Showing 24001 words to 27000 words out of 190738 words
Chapter 9 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt
Ridayya ta sauke mata wuƙar a wuyanta ta ƙara sauke mata a damtsen hannu, Khairy ta gantsare tana kare cikinta don a duniya yanzu ba abinda take so dama da cikinta.
"Jama'a wai ba kowa a gidanne? Zata kashe ni wallahi kashe ni za ta yi matar yayana ta haukace ku kawo mana a gaji" A guje ta buɗe ƙofa ta fita Ridayya ta bita da sauri, daidai nan Zameer na shigowa da Zainaba idanun Ridayya rufe kallon Zameer take tamkar Khairy ce a gabanta. Yana zuwa ya kifa wata wasu lafiyayyun maruka guda biyu sau biyu a jere ta yi taga-taga zata faɗi ta cake waje guda. Khairy itama wuƙar ta ɗakko ta ce "Wallahi ba ki jimi ciwo a banza ba, ƴar ta'adda kawai" Ridayya ta yi murmushi hawaye na fita daga idanunta bakinta na rawa ta ce
"Haka nake so daman, ko dai ki kashe ni ko kuma na kashe ki" Khairy ta ɗaga wuƙar zata kwaɗawa Ridayya a gigice Zainaba ta hankaɗa Zameer tsakiyarsu daidai nan Khairy ta sauke masa wuƙar a mara, ya fasa ihu yana riƙe gabansa saboda wani azaba daya tsarga masa jini ya fara zuba, ya faɗi ƙasa Khairy ta shiga ɗaki ta rufe ta fara haɗa kayanta.
Ganin Zameer kwance a ƙasa cikin jini ya dawo da Ridayya daga hayyacinta, ta rarrafa ta nufi inda yake ta fara jijjiga shi tana kuka tare da furta
"Ka tashi rayuwata, ka yi mini rai kar ka barni a cikin wannan halin da nake ciki" Zainaba ta ce "Ridayya mene ya sameki a fuska? Gobara kukai ta cinye rabin fuskar ko annoba ce ta faɗa miki? Zameer kuma ina ruwanki da shi, ai bake kika ji masa ciwon ba ki yi ta kan ki kawai" Wani irin kallo Ridayya ta yi wa Zainaba ta ce
"Ki fita daga rayuwata ki barni haka, mene rayuwarki da gidan aurena da mijina kuma? Kin saka mini ido kin takura ni"
"Ridayya ni kike faɗawa haka saboda kina son maso wani? Makauniyar soyayyar da bata da wata riba wajanki, munafukin mijin naki cima zaune wahalalle maƙaryacin" kuka kawai Ridayya take kafin ta ce "Kima siyar da rayuwa take, soyayya kuma bada rayuwa take, ki saurara mini ki barni ki tsahirta mini...,"
Saukar bulala ta ji ta ko'ina a jikinta, tun yana dukan ta da bulala har ya fara saka ƙafa yana ball da ita tare da taka mata ruwan ciki, daman buta ta ɗauka zata shiga banɗaki ta fasa, azabar bugun mararta da ya yi ta saki kashin wahala a kiɗime take cewa "Na tuba ka yafe mini tausayi ne, don Allah ka da ka kassara mini ɗan cikina" Bai kulata ba, dukanta yake da ko'ina tana ihu da ƙoƙarin guduwa har ta kasa motsi. Zainaba mutanenta na kusa jikinta ya fara rawa da ɓari ta ƙura wa Zameer idanu kafin ta yi ihu ta zube a ƙasa tana surutai.
"Tsinanne maciyaci, mugu macuci ba za mu barka ba, ka zalunci yarinyar jama'a ka ajiyye karuwa a cikin gidanka ƙarya yake ba ƙanwarsa ba ce zaman cin amana suke bashi da kowa a garin nan" Da sauri Zameer ya ce
"Munafukar banza na ci uwar aljanun" Domin ya ɗauka aljanun ƙarya ta yi. Baban hajjo Usman ya yi sallama Zameer ya ce "Yawwa! Babu matarka babu tawa duk abinda na yi mata zunubinta ya ja mata, ba zata raba mini aure na kasa gane kan matata ba" Usman ya ce
"Ai kowa ya yi na gari kansa, daɗin abin ba a duniya za mu tabbata ba" Yana faɗin haka ya kinkimi matarsa sukai waje, Zameer ya shige banɗaki sosai gabansa da mararsa ke masa ciwo har ɗingi shi yake. Yana fitowa ya shiga ɗaki ganin Khairy ya yi tana haɗa kayanta da sauri ya ajjiye wayar hannunsa ya nufi inda take, ta yi saurin kauce wa ta ce "Kar ka taɓa ni, kar ka fara" Zameer ya sauke numfashi yana yin ƙasa da murya.
"Haba dear, ki sassauta hukuncin nan" Khairy ta ce "Wato ni ba ƴa bace saboda ina zaman bariki da kai ko? Wallahi idan kaga ba haƙura ka bi mini hakƙina"
Riƙota ya yi gabaɗaya ya haɗe ta da jikinsa yana sauke mata numfashi a wuya idanunsa a saman kyakkawar fuskarta, a nutse daidai kunnenta ya ce "Za ki iya barina ashe?" Ya faɗa yana fesa mata iska a kunne. Jikinta ya saki sai kawai ta fashe da kuka ta ce
"Ka sauya mini matsayi, ka mayar dani matarka, zan yi istibira'i mu yi aure mu huta da wannan rayuwar na san cewa zaman kishi nake da tsinanniyar matarka mai zubin aljanu"
Hannu ya sa ya matse bakinta a hankali ya ce
"Kar ki mini tsiwa, ke kika bari har tasan da cikin amma nasan me zan yi" daga nan rufe ƙofa sukai abinsu tare da barin Ridayya yashe a ƙasa.
Usman ya ce "Kema Allah ya ƙara ya daɗa, kafirin iyayinki ne ya ja miki wahala" Zainaba na kuka ta ce "Baban hajjo ba zaka gane ba, jin Ridayya nake kamar ƴar'uwata wallahi tausayinta nake ji sosai" Bai ce mata komai ba don baƙin ciki yana jin da shi mai kuɗi ne babu abinda zai hana shi maka Zameer a kotu ko kuma ya kaiwa hisba ƙara. "In sha Allah Zameer sai ya wulaƙanta ba zai taɓa ganin daidai ba, ba kuma zan bar shiga gidan nasa ba"
"Azzalumi ba fa dole sai ya wulaƙanta ba, muddin zai tuba wajan Ubangiji" a fusace ta ce "Banda munafiki irin Zameer wanda shaiɗan ya yi wa fitsari aka".
Sanyin yamma ne ya dawo da Ridayya daga suman da ta yi, ta motsa kaɗan tare da yin ƙara saboda wani nauyi da hannunta ya yi mata, da ƙyar ta miƙe zaune sai a lokacin ta farga da kashin da ta yi, ta runtse idanunta zuciyarta na zafi da raɗaɗi na rashin mafita da abin yi. Ba zata iya tashi ba don haka ta dinga jan jiki zuwa banɗaki ta wanke jikinta tas, kana ta daddafa ta fito tare da haɗa kai da qwiwa ta shiga sauke ajjiyar zuciya wani irin matsanancin tsoran Zameer ya kamata, haka kurum ta shiga razana ita kaɗai, ga ciki a jikinta, ga duka ga wata kafurar yunwa dake mata barazanar raba mata hanji. Tunaninta ya tsaya kwakwalwarta ta gaza yin aikin komai da sarrafa wasu kalaman na Zameer. Bata da burin daya shige zuwa gidansu wajan Mami. A hankali ta miƙe ta saci jiki ta fice daga cikin gidan.
Duk inda ta gilma kallonta ake ana nunata, domin kawo yanzu a wannan sabon zamanin da muke ciki ba kowa zai kai Ridayya gidan miji ba, amma a yarda ake kallon nata da yawa sun ɗauka wata dattijuwar ce. Turus ta yi lokacin da taga gate ɗin gidansu a garƙame, gabanta na faɗuwa wani yaro ta gani, ta ya fito shi da hannu da gudu ya runtuma yana "Wayyo mahaukaciya" Ridayya ta dinga kallon kanta can wata yarinya ta fito daga gidan dake kusa dana su Ridayya, ta ce
"Don Allah masu gidan nan fa?" Yarinya ta kalli Ridayya tana ja da baya ta ce "Sun tafi Rano, sun daɗe da tafiya na ji ana siyar da gidan za a yi"
"Siyar da gida? Rano?"
Ridayya ta maimaita a fili, yarinyar tuni ta juya, zama ta dinga yi a wajan abin mamaki duk wanda suka zo shigewa sai su ajjiye mata kuɗi a gabanta, wani irin hawayen baƙin ciki ya ziraro mata a ƙofar gidansu ake bata sadaƙa? Ganin tana samun kuɗi taƙi tafiya har aka kira magriba, ta rarrafa ta miƙe a hanya ta siyi taliya guda ɗaya, da kayan miya da magi da mai. Tana zuwa ta fassakara itace tare da dafa jallof ɗin taliya ta saka daddawa. Zameer da Khairy suna ɗaki suka jiyo ƙamshin abinci nan da nan kwaɗayin masu ciki ya addabi Khairy ta ce "Baby matarka ke girki?"
"Ina ta ga kuɗin?" Saboda basu san ta fita ba ta ce "Ka duba please wallahi hankalina duk ya tashi" Ya yi murmushi yana cireta a jikinsa ya ce
"Idan ma ita ce dole zata bani ba zata iya cin abinci banci ba, idan ta bani zan kawo miki" Yana fita ya samu Ridayya na juye taliyar a faranti daman rabi ta dafa, ya tsaya tare da sassauta murya ya ce "Ridayya mai sona girki kike?" Shiru ta yi masa don magana yanzu sai dole ga zugin fuska gana hannu da ƙyar take motsa shi.
"Fushi kike dani? Bari na yi sallah na dawo mu yi magana ki jira ji" A hankali ta ce "To" Yana fita ta saka hannu a faranti ta fara cin taliyar ta cinye tas, saboda baƙar yunwa ta suɗe farantin kana ta yi alwala tare da yin Sallah, hannu ta ɗaga ta rasa wacce kalar addu'a za ta yi sai kawai ta yi shiru.
A zaune ta sameta ya ce "Ba dai kin cinye abincin ba?" Ta ce "Wanne abinci?" Ya ce "Wanda kika dafa" ta yi shiru ya sake magana shiru, ji ya yi kamar ya zabga mata mari amma ya daure
"Fushinki a zama ce mai raɗaɗi a gare ki wife, zan jure shurin kowa banda naki" Nan ma ta yi shiru. Cike da makirci ya fashe da kuka yana riƙe hannunta ya ce
"Saboda Allah ya jarabce ni da son ki, kike wulaƙanta ni Ridayya? Laifi ne don na so ki? Mene laifin zuciyata kar ki hukunta ni ta haka, nikam kar ki mini wannan azabar zan zutu da yawa" Kuka yake sosai ya ce
"I love You Ridha, wallahi ina son ki, ki yafe mini abinda na yi miki jiya"
"Me ka yi mini?"
Ya ce "ƙona ki da dutse, wallahi lemo aka bani na sha ashe akwai ƙwaya a ciki ita ta buge ni, har na ci zarafin matata ƴar aljanna, ba zan taɓa yafewa wanda ya sa na yi shaye-shaye ba" Ta yi murmushi mai ciwo ta ce "Ba komai" Ya rirriƙe hannunta ya ce "Hankalina ya tashi gudun kar ki yi kisan kai a kashe mini ke ya sa na dake ki, bawai saboda kin jiwa Khairy ciwo ba" Ya sauke murya ƙasa yana tausasa kalami ya ce "Wanne irin miji ne ni? Ridayya ban cancanta da rayuwarki ba ina zaluntarki, ki bari na sawwaƙe miki" Ya faɗa yana bugar cikinta.
"A'a, ka rufa mini asiri bani da kowa yanzu sai kai" Ta faɗa tana girgiza masa kai, ya ɓoye dariyarsa ya ce "Me ya sa kike zargin Khairy dani? Saboda ban taɓa faɗa miki Khairy nada aure ba? Laifina ne ƙanwata Khairy nada aure saɓani suka samu da mijinta shi ne ta nufi gida, a gida aka hanata zama ana ganin laifinta ne, ganin hannunka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar ya saka na dawo da ita gidana kafin Allah ya daidaita labarin auren"
"Kuma ciki bai bayyana ba sai yanzu?" Da sauri ya ce "Kwanciya ya yi, ai kwantawa cikin ya yi amma gobe zan je na same shi zata koma ɗakinta shikenan?" Ta jinjina kai kawai ya ce "A'a ki ce kin yafe mini" Ta ce "Ya shige ba komai ka bata haƙuri" Ya yi sai kuma ya ce "To ɗakko mana abincin muci mai sona" Ta ware idanu ta ce "Bani da abinci,nima bata ishe ni ba" Wata uwar ashariya ya narka Ridayya a zuciyarsa ya fice. Yana fita Khairy ta shigo ta ce "Yanzu kin fahimta ko?"
"Ki yi haƙuri ban ɗauka haka ba, Allah ya daidaita tsakaninku" Khairy ta ce "Wannan turaren naki da maganin matan za ki sammin please" Ridayya ta nuna mata lafiyayyiyar humra ce da kwalacca, tun kafin ta buɗe suka cika ɗakin da ƙamshi ita kanta Khairy ta san humra ɗin ta musamman ce ba a ko'ina ake samun irinta ba, tafiyayyiya ce, sai ka wanke kaya sau nawa ƙamshinta bai fita ba. Ta duba maganin matan duka ta kwashe ta yi waje Ridayya sam bata damu ba hankalinta ya kwanta bata da matsala da Khairy bata damu da sanin me za ta yi da kayan matan bai tunda ba a gidan miji take ba.
Cikin dare Ridayya ta kasa bacci hannunta ya kumbura, fuskarta sai jini take. Kamar an cillo Zameer haka ya faɗo ta kalle shi ya ce
"Ina buƙatar ki"
"Bani da lafiya, marata ciwo take hannuna haka ga fuskata" Rai ɓace ya ce "Nina ɗora miki ciwon? Sanda na biya sadakinki kin faɗa mini ba ki da lafiya ne? Bayan ba uwar tsiyar da kika iya sai dai ki kwanta kamar ruwa? Allah ya ƙara mini haƙuri, ga babu gyara ɗan ƙamshin nan na zamani ɗan farin da mata suke"
"Dame zan yi kwalliyar? Duk abinda na mallaka wana bawa ina cewa kai ne? Ya kake so na yi wai me ya sa duk ka sauya?" Ya ce "Bai dame ni ba, hakƙina na zo amsa" Mamaki ya cika ta ganin yana rufe fuska da face mars, daman tunda suke irin sumbatar nan ta Zameer bai taɓa yi mata ba, tamkar yana ƙyanƙyamin bakinta "Idan har da yarda ta ce to I'm not in the mood"
Ƙafa ya saka ya maketa ta faɗi ƙasa kamar mahaukaciya babu tausayi yana ya haike mata babu kulawa ba soyayya, ya yi forcing nata ne tunda bada yardar ta ba, haka ya shaƙe mata wuya tana kakari gabaɗaya bai san me yake ba kamar zai kasheta...
Kuka ta dinga yi ta kasa motsi saboda wahala wuyanta duk shacin yatsunsa saboda shaƙa. Washegari bayan Zameer ya fice Khairy ta shirya ta fice wajan samarinta. Mai gyara Zainaba ta kira ya duba hannun Ridayya ashe karyata Zameer ya yi tana kuka sosai da muryarta mai sanyin nan kamar shagwaɓa, saboda bata da hargowa sam. Bayan an gama Ridayya ta kwaɓe fuska ta kasa kallon Zainaba, murmushi kawai Zainaba ta yi ta ce "Alkawari na zo ki cika mini, ki bani labarin rayuwarki kafin aure" Ridayya ta lumshe idanunta ba dan ta so ba ta soma bawa Zainaba labarinta kamar haka.....
*Ga duk mai buƙatar humra da kwalacca lafiyayyun sa mai gida magana ka hanzarta neman wannan number 08164069385 suna aikawa ko'ina, akwai ta masu ƙarfi akwai ta masu ƙaramin ƙarfi, ba za ku taɓa ladamar siya ba muna maraba da masu siyan ɗaiɗai ko sari🥰🥰🤙🏼🤙🏼*
*✿ MUNAFUKIN MIJI ✿*
Ridayya's story
Page 10
BRIGHT PENS🤙🏼 free batch
Please ku yi following nawa a facebook🫶🏼👇🏼
https://www.facebook.com/naeemerh.suleiman?mibextid=ZbWKwL
*PAID ADVERT*
https://chat.whatsapp.com/LvflCjMI3U5IfUHobHzudk
*HAUSA AFFILIATE MARKETING (HAM COURSE)* Yadda zaka samu kuɗi a ƙalla 50k- 100k a wata online da wayarka ta hannu (Smartphone) Matan aure, Ma'aikata, Ɗalibai, Ƴan mata e.t.c 07063194432
*Ta ina zan fara ne? Ta haɗuwar Ridayya da Zameer a jami'a ko kuma ta amintarta da ƙawarta Mardiyya? Ko dai na fara ta riƙon da Ustaz Bilal ya yi mata, girman ƙaddarar nada faɗi, al'ajabinta na da girma, dafin ƙaddarar kan iya harbar kowa, babu kuma wanda akai wa shamafiki da zubar hawaye. lissafin ƙaddarar zai fi tafiya daidai, idan muka fara da tubalin ginin, ya sanya zan fara da sanda Ridayya Bilal Mansur Rano ta zo duniya!*
Gabaɗaya suna tsaye sun yi carku-carku yanayin sauyin fuskokin kowa zai labartawa mai kallon su akwai lauje cikin naɗi, abu biyu ya sanya zuƙatansu cikin halin da suke, dukda bai cancanci ace akwai damuwar da kan iya hana fara'ar fuskarsu bayyana ba, duba da tagomashin abin alherin daya samu zuri'ar Mai ran ƙarfe a safiyar yau ta juma'a. A kuma unguwar Darmanawa dake Jihar Kanon Nigeria.
Ciwo ɗaya idan ya samu mutum ɗaya a familyn, to kamar ya shafi kowanne daga cikin ahhalin ne kasancewar su, marasa yawa da girma, kowa a hargitse yake idan ka ɗauke Alhaji Mansur Rano, wanda ko zuwa cikin asibitin bai yi balle a san halin da yake ciki. Shekaru aru-aru bai taɓa nuna rashin kulawa akan jininsa ba sai yau, ranar da kowa ya girgiza ya kuma ji a jikinsa tare da shakkar Alhaji Mansur Rano, jinkimarsa da ainahin ɓoyayyiyar siffarsa ta bayyana, wacce ta nuna asalin halinsa wanda inuwarsa ta lulluɓe tare da yi wa jama'a katanga da ita. Reception ɗin asibitin a cike yake idan ka ɗauke wanda baya garin ma. Dr ya fito da sauri yana goge zufar data yanko masa, cikin sauri kuma Hajiya ta miƙe tare da tarar shi tun kafin ya ƙarasu.
"Likita ya ake ciki? Yarinyar nan har yanzu, ba amo ba labari wacce kalar naƙuda ce wannan?" Dr ya yi jim sai kuma ya ce "Sai haƙuri Hajiya..,"
Jikin Hajiya ne ya fara rawa nan da nan ta nemi rikicewa zuciyarta na bugawa ta ce "Ka...ka.. kamarya sai haƙuri? Kada ka kuskura ka ce mini Fatima ta rasu, kar ka ce mini na rasa surukata da abinda ke cikinta?" Ƙoƙarin yi mata bayani yake amma bashi da zarafi da ƙarfin qiwwar yin haka, shi kansa bashi da tabbaci wacce ake magana tana raye ko ta mutu ne. Amma ce ta share hawayen dake gudana a idanunta ta miƙe da ƙyar ta nufi inda Hajiya ta cakume Likitan tana surutai.
"Hajiya ki sake shi please, ki bari mu ji me ya zo da shi, allow him to talk" ta rarrashi Hajiya kana ta dubi likita ta ce "Dr meke faruwa? Ya jikin Fatima?" A karo na wajan uku ya ƙara girgiza kai ya ce "Tsakani da Allah tun yaushe ne ta fara naƙuda?" Amma ta yi jim ta ce "Bana ce ba gaskiya, Fatima ai zurfin ciki gare ta, kodayaushe cewa take lafiya lou take meke faruwa?"
"Follow me Maaa"
Amma ta ce "A'a batun na biyo ka bane, bani da kuzarin hakan ma kawai ka faɗa mini halin da ƴar'uwata ke ciki" Dr ya yi jim sai kuma ya ce
"Har yanzu bata sauka ba tun jiya da kuka kawota, maganar da ake mun fidda rai da ita, wasiyya take bayar wa kuma tana buƙatar ganin mijinta, don Allah ku kira shi tana cikin wani hali" Amma ta yi baya tana shirin zubewa Zuhura ta yi saurin tare ta ta ce
"Subuhanallahi, take it easy Amma In sha Allah babu abinda zai faru sai abinda Ubangiji ya ƙadarta" Da dugu Amma ta nufi Emergency room hankalinta baya jikinta, kai tsaye ta hankaɗe likitocin da suke wajan tare da faɗawa cikin ɗakin. Abinda idanunta suka gani ya yi matuƙar gigita ta, ta nufi gadon tana cewa
"Ba mu yi haka dake ba Fatima, kar mu