Showing 99001 words to 102000 words out of 190738 words
Chapter 34 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt
wanda ya riƙe ta yaushe ma ya zo gidan?
"Ina magana" a hankali ta ce "Babu kowa"
Wata razananniyar tsawa mai lafiya ya daka mata ta cikin wayar wacce ta kaɗa hantar cikin Ridayya tana mugun tsoron tsawa ko ihu a ka yanzu zata gigice. Nan da nan ta ruɗe tana ƙoƙarin kashe wayar a hargitse kuma a kasashe ya ce
"Don't try it" kuka ta fashe da shi sosai ta kasa magana yana ji tana kukan bai ce komai ba can dai ya kashe wayar.
Tsakanin minti biyar da kukan ya kira taƙi ɗagawa saboda tsoro ya yi mata DM da
_"Idan na ruske ki gidan Mahmah abin ba zai mana kyau ba ni da ke Shanshan. So pick my call"_
Tana gama karantawa ya kira hannunta na rawa ta ɗauka ta kasa magana bisa mamakinta sai ta ji ya sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya mai ƙarfi kuma muryarsa can ƙasa kamar ba Sadauki ba ya ce
"I am sorry Shanshan kar ki yi fushi dani" Ta yi shiru ya ce
"Ridayya ina da zuciya a nan ɗina" Ya nuna saitin ƙirjinsa dukda bata ganinsa "Yeah! Ina da zuciya kuma ina da masifar kishi a kan abinda nake so, idan da akwai abinda Ubangiji ya jarabce ni da shi a kwanakin nan bai shige ba, ke ɗin ƙaddarata ce kuma wallahi tallahi ba ki isa ki zama ƙaddarata ba sai dai mu zama ƙaddara juna. Ki saka a ranki duk inda kika sanya ƙafa za ki ga Sadauki a wajan, kuma ni na fi ƙaunar duk abinda yake bani wahala ko yake nuna mini ƙi so don't ever trying to reject me kar ki ce za ki bani wahala don sai dai mu wahalar da juna, yadda bana iya bacci ba zan barki ki runtsa ba sai dai idan ya kasance kina gefena ina jin saukar numfashinki a ƙirjina ina riƙe dake yadda na san ba za ki guje mini ba"
Tsoro ya kama Ridayya da ƙyar ta ce "Me ya kawo maganar nan Sadauki i think it's over between us, everything is over between us.....,"
"Uhm ko?" Shiru ta yi zuciyarta na bugawa dukda bata ganinsa tsoro da fargabar abinda zuciyarta ke ƙoƙarin ɗarsa mata a kan Sadaukin ya fara gigitata dukda ƙoƙarin da take na danne hakan bata son yarda ko gasgata hakan bata so bata shirya ba, ha dan komai ba sai dan illar da namiji ya yi mata a rayuwa a cikin kunnenta ta tsinkayi kalmar daya faɗa
“I have a feelings for you Ridayya no fall in love with you"
"Sadauki please, the game is over ka je wajanta ka faɗa mata"
A hankali cikin muryar tausayi ya ce "E zani, amma ke za ki rakani na faɗa mata yanzu ma ai ina rihazal ne"
Ta sauke numfashi ya ce "Ki yi haƙuri please na miki tsawa ban so ba" nan ma ta yi shiru ta ɗauka ba zai sake magana ba ne sai ta ji ya ce
"Zan zo fa, ba rana kawai ki jira zuwana bye ki kula mini da kan ki Shanshan ki shafa mini kan Son"
"To" kashe kiran ya yi ta jingina tana lumshe idanunta gabaɗaya abinda bata taɓa ji ba shi ke ƙoƙarin mamaye ta tare da yi mata shigar saurayi Sadauki yana da rigima kuma da saurin shiga rai don dole tana jin daɗin yadda yake ƙaunar Little har zuciyarta.
Sadauki na gama wayar ya miƙe ya nufi down stairs ya iske mother zaune tana kallo ya ƙarasa kusa da ita ya yi shiru yana kallon waje guda abu ne mai wahala Sadauki ya zo kusa da mother ya mata surutu ba shirun nasa ya bata mamaki ta ɗan taɓa jikinsa ta zare ido ta ce
"Baka da lafiya Sadauki?"
Ya girgiza kai kawai bai ma san me yake ba "Ya zaka girgiza kai bayan ga jikinka nan ya yi zafi, daman tunda ka shigo ka shige ɗaki na lura ko abinci baka ci ba what is the matter? Meke damun Sadaukina?"
"Ki yi mini addu'a mother ki sani cikin addu'arki don Allah" Ya faɗa yana lumshe idanunsa tare da ɗage girarsa kansa na yi masa wani irin ciwo ga zazzaɓin daya rufe jikinsa lokaci guda
"Addu'a kullum cikin yi maka nake ita Sadauki shi ya sa bana son ka saka abu a rai ka ƙwallafa na ci a kai. Ka yi ta addu'a ka ji ko komai ya yi zafi maganinsa Allah duk wata jarrabawa tana tare da nasara"
"In sha Allah love thanks"
Da daddare bayan sallar issha Ridayya na kwance a kan gado damuwarta ta dawo sabuwa fil ga tunanin rashin gata da iyaye ga tunanin Zameer da fargabar abinda zai iya aikatawa a kanta. Ga tunanin video idan ya fita da wanne idanu zata kalli Junior? Ta yi masa bayani ga al'ummar gari da suka shayar da ita maɗaci ga tunanin Sadauki da rigimarsa da sauyin da ya yi na lokaci guda idan ta tuna kalar rayuwar da ta yi a gidan aurenta sai ta ji a duniya ba abinda data tsana irin namiji da kuma aure idan ta tuna ƙauyen Batsari sai ta ji ko sunan Katsina bata ƙaunar ji.
A hankali take jiyo sautin muryar Tajj yana magana yanayin yadda yake shiru ya bata tabbacin bashi kaɗai bane a parlourn koma shi da waye muryar Tajj ɗin ita ce a sama wancan ɗin kuma maganar tasa gajeriya ce domin sai Tajj ya jima yana magana kafin ta ji ya yi shiru.
Yunwar da ta ci ƙarfinta ne ya sanya ta miƙe bisa dole ta sanya slippers tare da ɗora hula ta fito duguwar rigar bacci ce a jikinta wacce ta kwanta ta haska dark black skin ɗinta hasken idanunta da jajayen laɓɓanta kawai ake gani sai tulin gashin girarta.
Magana yake a nutse hannunsa riƙe da cup yana ɗan juyawa kaɗan saboda zumar dake ƙasan kofin fararen ƙafafuwansa gabaɗaya ya zuba su saman table ɗin da aka jera masa abin buɗe baki daman haka ɗabi'arsa take ko ya tanƙwashe ƙafafuwansa ko ya miƙar dasu saman abu. Kaɗa ƙafar yake a hankali yana jin Tajj na cewa
"Ai ni dole ya zame mini na yi maka biyayya babban yaya duk yadda ka ce haka za a yi amma nasu ka bari ba yanzu ba ko zuwa next week ne"
"Tajuddeen ina buƙatar hakan da ganin gilmawarta, ita ɗin wasiyya ce so a yi hakan"
"Ba zaka barta ta ƙara satin guda ɗin ba?"
Wani irin kallo Ustaz ya yi wa Tajj irin ai ko kwana guda ban ƙara barin Ustaza ta yi a Kano.
"Akwai aikin da zan gabatar na kwana uku zuwa huɗu haka. Zan jira bisa dole na gode da ɗawainiyya Allah ya yi maka Albarka"
Tajj ya yi dariyar dole ya ce "Amin Babana Abbiey"
Tsit ya yi kamar ruwa ya cinye shi bai san ta fito ba sautin da ƙirjinta ke bayarwa ya alamta masa hakan. Ya miƙa hannu ya kashe hasken ɓangaren shi tare da yin baya ya kwanta jikin kujerar idanunsa zube a kanta ganin yadda take tafiya kamar bata so Tajj ma ya bita da Idanu da kalar nasa tunanin ba jimawa ta fito ɗauke ta kofin shayi mai madara sosai ta nufi cikin bedroom ɗin da ƙyar ta ƙarasa domin ta kusa kifawa a jikinta ta ji kallonta ake.
Sun jima dukda tun tafiyar Ridayya ko tari Ustaz bai kuma yi ba. 12 daidai ya miƙe hannunsa riƙe da babbar rigarsa da key ɗin mota hular ma a hannunsa ya riƙe sumar kansa nata lilo a gefen fuska da wuyansa.
"Ba a nan zaka kwana ba dama? An gyara ɗaya part ɗin"
Ustaz ya yi kicin-kicin da fuska yana ƙanƙance idanunsa a hankali ya ce
"Ubangiji ga Tajuddeen ka yafe masa da tunanin Muhammad-Bilal zai kwana gidan mutane"
"Ya yafe maka dai Babban yaya kuma babbanmu"
Ustaz bai kula shi ba ya nufi bedroom ɗin da Ridayya ke ciki bakinsa ɗauke da sallama can ciki yasan abu ne mai wahala ba ta yi bacci ba, bata kaiwa haka ido biyu. Haske ya gauraye ɗakin tana tsakiyar gadon ta rungume Little ya ƙarasa jikinsa na yin sanyi bai kalli fuskarta ita ɗin dai yake kallo ya kalli shayin data ajjiye ya ɗauka ya kurɓa da ƙyar ya haɗiye yana runtse Idanu
"Iyayi dai Ustaza iyayi ne hakan da gaske suger ya miki yawa"
Ya dinga bin ɗakin ko wacce kusurwa da addu'a bayan ya gama ya saka hannu ya rage mata sanyin ɗakin yana jinjina wawtar Ridayya da bata san illar sanyi ba ya ja mata fargo a hankali ya durƙusa dab da fuskarta sai kuma ya janye jikinta yana kashe hasken ɗakin.
Washegari kiran Sadauki ne ya fara shigowa wayarta ta ɗauka da ƙyar kafin ta yi magana ya ce
"Subhi ce Shanshan kina ta bacci abinki"
"Abbiey" ta furta domin shi ne ya zo bakinta saboda ƙamshin shi ta ji
"Mijinki ne wannan ba Abbiey oyya wake up sweetheart"
"Oh bari na yi sallah"
"I'll call you later ki yi mana addu'a Allah subhanahu wata'ala ya ji tausayin Sadauki ya mallaka miki ke matsayin mata" Murmushi kawai ta yi ta kashe wayar.
Manyan mutane ne a cikin haɗaɗɗen parlourn duk wanda ka gani kasan sunansa ya yi amo ko wani shi a jihar. Zama suke na musamman wanda ya shafi yaran jam'iyya da shugaban jam'iyyar gabaɗaya.
Ya gyara zama cikin nusa iko da jin daɗin abinda yake faruwa ya ce
"Mu hakan ya yi mana kyau, su yi ta gwara kansu ya su ya su, za mu yi amfani da wannan damar wajan cimma manufarmu"
Hon. Mubarak Nas ya numfasa ya ce "Mene manufar ta mu madugu? Kaga kawo yanzu sun fi mu ƙarfin jam'iyya tun da ba mu jima da sauya wannan jam'iyyar ba"
"Na gode Allah da ka ce ƙarfin jam'iyya suka fi mu ba masoya da magoya baya ba, za mu yi musu kwantar ɓauna mu fid da ƴan'takarkaru kama da ga Gwamana mataimaki ɗan'majilissa na jiha dana tarayya, ƙasar ai ta mu ce ƴan'uba muka samu dole kuma zata dawo hannunmu"
Hon Iyantama ya ce
"Wannan haka yake kuma za a samu ƴan'anti fati kawai mu tsayar da kyakkawar manufa kar mu yi lako lakon da za a yi mana irin ta shekarun baya a ƙwace mana mulki mu shiga court a banza tunda kaga har koton ƙoli mun shiga amma result ɗin ɗaya ne, Shitu Bala shi ne Gwamna talakawa an saka musu tsoron fitowa sake bin wani layi domin kaɗa kuri'a"
Madugu ya ce "Wannan tsoron za mu cire musu mu tabbata sun tsaya akan a ƙidarsu da kwatar ƴan'ci ba wani dalili da zai zo a watsa musu hatsi kamar kaji su bi su tsince"
Hon. Mubarak Nas da Hon Iyantama duk sukai ma'ana da maganar uban jam'iyya madugu.
"Prof ana ta magana ka yi shiru?" Prof Hamdan Hamish ya ce "Gare ni komai yana going well"
"Prof ai shi ne ɗan'takararmu na ɗan majalisar Jiha ina fatan baka da wani abu a ɓoye wanda zai kawowa kujerarka tsaiko yana da kyau mu kawo ko wacce kujera"
Prof ya yi shiru sai kuma ya ce "Ba wata matsala, yanzu waye zai zama ɗan'takarar Gwamna a jam'iyya T.D.A?"
Madugu ya miƙe tsaye yana ɗan takawa cike da ƙarfin qiwwa kafin ya ce "Wanda za mu bawa kujerar Gwamna ba lallai ya amince ba, amma dole mu sanya masa ƙaunar hakan a zuciyarsa yana da farin jinin al'umma kuma bashi da wani tsaiko ko mugun halin da zai kawo barazana a kujerar da jam'iyya bakiɗaya ganinsa zan binka ai yana gari dole ya dawo mahaifarsa ya ceceta"
Da haka taron ya watse Prof na hanyar zuwa gida saboda kiran da Sadauki ya yi masa secretary ya tura saƙo kamar yadda yake nuna musu namiji da sauri ya juya kan motar zuwa hotel ɗin da suka saba haɗuwa.
Hajiya ta tashi Mai ran ƙarfe shi da wani mutumin nemawa Ustaz auren Mardiyya bayan sun je kawun Mardiyya ya yi mamakin jin Ustaz na son Mardiyya ya yi farin ciki da hakan domin ya san waye Ustaz girmama mutane sadaƙa da tausayi da ƙare hakƙin addini. Ya ce su je za su yi bincike kuma su zauna da yarinyar domin jin ta bakinta. Haka aka yi nan take Mardiyya ta ce tana son Ustaz kamar rai kuma ta amince. Suka ce za su kawo kuɗin na gani ina so da sadaki da lefe lokaci guda kuma a baki sun saka aure sati uku kacal as soon as Ustaz ya dawo Legas zai zo gaishe su kuma za a haɗu da komai na biki kawai yarinya ta zama cikin shiri ta faɗi duk mai take buƙata shi Ustaz na can Kano bai san meke faruwa ba.
Kwana huɗu Ridayya bata kuma saka Ustaz a idanunta ba tama manta da hakan tun abinda ya faru shima Ustaz tun daren bai ƙara zuwa ba abubuwa sun ɗan sha masa kai ƙoƙarin ajjiye matsayin Md yake a fidelity bank ɗin.
Yana zaune wani baƙin yadin kaftani ne a jikinsa mai kyau da laushi ya kwanta a jikinsa sosai ya ƙara haska farar fatar da har wani yellow take saboda haske. Babu babbar riga yau hannun rigar ma half ne saboda ciwon da kansa yake masa ya saka ya ajjiye zanna bukar ɗin a gefe sama-sama yake jin maganar Tajj suna zaune har a ka yi sallama.
"Sadauki wai yaushe gidan Mahmah ya zama gidan zuwanka?"
Sadauki yana kaɗa ɗan'mukullin motarsa brown ɗin wagambari ne a jikinsa ɗinkin 3 fisis na maza an jera masa bottles a tsakiya ya ɗora jaddara a kansa ya yi miskilin murmushi ya ce
"Uhm Commissioner kenan"
"Kira ni da sunan Hamza ai kaɗan daga cikin aikinka"
Sadauki ya girgiza kai ya ce "Ni yau ba faɗa na zo yi ba, unguwa za a rakani"
"Ikon Allah Mahmah ɗin ce zata rakaka unguwa ko Nadra?"
Sadauki ya gyatsina fuska ya ce "Me zan ɗauka da wannan ƴar'taka mai surutun tsiya, kuma ai ba su kaɗai bane Ridayya na zo ta rakani"
Cak Ustaz ya tsaya da danna wayar da yake yana nanata sunan wacce yaron ya kira yaushe Ustaza ta zama haka? Har take wa maza rakiya? A zahiri ba zaka taɓa cewa Ustaz ya san me suke cewa ba.
Tajj ya kasa cewa komai. Sadauki ya ɗauki waya ya kira numberta tana ɗakko ya sauke ajjiyar zuciya ya ce "Shanshan ina parlour ina jiranki, magana za mu yi very important a hanya, na nemi izinin Commissioner karki ji tsoron wannan bogin bindigar tasa, waiting for you"
Kashe wayar ya yi babu jimawa sai ga Ridayya ta fito cikin wata pink ɗin abaya mai kyau ta yi rolling kanta da vail ta yi ƙiba amma kana ganinta kasan bata cikin nutsuwa.
Tajj na jin lokacin da Sadauki ya sauke numfashi ya ce
"Rest of my life, i so much love you my ride or die"
Kanta a ƙasa ta ƙarasa tana ta wasa da yatsun hannunta "shall we?" Sadauki ya faɗa
"Abban Nadra zan raka S....."
Tajj ya yi murmushi a ransa yana cewa wannan faɗan da umarnin ba nawa bane.
Ridayya kowa maganar ce ta tsaya mata lokacin da idanunta ya sauka a kan Ustaz so da gaske shi ɗinne? Ta dinga kallonsa jikinta na rawa Sadauki ya ja mata masifa gashi ko inda take Ustaz bai kalla ba kuma tasan sarai ya ji muryarta.
"Mu je mana?" Cewar Sadauki ya faɗa yana miƙewa tare da kallonta
Ta kasa motsawa kanta a ƙasa a ɗan hargitse Sadauki ya ce "What are you afraid of.......,?"
Jin Sadauki na neman fasa masa kai ya saka Ustaz ajjiye wayar tare da ɗaga fararen idanunsa yana shigar da su ciki ya kalli Ridayya sosai da kyau sai ya ɗauke ganinsa
"Koma ciki"
Ya faɗa cikin nuna umarni da sauri ta juya Sadauki takaici kamar ya fashe waye wannan ɗin da zai nuna masa iko da Ridayya?.
Ustaz ya miƙe yana ajjiye wayarsa ya nufi ɗakin Ridayya ya murɗa ya shiga tare da saka key ya zare ya cillar saman wardrobe. Jikin Ridayya sai rawa yake da ɓari bakinta na karkarwa
"Abbiey da gaske kai ne? Ko mafarki nake yi Abbiey nane?"
Kallonta kawai yake yana nufar inda take tsaye bai san me yake ba shi dai ya tsinci kansa a gabanta ne hawayen fuskarta sun jiƙa masa tafin hannu kuka ta fashe da shi tana yin baya gani take har yanzu mafarki ne
"Daman nasan mafarki ne ba Abbiey bane me ya sa kasan ba kai bane zaka kora ni ka hanani bin Sadauki?"
Sai a lokacin ta girgiza kai yana jin kalamar Sadauki a kansa a fili ya ce "Ba ki da kai Ustaza"
"Innalillahi wai mafarki nake ko Idanu biyu muryar Abbiey nake ji Abbiey..m.," bata ƙarasa maganar ba ta ji ya cafko hannunta tare da haɗe ta da jikinsa ya riƙe ta gam a ƙirjinsa ba daidai kunnenta yana sauke numfashi ya ce "Ustaza Oum-Bilal" ya faɗa yana yi mata wata kyakkawar rungumar da shi kansa bai san ya yi ba.
Karanta ki yi comment ki danna share to all your groups
*MUNAFUKIN MIJI 30*
Mikiya Writers Ass...
Bright pens free batch
Nimcyluv sarauta
Zazzare Idanu ta yi sai ta ji wani iri ta kasa kallonsa sunan Oum-Bilal ya yi mata wani iri. Sakin ta Ustaz ya yi bayan ya gama zuge mata zip ɗin data mance bata rufe ba, wanda shi ne dalilin biyo bayanta da kuma kusancin da suka samu wanda a tunaninta rungumeta zai yi.
Ya ja baya tamkar bashi ya yi magana ba ya ce
"long time Sayyada, irin zuba kyau haka?"
Ridayya ta kasa ɗago kanta dake ƙasa tsoro da kunyar Abbiey ɗin ya mamaye mata zuciya, tunanin hukuncin da zai yi mata a kan Sadauki kawai take yi, daman yasan tana nan amma ya kasa nemanta cikin shekarun nan ko watanni?
"Zo mana"
Ustaz ya furta a taushashe bayan ya gama daidaita zaman shi a saman gefen gadon ɗakin nata idanunsa a kan wayarta dake ringing an rubuta “Sahibi”
Ta ƙarasa tare da zubewa a gabansa ƙasan ƙafafuwansa ko zama ta kasa bakinta na rawa ta ce
"Ina yini Abbiey?"
"Allah ya yafe miki Ustaza ba haka muka saba ba kin ji ko"
Hannunsa na dama ya miƙa mata a hankali ta ɗago kanta tare da cira hannunta na dama ta miƙa masa sukai musabaha ya riƙe ɗan mitsitsin hannu idanunsa zube a fuskarta ya ce
"Assalamu'alaiki"
"Wasallamu'aika Abbiey"
"Sannu Oum-Bilal kina lafiya dai? Komai ƙalau?"
Ta jinjina masa kai ya zame hannunsa yana yin baya ya jingina da jikin frame wasu sakanni ya ɗauka kafin ya ce
"Masha Allah. Rabbi ya yi miki albarka"
"Amin"
Ta