Showing 18001 words to 21000 words out of 190738 words
Chapter 7 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt
farga ya saka hannu ya fisge sauran farcen bata ƙara sanin meke faruwa ba sai da ta ji ana zuba mata ruwa ta sauke ajjiyar zuciya, lokacin ko kuka ta kasa sai jan numfashi ya ce
"Ai suma kikai wai? Ke komai na suma ne kamar mai cutar suma?" Ta cure waje ɗaya saboda bata ƙaunar tsawa sam ya ce
"To ɗoran ruwan tunda Allah ya nufa ba ki shige ƙiyama ba" bata iya cewa komai ba ta ɗora ruwan har ya yi zafi ta juye masa. Lokacin yatsar har ya kumbura.
Cikin bacci ta ji ya ce "Ridayya ke Ridayya" Yana saka ƙafa tare zungurin gutaccen kwankwasonta ta farka a firgice tana "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un don ka yi haƙuri zan dafa ruwan yanzu wallahi zan dafa" Takaici ya cika Zameer ya ce "Au ke nan har mafarkina kike? Saboda ga mugu azzalumi yaushe muka fara haka dake ina soyayyar tawa Ridayya ina zaluntarki ne?" Ta girgiza kai ta ce "A'a mafarki ne kawai da rayuwata" Ya sauke numfashi ya ce "Firfita za ki yi mini har na yi bacci zafi ya addabe ni"
Matsawa ta yi inda ya kwanta ta fara masa firfita bacci na ɗaukarta idan ta yi kamar zata kifa sai ya zunguro ta iska na busa shi a haka har ya yi bacci tana zaune.
Washegari Zameer ya shirya tsaf cikin wata shadda ash ta amshi jikinsa ya fito yana banza ƙamshi tare da murza hula, hannunsa zube cikin aljihu. Ridayya dake tsaye ta ce "Fita za ka yi?" Kai kawai ya jinjina mata bai ma kalleta ba a hankali ta ce "Babu ko hamsin ce na jiƙa kwaki?" Yana yin gaba ya ce "Sai dai ki jiƙani Ridha, neman kuɗi zan fita"
Ta ce "Allah ya tsare ya bada sa a, sharrin mutum da Aljan Ubangiji ya kare ya baka halak Ubangiji ya rabaka da haramun mijina" Bai amsa ba ta ce
"Don Allah kar ka kalli ko wacce ƴa mace ina jin kishinka har ƙasan zuciyata ina tsananin so da ƙaunarka Rayuwata" Zameer shi dariya ma ta bashi mace duk a jeme wai kar ya kalli kowa? Ya saka kai ya fice abinsa.
Kai tsaye wajan cacarsu ya nufa, yana tafiya ɗaiɗai duk ya samu team ɗinsu suna zaune A.y ya ce "Ango mijin Ridayya bada kanka a sare ka je gida kace ya faɗi, wuya ina wuya a gidan Ridayya daɗi a ina daɗi a gidan Ridayya ɗan'gatan Ridayya farin cikin Ridayya shalelen Ridayya kuma rayuwar Ridayya"
"Zan ci ubanka zan ci mutuncin ka A.y" A.y ya sheƙe da dariya sosai ya ce "Amma fa mutuina kaci uwar shadda dole mata su yi crushing a kan ka yarinya ta mace kana da kyau da zubin nagarta sai dai kai shaiɗanin ɓoye ne"
Zameer ya fara jan ajinsa da haɗe fuska. Gaza dake jinsu ya ce
"Zameer akwai caca mai kyau ƙila kana da rabo" Zameer ya ware idanu yana jiran ƙarin bayani, Gaza ya ce "kuɗaɗe ne za a samu wanda mutum da talauci sun yi hannun riga, a ƙalla ba a samu kuɗi ba shi ne miliyan 500 kai fima, mu ma duk mun shiga cacar babbar harka ce" Zameer ya ce "Kai me ka saka naka?" Gaza ya ce "Motata" Zameer ya ce "Na saka gidana" Duk suka zare ido suka ce "A'a banda gida ne idan aka cinyeka ina zaka saka Ridayya ɗin?" Ya ƙanƙance ido ya ce "Babu ruwanku da inda zan saka matata ni dai na shiga caca kuma na saka gidana" gabaɗaya suka amince Zameer ya ji cewa tabbas a wannan karan mafarkinsa zai cika akan nasarar caca.
"Wai yau wasan Barcelona da Real Madrid" A.y ya ce "Wacce match?" Gaza ya bashi amsa da "Afcon 2024"
Zameer ya ce "Madrid ne ma za su ci, su Barcelona uwar me suka iya?" Gaza ya ce "A'a fa, wallahi Barcelona za su ci wasan bana fatan gidan madara su ɗauki cup" Zameer ya zaro waya daga aljihu ya ce "Na saka wannan wayar idan Barcelona suka ci ka riƙe" Ya dinga juya wayar domin yasan ba wayar Zameer bace.
"Na saka Dubu hamsin"
Hira sukai sama-sama domin dukkansu zaman banza suke babu mai aiki arziƙi, sun fi ƙarfin aikin ƙarfi saboda sun yi degree aikin office suke jira sun ce amfanin karatun kenan. Daga nan Zameer gidansu ya shige
Lagos
A hankali yake danna system ɗin gabansa lokaci zuwa lokaci yake ƙara danna number Ridayya amma sai ya ji baya going, ya ajjiye wayar yana sauke numfashi. Daga bakin ƙofa aka yi knocking Ustaz ya dinga kallon ƙofar haka kurum ya ji baya buƙatar ganin kowa jin knocking ya yi yawa a hankali ya ce
"Uhm" Buɗe ƙofar akai tare da shigowa. "Assalamu alaika Ustaz Bilal" Ustaz ya ɗan ware Idanu sai kawai ya jinjina kai, laɓɓansa da suka motsa ya bada tabbacin ya amsa. Nasir ya ce
"Ai tunda na shigo nake tambayar Md aka ce baka samu damar zuwa ba, ina can ɓangaren customers care naga shigowarka ta baya, fatan ka zo lafiya Ustaz" Ustaz bai ko tari ba Nasir ya ce "Yaushe ka shigo Lagos ne? Har hutunka ya ƙare?"
"Nasir" Ustaz ya kira kamar baya son magana, Nasir ya yi dariya ya ce "Da alama yau kaɗaici kake ji ka yi aure kaƙi ƙaton gauro babu mai aurenka yanzu ai"
Ustaz da idanu ya bi Nasir idan suna maganar aure mamaki suke bashi suna ɗaukar kalma kamar wasa, bayan yana da kyau kafin namiji ya yi aure ya tsaya ya yi karatu guda akan sanin ma'anar aure da haƙƙoƙin auren, amma daga maza har mata auren kawai ake domin nishaɗi da magance abinda suke kwaɗayi. Nasir zai sake magana Ustaz ya lumshe fararen idanunsa wanda suke ɗauke da dugwayen gashi sukai kwance luf saman matar idon cikin muryarsa ta ustazanci ya ce "Ya isa, ya isa Nasir"
Nasir ya kwashe da dariya ya ce "Yanzu zaka fara Asstagafirullah, Hasbunallahu kamar an yi kalmar ɓatsa ustazan nan kuna yin abu kamar baku san komai ba, bayan kun fi kowa iya shege a gidan aure" Ustaz Bilal ya juya tare da ɗaukan gwangwanin Malt ya cillawa Nasir, da sauri ya miƙe yana cafe gwangwanin ya ce
"Ohho dai nasan kai ba waliyi bane" Ganin Ustaz ya miƙe yasa Nasir ya kwasa da gudu ya yi waje, girgiza kai kawai Ustaz ya yi yana zama saman kujerar dake office ɗinsa.
Wayarsa ta fara ringing ganin sunan Abban sama mahaifin Ridayya ya sa ya ɗauka ya ce "Baffa"
Ya yi shiru can ya numfasa ya ce "Allah ya sauwaƙe ku je kawai ban jin zuwa Rano"
Yana faɗin haka ya kashe wayar idanunsa ya lumshe a hankali ya shafa ƙirjinsa dake harbawa ya miƙe ya shiga zagaye office ɗin ya ƙara komawa ya zauna a taushashe ya ce
"Ustaza" Da sauri ya ce
"Asstagafirullah!"
Baffa ne ke kaiwa yana dawowa sai sura masifa yake Mami kan ta a ƙasa Amma ke bashi haƙuri Junaid dai bai tanka ba. Ya ce "A zuri'a ta jinina har na haifi ƴar da zata nuna tafi ƙarfinmu? Wallahi ba a haifeta ba idan har ni uban Ridayya ne kuma ta haifu wallahi tallahi sai na raba aurensu da yaron nan gwara ta zauna a gabana har ta mutu babu aure" ya juya kan Mami ya ce "Babu shasha wacce bata san darajar ƴarta ba irinki Mami, ni ba haka na tashi naga ko wacce uwa na yi ba, amma kin zuba idanu ba ki da wata asara ko gawarta za a kawo miki sbd ba ki san wahalar rainonta ba" Mami kanta a ƙasa Zainura sai kuka take ganin yar da ake wa babarta faɗa kamar za a dake ta. Baba ƙarami ya ce "Saurara Bawan Allah Fatima bata da wani laifi, a haka kuka ɗora ta tun zuwan Ridayya duniya,kuma da kake hayaƙin baki a kan taƙi ɗaukan mataki daman hakƙinka ne kwatarwa Auta ƴanci"
Baffa ya ce "To wallahi idan har ina raye sai na kashe auren Ridayya" Ya ɗauki waya ya shiga kiran layin Ridayya ba jimawa aka ɗauka Zameer ya ce "Barka da yamma Baffa"
"Ina ƴata? Ka ce ina buƙatar ganinta yanzu yanzu a gida" Zameer ya ce bari na bata wayar ya cire wayar daga kunnensa ya fara cewa "Wife... Wife sweetheart Baffa yana kira" ya ɗauki seconds kafin ya mayar da wayar kunne ya ce
"Baffa wai bata buƙatar magana daku, ta haƙura daku kuma ta yi nisa daku kamar yar da ta yi muku alƙawari" Wani tari ya turnuƙe Baffa da sauri Mami ta ɗauki ruwa ta bashi ya girgiza kai yana ture hannunta ya ce
"Ni mahaifinta? Ni Ridayya take faɗawa haka ashe girman haukanta ya kai haka?" Idanuna ya sauya Baba ƙarami ya ce "A kul ka zubar da hawaye saboda ita, idan ka yi hakan to ka bata lasisin ƙara lalacewa ka yi addu'a sharrin soyayyar zamani ne kawai" Ya jinjina kai ya ce "Ku shirya gabaɗaya a yau ɗin nan zamu tafi Rano duba Hajiya Junaid harku gabaɗaya ku shirya a faɗawa Balkisu, Zuhura Ustaz ya ce zai bimu daga can Lagos ɗin zamu bar wa Ridayya garin na wasu lokaci. Nan da suka fara shirin tafiya Rano a gaggauce gabaɗaya familyn banda Ridayya da Ustaz.
Mami kuka take sosai ta cikin waya ta ce "Haba Yaya A'isha ya ake so na yi, ni da Ridayya bamu da wata shaƙuwa ina buƙatar ƴata ina buƙatar tattaunawa da ita"
"Ki je gidan nata kafin ku shige Ranon" Tana kuka ta ce "Baffa ba zai barni ba, ya ɗauki zafi ban san me mijin Ridayya ya faɗawa masa ba"
Yaya A'isha ta ce "Fatima tun farko kin yi sake a yanzu kuma kafin ki gyara kuskurenki abu ne mai wahala raina ɓaci yake idan na zo gidanki amma ni zani gidan Ridayya ɗin ki kwantar da hankalinki" Mami ta ce
"Idan har ban mutu saboda baƙin ciki ɗa namiji ba, to tabbas Ridayya ba zata mutu ba, hakƙina akan ubanta ke bibiyar tata rayuwar ina mata fatan alheri a rayuwarta Ubangiji ya kawo mata sassauci"
Ridayya kamar an tsikare ta haka ta miƙe tana saka hijabi Zameer ya kalleta ya ce "Ina za ki"
Kai tsaye ta ce "Wajan Mami ina buƙatar ƙarin haske ina son ta fahimtar dani abinda na gaza fahimta"
Ya dinga kallonta mamaki ya cika shi jin yau ta ce Mami ba Amma ba, ya ce "Tab, Baffa ya dawo na je gaishe shi ba, amma ba kiga korar karen da ya yi mini ba, cin mutunci ta uwa ta uba kuma ya ce ko da wasa ya ganki a gidansa wallahi sai ya tsine miki" Zaman ƴan'bori Ridayya ta yi kanta ya kulle ta rasa wanne irin hali take ciki ne? Tana buƙatar zama a fayyace mata ma'anar so da ƙauna, so da birgewa da kuma soyayya ta gaskiya tana buƙatar ta fahimci mene take na kuskure. Kuka ta rushe da shi kamar ta yi hauka "Na shiga uku Baffa don Allah kar ka tsine mini zan dawo gare ku wayyo Allah na" Ficewa ya yi. Zainaba ta shigo da kwanon abinci ta ce "Ridayya don Allah don girma ki bani tarihinki wacece ke? Ki bani labarin rayuwarki da aurenki da Zameer don Allah kullum da kwaɗayin jin hakan nake kwana" Cikin kuka Ridayya ta ce "Babu komai a rayuwata sai tarin baƙin ciki da takaici sai baƙin cikin labarina ya haddasa miki ciwon zuciya ku yi mini uzuri a duk abinda na aikata wallahi ina cikin hankalina ko a mafarki bana ƙaunar tuna rayuwata ta baya" Kuka itama Zainaba take sosai ta ce "Wallahi ina tausaya miki ina jin tausayinki kayan haushinki da takaicinki ke mini yawa yana danne tausayin ji nake kamar na jaki na lakaɗa miki mugun duka wallahi, don Allah ki bani labarinki" Ridayya ta ce "Zan ba ki amma gobe da alƙawarin za ki riƙe mini sirrina" Zainaba cike da gulma da son jin zance ta ce "Kin yi alƙawari? Gobe da yaushe kuma kyan alkawari cikawa" Ridayya ta jinjina kai, a yanzu burinta bai shige ganin Mami da Baffa tana jin ko za a kasheta gobe sai ta je gida sun gana da Mami...
Tunda suka ɗauki hanyar Rano babu mai magana a babbar mota suke ciki gabaɗaya family guda ɗin, daga Kano zuwa Rano tafiyar 1 hr 18 min (68.7 km) ce kuma cikin dare suka tashi, a karo na farko Baffa ya ji wani matsanancin tausayin ƴarsa zuciyarsa ta shiga zullumi da zarar ya dawo zai dawo mata da duk abinda ta rasa a rayuwa. Junaid dake driving ya ce "Ustaz fa ba za shi wata Rano ba Baffa dabara kawai ya yi maka" Yaya Zuhura ta ce "Kai kam Junaid ka sakawa Ustaz idanu kamar wani sa'anka" Gabaɗaya cikin motar suka saka dariya banda Mami da Baffa Zainura na jikin Mami idanunta, Junaid ya shiga duba lokaci a wayarsa ɗaguwar da zai yi yaga wata ƙatuwar tirela tayo kan motarsu gadan-gadan tirelar na ƙoƙarin kaucewa motar su Baffa na ƙoƙarin kaucewa a ƙoƙarin Junaid na tsayar da motar a tsakiyar titi, gabaɗaya ya danne giyar motar kai tsaye ta yi ƙarƙashin tirelar Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Gabaɗaya tirelar ta bi ta kan motar ta danne jama'ar ciki baka jin komai sai salatin da jama'ar motar ke yi wasu na ihu a hankali aka daina jin motsin kowa sanda tirelar ta mirgina ta ƙarasa danne kan motar su Baffa....
Don Allah idan kun karanta a yi sharing please saboda masu nema a kuma yi comment kar ku manta free book ne.
08164069385
Na'ima Sulaiman Sarauta
*✿ MUNAFUKIN MIJI ✿*
Nimcyluv@Arewabooks
Page 8
BRIGHT PENS🤙🏼 free batch
Yau duk wanda ya karanta ina son ya shiga Tiktok ya yi mini comment ta can👇🏼👯🏻♀️
https://vm.tiktok.com/ZM6Q2SoAj/
Hatsari ne wanda duk wanda ya gani sai ya girgiza, wasu su kuka da faruwa mummunan al'amarina na yiyuwar rasa rayuka da dama, masu matsanancin tsoro ta iya yiwuwa su yi mafarkin yar da babbar motar ta bi ta kan, ta su Baffa. Titin ya cika da jama'a aka dinga parking da abeben hawa, da ƙoƙarin ceto wanda Allah ya nufa suke raye.
Da ƙyar aka samu damar zare motar jini na zuba sosai daidai ambulance suka danno kan motarsu, basu tsaya tantance akwai masu rai ko duk sun mace ba duka aka kwashe su zuwa mota aka nufi asibiti mafi kusa da wajan da hatsarin ya afku. Tsoran Allah ya ƙara shigar wasu.
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, yanzu haka ahhali guda ne irin tafiyar da ba'a so, duk wanda ya yi saura a dangin ji zai yi kamar shi ma ya mutu ya huta, sun fito lafiya babu wanda ya taɓa tunanin lokacin mutuwarsa ya yi, kana tafe ne baka san kwana ya ƙare ba, Allahu Akbar wayyo Allah!"
Wata mata dake gefen mota ta dinga faɗa kuka yaƙi tsaya mata hankalinta ya tashi ainun. Mijinta ya riƙe ta ya ce "Ki kwantar da hankalinki Madam, kar ciwonki ya tashi kuma, shi ya sa a kullum a kodayaushe ake son bawa ya dinga aikata abin arziƙi domin mutuwa bata sallama balle kasan ranar tafiyarka lahira.
"Allah sarki ni fa sai naga hannun wata kamar ya cire ga kan wani ya yi daga-daga wallahi zai wahala idan duk basu mutu ba" Nan da nan hankalinta ya ƙara tashi ta rushe wa mijinta da kuka da ƙyar ya lallaɓa suka shiga mota. Ana ta rai da neman taimako, a gefe guda kuma wasu sun taro sun sace kayan mamatan babu tsoran Allah da tunanin suma za su je inda sauran suka je.
Emergency ɓangaren ƴan hatsari aka nufa da su, aka shiga duba wa ko akwai sauran masu rai, aka bar likitoci su yi aikinsu, ƴan'sandan kuma suka shiga fafutukar inda za su gano ƴan wanne gari ne mamatan, da inda za su samu wani nasu amma har gari ya waye babu wani Information da zai tabbatar da su waye su, har lokacin ba'a samu cikakken bayani na kasancewar wasu a raye ba, ko duk babu.
Kwana biyu da faruwar lamarin Ustaz na zaune a parlon gidansa ko wajan aiki ya kasa zuwa, haka kurum ya ji faɗuwar gaba na ruskarsa, fargaba da tsoran da basu da masaniyar komai a kan wanzuwar su a zuciyarsa suka shiga ratsa shi. Ya rufe idanu sai ya buɗe da sauri shi kaɗai amma duk a firgice yake dukda ƙoƙarin riƙe kansa da yake da kyau da gudun hana faruwar tashin ciwonsa. Wayarsa ya ɗauka yaga Baffa ne last wanda ya kira shi sai kuma a lokacin ya lura da saƙon Baffa dalilin notification dake alamta masa zuwan saƙon. Kai tsaye number Baffa ya kira amma baturiyar wayar na zayyana masa wayar a kashe take. Ustaz ya yi shiru yana sauke numfashi can ƙasa zuciyarsa kuma sunan Allah yake kiran a kan ya sassauta masa fargabar dake shirin tarwatsa masa zuciya ya miƙe tsaye a hankali ya ce "Ya Allah, Rabbi inni lima anzalta min khairin faƙir..." Number Baba ƙarami ya kira itama ƴar'uwar ɗayar ce duk a kashe ya koma da baya kamar zai zauna sai kuma ya tsaya saƙon da Baffa ya tura masa ya buɗe, ya ware idanu ƙirjinsa na dukan tara-tara a hankali ya fara bin abinda saƙon ke cewa.
_Muhammad-Bilal zan so wannan maganar na yi ta ga-ni ga-ka babu mamaki zaka fi fahimtar hali da raunin da zuciyata take ciki, faɗar kalmar ban yi wa Ridayya adalci a rayuwa ba wannan kuskure ne, ina tunanin ta zaɓi rabuwa dani ne bisa ga abubuwan da suka faru a baya, Bilal girma muke nasan cewa mutuwa da rayuwa na Allah ne, amma babu tabbacin ganin gobe balle jibi balle kuma sanda zamu dawo daidai da Ridayya, Kullum Baffa take ce mini bata taɓa guduna ba, a wannan karan Ridayya ta zaɓi rayuwa da mijinta a kaina, bata ƙaunar ganina ta ce kar mu sake nemanta, ba zan wa Ridayya baki ba balle hakan ya haddasa ƙara lalacewarta. Muhammad-Bilal, Abbiey kullum Ridayya ke kiranka tun tana ƙarama har ta girma, sai daga baya ta fahimci ba kai ka haifeta ba...,_
Kasa ƙarasa karatun Ustaz ya yi saboda ƙafewar da yawon bakinsa ya yi, ruwa mai sanyi ya ɗauka ya sha kana ya kira number Junaid itama a kashe a fili ya ce "Ya Allah!"
Ya koma tare da ci-gaba da duba saƙon Baffa wanda yake tamkar wasiyya ce ga