Showing 84001 words to 87000 words out of 190738 words
Chapter 29 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt
biyu ina ƙoƙarin posting*
https://www.wattpad.com/1425391962?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=nimcyluv
"Accident? Mace da yaro?" Tajj dake bayan mota ya furta hakan, haka kurum gabansa ya faɗi bai tsaya an buɗe masa motar ba.
Ya ajjiye wayar hannunsa ya fito da sauri yana gyara zama suit ɗin jikinsa ya ce
"Subuhanallahi garin yaya aka bugeta? Is she alive?"
"Sir mun yi ƙoƙarin kauce mata amma mun kasa, da gudu ta shigo gabanmu kamar mahaukaciya ce ma ga baby a hannunta"
Tajj ya dinga kallon wacce ke kwance dukda abin bigeta amma tana ƙanƙame da yaronta wanda ya haska baƙar fatar jikinta. Ya ɗan juya kafin ya kalli sergeant Tukur ya ce
"Katsina to Kano awa ne zai ɗauke mu ne?"
"3 hr (176.0 km) Sir"
Ya yi jim sai kuma ya ce "Zata wahala har tsayin awa uku, ina tunanin za a yi booking Flight ni da ita da babyn kafin ku ƙarasa mun je asibiti" Cikin girmamawa Sergeant Tukur ya ce
"Yes sir"
Tajj bai tsaya tunanin wani abu ba ya ɗauki Ridayya ya sanya ta abayan mota, har lokacin bai ga fuskarta ba kawai ya samu kansa cikin mummunan faɗuwar gaba ne. Little Bilal kuma yana wajan sergeant a haka suka nufi masaukinsu kafin a samu booking Flight ɗin ya zama ready.
Cikin sa a suka samu jirgin da yake shirye da tashi har airport suka kai su a kan idanunsu suka shiga jirgin kuma basu bar wajan ba har jirgin ya tashi da D.c.p Tajj Mujid Baita da Ridayya da kuma babynta, sai sergeant da aka sanya shi cikin tafiyar saboda yaron, lokaci zuwa lokaci Tajj Baita ke kallon Ridayya da fuskarta take a rufe mamakin hakan ya cika sergeant domin ya fi kowa sanin waye Dcp ɗin baya shiga lamarin mace da sai dai idan harkar taimako ne yadda ya nuna tausayi da attention ɗinsa lokaci guda a kan Ridayya shi ne ya fi bashi mamaki sosai.
Aminu Kano Teaching hospital a nan aka kwantar da Ridayya nan da aka sanya mata ruwa tare da yi mata gwaje-gwaje bayan kammala komai Dr ya kalli Tajj ya ce "Office please" "Ok" Tajj ya faɗa yana rufawa Dr ɗin baya jikinsa a sanyaye ya shiga ya zauna sosai kafin Dr ya kalli Tajj ya ce
"Allahamdulillah mun kammala bincikenmu a kan wannan yarinyar?"
"Yarinya Dr?" Dr ya jinjina kai ya ce "E, yarinya zai wahala idan ta cika 17yrs daidai ma. Akwai abubuwan da take buƙata sosai" Tajj ya yi shiru jin hakan ya saka Dr gyara zama yana zame gilashin idanunsa ya fuskanci Tajj sosai ya ce
"Sir da farko tana buƙatar jini a ƙalla leda huɗu kenan,abu na biyu ta samu ƙari a wajan haihuwar da ta yi amma ba a kula ba domin wajan ya ɗan fara kamar ruwa zamu wanke kuma a yi mata ɗinki, a ɗinke wajan tas. Tana buƙatar hutu domin samun nutsuwar zuciya data kwakwalwa idan ba haka ba tunaninta na iya gurɓata ainun ko Depression ya kamata saboda bincike ya nuna mana tana cikin damuwa da ƙuncin zuciya duk wasu alamomin cutar damuwa sun gama bayyana tattare da ita"
"Dr na ji ba damuwa, a yi komai kawai" dr ya girgiza kai ya ce "A'a sir maybe da kwai wani abu ka fara shiga wajan yarinyar ka ganta ko?"
Ya ɗan ɓata fuska yana jan kujerar baya domin duk a gajiye yake ga wani irin bacci dake damunsa a kasalance ya ce "Ba sai na je ba ina tunanin ka tattara baya nan kuɗin ka bawa sergeant"
"Ka dai shiga"
Ganin yadda dr ya takura ya miƙe ya nufi ɗakin da aka ajjiyeta na musamman. Tunda ya ɗora idanunsa a kan fuskarta jikinsa ya yi sanyi ya ƙura mata idanu a hankali kuma ya ci-gaba da takawa zuwa gaban gadon zuciyarta na harbawa da ƙarfin gaske "You?" Ya furta daidai da kunnensa a zuciyarsa yake cewa
"Finally i got you" Wani irin tausayinta nan take ya mamaye zuciyarsa baya son mace cikin wahala da rashin kwanciyar hankali, hankalinsa tashi yake sosai musamman irin yarinyar da a shekarunta ba zai shige ace tana makaranta tana karatu ko gaban iyayenta ba, yana buƙatar sanin wacece wannan yarinyar, daga ina ta fito ina zata, last time ya ganta a Kano yanzu kuma ya ganta a Katsina meke faruwa? Dole akwai wani ɓoyayyen al'amari a cikin rayuwarta wacce ita kawai tasan hakan. Ya ɗan haɗe rai a fili ya ce
"Ba na ce miki ki kira ni ba when you need my help? Shi ne kika ƙi ko gashi nan na same ki ba zan ƙara barinki ba sai na taimaka miki" daidai da kunnensa yake maganar kafin ya juya ya kalli dr ɗin cikin nutsuwa yake masa wani bayanin yana mai ɗan matsa hannunsa
"Zan je gida na dawo kafin nan ka gwada jinina idan zai yi daidai da nata sai a ɗauka ga fuskarta ma kafin wani abinne ya sameta ko?"
"Ƙona ce" Laboratory suka shige aka ɗauki jinin Tajj Baita domin a gwada ko zai yi daidai dana Ridayya daga nan sukai sallama ya nufi reception na asibitin kai tsaye ya samu driver na jiran shi ya shiga bayan mota aka nufi da shi gida. Kasancewar a gajiye yake ya saka ana parking ya fito yana zame ƴar saman rigar tashi a hankali yake tafiya kamar baya so har ya nufi ƙofar farko ya buɗe ya shiga ya sake tura ta biyu ya shiga babban parlourn gidan. Da gudu wata ƙaramar yarinya kyakkawa da ita ta tashi tana faɗin
"Daddy daddy" Ya sunkuya ya ɗauketa yana cewa "Iyee ƴar Daddy kullum tana zaman jiran daddynta" Murna ta kama yarinyar ta ce
"I miss You Daddy jiya na dinga kuka a kai ni wajanka amma Mahmah taƙi ya" Mahmah dake fitowa daga ɗaya parlourn ta ce
"To farfesa komai a kai kamar kina kira ubanki ya dawo ki wassafa masa ko gulmarsa mukai a banza mukai" Yarinyar dai ta yi shiru ta lafe jikin babanta. Mahmah ta nemi waje ta zauna, shi ma Tajj ya zauna kusa da Mahmah ya ce "Barka da rana Mahmah mun same ku lafiya?"
"Allahamdulillah Tajuddeen ya aiki? Ka zo lafiya" ya ɗan gyara fuska ya ce "Aiki sai addu'a kawai Mahmah ko jiya an kai hari Katsina fa sun kwashe ƴan mata wallahi"
"Wannan ƙasata mu ko yaushe komai zai zama daidai? A dinga sace jama'a musamman ƴan'mata ga kashe al'umma ba gaira ba dalili idan zaɓe ya ƙaratu an dinga abubuwan da basa tafiya daidai" rufe idanunsa yana shafa kansa sosai. Jin ya yi shiru ya sa Nadra cewa
"Daddy Uncle ya zo yana nan" Idan ta ce Uncle ya san wa take nufi kuma bai yarda da maganar ta Nadra ba, yasan halin surutunta Uncle ba zai taɓa shigowa Kano ba saboda ya tsani kano a yanzu ɗin kuma daman rabon Uncle ɗin da gidan su Tajj har ya manta. Don haka ya share maganar ta Nadra ya rufe Idanu yana ji tana jan samarsa. Mahmah dake zaune ta ajjiye remote ɗin hannunta ta ce "Ustaz bari a ƙarasa kammala maka tuwon ko?"
Shiru kamar ba zai yi magana a hannun Tajj ya ji saukar muryarsa a nutse cikin kunnensa ya ce "No" Ya buɗe idanu sai kuma ya juya kallonsa ya sauka kan Muhammad-Bilal Ustaz dake zaune a saman kujera ya kishingiɗa a gefe kamar mai yin bacci fuskarsa a haɗe sosai tamkar bashi ne ya yi magana yanzu ba, dukda maganar bata arziƙi ba ce. Sosai Tajj ke kallo Ustaz ganin yau gwarjininsa ya fito ga wani irin kyau da ya yi ko dan bai taɓa ganinsa cikin wagambari ba? Getzner wagambari brocade ce a jikinsa sai ɗaukan Idanu take kana gani kasan an kashe kuɗi wajan siyan shaddar. Blue green ce ta yi wa farar fatarsa masifar kyau gashi saje da ƙasumba sun ƙara cika fuskanta ya gyara sosai sukai ma fuskar kyau nutsuwa da haibarsa ta sake bayyana ƙwarai a fili. Ya ɗan ɓoye shekarunsa ta hanayar tsare gira kodayaushe baya ƙaunar raini.
Tajj ya haɗe fuska shima ya ce "Lallai Babban mutum kana ciki na shigo amma ba magana?" Ustaz bai ɗago kansa ba balle ya kalli Tajj ko ya kula shi a nutse kawai yake danna wayarsa shi bai ma san me yake dannawa ba kawai rashin sabo da yin maganar ne ya saka ya fara danna wayar.
"Lallai ya yi maka kyau, ina yini ka zo lafiya zuwa yaushe?" A hankali ya ɗago idanunsa ya kalli Tajj sau ɗaya sai ya zame ganinsa ya yi shiru wasu daƙiƙo a shirun nasa can ya numfasa ya ce
"Kana lafiya Tajuddeen?" Tajj ya watsa hannunsa ya ce "Lafiya lou nake Babban mutum ya leges kuma? Ban yi tsammanin ganinka a Kano ba, ka ci sa a ni ma yau na shigo gari" Ustaz bai yi magana ba don zancen na Tajj ya masa yawa "Mahmah a kawo mana abincin nan ki kawo man shanu daban ni ban so Friend dai yana so"
"Ai da yake kai ne maybe ya ci, amma daman shi idan an ce abinci sai ya ce I'm full" Tajj ya yi dariya sosai ya ce
"He is always full daman amma banda yau" bayan tashin Mahmah Nadra ta bi bayanta tana tsalle Daddy ya dawo, ta ƙasan idanu Ustaz ya bi Nadra da kallo yana so da ƙaunar yara a hankali ya lumshe idanunsa yana tunanin yaushe zai samu nasa ne? Me ya sa ƙaddara ta yi masa kutse tare da yi masa tabo a zuciya me ya sa a kullum ƙaddara ke bibiyar rayuwarsa ne? Ya san hakan tabbatacce ne kuma al'amarin Ubangiji ne, tarihinsa ba zai taɓa cika daidai ba dole sai da sunanta rayuwa da ƙaddara abu ɗaya ne kamar yadda karatun littafin yake abu ne mai wahala na rashin sanin meke ƙunshe a cikinsa, idan ka karanta wannan shafin ba zaka san mene a shafin gaba ba dole sai ka buɗe to lissafi haka ne yaƙini da wanzuwar karatun littafin ƙaddararsa dole idan anga sunansa a gaba kaɗan za a ga nata bashi da tabbacin da numfashi da tunaninta wani ya fi yawa a ƙirjinsa. Ya ɗan sauke ajjiyar zuciya a sauƙaƙe yana riƙe yanayin da yake ji wanda ganin Nadra ya dawo masa da shi.
"Ga abincin fa ina ta magana". "Azumi"
Ustaz ya furta a taƙaice yana ɗauke ƙafafuwanta ya tanƙwashe saman kujerar parlourn Mahmah da shi wani ɗan gata ne tausa yake buƙata a gajiye yake sosai, ba uwa ba uwa ba ƴan'uwa ba mata ba ƴaƴa Maybe bashi da wani rabo ne. Tajj ya ce "Me ya sa kullum cikin azumi kake ne Ustaz? Ba a gane azumin lada dana kai da kai? Kalli yadda ka rame ka saurara da yin azumin nan"
"Kana da matsala da azumi na ne Baita?" Da sauri ya ce "Of course ina da shi ko dan lafiyarka" Ustaz bai sake magana ba sai da Tajj ya yi surutunsa shi kaɗai ya ga ji ko tari ya ji Ustaz bai yi ba kamar daga sama ya ji ya ce
"Labarin yarinyar na zo ka bani, ka sameta? Wace ita?" Ya yi maganar ɗaya bayan ɗaya yana mai jan gemunsa Tajj ya ce "A'a, nama manta da ita wannan ne dalilin zuwan naka?" Kafin ya yi magana an kira Tajj an sanar da shi jininsa bai yi daidai dana Ridayya ba. "Shikenan zan zo"
"Wai wanne labari kake da shi a kan Ridayya ne? Nifa bulayi nake bara a kofai ko ganinta na yi i can't recognize her saboda ko a picture baka taɓa nuna mini ita ba, kasa na fara tunanin ko dai son ƴar rainon taka kake yi labarin rainonta kawai na sani ba ita ba please ka nuna mini ita maybe ma na taɓa ganinta rashin sani ne" Ustaz ya miƙe ganin yana ƙoƙarin fita ya sa Tajj miƙewa ya ce "Ɗan jirani"
Ustaz ya fita zuwa waje ya shiga motarsa mai kyau blue black ce mai baƙin glasses ya ɗan jima kansa kife a jikin hannun motar kafin Tajj ya shigo ya ce "Muje" a hankali Ustaz ya yi bismillah ya yi wa motar key suka fita daga babban gate kai tsaye Tajj ya ce "Aminu Kano hospital please" Ya sauya direction mamakin shirun Ustaz da miskilancin shi yake bawa Tajj mamaki. Suna ta ce ya ce "Mun yi magana da Hajiya ai ta ce lallai nasa ka nemo matar aure ko kuma duk wacce ta yi mata wallahi ta aura mata cikin watan nan, kuma ni na yarda ta maganarta wallahi ka nemo matar aure ko na ce ka bata zaɓi"
"Ina ta magana ka yi shiru" Gabaɗaya Ustaz ya saki kan motar ganin yana neman kashe su jikin Tajj na rawa ya riƙe motar ya ce "Babban mutum mene haka kashe mu za ka yi saboda ka ga ji da rayuwarka?"
"Wallahi zaka fita daga motar nan da gaske zaka fita mtwsss"
"Commissioner guda kake wa haka? Tsawa fa yau guda yafiyar da kake nema wa jama'a bari na nemaka Allah ka yafewa Ustaz kar na kama shi na kai bayan kanta" har suka ƙarasa asibitin kamar an ɗinke bakin Ustaz yana kallo aka ɗauki jininsa leda biyu amma bai tambayi dalili ba, tambayar ma wahala take masa. Jiri na ɗan ɗaukar shi ya kifa kansa tsakanin cinyoyinsa. Mintina wajan goma ya ji muryar wani na mita..
"Tab gaskiya Yaya ka yi haƙuri i can't, jinina fa? Daman shi ne kiran da kake ta mini kamar zaka fasa mini dodon kunne"
"Ni kake cewa zan fasa maka dodon kunne? Zauna a ɗauki leda biyu ai aikin lada za ka yi banda rigima da rikici mai ka ajjiye har cewa na yi ina nemanka ka ƙi zuwa wai kar na juya ka?"
Ya haɗe fuska sosai "Da tausayi ɗaukan jini har leda biyu a wannan zamani salon ka saka wacce zan aura hasara, ni a faɗi nawa ne kuɗin na biya a siya kuma taimako ba sai mutum ya yi niyya ba"
Tajj ya juya ya kalli dr ɗin dake ta dariya yana mamakin ƙarfin halin mai maganar commissioner guda yake faɗawa haka shi kuma Tajj ya san matsalar baya son allura ne duk wannan hanya-hanya ɗin
"Lallai yaron nan au matarka? Oya zauna a ɗauki before i shoot your legs" ya ƙara yin kicin-kicin da fuska kamar ya ce ya shiga uku shi ya ɗauka ma bashi da lafiya ne da har ya kira shi zuwa asibiti ya zo
"A'a kafa daina ce mini yaro shekara 30 ba kwana uku bane ni kaga ma bana jin daɗi na ci maiƙo yau Olser ta mini mugun kamu"
Tajj ya dake ya ce "Dr ɗauki jinin please kar ka saurari maganarsa"
Ya girgiza kai tuni ya rikice ya ce "A'a dole a ji reason ɗina idan ba gado kake so a bani a nan ba, kuma a bari na shirya"
Kamar an tsikari Ustaz ya miƙe tsaye yana daddafe kansa yana jin kamar kansa zai rabe har tsakiyar kansa ya ke jin musayar yawun nasu ga wani jiri dake ɗaukarsa da ƙyar ya riƙe jikinsa ya fice. Da ƙyar ya bari aka ja jinin yana ta mita tunda aka soka allurar ya yi tsit fuskarsa ta sauya ana gamawa ya miƙe ya yi luuuu zai faɗi Tajj ya riƙe shi ya ce
"Be careful" a ƙasan maƙoshi ya ce "Cika ni" muryarsa ba wasa ya haɗe rai tamau kai ka ce shi ne gaba da Tajj Baita ɗin ya nufi ƙofa sai da ya je ƙofa ya tsaya ya ce
"Kuma wallahi sai ka biya ni ko na kwasa a kuɗinka" Yana faɗin hakan ya fice mamakin ƙarfin jininsa ya cika Tajj domin kamar bashi ne aka ɗauki jini har leda biyu a jikinsa ba. Nan da nan aka ɗaurawa Ridayya jinin Ustaz ya fara shiga jikinta bayan sun keɓe Tajj ya ce
"Dr matsalar fuskarta da kuma fatar jikinta fa?"
"Ina tunanin sai dai ku je asibitin Bela nan za ku samu likita mai kyau" godiya ya yi masa kafinwya fito daga Ustaz har mai mitar kowa ya shiga mota ya fice da ra'ayi iri ɗaya a zuciyoyinsu.
Sanda Tajj ya ga Little Bilal mamaki ne ya cika shi banda yasan waye Ustaz babu shakka da ya ce wannan jininsa ne ko kuma ɗansa ya ɗauki yaron ya koma gida Mahmah ta yi masa wanka ta sauya masa kaya nan da nan Tajj ya shiga yi masa pictures da video yaron sai dariya yake yana lumshe idanunsa ya ɗora shi a status da caption ɗin _My lovely son_
Zirga zirga take yi hankalinta yaƙi kwanciya ta juya ta kalli Zuhura ta ce "To yanzu da kika dawo gida da zuƙar yara uwar me zan yi miki? Kina nufin kashe aurenki za ki yi ki zo ki tare mini a gaba ko mekike nufi"
"To Ammi ni ya zan yi ne baya bamu abinci kullum cikin wahala nake gashi ni bani karatu na yi ba balle na samu aiki haka kurum yunwa ta kashe mu" Ammi ta ce
"To ba kece ba tun ina lallama ki ko ƴar diploma ki haɗa amma karatu baya gabanki yanzu wa gari ya waya ki barni da abinda yake damuna mana" Zuhura ta fashe da kuka ta ce "Wallahi don ba ki san wulaƙancin da Nura yake mini bane a cikin gidan nan kamar wanda ya fara neman mata. Kwata-kwata bana jin daɗin zaman gidan mijina"
"To dan ubanki ni daɗin zama nake a gidan uban naki, kina kallo yadda komai yake neman fin ƙarfina sai na yi kwana biyar a cikin gidan nan ban saka Alhji a Idanuna ba, sisi ta daina haɗa da shi ya tattara komai ya liƙe a gindin wancan shu'umar matar wacce ta gama a sirrice shi, ki duba ki gani wai don duk ya daidaita abubuwan da suka faru tsakanin Babban mutum da mummunan wannan yarinyar ya liƙa mana hatsarin ƙarya"
Zuhura ta ce "Ammi ai ba hatsarin ƙarya bane kawai dai Allah ya kiyaye muna da raguwar numfashi da motar da akai hatsarin da ta mu iri ɗaya ce muna baya ɗaya motar na gaba ta mu ta shiga cikin jeji ki duba yatsan Khaliperh kusan cirewa ya yi, kuma ni ina maganar gidan mijina mene nawa da nan gidan fisabilillahi"
A harzuƙe Ammi ta ce "To ba dole sai ina da kuɗi zan ji da matsalarka ba, addu'a nake Allah ya rusa farin ciki da