗa yana zaunar da shi saman gadon amma ya ƙi kwanciya bakin Baba ƙarami yake kallo yana son sake jin maimaicin furucin koda a sigar wasa ne.
Umma dake tsaye ta ce "Ohho dai batun aure abu ne wanda ba zai taɓa faruwa ba idan ina raye, ko ya aureta wallahi sai ya saketa tunda shi sakarai ne mai san ƙima da darajar da Ubangiji ya yi masa ba, ya zauna ya lalace akan wata yarinya ƴar cikinsa ma bazawara raguwar wani mai haihuwar yara biyu, baƙa mummuna a yadda ta saka a garari wallahi itama sai ta shiga" Ta yi ƙwafa sosai zuciyarta na yi mata zafi idan ta tuna yadda Ridayya ta watsar da Ustaz a kan wani, ta saka ƙafa ta shure duk wani gata da kulawa da yake mata bayan shi ne ya mayar da ita mutum mace kamar kowa amma abinda ta zaɓi ta saka masa da shi kenan.
Ta ɗora da cewa "Ka yi zaton ban san komai ba ko? Yarinyar daka kusa mutuwa a kanta sanda ta ce bata son ka, ka zauna tsayin shekaru 42 zuwa 43 yanzu babu aure bayan Ubangiji ya baka ikon auren mata huɗu ka liƙi a ɗaya? Ɗayar ma wacce iyayenta basu nuna mata gata ba, ɗayar ma wacce ake tantama a kan waye ubanta.....,"
"Shut up! Saurara ya isa haka. Me kike nufi?"
"Ina nufin abinda ka ji mana Alhji Tahir? Ba Alhji Mansur da kansa ya ce ba shi ne ubanta ba, ba shi ne ya haifeta ba ai wanda ya mutu shi a kewa ƙarya, na gode kuma saboda duk kuna wajan hakan ta faru"
Baffa ya rasa abinda zai ce bai taɓa yin ladamar abubuwan da suka faru ba irin yanzu, ya san ya yi kuskure ya shafawa Ridayya baƙin fentin da ba zai taɓa gogewa ba, ya ɓata career ta da kansa a matsayinsa na uba. Ustaz ya runtse idanunsa tare da tsune leɓensa na kasa ba tare da tunanin har ya fashe ba, sai da ya ji ɗanɗano ya fahimci jini ke zuba a lips ɗin na shi a tsakiyar ƙirjinsa ko wanne kalamai na Umma yake sauka bai taɓa zaton akwai ranar da Umma za ta ƙi Ridayya ba ko taƙi abinda ya nuna yana son kasancewa da shi.
Jijiyoyin kansa duk suka fito waje suna har bawa da fallasa raunin zuciyarsa da ƙyar ya cira idanunsa ya kalli Mardiyya dake tsaye tana jin yadda ake ciwa Ridayya mutunci ta samu lasisin yi mata gori.
"Keee" ya ce a wahale yana lumshe idanunsa ta kalle shi cikin yauƙi ta ce
"Ruwa za a baka?"
"Out!" Ya faɗa yana nuna mata hanyar waje alamar ta fice kuma sai runtse idanunsa yake yana dafe kansa wanda yake ji kamar zai cire.
"Da kai da out ɗin kun ci gidanku na bi out da gudu ban tsaya ba, matarka ce ta sunna kuma budurwa wacce bata taɓa haihuwa ita ce daidai kai ita kuma nake da burin ka zauna da ita har abada"
Wata dakakkiyar tsawa Ustaz ya dakawa Mardiyya da gudu ta fice jikinta na rawa don ta ɗauka dukanta zai yi shi da kansa tsawar ta bashi tsoro ya yi baya yana jingina da frame ɗin gadon idanunsa lumshe kaɗaici yake so ya samu da zuciyarsa.
Bayan fitar Mardiyya Baba ƙarami ya kalli Umma ya ce "Kin kyauta kuma kin yi yadda kike so, amma hakan ba zai hanani yin yadda na so ba, kece uwar Muhammad nine ubansa kina son Mardiyya ina son Ridayya domin jinina ce, ko babu aure ta zame wa Babban mutum dole hakƙinsa ne na kulawa da ita. Sai dai kin yi a banza domin sara da sassaƙa baya hana ganji toho, kamar yadda Mardiya take matarsa haka Ridayya take matarsa ta sunna babu mamaki ya zama na ita ce uwar gida domin idan aka bincka nata auren aka riga ɗaurawa"
"Can ta matse muku da kai da masu ɗaurin auren, da munafukar uwarta data goyi baya. Ko a cikin hadisi an ce ka bi uwa har sau uku kana uba, maganata kamar yankan wuƙa haka take a kan Bilal, ba shawara nake bashi ba umarni ne kuma zan ga wanda zai tilasta ya zauna da wata bazawara muguwa butulu wacce bata san halacci ba, balle ban yarda an ɗaura auren ba I'll never accept her as my daughter-in-law"
Tana faɗin hakan ta fice daga room ɗin, Baffa ya bita da kallo yana jin haɗin da sukai na neman sare masa tunda yana ƙoƙarin taɓa zumunci kuma ahli ɗaya. Kasa cewa komai ya yi sai ficewa daga room ɗin ya koma wajan Ridayya yaga halin da take ciki. Junaid ya kalli Ustaz da jikinsa har yanzu rawa yake ga wani irin zafin zazzaɓi dake farmakar shi a hankali ya ce
"A kira Dr Abba"
"Ba Dr Ustaz ke buƙata ba, ka je can wajan Baffa ka kula da ƴar'uwarka Junaid lokaci ne na bata gata da bata dukkan wani support da take buƙata kune yanzu muke buƙatar ku haɗe kan ku, mutuwa bata san inda rai yake ba, bata san inda ciwo yake ko shekaru yake ba, amma mu a kodayaushe ta Allah zata iya kasancewa da mu, kuma Allahamdulillah mun yi wa zumunci hidima dukda bamu da yawa. Jeka Junaidu maza jeka" Junaid ya miƙe yana jin ƙarfin qiwwa a maganar Baba ƙarami bayan fitarsa ya rage daga Baba ƙarami sai Ustaz da har yanzu idanunsa a rufe suke.
Waje ya nema kusa da Ustaz ya zauna, tare da kama hannunsa ya riƙe cikin nasa lokaci mai yawa basu samu kusanci da ɗan nasa haka ba, rauni irin na uba ya mamaye zuciyar Baba ƙarami ya san zurfin cikin Ustaz tun yana ƙarami mamakin yadda zafin zuciyata ya ragu sosai yake.
"Babban mutum buɗe Idanunka" A hankali ya buɗe sun yi wani irin jirkicewa yanayin da Baba ƙarami bai taɓa gani ba, ƙwayar idanunsa tamkar ba tasa ba, wani irin jan abu ya kwanta ciki tun ɗazo yake ƙoƙarin yin magana sai ya ji tamkar hayaƙi ne zai fito maimakon furuci. Baba ƙarami ya sake riƙe hannun Ustaz sosai a taushashe cikin kulawa ya ce
"Duk inda ake neman jarumin mutum kuma sadauki mai bada farincikinsa saboda wani ya yi murmushi to a nemi jarumin ɗana. Muhammad baka buƙatar damuwa a yanzu ƙarfin qiwwa kake buƙata ka yi haƙuri ka daure abinda kake ji karka bari rauninka ya fito, a wannan karan kar ka