Showing 159001 words to 162000 words out of 190738 words
Chapter 54 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt
MB USTAZ babu komai face farinciki da kwanciyar hankali, dukda akwai samun saɓani irin na ma'aurata wani lokaci duk wacce ta ce bata taɓa faɗa da mijinta ba ko misunderstanding ya shigo ciki ƙarya take, aure ibada ne kuma sunna zama ne na dindin wanda ake fatan sai dai mutuwa ta raba.
Da farin ciki ta shigo tun a parlor ta zare safar hannunta dana ƙafa ta cire madaidaicin hijabin wata takarda kawai ta ɗauka ta nufi babban part ɗin data tabbatar yana ciki a hankali ta murɗa ƙofar ta shiga parlorn farko mai ɗauke da haske ta shiga na biyun shi kuma duhu ta ƙarasa har cikin bedroom tana shiga ta hango shi kwance tsakiyar gado ya shiga cikin duvet yana bacci hankali kwance Ridayya ta saki murmushi mai sauti ta zauna kan gadon idan ta kalli MB USTAZ da kyau ta tuna shi ne wanda Ubangiji ya bata shi matsayin miji sai ta ji damuwar da ta yi shekaru da ita duk ta kau daga zuciyarta, ganinsa take tamkar ba a cikin zuri'ar Mai ran ƙarfe yake ba, shi kaɗai daban Ubangiji ya yi masa tsarinsa kaf familyn.
"Now is my turn Abbiey"
Sai tana bacci mai daɗi zai fara damunta bata bacci ya isheta yanzu ganin yana jin daɗin baccin sosai ya saka ta fara tashinsa ta hanyar zura hannunta cikin sumar kansa data rufe masa fuska a hankali take ya motsa masa kan tana murza tafin hannunsa daidai kunnensa ta ce
"Abbiey Abbiey Abbiey"
Amma ina bacci yake sosai saboda gabaɗaya satin bai samu ciakken bacci ba Ridayya ta dinga takura masa "Abbiey mijin"
Duka yana jinta ya yi luf can ya ɗan mirgina ya ɗauki pillow ya rufe kunnensa data miƙa hannu ta fara taɓa shi can zai make hannun yana sake mirginawa abubuwa biyu ke damunsa ba lallai ta fahimta amma yanzu baccin shi ne gaba da komai. Sake hayewa gadon Ridayya ta yi saman jikinsa numfashinta na sauka ta fara bugunsa da ƙarfi cikin magagin bacci ya ce
"Haramun Ustaza haramun zunubi kike ɗauka"
"Nima haka kake mini please ka tashi i want...."
"Are you sure u want this?"
Ya faɗa yana nuna mata wani abu ta yi saurin rufe idanunta a hankali shi kuma baccinsa ya fara warware wa wani abu ya danne baccin ya ɗan cije lips cike da mugunta yana juyata ƙirjinsa na matsewa sosai da kyau jikinsa na buɗewa yanayin na shigarsa da kyau yana ɗago kanta ya ce "Because once it is in, you will officially belong to me"
Ta zazzare idanu domin ita kwana al'amarin fitar mata yake daga kanta tana ɗan narke fuska murya shagwaɓe ta ce "Koma bacci abinka bari na gyara maka duvet ɗin"
Ya buɗe idanunsa da kyau yana rungume da ita suna daga kwancen ya lumshe ido ya buɗe magana yake son yi kuma ya kasa Ridayya ta ce "Allah ya yafe miki Ustaza ke yarinya ce"
Ya ɗaga mata kai alamar “Good” Ridayya ta gyara kwanciyar ta a jikinsa ganin ya mata shiru ta ce "Kasan me Abbiey?"
Ya zuba mata gajiyayyun idanunsa sosai mai ɗauke da abubuwa da yawa ya kasa cewa komai ta ce "Karatun daka koya mini shi ne aka yi mana a test kuma na cinye Assignment ɗin nan" Ya buɗe ido zai magana sai ya fasa ya yi kissig kumatunta muryarsa bata fita sosai da wani irin romantic voice ya ce
""أنا أحبك"
Murmushi kawai ta yi ita har yanzu nauyin faɗa masa kalmar soyayya take nauyinsa take ji sosai shi kuma baya takura ta yasan soyayya ba dole sai an furtata da baki ba wani a aikace yake yin komai
"Black tea Zauja ok"
"Right now Abbiey"
Ya sake ta can ciki ya ce "Barakallahu fiiki"
Gani yake komai ta yi yarinya ce ita tana buƙatar uzuri shi ya sa yake sassauta yanayinsa da fushinsa a kanta.
Fita ta yi da niyyar nufar kitchen ta haɗa masa tea ɗin sai ta ji telephone line ɗin gidan na ƙara ta jima bata yi ba da tunani Abba ne ko Baffa ta ɗauki kan wayar muryarta a sanyaye ta ce
"Assalamu alaika/ki"
"Allahamdulillahi! Ridayya are u alone oh sorry her Excellency"
"Daddyn Nadra ina yini"
"Ajjiye gaisuwa a gefe are u alone magana za mu yi ta fahimta bana son mijinki ya sani"
Tabbaci ta bashi ita kaɗai ce lafiya?
"Ridayya daman Tsohon mijinki bai sake ki ba? Guduwa kikai daga gidansa?"
Mararta ta ji ta ɗaure mata wani abu ya yi zillo ta ƙasan marar jikinta ya ɗauki rawa ta ce "Ka...ka...ka kamarya bangane ba"
Tajj Baita ya ce "Nima dai ban gane ba, ta bakinki nake son ji, ya ce daya aureki kina da ciki ba kowa ya yi miki ba sai His Excellency MB USTAZ kuma tun kina ƙarama yake lalataki ya rantse da Allah bai sake ki ba, shin Ridayya da gaske kin yi aure da ciki kuma na Ustaz ne?" Tajj Baita bai san meke faruwa daga ɓangaren Ridayya ba sai ji ya yi ta fasa gigitacciyar ƙara kiran kuma ya katse. Ustaz dake zaune da laptop a gabansa yana duba wani muhimmin saƙo da Muhammad Hassan ya tura masa ta email ya ji ihun matarsa cikin sauri ya miƙe a ɗan gigice yana addu'a ya nufi waje kwance ya sameta bata ko motsi jini na zuba ta ƙasanta bai tsaya jiran komai ya shiga kiran ambulance kafin su ƙarasa ya zura kaya ya sunkuceta sai ambulance.
Some hours left
Girgiza kai kawai yake idanunsa da suka nutsa ciki sosai da maka tantance yanayin su ne zube akan wanda yake tsaye a gabansa, shi kansa wanda yake tsaye ya firgita da yanayin Ustaz ya san halinsa idan ransa ya ɓaci
"Try to understand me ni ban san me ya saka Madam shiga halin da take ciki ba, kawai na san ana buƙatar ganin ka a gida"
"I hate liars, why?"
"Yanzu muje asibitin muga halin da take ciki"
"Tajjudeen Baita ka jima ba kaga rikicina ba, matata tawa ce ba ruwanka da na je wajan ta ko akasin haka. Firstly ka kira matata without my permission, secondly ka ce mata wani abu wanda ya saka ta shiga firgici, lastly ka shigo jirgi ka zo mini nan? Explain why? Menene?"
"Calm down please"
"Calm down? Assatagafirulla Allah ya yafe maka Ubangiji ka Tajjudeen" muryar Ustaz har shaƙewa take Tajj ya buɗe baki zai yi magana ya ji saukar wani mari a fuskarsa ya ƙara jin wani muryar daya jima bai ji ya ji ta masa amo! Da amsa kuwwa a kunne
"What is going on? Meke faruwa don't let me to repeat myself".
"Your wife's ex-husband"
Tajj ya ce yana riƙe fuskarsa sosai marin ya ratsa shi saboda a hagunce ya mare shi shirun Ustaz na nufin ƙarin bayani nan da nan Tajjudeen Baita ya zayyana masa komai da yake faruwa. Kan Ustaz a ƙasa murmushi kawai ya yi ya nufi wajan freezer ya ɗauki ruwa mai sanyi sosai ya ɓalle gorar kai ya shanye tas ya cillar
Murmushi ya sake saki ba za ka taɓa cewa ya damu ba ko maganar ya shige shi musamman furucin Baba ƙarami na cewa zai ɗaure shi, wai ciki? Ya lalata ƴar jaririyarsa shi kuma nasa salon kenan?
Ta cikin cikin zuciyarsa naman wajan rawa yake gumi ya lullube zuciyar har hucinta ya ke jin da maƙoshinsa wani irin firgitaccen yanayi ya ruftu masa zazzaɓi ya nemi rufe shi ya sake duƙar da kansa ganin idanunsa na rikiɗewa muryarsa na rawa ya ce
"Leave"
"Ta ya ya zan barka cikin wannan yanayin?"
Gabaɗaya Ustaz ya juya kan Tajj yana sake yin murmushi tare da ɗage girarsa duka biyun ya girgiza kai ya ce
"Allahumma yahdiìka, Allah ya yafe maka"
Tafiya suke har entrance kana suka nufi hanyar emergency daga nan suka nufi sashin ICU ɗaki na musamman a baƙin ƙofa suka tsaya shi kuma ya shige ciki. Idanunsa ya sauka a kanta tana kwance bacci mai nauyi ya ɗauke ta ga drip a jikinta kuma ga ƙarin jini ya sauke ajjiyar zuciya so wannan tashin hankalin ya sana Shalele shiga wannan halin?
Dr Lin daya shigo tun ɗazo ya ce "Karka damu she will be fine by the grace of God ɗan cikin yana mararta lafiya lou"
Da rashin fahimta MB USTAZ ya kalli Dr Lin gane hakan yasa Dr Lin cewa "Sir Allah ya kiyaye cikin bai bi jini ya gudu ba, babyn yana lafiya itama matan ki she will soon recovering"
Kallonsa kawai Ustaz yake Dr Lin ya bawa Ustaz wani file ya ce
"Your wife is pregnant"
A zaune yake amma bai san lokacin daya miƙe tsaye ba, da wani irin yanayi na farinciki yake duba wajan positive ya dubi Dr Lin dake murmushi baturen likita duk hasken shi amma Ustaz ya ɗara shi haske tunanin Dr Lin ko baya jin irin nasa turancin ne ko larabci yake ji?
Ustaz ya damƙe hannun Ridayya sosai ya haɗe fuskarsu waje guda ya kasa magana sai wani light kiss da ya yi mata a gefen lips ɗinta wani irin hawayen farinciki running down to his face ya sake sumbatar goshinta da kumatunta da ƙyar ya ce
"I love you Mintyna. Allahumma barik"
"What a love!"
Murmushi USTAZ ya yi ya mance damuwarsa ya rungume Dr Lin wani irin farinciki yake ji a ransa yana shiga dukkan ƙofofin zuciyarsa. ALLAH alhakkamu wanda komai nasa yake a tsare ya ƙara tabbatar rabon Little Bilal ya haɗa Zameer da Ridayya haka kuma wannan rabon ya saka su rabuwa ta dawo gare shi, rabo ajali haka ko mutuwa ce duk inda ya je sai ya dawo wajan mutum indai rabonsa ne. Wata bata haifar ɗan wani amma tana auren mijin wata hakan rubutacce ne a lauhil mahfuz Allah kaɗai ya san abinda ya ɓoye a aurensa da Ridayya koma mene yana fatan akwai zama tabbatacce wanda mutuwa ce zata raba.
Ustaz ya dinga murmushi shi ɗaya hannunsa riƙe dana Ridayya ya mance batun Tajjudeen Baita dana Zameer komai ya shafe a zuciyarsa sai Ridayya da abinda yake cikinta idan ya lissafa daidai babu mamaki tun a ranar budurcinsa Ridayya ta samu rabo ƙwallonsa ya isa ga raga haƙarsa ta cimma ruwa.
Cikin dare ta farko jikinta lafiya lou amma da kuka ta farko Ustaz dake ƙasa saman ladduma yana Sallah da addu'oi ya miƙe ya nufi wajan ta tana jinta kusa da shi ta fisge ƙarin jinin ta ƙanƙame Ustaz tana kuka sosai kamar ranta zai fita magana take son yi ta kasa ganin haka ya saka shi shigar da ita jikinsa ya rungume yana bubbuga bayanta.
"Abbiey ka yafe mini ka yafe mini Abbiey"
"Shhhh it's ok Mintyna"
"Na maka laifi Abbiey ka yafe mini ka ji tausayina"
A banza yake jin maganarta ya ci-gaba da rarrashinta ta fara sauke ajjiyar zuciya ya ɗago fuskarta ya ɗora tasa akai yana mata murmushi ya ce "I love you"
Ya shafa cikinta ya ce "Kin ji kyautar Allah ko Minty? Za ki bani babies ranar da nake jira ya zo tsayin shekaru babu adadi abinda nake fata da buri da kwaɗayi shi ne ki tabbatar ke jaruma ce baki amshi budurcina a banza ba, now let celebrate together wife"
Ta lumshe idanunta tana jin ɗumin tafin hannunsa a hankali ta zame ta kwanta a jikinsa tana sauke ajjiyar zuciya "Abbiey"
Ya ɗaga mata gira "Ka yafe mini ko?"
Ya yi kissig nata ya ce "Allah ya yafe miki Ustaza"
Ta yi shiru can ya matseta a jikinsa ya ce "Thank you"
Nigeria
Sosai hankalin Baba ƙarami ya tashi amma bai nunawa Umma ba, shi kansa Baffa ya ɓoyewa Mami komai a ɓangaren Umma ta ci-gaba da kula da Mardiyya har wata ramewa ta yi kamar itama laulayin take yi bata san nawa ta ƙarar ba burinta kawai jikanta ya zo duniya a ranar zata zuba ruwa a ƙasa kuma ta je ya direwa Ridayya ta kalli jinin Ustaz a duniya ta san jaririn dole ya kasance kyakkyawa Diyya fara tas haka Babban mutum tun yanzu ta fara nemawa yaro maganin baki.
Da Biba da Baffa kusan tare suka shigo cikin gidan kamar zata bige shi ta buɗe murya ta ce
"Ina kike ƴar matsiyata wacce bata san halacci ba wallahi kin yi kaɗan kuma kin jawowa kanki masifa" da Ammi da Umma kusan tare suka fito Ammi ta yi tsalle ta dire ta ce "Huhuhu ai daman na san za a-rina an saci zanin mahaukaciya har Ni za ki ci amana? Na baki ajjiyar kuɗi ki turmushe dake na kyatuminki ne?"
"Daɗin kuɗin ba naki bane kuma na cinye na ci banza" Ammi ta daki cinya tana tafi da juyi ta ce "Ahhayeee riiii ai yanzu kinga me gari ya waya"
Biba na huci ta ce "Ai ba ki ci lalas ba har ni za ki kira wanda zai aure ni ki ce masa wai zaman kaina nake yi? Banza mai kwacen saurayin wata annamimiya"
Magana Mami za ta yi Baffa ya hanata ya nemi waje ya zauna watching all of them da yadda dramar zata kasance. Zagi suka dunga ƙundumawa junansu da tunawa kai asiri kafin dambe ya ɓarke aka fisge ƙarin gashin Biba, itama Biba ta tsalle ta damƙo zanin Ammi sai ga ɗan tofi ya faɗo ta zaga rigar sharaf abubuwan suka bayyana kamar nono ya zube a kwalta.
"Za ki ci kaza kazanki ni za ki wa tsirara mai yawo hotel hotel"
Junaid ya yi saurin juyawa Yaya Zuhura dariya kawai ta yi mai ciwo Mami na riƙe da Junior Zainura ta ce "I have never watch a beautiful movie like this perfect drama in season finale"
Biba ta juya ta kalli Baffa ta kalli Mami ta ce "Ita ce nan ta yi asiri ta aureka kuma ta yi asiri ka tsani Ridayya saboda ta ji labarin zaka mallaka mata dukiya tun tana ciki wai ka zama Munafikin miji. Sannan ta yi asiri ka saki matarka Hajiya Fatima ka kwace Ridayya ka bata a ranar da ka bata jaririyar ta ajjiyata a bula ta kwana Muhammad Bilal ne ya ɗauke ta a wajan, kuma ta ƙonawa Ridayya harshe da wuƙa bayan ta gasata a gas ta yi jajur sannan ta fara bata maganin bacci har ya zame mata jinin jiki ta fara maida maganin na shaye-shaye shi ne ya taɓa mata ƙwaƙwalwa ta dinga amsar dukiya a wajanka kuma ita ta ɗauke tunanin Hajiya da Mai ran ƙarfe....,"
Sharaf suka ji faɗuwar abu da sauri Baffa ya miƙe ganin Mami zube a ƙasa Ammi ta dinga tsinewa Biba tana cewa ƙarya ne.
Fitowar ta kenan daga lecture fuskarta ɗauke da farinciki yau Abbiey da kansa zai zo ɗaukarta da ya yi mata text ɗazo kasancewar ya ji Nigeria ya yi wata guda a can abubuwa da yawa sun faru a can amma bai faɗa mata ba. Inuwar mutum ta gani a gabanta tun daga shap ɗin mutumin ƙirjinta ya duka abin cikinta ya juya gabaɗaya watan cikin shida sai ka ɗauka ta kusa saukewa hakan yasa Ustaz baya barinta iya ɗaya karatun ma don ya zama dole ne hatta Tajj bashi da labarin cikin Ridayya daga ita sai MB USTAZ.
Da ƙyar ta ɗago kanta numfashinta na riƙe wa idanunta ya sauka akan Sadauki dake tsaye cikin Black suit ya yi kyau ainun fuskarsa yalwace da wani irin murmushi na zallar so da ƙauna wanda yake nuna tsantsar kewa wani abu na fisgarsa zuwa gare ta ya azabtu ainun da rashinta ashe sa a ce ta kawo shi Japan har yana complain ba zai zo ba.
Ridayya komai nata ya tsaya zuciyarta take ji kamar tayo sama zata fito da maƙoshinta Sadauki ya matsa yana kashe mata idanu ya ce
"I so much miss....., shiru ya yi kalaman suka tsaya ganin turtsetsen ciki a jikinta.
A yi haƙuri idan aski ya zo gaban goshi ya fi zafi 😥🥰👏🏻
_*MUNAFUKIN MIJI*_
Nimcyluv
43
"Beloved" Sadauki ya furta idanunsa zube a kan ta, ganin tana jan baya hannunta dafe da cikinta daya girma sosai ya saka ya ƙara kusan ta kan sa zuwa gare ta, tana ƙokarin juyawa ta gudu ya saka hannu ya jawota zuwa jikinsa, abinda ya yi masa iyaka tare da yi masa shamaki daga rungume ta ya saka shi saurin sakin hannun Ridayya. Ciki! Shi ne abinda Sadauki ya gani har ya girma cikin haihuwa ko nacin abinci? mene ya haɗa his fiance da ciki? Innalillahi!
Zuciyar Sadauki ce ta fara rawa tana wani irin yunƙuru masa har maƙoshinsa yake jin numfashinta, ya sake buɗe idanunsa da sukai laushi ya zuba akan cikin dake maƙale a jikin Ridayya,what does that mean? Did she cheat or what? Hatta ƙafafuwansa rawa suke suna neman gaza ɗaukar gangar jikinsa a karo na farko kuma kusan na biyu.
Murmushi ya suɓuce masa dukda cewa idanunsa a rine suke tana iya hango yadda ƙirjinsa ke ɗagawa. Kallon Ridayya kawai yake irin kallon dake nuna, I love you so much, the kind of crazy love that even in Ustaz's eyes she has never seen that. Har ya juya sai kuma ya sake tsayawa irin me ya sa zan tafi? Why should i do that? Ridayya ce fa? Ba zata taɓa cin amanar shi ba, ya aminta da ita aminta mai yawa amintar da har zuciya da gangar jikinsa sai da suka shaida hakan, murmushi ya dinga yi shi kansa bai san dalilin faruwar murmushin nasa ba.
"Wow! U look so beautiful shanshan kin sauya a idanuna sosai" yana magana yana ɗan hargitsa sumar kansa alamar ya fara fita daga yanayin da yake na Hamza zuwa na Sadauki.
Ya zubawa cikin Ridayya idanu domin tabbatar da abinda zuciyarsa ke ayyana masa, idan cikin gaske ne mene haɗin budurwar da zai aure da cikin haihuwa? What bring her here? Me ta ke yi a Japan?
Ƙara matsawa ya yi wajanta ta girgiza masa kai irin ya dakata ɗin nan, he just trying to get more close to her a gigice Ridayya ta ce "Stop it, Stop it Stop it Sadauki" jikinta duka rawa yake tsoro da fargabar yanayin Sadauki ya saka mararta riƙe wa, idan ta tuna cewa Abbiey na hanya kamar yadda ya ce sai ta ji kamar abinda ke rayuwa a cikinta zai fito zuwa duniya ne, bata san hawaye ke fita daga cikin idanunta sai da ta ji saukar yatsar Sadauki manuniya ya sharce hawayen ta ɗago ta kalle shi ya mata murmushin a hankali nunfashinsa na sauka da kyar a fuskarta ya ce
"Wai Shanshan wannan sabon yanayin fa?