Showing 156001 words to 159000 words out of 190738 words
Chapter 53 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt
Yanzu ba wata damuwa"
"Sure Prof "
"Baka buƙatar kuɗi? New car, kayan sawa abubuwa dai"
"Kawai ka bani soyayyarka da addu'ar ka ka taimaka mini na samu Ridayya shi ne kawai abinda nake buƙata ka san ai ina da kuɗi ni fa ba lusari bane da komai sai iyaye sun mini now I'm going back to my business"
Hira sukai sosai Mother ta ji daɗi a lokacin tana buƙatar mijinta ta shirya tarɓarsa amma ana kiransa a waya jiki na rawa ya fice ya ce meeting ya tashi na gaggawa a jam'iyya.
Baba ƙarami ya dinga neman MB USTAZ a line ɗinsa na JAPAN amma baya samu hatta number da Ridayya ta kira Mami ba a samu suka rasa ta inda za su ɓulluwa lamarin. Akai suna jaririn Mami ya ci sunan Baffa Mansur ana ce masa Junior shagali akai wanda ba a taɓa yi ba, Mami ta dinga shiga tana fita Baffa ya yi bajinta sosai har kuka Mami ta yi Ammi ta ja ta yi gum plan ɗinta kawai take so ya cika a kan Zainura.
Watannin MB USTAZ ciff a Nigeria ana kamfel amma bai taɓa zuwa ba, ƴan jam'iyya da wanda aka fitar matsayin mataimakin Gwamnan jihar Kwamred Muhammadu Hassan da sakataren jam'iyyar Dr Gali Uba suke yin komai na kamfal ɗin, suna zagawa local government zuwa local government da ƙauyuka bisa mamaki an karɓi buƙatar su, dukda suna samun barazanar wai jam'iyya sabuwa ce inec bata san da zamanta ba.
Tajj tsaye yake ana masa tambayoyin ƙare dangi, MB USTAZ ta cikin Camera ya hango Tajj Baita ya danna wani layi ana ɗauka ya yi shiru ya dinga tunanin me zai ce ya jima kafin ya ja numfashi a takaice ya ce
"Allow him to come"
Ajjiyar telephone line ɗin ya yi yana zaune hakimce cikin wata dakakkiyar shadda fara tas jamper da babbar riga ya ƙara yin wani fresh ya yi ƙiba da wani irin haske da kumatu kamalarsa ta sake bayyana.
Yana jin Tajj na mitar kamar shi sai an tsare shi amma ya yi masa banza yana duba jarida wayarsa ce ta yi haske yaga message ne daga Ridayya ya buɗe short note ne ta ce
"I need you, i miss you, i love you Abbiey"
Wani kwantaccen murmushi ya yi har sai da dimples ɗinsa suka shige ya ji ita kawai yake son gani ya azabtu kwarai da gaske da rashinta reply ya yi mata da
“take a kiss Mu'ahhh"
Tajj Baita leƙawa ya fara ya ji an kai masa duka ya goce"zan watsa maka yatsu Tajjudeen Baita za ka ci gidanku"
"Allah ga Ustaz ka yafe masa"
MB USTAZ murmushi ya yi kawai wato komai ka zama a rayuwa akwai wanda ba za su taɓa girmamaka ba.
"Zameer ya matsa wai bai sami Madam ba, shi ya sa na ce ka sauke layukanka na san Baba ƙarami zai matsa ka dawo,kuma Umma still tana kan bakanta, ni na san Madam ba zata taɓa yin ƙarya ba da iliminta"
Shiru MB USTAZ ya yi idanunsa akan Tajj hakan yasa Tajj fahimtar Ustaz ba zai magana ba.
"Little yana nan cikin lafiya, babu inda ya barka shi kuma ana yin magana zai runtse idanu ya ce Assatagafirulla!"
Nan ma Ustaz bai magana ba can dai idanunsa lumshe ya ce
"Zaka iya tafiya ka saka idanu akan Mardiyya ok?"
"In sha Allah "
A lokacin ya nemi airplane zuwa JAPAN. Domin tuni ya samawa Ridayya makaranta ta fara zuwa a ɓangaren medicine kuma ta mayar da hankali sosai dole ya tayata cika muradanta idan lokacin komawa gida ya yi za su koma ne.
Shigar tsakiyar dare ya yi saboda ƴan jarida tafiyarsa a sirri take. Cikin bacci ta ji yanayinta ya sauya ga gamshi sosai dake ratsa hancinta ta buɗe idanu da kyar ta ganta kwance a ƙirjinsa ya rungume ta sosai numfashinsa na sauka a hankali alamar ya gaji wata uku kamar shekara uku Ridayya ta ji Abbiey ya sauya mata sosai ya ƙara mata kwarjini.
Ta kunna fitila tare da tsora masa idanu a hankali ta zura hannunta a sumarsa mai laushi ya ta nutsa taga da gaske bacci yake a nutse cike da tsoro ta sumbace shi ta ce “I love you Abbieyna”
“Love u too habib Albi”
Ta zare idanu tana ƙoƙarin matsawa ya riƙe ƙugunta da hannu ɗaya yana shagwaɓe fuska wacce ita kawai ke ganin baɗininsa ya ce
"I need more" ya nuna lips ɗinsa ya ce "The kisses"
Zameer zube gaban su Baba ƙarami da Baffa da Junaid ya dinga kuka yana masu bayani ya ce "Ku taimaka mini Ina son matata wallahi Allah na rantse da Allah ban sake ta ba.....
Ku yi sharing saboda sauran ƴan'uwa🥰👏🏻
*MUNAFIKIN MIJI 42*
Bright pens free batch
Nimcyluv
"Innalillahi baka sake ta ba ka ce fa ɗan nan?" Zameer ya girgiza kai idanunsa cike da hawaye ya ce "Da gaske nake Baffa ni ban saki matata ba, guduwa kawai ta yi ta bar ni babu inda ban nemeta ba har gidan rediyo" ba iya Baffa ba hatta Junaid da yake zaune maganar Zameer ta jijjiga shi.
"Kenan Ridayya aure ta yi akan aure?" Baffa ya miƙe tsaye ya shiga zirga-zirga a tsakiyar parlorn can ya juya ya ce
"Na kasa yin tunanin komai akan wannan al'amarin,abu kamar a wasan kwaikwayo da labaran hausa na tatsuniya?"
"Alhaji Mansur zo ka zauna" Baba ƙarami ya kira sunan Baffa yana nuna masa wajan zama domin ya lura gabaɗaya hankalinsa a tashe yake tsoro da firgici sun shige shi sosai ainun da gaske.
Junaid ya kalli Zameer yadda yake ta share hawaye tunda yake ko ada can baya bai taɓa ganin ladabi da tsantsar tsoro a fuskar Zameer ɗin ba sai yau bai kuma taɓa ganin hawaye akan fuskarsa ba, rashin yadda ya gitta a zuciyar Junaid ya ce
"Idan baka saki Ridayya ba, to akwai wani abu a ƙasa tunda da can bata taɓa yunƙurin fitowa daga gidanta ba, ta dawo gida a saboda ka saɓa mata ba, balle a yanzu da take tunanin bata da kowa tunda Ridayya ta dawo ne kafin ta san cewa muna raye. Me ka yi mata? Me kaiwa Ridayya da har ta baro inda kake ta gudu? Me ya sa baka biyo bayanta ba sai yanzu?"
Da wani kalar shock Zameer ke kallon Junaid da kuma sauraren shi, ganin yadda zai rutsa shi ya saka ƙaryar shi ƙarewa Zameer ya ce
"Yaa Junaid ai kasan ba zan yi ƙarya ba, go and ask her ta san komai she knows everything wallahi tallahi"
"Da mamaki wannan lamarin, ba a rabu da Bukar ba an haifi Babu, wacce irin ƙaddarar ke bibiyar rayuwar Ridayya" Cikin fusata Junaid ya ce "Karku yadda da shi, domin tun farko shi ɗin ba abin yadda bane ina da tabbacin Ridayya bata taɓa cutar da kai ba, balle ta aikata wannan babban lamarin"
"Ya isa Junaid please"
Zameer ya sake sauke kansa ƙasa cike da ladabi kamar zai yi sujjada muryarsa a raunace ya ce "Ita ta ce na taɓa cutar da ita? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Lallai a bar mace da kaidinta amma ni ba zan ce komai ba, idan kana ganin ta dinga yawo da aurena a kanta shi ne daidai to babu damuwa I'll let her be tunda kana ɗaurewa ƙanwar gindi"
Junaid ya kalli Zameer cike da ɓacin rai yana tuna abubuwan da suka shiga tsakaninsa da Yaa Bilal musamman a cikin asibiti a kan Zameer Ridayya ta yi wa Ustaz Allah ya isa kuma ta kira shi da sunan da ko a family shakkar kiransa ake da shi. Idan Junaid ya tuna ranar sai ya ƙara jinjinawa Ustaz na irin so da ƙaunar da ya kewa Ridayya.
Baba ƙarami ya yi murmushi irin na manya mutum mai tunani da girmama zumuncin Allah da bawa kowa haƙƙinsa ya ce "Ɗana Zameer kana ina Ridayya ta gudu garin yaya hakan ta kasance ka yi wannan sakacin?"
"Abba muna nan Garin Kano ba sakaci na yi ba cikin dare ta gudu wai ta gaji da zama dani saboda kuskuren dana tafka a rayuwa, na mata laifi ni ɗin mai kaifi ne Abba amma girman laifin bai ka ga Ridayya ta gudun daga cikin gidanta na sunna ba kuma tare ɗana. Abba kai mai fahimta nasan zaka fahimce ni"
Zameer sam bai kula da Tajj daya shigo ya zauna ba, yana sanye da black suit irin ta manyan ƴan sanda sai baza ƙamshi yake idanun Tajjudeen Baita zube akan Zameer shi ma yana sauraren shi. Tajj zai magana da hannu Baffa ya yi masa alama da ya yi shiru.
"Karka wani damu ɗana ka ɗauka ni ɗin tamkar uba mahaifine a gare ka zan saurareka kamar yadda zan saurari ɗan dana haifa kuma na maka alƙawarin wallahi wallahi wallahi uku kenan idan har kai ne da gaskiya to zan dawo maka da Ridayya cikin gidanka da yaronka matsayin matarka"
Da sauri Baffa da Junaid da Tajj suka kalli Baba ƙarami da yake ta murmushi, firit Umma t fito daga laɓewar da ta yi ta ce "Kai Allahamdulillahi idan hakan ta faru zan fi kowa murna da samun nutsuwa a zuciya, Babban mutum ya rabu da kwallon mangoro ya huta da ƙuda har abada. Na daɗe ban ji tsanar da na yi wa mutum irin ta matsiyaciyar ƴar nan Ridayya ba, ba zan taɓa ganin farinta ba wallahi mummunan mai baƙar zuciya mai kama da Alade kawai"
Baffa har ƙasan zuciyarsa yake jin zafin maganganun Umma amma babu yadda ya iya matar yayarsa ce dole ya zuba mata idanu. Mami data fito hannunta ɗauke da Junior ta tsaya cak saboda furucin Hajiya Hadiza karamcin Ustaz ya shige ta faɗawa babarsa magana wallahi Anty Kaltum ta ji maganar itama niyyar tafiya ta yi amma kawai ta juya cikin ɗakin Mamai ta yi alwala tare da gabatar da sallar asar.
Baba ƙarami bai kula Umma ya dubi Zameer ya ce "Wanne laifi ka yi wa Ridayya da kake neman yafiya?"
"Abba i was wrong i was totally wrong ban san da wanne harshe zan maka bayani ba komai zan ce komai zan furta ba lallai na ƙara fari a idanun Ridayya ba"
"Tunda you are already knew dat why are wasting your time here? Me ya sa za ka zo nan ne ma?"
Da ƙarfi Baba ƙarami ya ce "Abubakar Sadeeq!"
"I am sorry Abba"
"Ina jinka Zameer"
Zameer ya sassauta murya ya ce "Abba farkon fara haɗuwata da Ridayya a makaranta ne, na sameta tana ƙoƙarin kashe kanta ta hanyar rataya a ƙarƙashin bishiya, Allah ya kawo ni wajan domin na ceci rayuwarta Abba just to save her life. Ban tambayi Ridayya komai ba amma sai ta fashe da kuka ta fara zayyana mini halin da take ciki, ta ce mini mahaifinta ya tsaneta haka mahaifiyarta kowa na gidan baya sonta ƴan unguwa da ƙawaye haka a makaranta kowa na aibata halittar da Ubangiji ya yi mata sannan ta ƙara da cewa...,"
Ya yi shiru kansa a ƙasa yana girgiza kai ya kasa cewa komai. Baba ƙarami ya ce "Go on my dear ina jinka ka faɗa mini komai tsakaninka da Allah"
Hawayen da yake ta rikewa ne ya sake gangaro masa ya ce "Abba ka yi mini uzuri abar maganar domin zata iya rusa wannan zumuncin naku magana ce da zata iya sawa zuciyar kowa ta buga daga ciki kowa har kai Abba ko kuma Abban Ridayya just let bygones be bygones Abba"
Baba ƙarami ya miƙe tsaye ya ce "Ya zama dole ka ƙarasa faɗar abinda ka yi niyya ba a mini haka ba zaka fara mini ba kuma"
"To Abba ya zaka ji idan na shaida maka cewa Ridayya ta faɗa mini saboda ɗan'uwanta Ustaz wanda ya zama kamar uba a gare ta take son kashe kanta? Ya zaka ji idan na faɗa maka cewa sanda Ridayya ta je gidana ta je da shigar cikin da Ustaz ya yi mata? Ta shaida mini tun tana yarinya yake lalata rayuwarta kuma ya yi mata barazana da faɗin muddin ta faɗawa wani sai ya yankata da wuƙa? Me ya sa ba ku taɓa tunanin ƙin auren shi da ta yi a fari ba? Me ya sa ta zaɓe ni ta barsa? Abba da farko bani na fara cewa ina son Ridayya ita ce ta buƙaci hakan ni kuma na tausaya mata a haka har na fara son ta, Abba laifina a nan shi ne na ɓoyewa Ridayya gaskiyar waye ni maimakon Zameer sunana Giɗaɗo ɗan asalin Garin Katsina can ƙauyen Nahutu yankin batsari na zo Kano Almajiranci ne, ban yi haka don na cutar da mai so na Ridayya ba, na yi ne saboda kar na rasa ta na yi ne saboda na rufa mata asirin da ɗan'uwanta yake ƙoƙarin tuna mata na yi kuma da tunanin idan kun ganni talaka zaku hanani auren Ridayya, bayan ta gano gaskiyar dana ɓoye mata shi ne ta ce dole sai na rabu da ita"
Tunda ya fara maganar tasa Baba ƙarami zufa ke yanko masa jikinsa ya ɗauki rawa dukda cewa a zaune yake amma ƙoƙarin faɗuwa yake wani abu mai kama da tashin hankali da fashewar bom ya ji a zuciyarsa da gangar jikinsa kansa ya fara juyawa maganar Ridayya ta yi aure da cikin da Ustaz ya mata ita kaɗai ke gigita masa lissafi da ƙoƙarin saka zuciyarsa bugawa.
Ya kama hannun Zameer ya damƙe idanunsa na fitar da ƙwalla ya ce "Yaro ka ji tsoron Allah ka tuna zaka mutu da gaske ne abinda kake furtawa akan Bilalu ɗana? Babban mutum fa? Ka ji tsoron Allah karka goga masa baƙin fentin da ba zai iya shafewa daga jikinsa ba, ko ka yi ne don matarka ta dawo gare ka?"
"Haba Abba haba Abba ina dalilin wannan furucin naka? Mene ribata idan na wulaƙanta mutum kamar Muhammad Bilal? Gaskiya ɗaya ce kuma ita na faɗa"
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Hasbunallahu wani'imal wakil Muhammad Bilal? Babban mutum Allah ya...."
"A'a yaya don Allah, don't say that karka ce haka"
"Me kake so na ce Alhaji Mansur? Ɗana na cikina ya wulaƙanta ƴarka tun tana ƙanƙanuwa? Ta ina zumuncin Allah zai bar ni? Wannan shi ne dalilin daya saka ya ƙiyin aure? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un" nan da nan Baba ƙarami ya gigice ya riƙe ƙirjinsa hankalin Junaid dana Tajj Baita ya yi mummunan tashi wacce lukutar masifa ce wannan? Anya Muhammad Bilal zai aikata haka? Mene gaskiyar lamari? Only God knows! Likita aka fara ƙoƙarin kira Baba ƙarami yana cewa a bar shi haka nan
"Idan har maganar nan gaskiya ce wacce Zameer ya faɗa wallahi Allah sai na ɗauki hukunci sai na ɗaukarwa Ridayya fansa wallahi sai na ɗaure Muhammad Bilal da hannuna"
Da sauri Zameer ya ce "Ai gaskiya ce ma Abba kaɗan kenan daga abubuwan da suka dinga faruwa" wani irin hawayen baƙin ciki dana tsanar Ustaz Baba ƙarami ya dinga zubarwa deep down na zuciyarsa yana ƙoƙarin ƙaryata lamarin. "Kai out of this house before i count 1"
Junaid ya cewa Zameer miƙewa ya yi with confidence ya bar parlorn ya yi waje a zuciyarsa yana jin cewa wannan shi kaɗai damar da yake da ita wajan sawa Ridayya ta dawo inuwar aurensa yana jin wani iri idan ya tuna ta, he feel very comfortable without her, her love,her voice, her.... He miss everything about her more especially her soft skin ga kullum lips ɗinta dake masa barazana ga Black skin ɗinta sai ya ji gabaɗaya baya son farar mace baƙar matarsa kawai yake da interested akan ta wannan shi ake kira da LOVE!
"Good job Zameer ka yi abu cikin sauƙi u are smarter than everyone! Smart smarter smartest u are so lucky ka yi komai muddin Ridayya zata dawo kanka, ka so kanka fiye da kowa karka zama mai yadda da faɗuwa da karaya akan abu" Murmushi ya yi yana shafa samar kansa da lumshe idanunsa he is more than okay gani yake dawowar Ridayya ya zama dole ne. Tafiya ya fara yana barin entrance ɗin gidan.
Sosai Tajj Baita ya shiga tashin hankali fitar maganar nan waje yana nufin komai zai taɓa career MB USTAZ zai taɓa takararsa da jam'iyyar da yake ciki musamman ƴan jarida da ƴan media suka samu labari.
"Abba calm down please jikinka na girma ne kai hakan ya haifar maka da hawan jini ka ciwon ɓarin zuciya ka kwantar da hankali abi komai a sannu don Allah"
"Tajjudeen kasan zafi da raɗaɗin da nake ji a zuciyata? Idan na rufawa ɗana asiri Ubangiji zai yafe masa wannan zunubin ne?"
"Abba ba kyau karka yanke hukunci akan abun da babu tabbas ba evidence mu fara bincike.....,"
"Kai Tajjudeen! Na san ka san inda zaka samu Muhammad Bilal ka faɗa masa idan har ni na yafe shi ina buƙatar ganinsa nan sa kwana biyu" kana ganin Baba ƙarami kasan he's out of his sense he lost ciwo kawai zuciyarsa ke masa. Junaid ya ya jugum shi kansa kan nasa hayaƙi yake yana buƙatar ruwan sanyi. Tajj Baita ya ce
"Abba ina zanga His Excellency yanzu?"
Wani kallo da Baba ƙarami ya yi wa Tajj ya sanya shi yin shiru tare da yin waje a ransa yana jin dole zai saka a kama Zameer bayan election a sake shi sannan komai ya yi daidai samun nasara ko faɗuwa.
Yanke jiki Baba ƙarami ya yi ya faɗi Baffa da Junaid da Abubakar suka rufu a kan shi nan da nan aka ƙara kiran Dr gabaɗaya matan gidan basu san wainar da ake tuyawa ba hakan kuma ya yi wa Baffa daɗi a rai.
Japan
Dawowarta daga makaranta kenan saboda karatu ya ɗauki zafi shirye-shiryen exam suke ta first semester zangon karatu na farko a jerin sabbin ɗaliban da jam'iyyar Japan ta ɗauka a Kyoto University. Kyoto University is a Japanese national university that was founded in 1897. Ta ƙara samun gogewa da ilimin zaman rayuwa musamman data haɗu da mutane kala daban-daban kuma ƙabila daban-daban ta samu rangwamen tsana daga idanun mutane wasu kuma saboda baƙinta ya yi yawa sai su dunga guduwa tamkar zata shafa musu baƙin zunubi hakan baya damunta a yanzu tana da confidence na fuskantar ko wacce matsala da zata ƙalubalanceta ta samu ƙarfin zuciya da abinda ake kira Self-confidence ga mijinta wanda baya gazawa he is always supports her akan dukkan lamuranta yana nuna mata ita ma mutum ce kamar kowa tana da ikon yin dukkan abinda take so wanda bai saɓawa addinin Muslunci ba.
Zamanta da mijinta