Showing 174001 words to 177000 words out of 190738 words

Chapter 59 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17326

Allah, yaran waye don Allah?"


Abinda Mami ta hango kenan har ta juya ta kalli little itama taga kamar a fili ta ce "Allah yaye miki wannan tambayar Burhan dai ya haɗu da aiki" cikin sauri ta ce "Why Burhan Mami, wanne Burhan" Mami ta haɗe fuska ta ce "Wanda kika baro a parlour yanzu da yake mana sunturi" nan da nan hankalin Zainura ya tashi ta fara hawaye ta ce "To ni mene haɗina da shi kuma don Allah Mami?"


"Oh zan sanar masa ya tattara ya bar mana gida muna da wanda zamu bawa auren ki is that clear baby?" Zainura ƙirjinta ya buga ta kasa magana Mami ta yi murmushin ta ce "To ko dai na bari kya faɗa masa da kan ki?"


"Eh Mami zai ma fi fahimta" Murmushi kawai Mami ta yi a ranta tana jinjina ta ɓarar Zainura. Har Baba ƙarami ya gama cin abinci bai cewa Umma komai ba, ita kuma ta kasa sukuni burinta ta ji ya faɗa mata iyayen yaran amma ya yi gum da bakinsa. Sanda ta shiga bedroom ɗin Mardiyya ta same ta zaune tsakiyar gado da ƙaton ciki gaba Umma ta kalli cikin ta ce "Kila kema dai yara biyu za ki haifa gashi har kin gota Edd naki Daughter"


Mardiyya ɓata fuska ta ce "Wai yaushe Mijina zai dawo ne ni sam na gaji na kasa tantance ke nake aure ko shi?" Da wani irin yanayi Umma ta ce "Rashin kunya za ki mini Mardiyya ni za ki mannawa wannan maganar mai ɗaci a zuciya?"


Fashewa da kukan munafurci Mardiyya ta yi ta ce "Kalamanne suka kwace mini bana nufin hakan, amma ko dutse aka ajjiye da buƙatar a sauya masa wajan zama balle mace kuma mai ciki, akwai haƙƙina da yawa a kan mijina, yanzu ba'a tunanin halin da zan shiga da raina da lafiyata amma babu miji a kusa dani? Yanzu kuma idan na aikata wani abun sai ace mini na aikata zunubi da wannan abin gwara ya sake ni kawai nasan ni ba matarsa bace" ta faɗa gabanta na faɗuwa domin kalaman iya laɓɓanta ne ita kam idan Ustaz ya sake ta ai ta shiga uku balle yanzu da arziƙinsa ya buƙasa. Umma ta ce "Haka ne an yi miki laifi maganar dana shigo na faɗa miki kenan cewa yana hanyar dawowa" cikin hanzari ta ce "Don Allah da gaske Ustaz na hanya kai na ji daɗi in sha Allah idan zai koma tare zamu tafi"


"In sha Allah "


Kawai Umma ta ce amma ƙasan zuciyarta kalmar da Mardiyya ta faɗa ke ta yi mata yawo a zuciya babu kunya ko ɗa'a a furucin Baba ƙarami ta samu yana waya a hankali ya ce "Tajj ya mai jikin?"


"Da sauƙi Abba, ita ta sani kiranka ma"


"Ikon Allah lafiya?" Tunanin Umma ya bata Muhammad ne hakan ya saka ta nemi waje kusa da mijinta ta zauna, ta cikin wayar Tajj ya ce


"Ban san me take buƙata ba Abba, ta dai matsa tana son magana da kai wai akan Shari'a na faɗa mata ai ka daina ka yi ritaya amma dai ta saka rigima ka san yadda ta dawo yanzu abu kaɗan kuka kuma har yanzu taƙi ce mana komai"


Baba ƙarami ya juya ya kalli Umma kamar zai tashi sai kuma ya ce "Bata wayar?"


Tajj ya kalli Hajja Azizat dake cikin baƙar abaya ta yi rolling kanta sai idanunta dake a jeme saboda kuka duk ta rame damuwa ce take ta cin ranta hannunta ta zura tsakiyar cibiyoyinta tana girgizawa a hankali kamar wata Balarabiyya ta zubawa Tajj idanu ya yi murmushi ya ce


"Anty gashi ki yi magana" yana bata wayar ya miƙe jin sallamar Nadra wacce ta yi wayo ta girma kuma sosai ya ɗaga ta sama ya ce


"My queen my happiness an dawo?"


Peak ta yi masa ta ce "Yes Daddy, ina abokina ne?"


"Anjima za su zo shi da Zainura" Nadra ta dinga murna little zai zo. Hannunta ya kama suka nufi bedroom ɗin Mahmah.


Tajj na fita Hajja Azizat ta damƙe wayar a hannunta kana ta kai kunne, Baba ƙarami ma shiru ya yi yana jiran me za a ce masa, Umma kuma ta zubawa masa idanu musamman wayar data kasance a speaker.


Can a ƙasa a taushashe kamar dirar mikiya ya ji muryarta ta sauka a kunnensa.... “Abbaa”


Hajja Azizat ta ce muryarta na rawa domin bata da wani suna da zata iya kiran shi da shi sai Abba ɗin da ta ji Tajj na faɗa as always.


Lokaci ɗaya shi da Umma suka kalli juna fuskar Umma ta sauya, Baba ƙarami kowa ƙirjinsa ya doka da ƙarfi kansa ya juya gargasar jikinsa suka mimmiƙe ba zai iya tuna rabonsa da jin wannan yanayin ba sai yau.


Kashe wayar kawai ya yi ya ajjiye a gefensa yana ɗaukan jarida Umma ta ce "Ai dole ka kashe saboda kar ka yi waya da budurwarka a gabana"


Da mamaki ya ce "Budurwa kuma Hadiza?"


"E, idan ba budurwa bace ka amsa mana? Ji yadda ta narke murya fa wai Abbaa yaushe ka haifeta da zata ce haka? Yadda ƙirjinka ke bugawa ya ƙara tabbatar mini da haka"


Ya girgiza kai kawai a hankali ya ce "Na ajjiye yaro mai shekaru wajan 40 da jikoki amma ki dube ni ki ce wai budurwa? Ai kece matata kuma kece budurwata"


"Ai ko maza ne baku da wani tawadiƙu akan mace wallahi, ni dai idan ta sake kira wallahi ban yafe ba"


"To Hajiya mai ran ƙarfe"


Tajj ya ce "To mene abin kuka kuma?"


Ta ɗan girgiza kai tana cewa "Bai amsa ni ba fa, kuma ya kashe wayar, ya kashe wayar fa son"


Cikin rarrashi Tajj ya ce "A'a maybe yana cikin jama'a amma zai kira ne"


"Ka kai ni gidansa mana" Tajj ya kalli Mahmah ta yi saurin girgiza masa kawai ya ce "To zan kai ki amma ki kwantar da hankali Anty shi baya magana da wanda suke yawan kuka da riƙe damuwa" ta ɗauke kai taƙi cewa komai.


Gefe guda Baffa ya bawa Burhan sanda ya tabbatar ya daina dukkan abinda yake kuma hakan ya faru ne dalilin son da ya kewa Zainura daman so babu abinda baya sawa, bayan bincike da tabbatar da cewa Burhan halin rayuwa ne ya saka shi lalacewa tun farko tun yana ƙarami ba'a bashi ilimi ba, babu abinci yabi abokan banza suka fara bangar siyasa daga nan ya tsallaka zuwa Lagos a can ya koyo turanci da dukkan wani tantiranci Ammi kuma ba ruwanta bata nemansa zai yi bata wani abun hakan ya saka Baffa dawo da Burhan gidan ya tabbatar ya zama mutum kamar kowa... Prof ya shiga tashin hankali duk hanyar da zai samu ya yi magana da matarsa Hajja Azizat ta toshe ta, gefe guda kuma tashin hankalin ya fi gaban kwatance Talatu ƙarin kunama ta tura masa wasu bidiyo da hotuna wanda ta ɗauke su tare suna tsaka da sheƙe ayar su, kuma tsirara ta umarci ya bata miliyan 50 ko ta saki bidiyon a yanar gizo ita daman ko a jikinta, ta bashi kwana biyu tal ba kuɗinne matsala ba fitar da bidiyon tsayin shekaru Hajja Azizat bata taɓa sanin wata aura ba, kuma wa take aure ba.


Zameer kamannin yaransa suka ci-gaba da firgita shi cikin dare, ƙiri-ƙiri zai je da buƙatar shi wajan Hanne amma ta yi masa fur ta ce ba jaka bace ita da zai dinga shaƙe mata wuya kamar dabba, ta ci masa uwa ta tattara duka kayanta dana yaran ta bashi haka zai wanke, ya tuna sanda Ridayya ta tsohon ciki take masa wanki ya tuna sanda ya ƙona mata fuska saboda ta ƙona masa kaya, da sanda ta datse yatsa a garin yin faskare, bai bata ci ba ba suttura amma kodayaushe ya je da buƙatar shi haka zata saurare shi babu wata mace da zata iya haƙurin zama da shi sama da mai son shi Ridayya ya yi believing yana haɗa idanu da ita dukkan wata soyayyar shi data narke a zuciyarta zata dawo ta zama sabuwa fil.


A can ƙasar Japan kowa Ridayya ce zaune ta zubawa yaran nata idanu da suke bacci cike da nutsuwa cikin kyakkyawar tofa har sun zarta sati guda a duniya yanzu. Ta juya ta kalli MB USTAZ dake zaune saman kujera ya tattara hankalinsa guda akan laptop ɗin gabansa, wando ne trouser a jikinsa wanda ya kama shi fari tas da shi, jikinsa kuma babu riga gabaɗaya gargasa ce a saman farar fatarsa ta yi luff sai sheƙi take dalilin farin daya ƙara, ta ɗan kalli damtsen hannunsu da yake a ɗan murɗe kamar mai ɗaga ƙarfe a hankali ta mayar da kanta wajan sumar shi, tana mamakin yadda kullum sumar kansa ke ƙaruwa ta sakko harta zarta kafaɗa ya ɗaure da wani abu kamar ribbon, gash ta wani cuccure kamar indomie Saboda yawan saloon da yake mata, girarsa tamkar zasu haɗe da juna gasu baƙa ƙirin gabaɗaya ta rasa wa Abbiey ya ɗakko a kama? Da zai shiga cikin Larabawa babu shakka zai iya fin wani balaraben kyau da hasken fata, gashi a dire yake dogo da shi faffaɗa yana da jiki ba can ba ga kuma Brest ɗinsa da suka ƙara girma alamar lafiyayye ne shi gaba-da-baya. Ganin baya kallon ta saci kallon yaron dake tsakiya wanda ta yi masa alamar baƙin zare ta taɓa hancin yaron har zuciyarta take jinsa ba ƙaramin kima Abbiey ya ƙara a idanunta ba daya saka sunan Sadauki kulawa ta musamman take son bash da nuna masa soyayya tare da muhimmancin mai sunan.


"Ba sai kin yi haka ba za ki tantance Sadauki a ciki ba Mimi" ta zaro idanu ta yi saurin matsawa ya miƙe da laptop gabaɗaya ya ƙarasa inda take hannu ya miƙa mata ta ce "Me za zan baka" hannun data miƙa masa ya doke yana harararta speaking calmly ya ce "Wajan za ki bani"


Ya cafke yatsu biyar ɗin hannunta ya ɗago ta bakiɗaya ɗaya ya koma inda ta tashi ya zauna, ta saki baki tana kallonsa duk faɗin wajan nan sai nan ne ya yi masa?


"Zauna"


"Kafa tare mini waje Abbiey ina zan zauna" bai ce mata komai ba ya jawo ƙugunta da ya yi wani faɗi ya buɗe har rawa yake ya zaunar da ita a cinyarsa, ya ɗora laptop ɗin a cinyarta a hankali ya zuro da hannayensa ta ƙasan hammtarta ya ɗora tafukan hannayensa a saman nata, ya fara shafa keyboard ɗin jikin laptop ɗin yana yi yana shafa mata ƙwantaccen gemunsa mai laushi tare da manna mata laɓɓansa masu sanyi a ƙasan wuya ta runtse idanunta


"Abbiey.....,"


Ta ce da ƙyar saboda wani abu daya tsarga mata bai ce komai ba sai da ya sauke numfashi ya ce "Look!"


Can ƙasan maƙoshi manyan Haɗaɗɗun gidaje ne na kice raini har guda uku ta dinga kallon pictures ɗin gidajen kafin ta ce "Na mene wannan?"


"Wanne kike so mu zauna?"


"A ina?"


"Nigeria"


Cikin wani farinciki ta juya gabaɗaya itama ta zura hannunta kamar yadda ya yi mata tana kallon cikin idanunsa ta ce "Abbiey da gaske gida zamu koma? Kuma ba zamu sake dawowa nan ba?"


Ya dinga kallon laɓɓanta masu taushi da ɗan tudu yaƙi cewa komai sai idanu yake bin ta da shi ta ɓata fuska ta ce "Uhm'uhm"


"Kin gaji da ni?"


Ta waro manyan idanunta tare da ɗora hannunta akan wajan brest ɗinsa ɗaya ta girgiza ta ce "Ka zama jinin dake yawo a jikina Abbiey, gajiya da kai har abada"


"Show me"


Ta yi shiru ya kama hannunta ya ƙara manna shi a wajan ƙirjin ya ce "Mimi"


"Abbiey"


"Hug me and kiss my lips"


Ta tura baki ta ce "To rufe idanunka"


"Barshi kawai.....," kafin ya ƙarasa ta yi saurin riƙe lips ɗinsa tare da bashi wani irin deep and hot kisses idanunta cikin nasa ya saki laptop ɗin ganin zata faɗi ya yi saurin manne Ridayya da ƙirjinsa ya riƙo laptop ɗin....... Ƙauna ce mai tsayawa a zuciya ta wanzu a lokacin cikin sauri ta matsa ta ce


"Yaranmu Abbiey"


Ya girgiza kai kawai yana kallon ta da wani irin yanayi mara misaltuwa a hankali underneath his breath ya ce “I love you Mimi"


"I love you Abbieyna"


Ya yi murmushi mai taushi ya ce "To zaɓi"


"Wannan farin yafi kyau Abbiey" Ya jinjina kai take ya yi order na furnitures na gabaɗaya gidan tare da biyan kuɗi ya kuma tura kalat decorations ɗin da yake buƙata.


"Ɗaga ni to"


"Wallahi cinyarka laushi Abbiey" bai kula ta ba ya san tunda ta ce haka ba zata tashi ba, ya ɗauki Sadauki dake kuka ya ajjiye a cinyarta ya ce "Ki duba yatsunsa yana da cindo a gefen na dama, babu buƙatar tantance shi da zare Mimi, Baffa kuma yana da cindo a ƙafarsa na hago Baba ƙarami kuma duk ciki shi ne tawadar Allah a saman leɓen shi" "Abbiey ya akai ka gane?"


"Kece malamar yaranki ke ya kamata ki fara gane hakan Mimi, yanzu you're no longer a child na fita daga rainonki da tarbiyyarki dukda cewa tarbiyyar mace bata ƙarewa, ke yanzu uwa ce Mother of her childrens mother of 4 Childs Mimi, tun yaranki suna yara za ki kula da takun kowa muradan su, da abinda suke so hatta kukan su yana da kyau ki bambance su, ki tsaya a kan tarbiyyarsu da girmama junansu addininsu Mimi bana son rashin kula akan ibada kema ban ɗora ki haka ba, ina miki uzuri a baya amma idan kika nuna rashin kulawa da sake da tarbiyya za ki san wa kika aura"


"Duka na za ka yi?"


Ta faɗa a raza ne kuma da gaske har zuciyarta ya kame fuska sosai ya ce "Ai saboda haka na nemi dorina"


Nan da nan idanunta ta sauya ta ƙasa magana "Idan kika nuna bambanci a yaranki za kiga bambanci, ina tunanin wannan zai zama aya ma a gare ki, domin nuna Banbancin da Baffa ya yi akan ki tun kina ciki shi ne ya yi sanadiyar samuwar ƙaddarar data same mu duka, domin na azabtu sanda na tabbatar kin zama matar wani i cry Ridayya...."


"Abbiey please abinda ya faru ya faru"


Ya ɗage mata gira duka biyun alamar YES a fili ya ce "ƙila idan na faɗa zan mata"


Hawaye ne ya fara sakkowa daga cikin idanunta ta fara shassheƙar kuka ya ce "You broke me"


Kawai sai ta faɗa jikinsa ta ƙanƙame shi tana fashewa da kuka, tare da ɓoye kanta a ƙirjinsa tana kuka sosai da dukan ƙirjinsa ƙanƙame ta ya yi da kyau a ƙirjinsa yana dariya sosai dimples ɗinsa na lotsawa idanunsa suka sauya a daidai kunnenta ya ce


"I am always in pain i've never cry for love but you make me cry, my heart hurts my chest is burning i beg you to stay with me amma.....," cikin sauri Ridayya ta hankaɗa Abbiey kan gadon ya yi saurin gocewa zuwa gefe gudun karya danne yaran tare da ƙoƙarin miƙewa zai gudu amma Ridayya ta yi namijin ƙoƙarin hana shi ta hanyar rufe bakin maganganun da yake ɗarsa mata masu zafi a zuciya ta shiga yi masa sumbata ƴar sunna kamar yadda ya koyar da ita....




Abbiey na zaune idanunsa zube akan waya Ridayya kuma hannunta riƙe da Al'hassan mai sunan Sadauki ta yi kwalliya cikin shigar atamfa ta murza ɗauri itama pictures ɗin take kallo "Amma ya akai ka fini kyau a nan Abbiey?"


Ya murguɗa mata baki picture ɗaya ya ɗauka wanda aka jere yaran guda uku akai musu a tare suna ta bacci WhatsApp ya shiga a main account ɗinsa wanda kowa da kowa yake da shi ya ɗora a status tare da caption ɗin.


_Allahamdulilah! Al'hassan, Al'hussan,Gambo_


In one minute reply yafi talatin kamar jira ake cikin mamaki Abbiey ke kallon first person daya fara reply ya ɗaga idanu ya kalli Ridayya ya ce


"Mintyna zo" ta miƙe ta ƙarasa tana leƙewa ta waro idanu ta ce


"Umma ce ai"


Ya jinjina kai ya buɗe maganar nata inda ta yi reply ta ce


"They're the same babies, Allahumma barik Allah ya yi musu albarka da rayuwa mai kyau cikin aminci ya haɗa kan iyayensu"


Abbiey ji ya yi gabaɗaya hankalinsa ya yi gida kewar Umma ta fara addabar shi. Ya kasa ce mata komai kafin ya fita ta ƙara masa magana ta ce "I miss you darling son, hukuncin ya tsauri come back don girman Allah"


Saurin fita ya yi. Daga nan ya ga reply ɗin Tajj inda ya ce "Kan uba, har yara uku Ustaz ka yi ɓarna Allah ga Ustaz ka yafe masa" ya faɗa da emojin na dariya kana ya yi addu'a nan take ya saka status shima.


Junaid ya turo emojin na rawa ya ce "The day i have waiting for, yaran auta da Yaa Bilal" murmushi Abbiey ya yi ya juya ya kalli Ridayya hannu ta miƙa masa suka tafa suna dariya. "Wannan Antyn taki surutu ne da ita"


Anuty Kaltum ce ta turo emojin ta riƙe haɓa ta ce "Ikon Allah har uku" maganganun mutane da yawa suke ta gani har mamaki suke Mami ta yi viewing amma ta kasa cewa komai.


"Wai Mami kunyar ƴar fari take ne Mimi? Kowa ya yi magana banda ita, to bari mu bita har pravt kawai" Ridayya ta ɗora kanta a kafaɗar shi har zai turawa Mami pictures sai kawai ya danna video call Mami ta yi zaton Ridayya ce daman tun ɗazo take ta auna yadda zata yi magana idan Ridayya ce ta haihu akwai buƙatar ta dawo gida a kula da jego, gashi yara har uku tana ɗaga kiran fuskar Ustaz ta fara cin karo da ita sai Ridayya dake dariya cikin sauri Mami ta kashe kiran tana dafe ƙirji Ustaz ya dinga murmushin ya ce "Surukata bafullata na ce"




Kamar yadda sanarwa ya zo wa Familyn Rano yau Ustaz yake sauka Nigeria da matarsa daya aura acan kamar yadda Baba ƙarami ya ce, tun safe ake shirye-shirye na zuwan nasu abinci kala-kala, Umma sai farin ciki take dukda cewar hankalinta ya rabo biyu saboda Mardiyya dake naƙuda tunjiya kuma ta haɗa kaya kamar ba'a magana wanda Baba ƙarami ya saka ta yi. Naƙudar Mardiyya bata saka Umma ta yi noticing ƴan uwan Mami da suka cika part ɗinta ba Burhan na can wajan mai gadi saboda baya son hayaniya sai kwaɓe fuska yake lokaci lokaci yake kiran Zainura kamar zai mata kuka wai kansa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login