Showing 63001 words to 66000 words out of 190738 words
Chapter 22 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt
ƙarfe, Zuhura da Balkisu kowa yana nan Alhji Mansur Rano da Baba ƙarami, sai yaran su. Ammi, da Mami. Farin ciki sosai a zuciyar Mami ganin Zainura da Ridayya cikin kaya iri ɗaya. A ka ci aka sha za a fara tattaunawa Baffa ya ce "Ke tashi kibar nan" Tasan bada kowa yake ba sai ita, ta miƙe hakan yasa Ustaz miƙewa Baffa ya ce "Ya zaka tashi?"
"To bari na dawo na zauna, Ustaza jinin jikina ce, nima na yafe" Mami ta miƙe zata bar wajan Ammi ta ce "Fatima lafiya za ki tashi?"
"Lafiyar kenan"
"Ikon ko na yi miki laifi ne Fatima? Kwana biyu kamar gaba kike dani ma wallahi, me na yi miki? Bafa ni na sheganta miki yarinya ba, bani nakar zomon ba rataya aka bani"
"Don Allah kin ishe ni Maryam, na ce miki wani abu? Rayuwa ce fa kowa ya tashi gina ramin mugunta sai ya gina daidai da shi gudun watarana" a zafafe Baffa ya ɗauke Mami da mari kafin ya sauke hannunsa ya sauke wa Ammi lafiyayyun maruka guda biyu tunda ba zata iya marin mijinta ba ta ce
"Ki saurara mini, kin hana ni sukuni kin takura ni haba Maryam me na tsare miki ne? Me na yi miki don Allah kishi hauka ne?"
"Ban taɓa ganin inda abin alheri ya zama sharri ba, ni kika mara Fatima duk ƙoƙari na wajan gina rayuwar Ridayya, kin watsar da ita ko kallo bata ishe ki ba" kuka sosai Ammi take na kissa hakan yasa Hajiya ta ji ba daɗi nan suka ɗorawa Mami laifi ba ta yi halacci ba ta riƙe mata jaririya har girma amma duk a banza ashe take gani. "Hajiya ki yi mini uzuri, babu inda uwa zata haifi ɗa kuma ta bar shi ya wulaƙanta, ku ke a gwada Ridayya cikakkiyar ƴar maye ce ƴar srup duk sanadin Maryam idan kuma hakan shine soyayya babu laifi" Tana faɗin ta fice rai ɓace haƙurinta ya je ƙarshe hakan kuma baya rasa nasaba da kukanta da ta kai wajan Ubangiji.
Ustaz ya dinga kallon Ridayya yana jinjina kalmar shaye-shaye sai yanzu ya fara fahimta wasu lokacin da take masa magana ba kai ba kan gado yawan bacci ko idanunta biyu sai ta dinga lumshe Idanu. A fusace ya damƙi hannun Ridayya ta fara kuka Umma za ta yi magana Baba ƙarami ya dakatar da ita "Ba ruwanki bake kike masa tarbiyyarta ba, ki bar shi"
Kuka take sosai tana "I am sorry Abbiey ka yafe mini don Allah.....," Hannu ya watsa mata a fuska a karo na farko a rayuwarsa idanunsa suka firfito waje fuskarsa ta yi jajur, masifar zafin hannu ne da shi hannu ya ɗaga zai ƙara zabga mata wani marin ya ji ta faɗa jikinsa ta ƙanƙame shi a rikice daga nan kuma ta zube a ƙasa jikinta na rawa da ɓari tana cuccure wa waje guda. Ustaz ya lumshe idanunsa yana murza goshinsa sosai da kyau a hankali ya ce "I am sorry Ustaza...!"
"Gayu an sanku ba a san makwantar ku ba, kaga samarin ƙauyen Nahutun Batsari Giɗaɗo ikon Allah" Zameer ya haɗe fuska ya ce "Wanne cin fuska ne haka Mujahid?"
"Gaskiya dai, bani hakƙina" Zameer ya ciro gudar ɗari biyar ya bawa Mujahid ya ce "Mene wannan ai dubu uku zaka bani, kayan da ka yi opay sababbi ne ko mai shi bai saka ba wlh"
"Sune dani" Mujahid ya ce "Tab, sunanka Zameer Mahboon Dollar fa? Kai da zaka bani dollar naga Naira, Naira ɗin ma ɗari biyar ba girman ka bene" tsaki Zameer ya ja ya fice daga wajan ya nufi makarantar allon domin yamma ne yana zuwa malam ya haɗa shi kula da almajirai yana fita ya tashi ya nufi gidan Mama ta dinga murna data gansa ta ce "Ɗana na kai na, kwana biyu na ji ka shiru na ɗauka ka koma ƙauyen naku?"
"A'a" Ta ce "Wai wanne ƙauye ne?" Ya ce "Ni fa ina da wani deal bana son kina nunawa bake kika haifan ba, zan kawo wata gidan nan ki nuna gyara ake mana sabon gida shi ne muka dawo nan ki nuna yadda nake da nutsuwa hankali da dukiya" Ta ce "A nawa?"
"Kin ji matsalarki ai, ana maganar yadda za a samu miliyan goma kuɗi zan ba ki sosai"
"To shikenan"
Kyakkawar mu'mala ke wanzuwa tsakanin Meer da Ridayya, ta daina ganin kyan Abbiey ta janye jikinta yanzu ganinsa take koma baya cikin maza bai iya wanka ba, gashi yanzu yana ɗan haɗe mata fuska sai dai tasan Abbiye mutum ne mai tsananin kwarjini, nutsuwa kamala da haiba kyakkawa ne shi mai tarin baiwar ilimin addini dana boko. Ita kam Zameer yana tsananin burgeta gashi a iya magana kullum suna maƙale a waya. Babban kuskure wanda da shi Zameer ya gina tarko yadda Ridayya ta fara furta masa kalmar Soyayya, ya shure kimar da Ubangiji ya yi mata na ɗiya mace ta nuna ƙaunar ta ga namijin da bama ɗigon soyayyar ce a ran shi ba. Sanda ta faɗa masa tana mai cewa "Ka taimaka mini an ce ba zan taɓa samun mijin aure ba, ni kuma hankalina ya kwanta da kai komai naka yana burgeni" Kasa magana ya yi, sai da ya kira Moo ya ce "Done, she said it, she said she love me wow!" Moo ya ce "Kana da sauran aiki"
Ganin kiran ta ya saka ya ɗaga "Muna magana ka kashe" Ya ce "Ridayya dole na kashe na jima ina son ki amma sai naga tamkar hakan ba mai faruwa bane, kina da kyan da zamanki mata a gare ni zai an tona"
"A'a wallahi zan aure ka, ka amince mini please, kai ne ma kafi ƙarfina duk gidanmu babu mai so na sai Abbiey da iyayensa Kullum Baffana ai ban tani yake....," Daɗin soyayya da shauƙi ya saka Ridayya kwasar komai na sirrin rayuwarta dana gidansu ta faɗawa Zameer ya ce "Ina son ki ni ma Baby pretty na" Ta ce "Na gode sosai da amsar ta yi na"
A hankali ya tsuke bakinsa ta cikin speaker wayar ya ce "Mu'ahhh take this as my appreciation" Ta yi murmushi kiss ɗin har cikin zuciyarta ya ce "Wannan na waya ne kafin gobe ai haka ake soyayyar" WhatsApp suka koma ta ji ya ce
"I love You Mrs Zameer, i so much love you Baby"
"I love you too"
Huci da fusgar wayar da aka yi ya saka Ridayya juyawa a ruɗe jikinsa taga yana rawa kamar ana kaɗa masa ganji gargasar jikinsa duk sun mimmiƙe a karo na farko taga sauyin yanayin idanun Abbiey ya yi jajur ta miƙe zata kwasa da gudu tako ɗaya ya yi ya damƙo ta "Don Allah Abbiey kar ka dake ni i am sorry please...,"
Kai kawai yake girgiza wa ya kasa magana ya damƙe hannayenta duka biyun cikin nasa, yadda jikinta ke ɓari haka nasa ke yi da ƙyar ya fusgi maganar
"Soyayya? Wani kike cewa i love You Ustaza?" Ya Girgiza kai ya ce "Ba haka mukai dake ba, kin ƙarya al'ƙawari Ridayya ban shirya hakan a gare ki yanzu ba, karatu nake son ki yi ba Soyayya ba" Ta kasa magana ya sake matse hannunta yana jawo ta dab da shi muryarsa bata fita saboda rawar da take ya ce "Soyayya Ustaza? Mene laifina da za ki hukunta ni ta wannan hanyar?"
"Aure nake so ba karatu ba Abbiey ka tausaya mini ina......," A bazata ya tsinkayi maganarta gane abinda take ƙoƙarin faɗa wanda faruwar hakan daidai yake da tarwasa zuciyarsa ya saki hannunta ya matsa kafaɗunta yana sake kusanta kan shi gare ta a fusge ya ce "Karatu nake so ki yi ba soyayya ba, idan soyayyar kike shi ma za ki iya, idan auren kike so ba gani ba? Ustaza idan auren kike so ba gani ba? Nine ya dace dake ni ne kuma zan aure ki.....
As your wish as my own wish ga update ne🥹🧚🏻♀️
Na'ima Sulaiman Sarauta
Nimcyluv
08119237616
*✿ MUNAFUKIN MIJI 21✿*
Mikiya Writers Ass....
BRIGHT PENS🤙🏼 free batch
Nimcyluv
Ustaz ya kasa magana sai kafaɗun Ustaza daya sake matse wa yana jijjigata idanunsa har wani ruwa ke kwanciya a cikinsu.
"Ustaza why? Ni na ce ba zan iya aurenki bane? Kar ki hukunta ni ta wannan hanyar Ustaza, na yafe miki ki janye maganar nan" Zuciyar Ridayya ce ta yi wani irin tsalle da ya tilasta mata rufe idanunta tare da ware su da kyau ta watsa a kan rikitacciyar fuskar ta Abbiey ɗin nata, bata san mene a idanunsa ba da yake mata shamaki wajan nutsa ganinta cikin nasa, ta kasa bisa dole ta janye idanunta na zubar da hawaye ta ce
"Me kake nufi Abbiey, ban gane ba wa zaka aura? Wani laifi ka yi mini Abbiey?"
Ustaz ya runtse idanunsa takaicin yadda maganin shaye-shayen nan ya dauɗar mata da kwakwalwa ke ƙuntata zuciyarsa a hankali ya ce
"Kin gane mana Ustaza, bambancin ko wacce rana shigar ta da fitar ta, na ƙara kusanta ni dake, ki yi mini alfamar a bar maganar haka nan"
"Ina son auren shi bana son karatun aure nake so nikam" ta faɗa hawaye na sake wanke mata fuska zuciyarta na yin ƙaura zuwa ga tunanin Zameer ɗinta.
"Ok zan miki aure, zan haɗa ki da miji na gari Ridayya" Kuka take sosai ganin yadda Abbiey ya kasa fahimtar ba kowa take muradin aure ba sai mutum ɗaya wanda a duniyar Ridayya babu wanda ke burgeta sama da shi domin har yanzu bata san ma mene soyayya ba, ta ɗauki alhakin yadda take jin a kan shi da yadda komai nasa yake Unique matsayin SO. Bata da hankali da nutsuwar tsayawa ta gane bambancin dake tsakanin SO da BIRGEWA.
"Shi ma na gari ne, wallahi Zameer na gari nikam shi zuciyata shi ta ke da muradi" A wannan karan wata tsawa Ustaz ya daka mata amma ko gezau ba ta yi ba, sai ma haɗe fuska da ta yi tana sake ci-gaba da kukanta.
"Shin ni bani da Qualities ɗin zama miji na gari a wajanki Ustaza? Ki yi tunani shekaruna nawa, mene ya hanani kasancewa da wata ɗiya mace, just because _I love you_"
Da sauri ya sake ta, jin yadda kalaman sukai futar da kan su tare da zama daram a kan shi bai shirya ba, bai san yadda akai ya saki abinda zuciyarsa ke danƙare da shi ba. "Kashe ni kawai Ridayya" Muhammad-Bilal Ustaz ya faɗa yana jin alamun zufa na yanko masa daga tsakiyar goshi zuwa bayan wuyansa, idanunsa na lumshe wa har wani dishi-dishi yake gani tare da wata yana-yana.
Ta durƙushe ta ce "Wallahi ban taɓa mafarkin ganin kai na a matsayin matarka ba, kai ɗin uba ne, babu wani tarihi da zai zo ya sauya sunana daga matsayin Ridayya Muhammad-Bilal Rano, bana son ka Abbiey komanka baya burgeni kana da tarin bambanci da Zameer wallahi.....,"
"Ya isa! Allah yafe miki Ustaza nikam na yafe miki" Yana faɗin hakan ya juya da sauri ya fice daga cikin ɗakin. Rasa inda zai nufa ya yi, baya da wani da yake sharing damuwarsa da shi, baya son mutane sam mutane basa ɗaukar hankalinsa. Ya tsani ƙarya magana biyu cuta ha'inci uwa uba rainin hankali wannan dalilin yasa ya ware kansa. Yana shiga bedroom ɗinsa ya dinga safa da marwa zufa ta gama wanke shi tas hannunsa goye a bayansa maganganun Ridayya na amsa kan su da kan su a kunnensa. Da sauri ya fice daga ɗakin ya nufi bedroom ɗin Baba ƙarami domin Umma bata nan.
Baba ƙarami na zaune saman laddumar dake shimfiɗe a carpet yana duba jarida. Idanu ya ji a jikinsa ganin daya bambanta dana ko wanne lokaci ya ɗago kai a hankali idanunsa ya sauka a kan na Muhammad-Bilal Ustaz. Rabon da yaga yanayin mai firgitar wa a tattare da Ustaz ya manta wannan shi ne karo na farko daya taɓa shiga irin wannan situation ɗin, tun yana ƙarami sai kuma yanzu. Kafin Baba ƙarami ya yi magana Ustaz ya ƙarasa ciki da sauri kuma ya kwanta yana ɗora kan shi a cinyarsa mahaifin nasa.
"Subuhanallahi! Babban mutum lafiya kar ka rikitar dani da wannan yanayin mene ne? Ridayya ce babu lafiya mene ya same ta?"
Domin a ransa yake jin babu wani abu da zai iya saka Ustaz shiga wannan halin sai Ridayya ko ciwon nata ne ya motsa? Mene ya samu Ridayya? "Babban mutum bar rufe ido faɗa mini ne kar ka yi give up da wurwuri kana da rayuwar muradan daya kama ta ka cimma"
"Abba ka yi mini addu'a" Da ƙyar yake maganar saboda wani zazzafan zazzaɓi da ya cimma shi lokaci guda. Ya damƙe hannun Baba ƙarami ya ɗora a saitin zuciyarsa dake dokawa da matsanancin ƙarfi kamar zata fito ta ratso ta tsakiyar ƙirjinsa. Jijiyoyin kansa sai harba masa suke ciwon kan shi ya tashi nan da nan idanunsa ya fara rufewa. Jikin Baba ƙarami ya fara rawa ganin yadda jikin Ustaz ya saki ya ɗauki waya ya kira Baffa ya sanar da shi kana ya kira mahaifiyar Ustaz ya faɗa mata. Ustaz bai san yaushe ne ba, kuma san ya akai ba kukan da ya addaba masa yake shirin fasa masa kai shi ne ya saka shi buɗe idanu, tashin farko ya fahimci a gadon asibiti yake ga ruwa na bin jikinsa meke faruwa?
"Sannu Babban mutum ya jikin?" Cewar Ammi ya haɗe fuska tamau yana shigar da idanunsa ciki, a hankali ya dinga bin mutanen ɗakin. Baffa na zaune a gefen Ustaz idanunsa sun faɗa sbd fargaba, sai Baba ƙarami da baya cewa komai, sai Umma da kuka take, sai Ammi, sai kuma Mami data rufe idanu tana jan carbi Zainura a gefenta sai Zuhura Balkisa. Sai kuma sauran mazan gidan ga Junaid ma. Mutum ɗaya ce babu wato Ridayya to me ma yake a asibiti mene ya samu Ustaza da babu ita? A nan ɗin.
"Sannu Yaa Bilal"
Ya kame fuska ya ce "Wai wani ne ya mutu ne da naga gabaɗayan ku?"
"Wani ne dai yake jinya" Junaid ya bashi amsa Zuhura ta ce "Kenan bamu kyauta ba da muka damu da ciwonka kake ta haɗe fuska?"
"Ban sa dake ba, daga ɗan yin ciwon kai na kwanta bacci sai na ganni a asibiti?" Junaid ya riƙe haba yana jinjina wulaƙancin Ustaz ya ce
"Gafa ciwon kai nan mun gani, kama ce da ƙafar ka zo kwanan ka biyu a sume fa, wai mene ya same ka har haka"
"Ubanka ne" Baffa dake kusa da Ustaz ya ce "Gani nan ina godiya kuma" Ya yi saurin rufe ido sai kuma ya sakko "Ina zaka?"
"Ko second ba ƙara yi cikin asibitin nan ba" Kafin sun yi magana ya fice yana jira yana mai dafe kansa da ƙyar ya shiga napep ya yi gida ko kuɗi bai bawa mai napep ɗin ba ya nufi cikin gidan kai tsaye bedroom ɗin Ridayya.
"Allah ya baka lafiya"
Cewar mai napep ɗin yana jan a bar shi ya bar wajan. Domin tunaninsa zafin ciwo ne ya sa bai bashi hakƙinsa ba.
Sautin kukanta ne ya fara sauka a kunensa ya shiga da sauri ya ganta kwance ta yi zuru daga ita sai body short ya zauna a gefen gadon dab da ita ya ce "Kuka Ustaza? Mene haka?"
"Abbiey don Allah don Annabi ka tausaya ka aura mini Zameer wallahi ni bana son ka, ba ka yi mini matsayin miji ba"
Maganar ta daki Ustaz jin kai tsaye yadda Ridayya ke jin gina kalmar rashin so a gare shi. Ya sunkuyar da kan shi sai kuma ya ɗago fuskarsa ba yabo ba fassala ya ce "Babu laifi, ki turo shi ina neman shi ok?" Nan da nan murmushi ya mamaye fuskarta tana ƙoƙarin shigewa jikinsa tare da yi masa godiya kamar yadda ta saba ya yi saurin miƙewa.
"Na gode sosai Abbiey ubana maganin kukana thank you" Bai ce komai ba ya fice daga ɗakin sai ya ji kanon ta yi masa zafi sosai da sosai yana son samun kaɗai ta baya son a fahimci rauninsa ko kaɗan gashi gab yake da bayyana.
Cikin farin ciki Ridayya ta kira Zameer lokacin yana kwance a ɗan ƙaramin shagon sa suke kwana su wajan goma, banda tsami da warin kayan Almajirai babu abinda shagon ke yi ga allo kala-kala da rubar bara ta almajirai. Wayarsa mai ƙirar Vivo ta fara ƙara ya duba yaga an saka "My target" Tsaki ya yi a fili domin baya son yadda take takura shi da kira sosai idan ya tuna target ɗinsa da plan ɗin da yake da shi a kan ta sai ya daure. "Hi baby"
"Abbiey ya amince ya ce ka zo yana son ganinka" Zameer ya ɗan taɓe baki a fili kuma ya sauke wani irin numfashi ta cikin wayar murya can ƙasa ya ce "Wow har na fara hango kai na matsayin mijin My pretty babyna" Ta yi murmushin ta mai sauti ba tare da ta ce komai ba. Ya ce
"Yanzu bana ƙasar Daddy ya aike ni zuwa Switzerland a nan zan haɗo miki lefe ma, kuma gidanmu ana ta gyara ne" Kai tsaye ya ce Switzerland ɗin ba tare da ya san wacce ƙasa ce ba, kawai da ya yi searching na best country in the world sai suka nuna masa Switzerland ɗin matsayin ƙasar da ta fi ko wacce shi ya sa ya faɗa mata.
"Oh Allah ya dawo da kai lafiya" Ya ce "Cewa za ki Allah ya dawo mini da mijina lafiya, ki daina jin kunyata fa" Ta yi murmushi kan ta a ƙasa ta ce "To na ce"
"Ridayya"
"Na'am" Ya yi jim sai ya ce "Me ya sa mutane basu da uzuri ne? Suna manta Ubangiji ke yin halittar bawa a yadda ya so, bana jin daɗin yadda friends ɗina ke nuna mini wai bai dace na aure ki ba" A rikice ta ce "To saboda me?" Ya ce "Saboda yanayin halittarki wai muninki ya yi yawa, nikam cin uban shegu nake ai basu san daraja da alfanun baƙar mace ba wlh, kuma ina ce musu you're the first person da kika nuna kina so na kuma na yi supporting tare da accepted naki a yadda kike"
Jikinta ya yi sanyi kar a raba ta da wanda take ganin tuni ya zama miji gare ta, tana tabbacin idan ta rasa Zameer to babu wani namiji da zai ƙara ce mata hello ko da wasa balle