Showing 135001 words to 138000 words out of 190738 words

Chapter 46 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17328

yi saurin saduda ba har haka, girman abin da yake karantawa tamkar zunubi ne a wajan shi hakan ya saka Baba ƙarami rufe paper ɗin ya yi shiru na wani lokaci yana jan numfashi.


A wannan karan cikin muryar rauni ya kira Umma ya ce.


"Me kika ɗauki bazawara ne?"


"Ni ban ce na ɗauketa wani abu ba, amma yana da kyau ko wanne saurayi ya auri budurwa don Allah ka yi mini adalci"


Sai ta fashe da kuka sosai ta ce "Ni da kai na faɗa maka Babban mutum yana son Ridayya, ka ce mini taya na sani, ka sani ni uwa ce a cikina ya fara rayuwa kafin ya zo duniya dole zai fi kowa sanin waye Ustaz halinsa da ɗabi'unsa duk uwar da zata ce bata halin ɗanta ba wallahi ƙarya ne, idan yaranka goma ka san halin kowa, i told you abaya kan ka yi wani abu, tun kafin alaƙar su biyu ta yi zurfi but you refused ka ƙi ka share, shikenan bashi da aiki sai ƙarar da lokacinka a kanta, wayyo ta ce yanzu zai yi zumbur, sanda ta fara girma ba shi da nutsuwa tunaninsa kar shukar da ya yi wani ya zo ya girme kar ginin daya jima yana yi wani ya rusa, shikenan zarya from Lagos to Kano daga Kano sai Lagos saboda Ridayya, ya ƙarar da ƙuruciyarsa samartakarsa duk saboda farincikinta. A karo na biyu na zo maka da maganar ka gagauta haɗa auren domin yarinyar ta sauya, na san komai fa har irin wulaƙancin da ta yi masa da dalilin ciwonka, da rashin lafiyar da ya yi aka kawo mana shi kamar gawa daga Lagos, amma ba ku ɗauki hukuncin komai yana gani ya sadaukar da soyayyarsa saboda ita shi kuma ya wahala sai yanzu da komai ya ƙare mata za a haɗa su aure? Wallahi muddin ina numfashi ba zan bari ba, dole ta wahala kamar yadda ta wahalar da shi, Ridayya ita ta saka mini tsanarta da kanta ban jin kuma akwai dalilin da zai saka na yi accepting nata as my daughter-in-law"


"Ke kuma a matsayin ki na uwa kina son kashe ɗanki da kan ki ne, kuma duk ranar da hakan ta faru ba zan yarda ba wallahi Allah" gabaɗaya ransa ya gama ɓaci dole ya fito mata a mutum ganin yana mata shiru zata ɗauki kamar bashi da ƙarfin qwiwar yin magana da tsawatar da ita ne.


Ya gyara zama cikin dakakkiyar muryar ya ce


"Akwai bambancin na abinda idanunmu ya nuna mana da abinda zuciyarmu ke zargi akai, ba a yi wa ƴa mace gaggawa cikin rayuwarta da tarbiyyarta, haka ba a yi wa ɗa namiji katsalandan a cikin rayuwarsa musamman irin Muhammmmd. Na fiki sanin yana son Ridayya na share shi ne tunda yana ganin hakan shi ne daidai, kuma babu inda zurfin ciki yake da magani ko mafita, yasan mene daidai shi tunda ya ja bakinsa ya yi shiru hakan yana nufin wani abu. Harkullum mu iyaye nutsuwa da fahimtar yaranmu shi ne abinda ya fi dacewa a gare mu, ba wai mu yi musu kutse ba, Allah da kansa ya ce yara amana ce a gare mu kuma kiwo ne, zai tambayi yadda muka kula da wannan kiwon idan mun koma gare shi. Ki faɗa mini wani abu mana Hajiya Hadiza, Ridayya ta ce aure take so kamar yadda kika ce, ya ce zai aureta ta ce a'a tana da wanda take so, me kike so Ustaz ya yi ko kuma ni na yi? Saboda ya kula da ita sai ya tursasata yin abinda ba ta yi niyya ba? Ko kuma ta yi masa halacci na abinda ya yi mata? Shi abin alheri ana yi ne domin Allah kuma masoyin gaskiya shi ne zai sadaukar da nasa farincikin domin wanda yake ƙauna ya yi farin ciki. Ba kisan komai ba game da so tunda kina kwaila na je garinku aka bani ke, ni na kula dake na nuna miki mene so har kike jin idan bani ba za ki iya rayuwa ba, ki saka a ranki tarihi ne zai maimaita kansa"


"Ok gori za ka mini kenan? Amma ita Ridayya ɗin ai ta san halacci ko?"


"Wanda ya faɗa soyayya mai zafi ko jarrabawa ta saka ya faɗa soyayya baya buƙatar neman dalili ko hujja, wanda yake so ɗin nan shi ne kawai a gabansa, da idanun zuciyata. Duk abinda ya faru dalili biyu ne ƘADDARA kamar yadda zanenta ya bayyana ƙarara a rayuwar yarinya da bata ji ba, bata gani ba, idan soyayya kike so mai zafi da sanin masoyin gaskiya da faɗa akan masoyi na bin abinda zuciya ke so, ki je ki karanta littafin *DIYAANA*. Zurfin cikin Ustaz ya ja masa rasa Ridayya da son nuna mata ikon uba, ita kuma ƙaddarar data faɗa na ƙiyayyar uba da damuwa na aibata halittarta ya saka ta faɗa tarkon MUNAFUKIN MIJI, a lokacin ba soyayyar ce a gabanta ba yadda zata bar gidan mahaifinta ta rayuwa inda babu duka, ba zagi ba tsangwama shi ne fatanta, ƙaddara kuma ta raba ta da mijin ta kuma sake dawo da ita hannun Ustaz"


Baba ƙarami ya nuna Umma da yatsa ya ce


"Wallahi wallahi idan kika ce za ki ja-in-ja da wannan ƙaddarar to ranki zata ɗauka, ki sani Babban mutum ya yi nisan da ba zai ji kiran ki ba yanzu a shirye yake ya yi faɗa a kan abinda yake so, kuma ganinsa zai miki wahala zai miki abinda za ki yi kuka da kan ki I'm telling you ba a yi wa ɗan yau haka musamman akan soyayya a wannan gaɓar kurame suke zama"


"Yanzu dai saki nawa ya yi mata Allah ya sa ukunne kawai"


"Ba matsalarki bane wannan tunda kin saka ya yi sakin ya kuma bar miki gidan shikenan"


Ransa ɓace ya bar parlourn ya rasa meke damun matar tasa bai santa haka ba bai kuma san yaushe ta lalace ba. Sashin baya ya nufa inda bai fiya zuwa ba, daga nan kuma akwai ƙofar dake kai mutum kai tsaye zuwa bedroom ɗin Ustaz ba tare da kowa ya sani ba, tun kafin ya ƙarasa ya kira Tajj ya ce yana buƙatar ganinsa Allah ya sa kuma yana gari.


Tsaye ya samu Ustaz ya yi shiru idanunsa buɗe kansa kuma a ƙasa ya kalle shi na wani lokaci kana ya nemi waje ya zauna ya ce


"Muhammad-Bilal Tahir Rano dawo nan"


Kamar baya son ɗaga ƙafarsa haka ya jata ya zauna ƙasa wajan ƙafafuwan Baba ƙarami wani hucin zafi ke fita ta cikin bakinsa da hanci.


"Babban mutum me ya sa ka yi haka? Kar ka bani kunya har ka sare da wur wuri ashe daman soyayyar tatsuniya kake ma shalalen ko?"


"I have no idea father, bana shiga shiga fushin uwa"


"Kuma saki ba kyau, halak ne amma Allah baya son shi. Babu zunubi ko kaɗan a aurenku babu abinda ƴar'uwarka ta yi maka, a zahirance ma bata san matsayinka wajanta ba"


Ustaz ya yi shiru Baba ƙarami ya ce "Do something Abokina ɗaya tal, ka yi abinda zai bawa kowa mamaki ni dai ba zan ce ka rabu da Mardiyya ba domin tana da hakƙi akan ka, haka ba zan lamunci abinda ka yi ba"


A hankali ya jinjina kai don baya jin zai iya magana rauninsa gab yake da gama bayyana.


"Ina zaka?"


"Bana son zaman nan, zan je wani waje daban idan akwai alheri tsakanina da Ustaz tabbatas Ubangiji ya ba zai bar mu haka ba"


"In sha Allah. Ka je ka ɗauki abinda ya dace Tajj yana waje zai yi dropping naka, nasan ba zaka iya driving ba"


Part ɗinsa ya shiga ta bayan ya ɗauki atms ɗinsa files ducoments da abubuwan da zai iya buƙata ya haɗa kaya cikin luxury trolley ya nufi waje. A tsaye ya samu Tajj shi da Zainu yana ta tsokanarta tana tura baki.


"Tab Yaya Ridayya ɗin ce ta fini kyau, ana ta cewa ni kyakkawa ce"


Tajj ya buɗe ido ya ce


"Subuhanallahi amma masu faɗa tsoran Zainura suke, ai colour ɗinku sun yi yawa gari da society namu yanzu baƙar kala ake ya yi"


"Tamɗijam! Kawai ka fi son Yaya Ridayya kai da Yaya Ustaz"


"Yes we love her, saboda she is a durlin.....,"


Wani irin kallo Ustaz ya yi wa Tajj fuskarsa ta haɗe ta yi jajur Zainura ta ce


"Ina yini Yaya Ustaz"


Wata tsawa ya daka mata ita da Little dake hannunta suka firgita nan da nan Ustaz ya rikiɗe kamar ba shi ne fara'ar sisi babu a fuskarsa kamar an yi masa mutuwa. "Mu je na sauke ka"


Ya yi masa banza ya buɗe bayan mota ya saka kayansa ciki ya nufi ƙofar motar. "Ya ina ta magana ka yi shiru, ka bani key ɗin ko ka shiga motata ban fito da securities ba"


"Ka tsahirta mini kafin na watsa maka yatsu"


"Ikon Allah me na yi kuma ni ka zo ka yi wa yarinyar tsawa har yaro yana ihu ka zo kana mini faɗa? Daga zuwa aikin lada"


Tajj ya ƙwace key ɗin ya juya yana buɗewa MB USTAZ motar, kamar ba zai shiga sai kuma ya shiga ya yi wa motar key. Tajj shi kaɗai yake maganarsa Ustaz ji yake kamar ya yi bindiga a haka suka ƙarasa airport sai a lokacin ya juya ya kalli Tajj shi kuma ya ɗaga masa gira ya ce "Dole haka za a yi fa"


Hankalin Umma kwance tunda ta san aure dai babu shi ta zaunar da Mardiyya ta yi mata bita da zarar Ustaz ya sauka daga fushi ya dawo ta yi duk iyakar yinta wajan ganin sun samu daidaito kafin ƴar mayun ta dawo. Har sama da sati kuma babu alamar BM USTAZ numbers ɗinsa duka a kashe suke. Umma ta share tasan dole duk inda yake zai dawo ya sameta ne for sure.


Mami na zaune da yammacin ranar ita da Yaya A'isha da suke magana ta ce "Ina jin tsoro Yaya A'isha Ridayya har yanzu babu kulawar uwa a tare da ita, bata san ya kamata ba, ta rasa abubuwa da dama"


"Me kike tsoro ne Fatima?". "Aurenta da Ustaz bata san komai akai ba yana da kyau ta sani, gashi Umma bata ƙaunar Ridayya ko kaɗan ga Mardiyya ta fi Ridayya buɗewar ido wayo da ilimi da sanin kan duniya ina tsoro Ustaz ya rabu da Ridayya ina tsoran wannan ranar"


Yaya A'isha ta yi murmushi irin na manya ta ce "Bari na fara da magana mai muhimmanci ki daina mafarkin Ustaz zai rabu da Ridayya, su ɗin tamkar ruwa da iska ne, kamar Inuwa haka suke, haka kamar rayuwa da mutuwa haka su duka biyun suke, ƙaddararka zane suke dana juna. Ridayya matar so ce, Mardiyya haɗin Hajiya ne a kuma rashin Ridayya aka bashi Mardiyya, auren Mardiyya da Ustaz kamar auren cin amana ne ta yi shi wa kika taɓa gani ya ci amana kuma ya zauna lafiya? Ilimi kuma Ridayya za ta yi shi, za kuma ta waye ke kan ki zata ba ki mamaki musamman ta zama her Excellency"


"Her Excellency kuma?"


"Uhm ai abin duniya baya ɓuya tuni zance ya zaga ana son tsayar da BM USTAZ takarar gwamna"


Mami ta ce "Ikon Allah"


Yaya A'isha ta ɗauki waya tana buɗe furnitures ɗin da dukai order na gidan Ridayya ta ce "Ai da ruwan ciki ake jan na rijiya, abinda ya taɓa hanci dole ido ya yi kuka idan ta yi yunƙurin raba Ustaz da Ridayya to ɗanta zata rasa, ƙoƙari ɗaya za mu yi mu fahimtar da Ridayya Ustaz fa ba ubanta bane mijinta ne, idan har tana masa kallon uba to kunya ce zata shiga tsakani ta zama hijabi namiji kuma baya son kunya a zaman aure, balle kuma wannan Babban mutum ɗin daka gani ɗan Soyayya ne kuma za ku ce na faɗa"


"Kai Anuty shi da yake Ustazu malami"


"Zainura get out, sai nawa zan ce idan manya na magana ki daina saka baki ne?" Miƙewa ta yi ta fice. Yaya A'isha ta ce "Wannan ƴar autar taki ta cika kanzagi, da alama kuma kamar kin haɗiyi wake"


"Rufa mini asiri Yaya, Ridayya na haihuwa ni na haihu ai da kunya"


"To za mu gani ai ɗan duma ne dole zai bayyana kansa, wannan karan maga haukan da kishiyarki za ta yi"


Murmushi kawai Mami ta yi suka ci-gaba da duba furnitures ɗin da sauran kayan da za su yi Ridayya da kayan sawa komai da komai daga ɓangaren dangin uwa. Bayan sun gama ta fito raka Yaya A'isha suka tarar da yaya Zuhura zaune tana rusar kuka kamar ranta zai fita Ammi sai masifa take mata ganin su Mami ya saka ta yi shiru cikin sakin fuska da yaƙe ta ce


"Hajiya A'isha kin fito ashe sannu da zaman ɗaki"


"Yawwa sannunki da zaman gadi ana shan A.c" Yaya A'isha ta faɗa tana dariya tare da mayar wa da Ammi raddin maganarta.
Murmushi ta yi ta ce
"Ke kuma tashi wai fa surukar ta ce babu lafiya shi ne take wannan kukan kamar ni na mutu, ke kam an yi sakarar wofi"


"Allah sarki idan da kima uwar miji ai uwa ce" Yaya A'isha na faɗin hakan ta shige abinta Mami daman bata ce ƙala ba wayarta kawai take dannawa gabaɗaya nutsuwar Mami Ridayya ta ɗauke ta ciff ba abinda ta manta bata ɗauka ba a wannan ɓangaren.


Suna barin wajan Ammi ta ce "Wallahi tallahi sai kin koma gidan mijinki magana ɗaya ki dako ya ji ki dawo gida so kike a samu abin magana a kai na kenan ko? Ko Ridayya data auri miji mara kirki bata taɓa yin yaki ba sai ke da kikai auren soyayya miji na gaban kwatance, to Allah kar ya nuna mini ranar da zanga ƴata na zawarci"


"Haba Ammi ni kaɗai nasan wahalar da nake sha ba, tun yana waya da ƴan mata a ɓoye har ya zamana baya jin tsorona, baya bani abinci yanzu haka dukana ya yi a gaban ƴaƴana kuma ya ce na bar masa gidansa ni kuma kamar mayya sai na zauna don Allah?"


"Ai wallahi sai kin koma tun kafin kowa ya ji ni zan zo na samu mijin naki gantalalle shi ma"


Bata bar Yaya Zuhura ta zauna ba ta mayar da ita da masifa da komai. Koda Ammi ta ce gidan Yaya Zuhura ta iske mijin ya zage yana nanawa Yaya Zuhura wuƙa a wuya gabaɗaya ya ƙona mata wuya da wuƙa nan take abinda ta yi wa Ridayya ta faɗo mata ta hau masifa da bala'i.


Ya kalli Ammi ya juya mata baya tare da cewa "Na ki rududu wannan faɗan ba zai mini ba, ƴarki ce bana so bana ƙauna a yanzu"


"Ashe baka da mutunci ɗan wahala ne kai gayyar tsiya? Ashe ɗan kwalta ne kai?" Ya ce


"Yanzu zan yanka miki rashin mutunci wallahi ki ɗauki yarƙi ku bar mini gida immediately"


A gigice Ammi ta riƙe hannun Yaya Zuhura ta ce "Ɗan'tadda ne ashe mijin naki na san maganinsa da Burhan zan haɗa shi wallahi" banda kuka babu abinda Yaya Zuhura take kuma ya hana ta ɗauki yaro ko ɗaya har wacce take shan nono ya kwance ta.




Sadauki ya samu relief daga nauyin da zuciyarsu ke yi masa dalilin wayar da suke yi da Ridayya ta tabbatar tana dawowa z a yi maganar komai a shige wajan.


Yanzu ma yana cikin mota yana driving bluetooth maƙale a kunnensa farin yadi ne a jikinsa mai laushi ya ɗora hula kasancewar yau juma'a ya je masallaci juma'a daga nan ya leƙa wajan aiki yanzu kuma ya ɗakko hanyar gida.


Ya lumshe idanunsa da suke zube a kan titi cikin kasala ya ce "Allah Shanshan sai na dinga jin faɗuwar gaba, please come back ko sbd ni ne"


Murmushi kawai ta saki ta cikin wayar ya marairaice mata ya ce "To ki bani address zan zo na gaji da rashin ki ba ki san yadda nake jin ki a zuciyata bane, i so much loves you sweetheart"


Muryarta bata fita sosai ta ce "Ka jira lokaci banda gaggawa Sadauki"


"Yaushe za ki dai na kira da Sadaukin nan ne? Well is allowed ai ni ɗin Sadaukin ki ne ko ruwa ban bari ya taɓa mini ke i swear"


Ta yi shiru shi ma shirun ya yi haka kawai ya ji kamar tana cikin damuwa kuma tsoro a kama shi ya ce


"Ridayya" Ya kira da murya mai rauni bayan ta amsa a ƙasan maƙoshi ya ce


"You are the most beautiful person, both inside and out. I am so lucky to have you as my girlfriend. Ina son ki Ridayya don Allah kar ki cutar dani idan na rasa ki ban ya zan yi ba, i don't know what to do seriously"


"Addu'a"


Ya ware idanu kamar tana gabansa ya ce "Oh kina nufin zan rasa ki?"


Ta yi saurin girgiza kai kamar yana gabanta ya fahimci hakan ta yi ya ce "Shikenan bari na ƙarasa gida zan duba ki online take care"


"Send my regards to your family"


"I will. I love you"


"Thank you" a fili ya maimaita “Thank You” mai yasa Hausawa suke haka ne, kunya ce ko rashin damuwa? A muryarsa ta ji bai ji daɗin hakan ba.


"Uhm ki riƙe alƙawari" ya faɗa yana kashe wayar bakiɗaya.


Kuka Ridayya ta saka bayan ta ajjiyar zuciya zuciyarta babu daɗi sam Anuty Kaltum ta ce


"Mene abin kuka kuma?"


"Anuty tausayin Sadauki nake idan na ji labarin Abbiey ya aure ni ban san ya zan yi ba"


Anuty Kaltum ta sauke ajjiyar zuciya domin ta yi wa Ridayya bayanin komai da matsayin MB USTAZ a wajanta kuma ta yi accepting ɗinsa matsayin miji sai dai bata san a wanne gurbi yake a zuciyarta ba, abu ɗaya ta sani tana jin wata matsananciyar kunyar Abbiey ɗin nata, ba zata iya haɗa idanu da shi a matsayin mijinta ba na sunna.
Jin daɗinta ɗaya tunda bashi da lafiya dukda bata taɓa kawo wani abu a ranta ba, first kisses ɗin daya wanzu tsakaninsu ta bar shi matsayin kuskure, kullum yana maƙale a zuciyarta wani lokacin har shafo lips ɗinta ta ke yi tana tunawa tsigar jikinta zata mimmiƙe wani lokacin har rufe jikinta take da bargo bata taɓa tunanin akwai wani abu a zaman aure wai shi “Kiss” ba.


"Ridayya kin mini al'ƙawarin daga yau ba za ki ƙara waya da Sadauki ba, kuma kin ɗauki karatun duk da muka yi miki ni da Yamara, ki nutsu ki rayuwa mai kyau da tsafta ke da mijinki"


Ta kama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login