Showing 39001 words to 42000 words out of 190738 words
Chapter 14 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt
detol a ciki.
Zabura Ridayya ta yi sanda ruwan ya ratsa ta, ga sabuwar fata ga ciwo ga zafin ruwan wanda Ustaz ya kasa fahimta ya ɗauka duk ciwonne ya sata kuka, ya dinga wanke mata jiki a hankali kamar ƙwai ya gama ya sake haɗa wani ruwan ya mayar da ita har fatar ta ɗan washe cinnakun suka fita a towel ɗinsa ya naɗe ta, tare da fitowa.
Farar jallabiyyar Ustaz ta ɓaci da jini ya ajjiye Ridayya saman gado zai juya ta canyara ihu ya yi saurin dawowa ya ɗauketa ya sata a kafaɗa. Fatar wuyansa ta fara tsotsa kamar ta samu nono.
Murmushi ya saki mai taushi jin yadda take ƙoƙarin neman abinci ido biyu, sakkota ya yi sai ta fara motsi da nishin kuka ya saka mata yatsarsa a hannu da sauri ta fara tsotsa tana sauke ajjiyar zuciya. Ustaz ya lumshe idanunsa wani irin tausayi ya kama shi, bai taɓa ganin wannan rashin imanin ba ko a fina-finai Hausa da littafan Hausa ta marubuta suke yi. Ruwan zam-zam ɗin daya jiƙa tare dabinon ajwa ya ɗakko ya yi kauri sosai ya bata ta dinga sha, sai ta sha sosai kana ya cire. Jin ta yi shiru ya miƙe ya watsa ruwa a jikinsa ya sauya kaya daga jallabiyya zuwa three qauter Ustaz baya son kaya masu nauyi shi ya sa ba kowa ke shigowa bedroom ɗinsa ba, idan har shi kaɗai ne za ka iya samun shi daga shi sai trouser.
Sai a lokacin ya samu damar ƙare wa yarinyar kallo, idanunta rufe har yanzu babu wanda zai ce ya taɓa ganin su. Idan ka ce real definition of blac skin kai tsaye Ridayya ce, baƙin mai duhu sai da yana haske za kaga har ɗaukan idanu yake, yanayin shi bama mai irin maiƙo ɗin nan bane ya fi kama da baƙi irin na ƴan Ethiopia. Laɓɓanta jajur suke duk da suna da girma da kauri amma kamar a tsaga jini ya fita, gashin gira a cunkushe suna neman haɗe wa waje guda, ga gashin ido zara-zara sumarta har ta shige goshi ko'ina na jikin Ridayya suma ne.
Ya kai hannu ya taɓa lips ɗin da sauri ya ɗauke hannun yana yarfe wa jin kamar fatar wajan zata ciro saboda laushi ya rufe ido kamar mai koyan magana ya ce
"Ya subuhanallahi!"
Yana faɗin haka ya yi shiru, har gari ya yi shiru dab da subhi Ustaz na zaune ya saka Ridayya a gaba da kallo a hankali ya zunguri cibiyarta.
"Open your eyes shalele"
Kamar tana jinsa haka Ustaz ya ga idanunta sun buɗe ta kalli sama da sauri ta rufe saboda haske, can ta ƙara buɗewa ta ƙura wa waje guda da kallo, Ustaz sai yaga kamar shi take kallo bai san kallon ƙoda bane. "Allahu Akbar, Ma sha Allah laƙuwata illabillah"
Idanun Ridayya irin su a kaf gidan, tsarin halittar da Ubangiji ya yi mata daban yake, kamar yadda kamanninta ya sha bambam dana jama'ar gida haske tas da su kamar ƙwalla ta kwanto manya wanda idan ta kafe ka da su sai ka firgita, akwai wani irin sirri a cikinsu.
Ya kwanta gado ganin kamar tana jin sanyi ya saka ya cire towel ɗin ya ɗora ta a saman ƙirjinsa ya rufa mata towel ya rungume ta, a ransa yana so ita ma ta ji ɗumin jikin uba mahaifi.
"Babana" Ya ji kiran sunan a saman kansa, bai buɗe ido ba ya sake bubbuga pillown da yake kai ya ƙanƙame abu a ƙirjinsa ƙafarsa ɗaya a ƙasan gadon wacce yake jijjiga wa har bacci ya ɗauke shi. "Za ka yi missing jam'i ka ɓatawa mutane lokaci"
Bakinsa ɗauke da addu'a ya buɗe ido, sai kuma ya ƙanƙance su ya kalli Umma ta ce "To Babana kar ka mini faɗa, mutum kamar rainon iska ya ce wai baya son magana a saman ka? Baya son faɗa baya son tsawa?" Ya sake shigar da idanunsa ciki ya kalli Umma can ya girgiza kai a hankali ya ce
"Faɗa da asubar nan faɗa Umma? Kai na zai cire nikam zai cire" Idanunsa sukai jajur. Umma ta riƙe haɓa ta ce
"Me kake ƙanƙame wa ne haka Babana?" Ya shiru ta miƙa hannu zata cire towel ya yi saurin riƙe wa ya kalli Umma yana kicin-kicin da fuska ya ce
"Tsaraici na, umma tsaraicina za ki yaye?"
"Gidanku kai da tsaraicin, ni uwarka ce har wanka na yi maka ko yanzu ta kama ki tas zan wanke ka" A gigice ya ɗago Ridayya daga ƙirjinsa da numfashinta ke sauka a hankali ya leƙa, wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ya sauke shi kam da idanun Shalale biyu ai Umma ta gama zubar masa da girmansa wallahi. "Matata kawai ke da ikon ganin tsaraicina, ki tausaya mini a rufe maganar nan nikam"
"To da za ka yi auren ma ni ba haka ba? Ni tun da ƙuruciyarka nake ganin matarka" Ta faɗa tana mamakin abinda Muhammad-Bilal ke ɓoye wa a ƙirji. "Ni fa ba zan aure ba" Gaban Umma ya faɗi ta ce "Me kake nufi"
Ya yi shiru bai tanka ba, yaƙi motsa wa, tana kallon yadda jijiyoyin kansa duk suka fito ƴar wannan maganar da ya yi ta ce "Idan ba zaka samu damar yi wa jama'a jam'i ba a sanar wani ya yi" Tasan ko zai makara ba zai taɓa tashi ba, duk duniya Ustaz ya tsani wani yaga surar jikinsa. Fita ta yi tana jan ƙofar ya bi bayanta da kallo. Ya miƙe yana ajjiye Ridayya ya rufe ta ruf, wanka ya yi ya shirya cikin jallabiyya mai taushi kana ya ɗauki carbi ya rufe ƙofarsa da key ya nufi masallaci. A nan ya samu shi kaɗai ake jira, son girman Ustaz ya saka suke girmama shi hakan yana masa daɗi uwa ub kaifin tunani da basira bayan idar da sallah suka jero da Baffa da Baba ƙarami ya gai da su bai tsaya jin me Baffa ke faɗa ba ya yi gaba. Wani wankan ya yi Ridayya ya saka mata fararen kaya tare da hula wanda ya siya mata ta yi luf har yanzu fatar kuma a kumbure take, ba tare da kowa ya sani ba ya nufi asibiti da ita.
Ustaz na zaune gaban Dr yana jin bayaninsa da yake cewa "Kawo yanzu bamu da tabbaci da zubin hankalinta, amma ganinta lafiya yake matsalar bakinta kuma da hanci ya faru ne dalilin jijjigar daya taɓa ta tana ciki, zamu ɗora ta a magani kuma zamu ajjiyeta a wajan mu, komai zai daidaita In sha Allah" Ustaz idanunsa rufe ya jinjina kai.
"Cikakken sunanta?"
"Ridayyerh Muhammad-Bilal Rano" Dr ya kalli Ustaz da kyau, ya san Ustaz amma bai taɓa ganin mutum mai bala'in jinkima da rashin damuwa da abubuwa ba sai shi. Ya cike komai kana ya ce "Ustaz yarinyar nan idan na ce bata buƙatar kulawa na yi ƙarya, domin cinnakun da suka shiga gabanta sun yi mata illa sai yanzu muka cire wasu, fatar wajan.....,"
"Faɗi wani abu, ba wannan ba" Dr ya ce "Tana da ƙarancin lafiya a nutsu a tsaya a kanta a bata kulawa sosai da sosai, bayan mun sallame ta zan rubuta madarar da za a bata da yadda ake amfani da ita, dukda na so ta samu ishasshen nonon uwa ko dan kaifin basira amma kowa da nasa ƙaddarar"
"Ni zan shayar da ita" Dr ya zaro ido waje sosai sai kuma ya yi dariya ya ce "Shayarwa ta iyaye mata ce" Ustaz ya miƙe tsaye can ya ce "Maza ba sa yi?" Yana yatsuna fuska kamar me.
"Halittar maza data mata ai bambancin su a bayyane yake, ban taɓa ganin namiji ya shayar ba, tunda Ubangiji daya halitta nono a ƙirjinsa bai halitta shi da ruwa a ciki ba, wannan ƙudirar da bowayar mata iyayenmu Ubangiji ya bawa, Allah kuma ya saka musu da fificin alheri domin bama da abin da za mu biya su, za su shayar damu tsayin watanni ashirin wasu shekara biyu ba, ba tare da gajiyawa ba, ba tare da tunanin sun ci ko ba su ci ba, ko uwa zata yini bata ci komai ba; ba zata fasa shayar da ɗan ta ba, ai uwa ta musamman ce shi ya sanya Ubangiji ya fifita ta fiye da uba, duk wanda bai ni mahaifiya ba wallahi ya shiga uku"
Ustaz ya yi jim tunani fal ransa, taya zai zama uba kuma uwa a wajan Shalale? Da wannan tunani ya fita wajan biyan kuɗi tare da barin asibitin ko ɓangaren su Mami bai je ba, tunda bashi da masaniyyar sun koma ICU.
Gabaɗaya Ammi ta manta da batun wata jaririya domin ba ita ce a gabanta, har wajan ƙarfe 11 na safe tana Hakimc ce a parlon tana jiran zuwan Biba, 11:30 daidai ta ƙarasu duk suka zauna a parlo tun kafin su gaisa Biba ta ce
"A haɗa mini breakfast please, lafiyayye da naman kaza" Ammi ta ce "Biba kamar wacce ta yi kwanan yunwa?"
"Uhmm Zawarci masifa ne Maryam, bani da kuɗi gida kuma a wulaƙance ake kallona wai saboda na kashe aurena" Ammi ta girgiza ƙafa cikin izza ta ce "Lallai, ai laifin ki ne Biba wake wasa da gidan miji? Ai idan ba ki kori ta ciki ba, bata isa ga kora ki ba yanzu ai ta ci bulus"
"A'a fa, na fita ne kawai amma babu abinda muka fasa yi da Muktar wallahi ko ƙwayar shinkafa sai bawa iyalinsa sai da umarni na, ai lafiyayyar mallaka aka yi mini a kansa, wai a haka bana wani son shi,da son shi nake ko uwarsa sai da izinina sai gaisar" Ammi ta miƙe
"Makira ce ke, shu'umancinki ya girmami nawa Biba ajina bai kai naki ba" Biba ta cire mayafi ta yar, tana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ta ce "Ai gida yanzu ya zama namu, dole na zo na ci rabona bati available" Ammi ta dawo ta zauna ta ce "Yanzu za a kawo miki, to ya ake ciki kin tura kuɗin?"
"Na tura, ya kuma ce dole ki zage damtse domin akwai wani rabon mai ƙarfi tsakanin Mansur da Fatima, iyayenta malamai ne a kodayaushe aikinmu zai iya lalacewa" Ammi ta miƙe tsaye ta ce "Tab ɗin, to wallahi tallahi Fatima ta yi kaɗan, ita da gidan nan har abada komai nata sai na mallake shi" Biba ta girgiza kai ta ce "Maryam shi fa yaƙi ɗan zambo ne, idan ba ki iya ba sai a tashi dake, kamar wasan ƙwallo ne mai tunani da kaifin basira shike da nasara, cin nasarar ki da Maryam dole a sauya taku"
Ammi ta dawo da baya ta ce "Ya zan yi yanzu?"
"Ki zauna" cewar Biba, ta girgiza kai ta ce "Bana jin zan iya zama, ba ki san yadda Mansur yake mutuwar so da ƙaunar Fatima ba, ba ki isan irin burin daya ɗauka a kanta da abinda zata haifa ba, komai ya samu Fatima baya ɓoye so da ƙaunarta a kan idanuna, ya ɗanɗana mini azaba, ko a kwance muke idan zai kira sunana Maryam wallahi Biba na faɗa miki sunan tsinanniyar yake kira, a plan ɗina babu kishiya ko dana barshi ya aureta baya nufin da zuciya ɗaya na yi hakan, na rasa uwar da Fatima ke bashi"
Biba ta ce "Biyayya, soyayya" Ta faɗa tana zuge cinyar kaza a bakinta ta ɗora da "Kin san biyayyarku ba ɗaya bane, Fatima ta iya soyayya ta iya zama da mijinta, kuma ba ki san wani abu ba, soyayyar gaskiya bata da dalili ko hujjar yinta musamman first love, shi kansa bai san dalilin daya saka yake son Fatima ba"
"Mene mafita? Ko mu kashe yarinyar ya zama babu wani abu daya yi saura tsakaninsu" Biba ta ce "Matsalata daƙiƙiyar ƙwaƙwalwa ce dake wallahi, ai da yarinyar za ki yi amfani kina kwashe komai daya mallaka kafin tunaninsa ya dawo, daga nan sai mu je plan ɗinmu na gaba" Ammi ta jinjina kai daga waje suka ji Junaid na ƙwalla kiran sunan Ammi ta miƙe ta nufi hanyar fita. Baba ƙarami ta gani zaune a parlo shi da Junaid sai kuma Zuhura, fuskarta ɗauke da fara'a ta zube a kan ƙafafuwanta ta ce
"Baba ƙarami an yini lafiya? Ya Umman Ustaz?"
"Allahamdulillah"
Ya bata amsa ta ce "Ma sha Allah, Allah ya ƙara girma da ɗaukaka ya ƙara lafiya da nisan kwana, Baffa bai fito bane?" Ya ce "Ba wajan Mansur na zo ba, ƴa ta na zo gani"
"Ƴa kuma?" Ya ce "E, ƴar gidan Muhammad-Bilal" Gaban Ammi ya faɗi sosai domin ta manta da batun wata Ridayya sam ta ce "Au ai yanzu na yi mata wanka har ta yi bacci wajan Baffa" Sosai Baba ƙarami ya ji daɗi ya ce "Ikon Allah shi Mansur ɗin ya ɗauke ta?"
"Sosai Baba, daman rashin fahimta ne kuma yanzu Allahamdulillah na fahimtar da shi idan ta tashi zan zo na kawota ba ruwanta ai bata rigima sam" Ya miƙe ya ce "Sannu Maryam, Sannunki Allah ya saka miki da alheri yadda kika kula da Ridayya Allah ya kula dake" Fara'a kamar zata yi magana a fuskar Ammi ta ce "Ba komai ai ɗa na kowa ne, bamu san wanda zai ji ƙanmu ba, Fatima ta fi ƙarfin komai waje na" Sallama ya yi mata ya bar gidan. Ta samu Baffa zaune a kujera ya yi shiru idanunsa a sama "Baffa" A tsorace ya miƙe jiki na rawa ya ce "Ranki ya dade an yini lafiya?"
"Lafiya lou, ni fa ban ga Ridayya ba" Ya ce "Wace haka?" Ta ce "Ƴar Fatima daka maƙala mini riƙo ita nake magana" Ya taɓe fuska ya ce "And so what? Ki share kawai"
"Mansur!" Ta daka masa tsawa ya ɗimau ce ya zube gabanta ya ce "Na tuba ki yafe mini"
"Kar ka bar su Hajiya su dawo ganin Ridayya ka ce kun daidaita da Fatima ta dawo ka ji ko? Kuma ka fita neman ƴarka wallahi kai hukuma za su rufe bani ba"
A ɓangaren Mami jiki sai addu'a domin bata san idan kanta yake ba tunda da aka kai ta ICU. General ya dawo Anuty Kaltum ta zayyana masa komai ya ce Baffa zai ci Ubansa sai ya karya masa hannu sai ya sauya masa kama zai kuma kulle shi, idan shi mahaukaci ne zai nuna masa ƙarshen hauka, idan mugu ne shi zai nuna masa shi a iya mugunta babansa ne, zai maka shi a court zai yaɗa har Human rights su Unicef duk sun shigo Maganar a ina ya taɓa ganin uwa na raye an bawa kishiya riƙo? Kuma ya ƙwace jaririya ai ko yana da iko yin haka banda a kan jaririya. Ko da Dada ta ji abinda Anuty Kaltum da General suke shirin yi ta dinga masifa ita yanzu ta lafiyar ƴarta take tana sane da komai, kuma za ta yi taking action on it, but not now har sai Mami ta samu lafiya, kuma ko da wasa ta ji labarin Anuty Kaltum ta je gidan to wallahi bada yawonta ba sai ta sassaɓa mata idan ranta ya yi dubu sai ya ɓaci, banda zafin rai babu abinda ta iya. Anuty Kaltum ta fusata ta tattara kayanta ta bi mijinta suka bar ƙasar bakiɗaya.
Lokacin da Ustaz ya dawo da Ridayya daga asibiti ƙaramin yaƙi a kai a gidan, har Baffa na cewa wallahi sai ya ɗaure Ustaz muddin ya ƙara taɓa Ridayya idan kuma da gaske shi ne ya cikinta basu da labari sai a faɗa. Ranar kukan makirci Ammi ta dinga yi tana iƙirarin zata bar wa Baffa gidan, sosai Baba ƙarami ya ji zafin maganar sai bai nuna ba, Umma kuma ta ce idan har ita ta haifi Ustaz wallahi ta sake ganin da yarinyar sai ya san true color ɗinta, ya fusata ya tattara kayansa ya bar garin daman karatu zai je ƙaruwa na shekara huɗu duk a kan Ridayya domin ya bata rayuwa mai kyau, riƙon Ridayya ya dawo hannun Ammi, ta kaɗa ruwan gasara ta ɗora mata cikinta ya kumbura kuma ta hanata ruwa, izaya kala-kala Ridayya ta tashi wata gala-gala sai a kira sunanta bata san ita ake kira ba, kullum tana naɗe kanta yaƙi tsayiwa. Daga ƙarshe maganin bacci Ammi take bata yarinya ta yi ni guda cur tana bacci tana farkawa zata sake bata, har ya yi effecting nata, bata taɓa yi bacci idan ba a bata maganin ba, ta zama ƴar maye wanda ƙarfin maganin ya girmeta ya fara taɓa tunaninta yanzu za ka yi magana yanzu zata manta me ta ce. da ƙyar aka samo ta fara tafiya yi ɗaya biyu zata faɗi ko abinci aka bata ci idan ba gasara ba sa maganin domin su ta sani matsayin abinci sai gayen tuwo. Sanda ta isa saka makaranta Ammi ta ce ba yanzu ba, a tausaya mata ai yarinyar ba wani wadataccen hankali gare ta ba, karatun ma ba lallai ta fahimta ba, dukda cewa akwai makaranta irin ta su ta samu rangwamen hankali. Ustaz har tsayin shekaru huɗu bai dawo ba, ya tafi ta biyar farin ciki ya kama Ammi lokacin ta mallake gida da ita sai yaranta. Baba ƙarami ya daina shiga part ɗin saboda Baffa bai fiya zama ba, arziƙi ya ci uban na da ta ko'ina alheri zuwar masa yake.
Shuɗewar shekaru shida.
(After 6 years)
A hankali ta lallaɓa kitchen ta leƙa tukunyar da ta hangi nama, sau biyu ta taɓa ci amma a rayuwarta tana son nama hannunta na karkarwa saboda rashin ƙwari idanunta na yi mata yana-yana saboda yawan bacci. Wani kyakkawan murmushi ya suɓuce mata lokacin da hannunta ya isa kan tsokar nama ɗaya.
"Ihee Mama, Abbiey"
Domin komai a wajanta Abbiey idan Baba ƙarami ya kira Ustaz sai ya haɗa su, bata iya cewa komai, Ustaz ne yake cewa "Shalale ce Abbiey" da haka ta haddace sunan raɗau a bakinta komai Abbiey. Tana saka naman a baki Ammi na shigowa Ridayya ta yi wuƙi wuƙi da manyan idanunta, tun tuni ta daina kuka ya zama jikinta, a tsorace ta yi baya tsautsayi tukunyar naman ya kife gabaɗaya a ƙasa, Ammi ta ƙunduna ashar ta ce
"Ƴar banza mayya nakashsshiyya tsinanniyar ƙarshen muni mara amfani a cikin mutane wallahi yau za ki san ni ki kai ma ta'addi, daman kin kashi ɗazo a wando" Biba ta leƙo ta ce
"Lafiya Maryam?" Ta ce "Wanne lafiya? Farfesun da na yi wa Alhaji Mansur