Showing 132001 words to 135000 words out of 190738 words

Chapter 45 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17271

sauka tare da tsayawa a kan ƙafafuwanta ya dinga binta da Idanu ya kasa furta komai. Anuty Kaltum ta ƙarasu wajan ta ce "Mu je ko ana ta jiran mu" Ridayya ta ɗan ji ba daɗi ta juya ta kalli Ustaz shi kam ya share ya yi kamar bai gani ba


"Abbiey zan tafi" Ta faɗa idanunta yana cika da hawaye ya juya yana riƙe kansa da yanayinsa da kyau a ɗan kame kamar koyaushe murya a taushashe ya ce


"Mene na kuka?"


"To za ka zo ne? Zaka kira ni a waya?"


"To ki haƙura mana Ustaza" Ta girgiza masa kai ya ɗan matsa kusa da ita ya ce "ki kula da kan ki, ki girmama kowa banda raini banda surutu da maza, be careful" Ta jinjina kai ya shafa kanta ya ce "Allah ya yi miki Albarka, Little fa?"


"Wajan Mami zai zauna" ya sauke numfashi yana ta kallonta taƙi yarda ta kalle shi sai ya sake ta ya ce "Take care of yourself Ustaza"


"To Babban mutum za mu shige mu duk ka cinye mana lokacin" Bai kalli Anuty Kaltum ba ya miƙa mata robar hannunsa ya ce "Duk dare ta sha, ki kula da ita please"


Yana faɗin hakan ya juya zuwa cikin gidan su kuma suka shiga mota zuwa wacce zata kai su Maiduguri driver ɗin sai mita yake musu.


Ridayya bata saba tafiya haka ba tun tana ware idanunta na kallon hanya har bacci ya ɗauke ta. Anuty Kaltum tana ƙara jinjina girman so da ƙaunar da Ustaz ya kewa Ridayya ta ɗauki niyyar ko komai nata zai ƙare a wannan karan za ta yi zumunci aiki Ridayya zata share masa damuwarsa zata zame masa irin matar da yake so, bazawara zata ɗauke masa dukkan buƙatunsa koma zata saka Umma ta dawo cikin hayyacinsu ta fahimci zawarawa suma mata ne. Balle irin Ridayya sauta ga wawa?


Sanda Ridayya ta farka ta samu Anuty Kaltum na waya da General yadda ta ji ana musayar kalaman soyayya ya bata Maman ƙwarai da gaske, har take ganin wannan rashin kunya ce ta yi zuru tana kallonta. Ridayya ta yi mamakin ganin ƴan'uwan kakarta wacce ta haifi Mami wato Dada kusan ita ce ta ɗauki yalwar suma irin nasu, asalin kanuri cikakkun mazauna garin Maiguduri yawanci sun saka lafaya ga wani irin kitso a kansu gwanin sha'awa kowa ka ganni akwai zanen lalle a ƙafarsa so ma sha Allah. Dangi aka yi ca ana ganin cikar Dada ta wajan Fatima Batula aka sauke su da shatara ta arziƙi tun a lokacin Yamara ta fara fito da kayan gyara tsofaffin ajjiya aka haƙa rami aka fito da wasu itatuwa da tsumammun turarruka aka wanke ramin tsugo tas. Tun a daren data bawa Ridayya wani magani tasha wani irin ruwa ya dinga fita daga jikin Ridayya mai yauƙi yauƙi kwana ta yi ba tai bacci ba sai sauya zani take.


Kwananta biyu tana shan maganin sanda aka zo gyaran fata har kuka ta yi saboda azaba sai ta ji kamar fatar jikinta zata kwailaye kafin ka ce baƙar fata da dawo wani special colour na musamman ita ba za a ce baƙa ba, kuma ba za a ce chocolate ba. Idan ta hau ramin tsugo kowa ba a magana sai jikinta ya gaya mata, ta ji ta matse da kyau kamar ba ita ba, ko sanda aka yi mata wannan ɗinkin na haihuwar Little bata ji ba domin tunani take anya zata iya fitsari? Bayan ta yi turare sai a haɗa ruwa a babban baho mai ɗauke da kaya kala-kala ace ta zauna ciki sai ta yi awa guda, idan dare ya yi sai a bata na shafawa kala biyu dana fata da wanda zata shafa a gabanta.


Yamara da kanta ta haɗa mata mai na amfani iya fuska mai ɗauke da aloe vera da honey da ƙwai cikin sati guda jikin Ridayya ya dinga wani glowing duk inda ta zauna kuma sai ta bar alama ko waje ya jiƙe ga wani mafifaffen ƙamshi daya zauna a jininta na musamman. Aka dawo kai kullum sumar sai an wake da karkashi da wasu tarkace ashe duk tsayin gashin ba iya haka yake ba, daman gashi da laushi sai ya zamana ko kalba akai baya zama ware wa yake.
Ridayya duk da gyaran ne a gabanta ba yadda Yamara ke yi mata wani karatun ne bata ganewa idan ta faɗi wata maganar sai Ridayya ta runtse idanunta sannan ta sake fahimtar lallai akwai wani abu da take ji game da Ustaz, ga tsoran kasancewarta bazawara ga babban zunubin data aikata idan ta tuna wannan sai ta share domin har lokacin bata san Ustaz mijinta bane, a ranta take jin abinda yake mata ya shige misali kuma babu kyau ba zata bari hakan ta kasance ba. Ga wani baƙin cikin Mardiyya da take ji idan ya tuna ta sai ta ji gabaɗaya haushin Ustaz ɗin ya kamata.


Satin ta biyu tana zaune kamar sabuwar halitta hannunta riƙe da tsumi tana ta kwaɓe fuska kira ya shigo wayarta ta dinga bin number da kallo tunaninta Ustaz ne tunda har yanzu bai neme ta ba. Ta ɗaga wayar ta kara a kunne muryarta a kasalance ta ce


"Hello"


Ajjiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi ya ce "So is true"


Gabanta ya faɗi jin muryar Sadauki a hankali ta ce "Sadauki"


"Why Ridayya? Why why kashe ni kike son yi ko so da gaske kin yi blocked number na?"


"Kamarya"


A raunace ya ce "Kamar yadda na faɗa miki Shanshan sau nawa zan kira number ki baya tafiya, na shiga damuwa da tashin hankali gashi ban san gidanku ba, yin duniya Tajj ya faɗa mini yaƙi wallahi na kusa mutuwa a kan yanzu haka drip ne a hannnuna Shanshan"
Kamar zai yi mata kuka yadda yake marairaice murya can ƙasa "Ayya sannu ya jikin me ya same ka"


"You are the reason behind anything, kin guje wa ganina, na rasa kallonki da muryarki da jikin nan naki mai ƙara sawa na ji babu wata mace a duniya sai ke, Ridayya Allah ne shaida ina tsananin son ki"


"Uhm be patient Sahibi"


"Where are you zan zo na ganki" Ta ce "Kai da baka da lafiya?"


"Zan iya, idan na ganki zan warke daman rashin ki n Shanshan"


"Ka bari ka ji sauƙi mana"


Sadauki ya zare ruwan hannunsa yana miƙewa daga cinyar mother data gama cin kuka sosai ya ce "Uhm just tell me kina ina? I'll be there for you"


"Maiguduri"


Ya zare idanu sai kuma ya ɗan yi baya ya zauna, yana dafe kansa dake matuƙar sara masa ya jima kana ya sauke numfashi ya ce


"Yaushe kika je, when za ki dawo kuma?"


Tana ɗan kallon Anuty Kaltum ta ce "Sati na biyu sai na yi wata a can, idan na dawo zan faɗa maka" tun kafin ta ƙarasa maganar Sadauki yake girgiza kai ya ce "I can't wait any longer Shannn, ba zan iya zaman jira ba ki bani address zan zo na ganki mu tsayar da magana"


"Please mana ka bari ka ji sauƙi" Sadauki ya nace sosai ta ce "Shikenan to ko na faɗa maka ka zo ba zan fito ba"


"Shikenan Allah ya dawo mini dake lafiya, but promise me kina dawo za a tsayar da maganar auren mu already na faɗawa Prof da Mother"


"Na yi" Ya sauke numfashi mai ƙarfi yana ƙanƙame wayar ya ce "Thank you Shannn shaaa. Zanna kiran ki ok ki kula"


"Tom"


“I love you”


"Thank you" Ya sake cewa "I love you" ta ce "Thank you"


“I LOVE YOU JAANN”


Cikin jan aji ta ce "Really appreciate Sahibi"


“Mu'ahh💋"


Ya sakar mata ta cikin wayar tsigar jikinta ya tashi ta yi saurin kashe wayar tana lumshe idanunta tare da ƙanƙame wayar a ƙirjinta, ta jima a haka sai kuma ta ɗauki wayar ta kira number Ustaz da aka saka Abbieyna ana ɗagawa ta fara jin ruwan ashar kwando kwando kuma muryar Umma ce.


"Haihuwar tsiya mai raba ɗa da uwarsa Allah ya fiki kuma ke da shi har abada sai dai ki hange inuwarsa in sha Allah, bazawarar kawai baƙa gayyar muni ai kin yi kaɗan ɗana ya dinga wahala a kan ki mai baƙin jini wacce ta rasa mijin aure mijin nata ya kure ta....,"


Da sauri ta kashe wayar Anuty Kaltum kuma ta ji komai Ridayya ta fashe da kuka ta ce "Na shiga uku wallahi Giɗaɗo ba kura ta ya yi ba, ni ce na ce ya sake ni bana son zama dashi, don Allah Umma kar ki raba ni da Abbiey zan jure komai banda haka ni ban masa asiri ba ban san yaya ake yi ba"


Kuka take kamar ranta zai fita babu abinda ta tsana irin a ce ta rasa miji bata so, ta tsani gorin aure ko da sigar wasa ne sai ta yi mai isarta Anuty Kaltum ta bata ruwa ta sha kana ta ce "Mene damuwar don an rabaki da Ustaz?"


Da mamaki Ridayya ke kallon Anuty Kaltum "Yi ta kallona ba yanzu kuke waya da wani ba har yake miki kiss kina tunanin idan kika aure shi zai jure ganinki da Ustaz ne? Duk da muharraminki ke amma ai akwai aure tsakaninki da shi, idan bakya son rasa Ustaz so be with him, a yanzu ne yake buƙatarki bari na faɗa miki abinda baki sani ba Ridayya. Ai kin tuna sanda ya faɗi a Lagos ko?"


Bata amsa ba kallon Anuty Kaltum take kawai ta ɗora da "To tsautsayi ya saka Ustaz ya faɗa saman dutse ina nufin mararsa ta sauka akan dutse har aka yi masa aiki a mararsa, abinda ba ki sani ba ake ɓoye miki Ustaz ba zai taɓa haihuwa ba, kuma ba zai iya tarayya da mace ba a duniya saboda ya nakasa kinga kenan babu yadda za a yi ya samu macen da zata zauna da shi tsakani da Allah sai dan kuɗinsa, tunda da shi za fankon ashana duka ɗaya suke. Idan ke baki amshe shi ba waye zai amshe shi? Ki yi amfani da damarki kafin ta ƙwace miki, kina ji kina gani ganinsa zai yi miki wahala kina yawan ƙaryata abinda zuciyarka ke ƙoƙarin bayyanawa amma ba za ki iya ba, domin soyayya gaskiya ce yanzu ya rage naki ki rungumi Ustaz da ƙaddararsa ki taya shi share hawayen idanunta kamar yadda ya yi miki sanda kike neman mataimaki, soyayya bata ɓangare ɗaya bace kuma ƙarfe ɗaya baya amo!"


Tashi ta yi ta bar mata wajan cike da takaicin Ridayya da uwar Ustaz Umma kenan. Ridayya ta dinga juya maganganun Anuty Kaltum a kanta.


***
Tun bayan tafiyar Ridayya Umma ta saka Ustaz a gaba da masifa a kan ya saki Ridayya tun kafin ta dawo idan kuma har ta isa fa kenan. Ta ƙwace wayoyinsa gabaɗaya kamar yaro komai ta ce biyayya yake mata amma yana cikin azaba ya san ko yanzu ya faɗi ya mutu Umma ce sila a wannan lokacin ba Ridayya ba. Mardiyya aka samu abin yi Umma ta ƙara tabbatar mata Ustaz lafiya yake ta yi ƙoƙari su fahimci juna kafin mayyar ta dawo ta suɗe masa kurwa ko kunyar Baffa da Mami bata ji.


Ustaz ya samu meeting da Madugu kai tsaye Magudu da secretary na Jam'iyya suka faɗawa Ustaz ƙudirinsu na son tsayar da shi ɗan takara a matsayin gwamna a ƙarƙashin jam'iyyarsu. A nan take ya nuna he is not interested siyasa ba ita ce a gabansa secretary ya fara lallaɓa shi meeting ɗin ya ƙare babu daɗi amma Madugu ya kafa na ci.


Alhji Mansur da Alhji Tahir suka tsayar da biki wata uku masu zuwa ya yi daidai da kammala ginin Ustaz na gidansa Mami ta shiga shirye-shirye ita da su Yaya A'isha. Ammi ana ta ɓangaren tana ta haɗa plan B ɗinta ita da Burhan ba wanda ya san me take yi. _Only God knows!_ Ga Anuty Zuhura mijinta ya sake halin ta yi ya ji ta dawo gida.


Ustaz ne durƙushe gaban Umma hannunta riƙe da farar takarda da biro ta ce "Muhammmmd"


Ya ɗago kai ya kalleta ya kasa magana ta ce "Well is allowed ai kana ji, idan ni ce uwarka na yi cikinka na kuma na raini cikin tsayin wata tara, na yi nishin naƙudarka na shayar da kai nono na shekara biyu ciff wata ashirin da huɗu to ka gaggauta rubatawa Ridayya sakinta a wannan takardar idan ba haka ba wallahi wallahi sai na ɗaga maka nono kuma na yi maka Allah.....,"


Jikinsa na rawa ya amshi paper ɗin gumi na yanko masa all over himself idanunsa ya jirkice ya ce "A'a kar ki mini Allah ya isa zan yi yadda kike so"


Rubutu ta fara a takardar yana gani dishi-dishi ya gama ya ninke sosai ya miƙewa Umma duk abinda yake faruwa Baba ƙarami yana kallo shigowarsa kenan cikin gidan. Umma ta yi murmushi ta rangaɗa buɗa ta ce "Allahamdulillah yadda yarinyar nan ta baka wahala albarkacin Annabi sai ta wahala a kan ka, ai daman na san ba za ka ƙi yi mini biyayya ba yanzu ka rungumi matarka baka da mace sama da Mardiyya"


Ustaz tunda ya miƙe tsaye jiri ya fara ɗaukar shi idanunsa baya buɗewa, yana jin idan har ya samu zarafin fita to ƙasar zai bari gabaɗaya kuma sarai ya san inda Ridayya take domin Zainura ta faɗa masa, ya ji a ransa ba zai ƙara kwana a gidan ba, ba zai ƙara kwana ɗaya a kano ba kuma ba zai sake yin sati guda a Nigeria ba. Zuciyarsa na bugawa da ƙarfi yana riƙe jikinsa a haka ya nufi hanyar waje Umma ta ce "Maza jeka sha iskar ƴan'ci ka dawo wajan matarka Allah ya yi maka albarka ba dai biyayya ba"


Ustaz ya juya ya kalli Umma sai ya ce "Ki yi haƙuri na yi miki abinda kike so wanda ya sanya zuciyata cikin ladama da fargaba ba kuma zan taɓa yafe wa kai na, tunda kika saka na saki Ridayyerh ni ma ba za ki sake ganina ba" Yana faɗin haka ya fice yabar gidan gabaɗaya kai tsaye da niyyar zuwa Maiguduri ya fita daga gidan.


More comment more update
RAMADAN MUBARAK


*MUNAFUKIN MIJI 37*
Mikiya Writers Ass...




Bright pens free batch
Nimcyluv




Bayan ya fita daga gidan bai samu zarafin shiga motarsa ba, texci ya shiga zuwa tasha suna tafe Idanun Ustaz rufe zuciyarsa na bugawa da matsanancin ƙarfi.


A hankali a fili cikin sautin da shi kaɗai zai iya ji ya furta.


“Ridha, you are my choice, always. Even if fate brings me a fated mate, my heart will remain yours”
Ya sauke numfashi yana jin komai na fice masa a rai,hukuncin da Umma ta saka ya yanke daidai yake da tsaiwar numfashinsa wanda hakan ke nufin rayuwarsa na dab da zuwa ƙarshe.


Love is nothing but a destiny; dole kowa ya yarda soyayya ƙaddarar ko wanne mai rai mai zuciya ne a ƙirji. Ƙaramar wayarsa ya ji tana ringing ya kasa motsawa balle ya duba yaga waye? Kawai ƙasar yake son bari amma komai nasa yana gida bai san ya zai yi ba, ya koma ne ko ya tafi haka?


Wayar ya zaro ganin Baba ƙarami ya saka cikin nutsuwa da ladabi ya ɗauki kiran, yana mai yin shiru tare da sauraren abinda Baba ƙarami yake cewa can ya nisa ya ce
.
“Huh! In sha Allah”


"Turn the car driver"


Cikin sauri driver ɗin ya juya lokaci zuwa lokaci yana juyawa tare da kallon Ustaz ganin yadda fuskarsa ta yi jajur har wani ruɗi-ruɗi take gabaɗaya jijiyoyin kansa sun tashi. Yanayin shi bai bari an gane ya yake ciki ba zafin ransa dai a bayyane yake.


Umma ta miƙe tsaye tana juya farar takardar dake naɗe a hannuna ta ce "Allahamdulillah! Allah abin godiya sai yau zan yi cikakken bacci tun bayan auren ƙaddarar nan bana runtsawa da kyau. Yadda ka yi shekaru har 43 ba zaka ƙare rayuwarka a bazawara ba, ina son ka yi aure na ƴanci ka bawa zuciyarka da gangan jikinka abinda ko wanne namiji yake buri, buƙata, da kwaɗayin samu. Yaro gabaɗaya ya gantalar da rayuwarsa akan bautawa yarinyar da bata son ciwonsa ba, bata san damuwarsa ba, sai da ruwa ya ƙare wa ɗan'kada za a ƙallaga masa ita banda ƙaddara da naci da kuma maitar soyayya wallahi Babban mutum ya fi ƙarfin auren Ridayya ta ko wacce siga" Ta faɗa rai ɓace fuskarta kuma na bayyana tsantsar farincikin da take ciki.


Baba ƙarami ya ƙarasa shiga ciki jikinsa duka a sanyaye tunanin makomar Muhammmmd kawai yake domin Allah ne shaida yana yi wa Ridayya son da shi kansa bai sani ba tun yana rufewa da murfin zuciyarsa har murfin ya gaza ɗaukan girman al'amarin rauninsa a kan ta ya fid da kan shi.


"Kin yi farincikin?"


"Kamarya?"


Baba ƙaramin ya zauna ba wasa a fuskarsa ya ce "E, you have to tunda kin yi abinda kike so yana da kyau ki zuba ruwa a ƙasa ki sha ko kuma ki kunna kiɗa ki taka rawa, kin saka an saki ƴar ƙanina kin mayar da ita bazawara"


"Wannan shi ake kira ga fara sa banga ƙaho ba, bazawara ta nawa kuma? Ba a zawarcin aka maƙala masa ita ba? Sanda take budurwa wane a cikinku ya yi tunanin haɗa auren su? Sai yanzu ta yi aure ta sha baƙar wahala miji ya ci ubanta son ran shi ta haihu ya gama kwashe albarka da ni'imar jikinta sannan kuka tuna da Muhammmmd ko? Uhm ni da bana ƙwai na sai da zakara kuma wallahi Babban mutum ya zama kwankwason jimina mai wuyar shafawa, ya ma ƴarku nisa"


"Ni kike zagi Hadiza?"


"Ni? Yaushe?" Umma ta ce tana gwalo Idanu.


"Ridayya bata da uban daya shige ni, kamar yadda Muhammad-Bilal ba shi da uban daya shige ni Alhji Tahir Rano. Kin yi playing role ɗinki da kyau amma ki sani Ridayya ba za ta yi zawarci ita kaɗai ba, dole ne su yi tare da surukarta idan kuma ta samu miji ta bar ki a titi mafi mushkila"


"Me kake nufi Alhji Tahir?"


"Ina nufin abinda kika ji Hajiya Hadiza. Bani takardar domin nasan saki nawa zan iya miki"


Tana karkaɗa ƙafa ta miƙa masa cukurkuɗaɗɗiyar takardar dukda ƙasan zuciyarta fargaba ce fal ita kam ina takama tsofe-tsofe da ita da yin wani zawarci?. Baba ƙarami ya buɗe paper ɗin a hankali ya fara dubawa gumi na yanko masa all over himself bai taɓa zato ko tunanin hakan ba, bai taɓa kawowa a ransa Ustaz zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login