Showing 72001 words to 75000 words out of 190738 words

Chapter 25 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17304

lokacin kuma tana kallon sai su kwana ɗaki ɗaya da Khairy ta yi magana ya ce ai ƙanwarsa bai zarge ta ba sai shi zata zarga? Ta kira Mardiyya a waya a lokacin shi ne suka faɗa kaca-kaca a kan ta ce namiji ba ɗan goyo bane musamman Zameer kuma Khairy ba ƙanwarsa bace farkar shi ce ta ce babu ita ba Mardiyya har abada, a ranar ne kuma da daddare ta samu Zameer a ɗaki shi da Ridayya turmi da taɓarya har ta nemi kashe kanta da fiya-fiya


WANNAN KENAN.


BACK TO STORY
Kuka sosai Zainaba ke yi haka Ridayya, Usman mijin Zainaba ya rushe da kuka har da face majina aka rasa wanda zai rarrashi wani da ƙyar Ridayya ta ce "Duk abinda kuke faɗa na sani bani da wani option wanda ya shige watsar da maganganunku na riga na bawa Zameer mutuncina, kuma a duk sanda na yi yunƙurin rabuwa da shi ya ce zai saki vedion a duniya"


"Tsinanne matsiyaci ce *MUNAFUKIN MIJI* wutar Allah ta ci shi" Ridayya ta goge idanunta ta ce "Amma wallahi tallahi sai ya sake ni na koma wajan Abbieyna, ko da zai saki vedion zinar da mukai ne.......






Share and share please
Ina godiya da comment da goyan baya masu zagen Ridayya ku yi mata uzuri please Allah ya yafe mata.




Na'ima Sulaiman Sarauta
Nimcyluv
08164069385
*✿ MUNAFUKIN MIJI 23 ✿*
Mikiya Writers Ass....




BRIGHT PENS🤙🏼 free batch
Nimcyluv


"Yanzu kina nufin Ustaz bai san kin watsar da tarbiyar da ya yi miki ba, ba shi da labarin kin bawa saurayi budurci tun a waje saboda soyayya da ganin idan ba ki ba shi ba zai aure ki ba?"


Ridayya ta kasa magana sai wani irin ajjiyar zuciya da take saukewa, a kawo biyar na damuwa da ƙuncin data wanzu da shi tun haɗuwar ta da Zameer yau babu kaso ɗaya. Zainaba ta girgiza kai kawai har yanzu kuka take ita har yanzu tana ɗorawa Ridayya laifi, dukda cewa rayuwa da ƙaddara suna tafiya daidai ne kamar shaƙar numfashi ne da bugun zuciya.


"Wallahi ji nake kamar na ja ki ka zaune na yi miki mahaukaciya dukan kawo wuƙa, to kar na ƙarasa gawar da bata wa ba, amma Ridayya ba ki wa kan ki da Ustaz adalci, ba ki wa zuciyoyinku halacci ba, ina da tabbacin duk sanda Ustaz ya yi baki babu shakka sai ya biki, ya yi miki abinda uba da uwa ba su yi ba, ya raine ki da tafukan hannunsa, ya ciyar dake daga dukiyarsa, ya ba ki ilimi daga baiwarsa, ya ba ki tarbiyya daga cikin abinda ya sani, ya nemi aiki domin ya kula da rayuwarki. Ya yi miki wanka, ya yi miki tsifa ya gyara wannan sumar kan naki mai kama da bishiya, ya goya ki kin zama tamkar bakwaini amma haka zai yi amfani da ɗumin jikinsa domin ki ji shi tamkar cikin uwa mahaifiya, kin yi babban zunubi Ridayya. Da na san abinda kikai masa kenan wallahi tallahi ba zan barshi ya kai ki asibiti gwara kawai ki mutu ya yi jinyar zuciya da kuma mantawa dake bakiɗaya"


Shassheƙar kukan da sai yau ta samu damar yin mai isarta ta ci-gaba da yi tasan ba kowa zai yi mata uzuri ba, ba kowa zai fahimci dalilinta ba.


Zainaba ta ja tsaki tana zabga mata harara ta ce "Wallahi hannuna rawa yake ki daina wannan kukan banzan ko ka kwasa miki mari mtwsss" Ta girgiza kai ta ce


"Samarin yanzu? Wannan gantalalliyar soyayyar da kalaman da mazan zamani ke amfani da shi haka yake ruɗa ƴan'mata fa, musamman a ga namiji fari tas da shi yana saka suttura a tsayar da gemun da wani mai yake shafawa na bana Allah da Annabi bane, da kalaman ƙarya na bugi da zarar ya samu nasarar a kan mace kuma shikenan fa, wata mara kan gadon ma ki na da saurayi amma ba ki san tuni an yi masa baiko da wata ma. Uhm! Soyayya har haukata ɗiya mace na yi tafi talauci barazana ga rayuwar yara mata......,"


"Ai ita ma a haukace take, ta haukace a lokacin" Usman mijin Zainaba ya katse maganar matarsa ta hanyar ɗaga labulen ɗakin ya zuro kai yana faɗa tare da face majina.


"Kai fa Baban Hajjo ba zan taɓa yi wa Ridayya uzuri ba, Allah ɗaya kawai za ta ce mini na yarda. Ka yi tunani idan har Ustaz ya ji labarin abinda ta aikata na yin iskanci da wani ya sai tsinci kan shi? Tsaf zuciyarsa zata buga kwarankwasa"


Ras! Zuciyar Ridayya ta bada sauti ita koda wasa bata taɓa zama ta yi tunanin abinda hakan zai haifar wa Abbiey ba, bata taɓa tunanin kuskure ta aikata ba domin a lokacin mahaukaciya ce ita, ta samu makantar zuciya data kunne aure, soyayya, da Zameer ɗin sune kawai a idanunta.


"Don Allah mu bar maganar nan Maman Hajjo, ki ɗauka ban taɓa faɗa miki ba, don girman Allah kar ki kalle ni da wannan sigar"


"Wannan zunubi kike faɗa kina wasa ne don ba ki san yadda nake jin zuciyata ba, uwa ce ni fa? Wallahi ina miki kallon wacce ta wofintar da kan ta a waje tamkar tsirara haka kike a idanuna" Wani abu ya caki zuciyar Ridayya ta runtse idanunta zuciyarta na yi mata zafi da raɗaɗi na maganganun Zainaba ta san kuma ba ita kaɗai ba duk wanda ya yi da kalar maganar da zai jefe ta da ita take, ta yi kuka har ta gaji a ranta tana karkarta tubalin ginin ƙaddararta da Ahlinta.


Da ƙyar ta miƙe ta yi sallar asuba domin daman ba bacci ta yi ba. Zainaba ta lallaɓa ta tare da cewa ta yi wanka da ƙyar da ta yi domin ita yanzu tana jin bata wata wani saura banda jiran ranar da mutuwarta zata rusketa. Bata tsaya ta ci abincin da Zainaba ta bata ba ta lallaɓa tare da ficewa daga cikin gidan.


Tunda ta fara take tafiya ta ji faɗuwar gaba na tsananta a ƙirjinta, ta dinga addu'a tana jin komai ya kusa zuwa ƙarshen ta kusa isa gida babu mamaki ma ta tarar da Abbiey yana ciki. Ta faɗaɗa murmushinta ganin gate ɗin gidan abu tare da ƙara tafiyar da take zaton sauri take har ta shiga cikin gate ɗin lokacin Maigadi yana cikin ɗan ƙaramin ɗakinsa. Ridayya ta wanzu tana tunanin ina zata fara zuwa wajan Mami? A hankali ta girgiza kai ta nufi ɓangaren Baba ƙarami kai tsaye bedroom ɗin Ustaz ta nufa da siririyar muryarta tana faɗin.


"Abbiey.... Abbiey.... Abbieyna"


Babu magana sai tashin kiɗa dake tashi a hankali, direction ɗin da ta ji sautin kiɗan ta bi da kallo a tsaye ta gan shi gaban madubi ya zage yana taje gemu da mataji farar fatarsa ta sauya sosai daga yadda ta santa a baya ta sake yin fresh. There is a difference between her previous Abbiey and this Abbiey. Domin wannan riga Armless ce a jikinsa ta kama shi, ga gajeren wandon dake jikinsa, idan ya yi tazar sai ya fara goge tsakiyar goshinta kamar Abbiey.


"Abbiey ina ta magana" Ta faɗa tana matsa wa inda yake tsaye amma har lokacin bai juyo ba, da alama bata san yana yi ba ta buɗe iyakar muryarta ta ce "ABBIEY!"


A hargitse ya juyo yana gwalo Idanu waje saboda tsoro, ta ƙwalla ƙara saboda razana ta yi baya jikinta sai rawa yake tamkar mazari daman ba wani ƙwari ne ita ba.


Ya riƙe ƙugu daman tun safe ransa a ɓace yake ya kalleta sosai ya ce


"Lallai ji mini wata tsohuwar kilaki da alama kece iyar da aka ce za a kawo ƴar'aiki sabuwa ko?" Ridayya ta saki baki


Iya? Ta maimaita kalmar a zuciyarta kenan burin Zameer ya cika bai barta da komai na ɗiya mace kuma budurwa ba? Ya tatse komai na albarkar jikinta har ta yi kama da tsohuwar da za a cewa Iya? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!.


"Wait wai mene ya kawo ki bedroom ɗina? Na faɗawa Alhji ban buƙatar maid duk ƙazamai ne kamar ke ɗin nan"


"Ina Abbieyna?" Ridayya ta faɗa muryarta na rawa sosai. Ya sake riƙe ƙugu ya ce "Ji rainin wayo waye kuma Abbiey ki shigo har gidan uban cikin ɗakina ki kuma tsare ni da wani ido kina tambayar wani? How dare you?"


Ridayya dai kallon yadda yake zuba masifa hankali kwance take shi kaɗai duk ya hargitsa kan shi. Da sauri wata ta shigo ɗakin Matashiyar mata mai zubin haƙuri da nagarta ta ce


"Lafiya meke faruwa ne tun daga parlour na jiyo wannan muryar taka kullum cikin faɗa baka gajiya kamar Dage?"


Ya ɗage gira ɗaya cur kuma ta tsaya dake cikakkiya ce ya ce.


"How can i know mother? Kawai ta shigo ɗakina wai ina Abbiey nata? Na bi Abbiey da gudu ba wando wai banda lalacewa maid ce zata shigo kai tsaye ɗakina without my knowledge?"


Wacce aka kira da mother ɗin ta kalli Ridayya tun daga ƙasa har zuwa sama take kallonta kafin ta girgiza kai ta ce.


"Zafin rai Sadauki? Ka dinga yayyafawa zuciyarka ruwa kana shan ruwan alwalar sallar asar"


Sadauki ya dafe kansa ya ce "Kawai ta faɗa miki wace ita duniyar nan babu gaskiya mother"


"Wacece ke wa kuma kike nema ƴar nan?" Sadauki ya yi caraf ya ce "Wacce ƴar? Tsohuwa ce wannan....,"


"Ya isa ya isa Sadauki kar na ƙara jin bakin ka nan wajan" Ya yi shiru kawai yana jijjigata kan shi


"Ya sunanki?"


"Ridayya" Hajja Azizat ta ce "Ohh wakike nema? Kin shigo har cikin gidanmu kin taho ɗakin ɗana kin san shi ne?"


"Wallahi bata sanni ba, kawai ki tambayeta me ta zo yi mini" Hajja Azizat ta girgiza kai daman ta san ba shirun zai yi ba, ƴar banzar mita gare shi.


"Ina jin ki baiwar Allah"


"Abbieyna na zo nema ai gidanmu ne nan ɗin kuma nan ne ɗakin Abbiey"


"Kutumar u....,"


"Kar ka ƙarasa ta a kunnena Sadauki" Idanunsa har hayaƙi yake, ya yi ƙwafa yana ɗauke kan shi zuwa gefe. Hajja Azizat ta ce


"Ikon Allah gidanku? Allah sarki to saɓani aka samu domin mijina ne ya siye wannan gidan gabaɗaya idan kin lura mun yi gyara sosai kafin mu tare, wannan ɗin ɗana ne sunansa....,"


"No please mother"
Ya faɗa yana haɗe fuska tare da girgiza mata kai alamar baya son a faɗi sunansa mene haɗinsa da ita, wayarsa ta fara ringing ya ɗauka da sauri a hankali yana cewa.


"She is already here, yes Nadiya" iya abinda ya faɗa kenan a ɗakin ya fice.


Kuka sosai Ridayya ke yi tana durƙushe wa a wajan hannunta bibbiyu ta haɗe ta ce "Don Allah don Allah karki kure ni a gidan nan wallahi gidan Baffana ne kuma nan ɗin ɗakin Abbieyna ne, ki ji tausayina ki faɗa mini inda Baffa Mami Abbiey suke don Allah"
Jikin Hajja Azizat ya yi sanyi tausayin Ridayya ya kamata amma tasan halin mijinta baya ƙaunar kowa cikin gidansa idan ba su ba. A sanyaye ta ce


"Babu shakka da ina da hali zan taimaka miki da inuwar da za ki shiga ki samu sanyi, ni ma zama nake a ƙarƙashin wani bisa umarninsa nake komai" Ta tausasa harshe ta ce "Komai ya yi zafi maganinsa Allah, ki ɗauka gobara ce ta tashi a cikin kogi Ubangiji ne kaɗai zai yi maganin al'amarin"


Ridayya ta miƙe idanunta ya kumbura sosai jiri na kwasarta don yunwa. Hajja Azizat ta ce "Amma ke kina ina iyayen naki suka bar gidan? Ki kira number su mana idan suna kusa sai ki je" Ridayya bata ce komai ba can ta ce "A wajan wa kuka siyi gidan?"


"Gaskiya bana ce ba domin mijina ne ya san mutumin. Ki tsaya ki yi ƙarya sai ki tafi"


"Na gode" Zuciyarta babu daɗi ta nufi hanyar waje yau ita ce ta shigo gidan ubanta amma bata da iko da shi,duk yadda take ƙoƙarin goge hawayen sai kallon gidan take rayuwarta ta baya na dawowa fes cikin tunaninta rayuwar gidan da a yanzu ita take buƙata fiye data gidan miji.


Yana ganin ta fito ya kashe wayar da yake ya diro daga kan motar hannunsa ɗaya riƙe da ball yana juyata tare da binta da kallo can ya girgiza kai ya ce


"Who are you? Wace ke?" Ridayya ta yi shiru kan ta a ƙasa ya matsa yana ja da baya tare da leƙar fuskar ya ce
"Sai fa kin faɗa mini mene ya kawo ki bedroom ɗina fi not"


"If not zaka dake ta ne?" Ya kame fuska ya ce "Kar ki shiga faɗan nan Mother ki bar ta mini bayanin kan ta da wannan bakin nata"


"Sadauki wallahi baka ɗauki halin mai sunanka ba, kasan daraja da kimar sunan da a sanya maka" Ya turɓune fuska ya ce


"Na sani" Ta ce


"Bari na tuna maka Hamza sahabin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, cikakken sunan shi Hamza Ibn Abdul mutallib,ya kasance sahabin Manzon Allah (SAW) ne kuma kawu ne na Manzon Allah Muhammad (S.A.W), jarumi, mai farautar zaki"


"E to tunda ni ban samu zakin ba ga zakanya nan a bar ni na farauce ta, sai fa ta faɗa mini wacece ita" Gabaɗaya ya Sadauki ya tare hanyar tare da babbake ta, ba ruwansa da yadda yake acting shi bai ƙi ya cire a daku ba, daman ɗan rigima ne kuma shi ne ɗaya tilo ɗan fari kuma ɗan auta abin ya haɗe masa gashi ƙato da shi saboda ɗaga ƙarfe.


Sai yanzu ta ɗago ta kalle shi, shi ma ya kalleta da sauri ta zame idanunta sanda ta tuna akwai igiyar aure a kan ta. Sadauki bai damu da yadda take ba kawai yana mamakin ashe duk baƙinsa akwai wacce ta ci ubansa a baƙi.


"Ka bani hanya please" Sadauki ya muryar Ridayya ta amsa a kunnensa ya runtse ido ya buɗe yana girgiza kai tare da tattara hannu ya ce "Kin ji ba mother? Muryarta kamar kamar ana busa irin jita ta amma kalle ta tsohuwa? Yasin da akwai abinda ke tattare da ita"


"Yi tafiyar ki kin ji" Sadauki ya yi sauri zai bita Hajja Azizat ta riƙe shi tana murɗe kunnen shi. Ya juya ganin Ridayya ta ɗan fara nisa ta kusa gate ya ɗaga murya ya ce


"Kuma sai na rama ko ba yanzu ba, sai na shigo miki ɗaki ki ji idan daɗi, ki saka a ranki zan sake ganinka Sadauki baya mantuwa"


Da sauri ta fice don ba zata iya da masifar wanda aka kira da Sadaukin ba.


Bata taɓa zuwa gidan Dada ba, balle gidan Yaya A'isha Anuty Kaltum daman ba mazauniyya ba ce. Ta rasa inda zata saka ranta ta ji daɗi a rayuwarta, zuciyarta wani irin zafi da raɗaɗi take mata ga wani irin ciwon kai dake damunta tana jin abinda ke cikinta na juyawa yana sanar mata shi ma yunwar yake ji. Mardiyya ce ta faɗo mata ta mance ma da abinda ta yi mata tana zuwan gidan ta ruski sun yi tafiya zuwa biki sai wata wacce take haya a gidan da alama bata jima da tarewa ba ganin bata da mafita wacce ta shige komawa gidan Zameer ta ji ta bakinsa ya saka ta nufi gida.


Tana ƙoƙarin shiga layin aka ce "Ridayya" Gabanta ya faɗi ta yi saurin juyawa wani matashi ta gani tsaye a gabanta jikinta na ɓari ya ce


"Kar ki ji tsoro, matar Zameer ko?" Nan da nan ranta ya ɓaci jin sunan Zameer take kamar saukar dalma a zuciyarta ya gyara tsaiwa ya ce


"Zan faɗa miki wani abu da ba ki sani ba game da mijinki Zameer. Ya yi auren caca dake da niyyar idan kikai soyayya da shi kuma ya samu budurcinki yana da Naira miliyan goma, sai ya ci sa a kece kika fara furta cewa yana son ki, ya dinga amfani da soyayyarki da kuma rauninki na cewa kar ya barki saboda ba za ki samu mijin aure ba. Zameer bai taɓa son ki ba koda da rana ɗaya ne. Ya yi ƙoƙarin barin ki bayan ya cimma burinsa sai ya ga wata sabuwar damar, kin faɗa masa an mallaka miki kadarori wannan dalilin yasa yake zaune dake saboda su zama mallakinsa one day"


Ƙoƙarin faɗuwa take ta riƙe jikinta sosai ta shiga girgiza kan ta. Gaza ya ce "Ba iya wannan ba ai, gidan daya fara kai ki ara ya yi ba nasa bane, plan ne da ƴan kai amarya sun tafi zai kai ki asalin gidan daya tanada domin ki, lefan da aka sace naki shima haya ya yi da niyyar kai musu bayan biki shi ne akai plan a zo a ɗauke kamar ɓarayi duk shi ya shirya. Uhm! Sai furnitures ɗinki daya siyar ya ce kasuwanci zai yi ko? To caca ya shiga da kuɗin wanda ya ci yana da miliyan kusan 30 ya yi hakan ne idan ya samu ya auri budurwarsa da yake mugun so, ya sace atamfofinki ya shiga caca, ya sace wayarki ya shiga caca maganar da ake yanzu hatta gidan da kuke ciki ya shiga caca da shi kuma an ciye yanzu ba mallakinsa bane shi ne ya ce ma za ku tashi right?" Jin Ridayya bata ce komai ba ya sanya Gaza ɗorawa da faɗin.


"Zameer bai taɓa so da ƙaunar baƙar mace ba, ki yi tunani tunda kuke sumbata ta taɓa haɗa ki da shi? Saboda yana tsantsamin wai dugun bakinki, yana sane ya daƙile miki karatunki saboda kar ki zama wata idan har kikai ilimin mai zurfi za ki hana shi samun abinda yake kwaɗayi wata dukiyarki, ki nazari akwai baƙar macijiyar da kike rayuwa da ita ki gaggauta yin maganinta dukda kin ɗakko hanya"


"Ya isa zuciyata dab take da fashewa don Allah ka ce mini ba gaskiya bane, ka ce mini mijina yana so na wallahi zuciyata zata buga" Gaza ya ce


"Bai kamata ta buga tun yanzu ba, ai kina da rayuwa mai tsayi da muradan daya kamata ki cimma ki yi achieving nasu tas. Wannan kenan abi na gaba shi ne iyayenki"


A gigice Ridayya ta damƙe hannun Gaza ya ce "Su nake nema sune suka rage mini a yanzu ina gama ka da girman Allah ka kai ni wajan su"


"Abu ne mai wahala gawar dake cikin kabari ki ga ta tashi, kamar yadda yake abu ne mai wahala buduwar da bata da mijin kiga ta samu ciki sai dai idan ƴar'iska ce. Ridayya ki yi haƙuri da abinda zan faɗa iyayenki su duka basa raye sun mutu daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login