Showing 168001 words to 171000 words out of 190738 words

Chapter 57 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17289

data auri Sadauki ta haɗa biyu shi da Abbiey amma bata da wannan ikon. Tari ya fara da ƙarfi jini ya fara zuba hanci da baki yana ƙoƙarin miƙa hannu ya taɓa ta, da ƙyar ya ce "I will die for your love Ridayya Ubangiji shi ne shaida, stay with me please hold my hands ko sau ɗaya" Girgiza kai ta yi ta ce "I can't i can't Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun na shiga uku wai meke damuna mene ya yi coursing problems ɗin nan a rayuwata why all this happens to me, forgive me please Sadauki a gigice ta yunƙuru tana nufar kansa ganin idanunsa ya yi sama zuciyarsa ta daina bugawa ta fasa ihu ta ce "Karka ka mutu Sadauki don Allah karka mutu i love you....." Ta girgiza shi ta taɓa zuciyarsa bata bugawa ta taɓa agogon hannunsa baya harbawa wani irin ihu ta yi ta ta ce "Nooooo karka mini haka Sadauki don't leave me




Daga yau in sha Allah kullum za a dinga yi har a kammala babu jira kuma kafin sallah mu idda ai alamu ya nuna ma...


A yi comments a yi sharing
08164069385
*MUNAFUKIN MIJI*


Nimcyluv......
45


*Masu arewabooks ku yi following account ɗina domin samun duka books ɗin 👇🏻*
https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv






Ba ƙaramin gigicewa Ridayya ta yi ba ganin gawar Sadauki a gabanta, a ƙasar da babu kowa nasa ba uwa ba uba, ba ƴan'uwa hatta ita kanta bata da kowa wanda ya shige Ustaz gashi kuma yabar ƙasar ya koma Naija? Ta rasa mafita sai kuka take tana girgiza shi ta fita hayyacinta sosai gani take tamkar ita ce silar mutuwar Sadauki "Don Allah ka tashi karka zama ragu a soyayya shin ba ka ji sunanka bane Sadauki? Ya zan yi dakai a ƙasar da bamu da kowa ka farka don Allah na san suma ka yi soyayyata ba zata taɓa zama ajalinka ba..." Sosai take kuka ga wani abu daya tukare mata a ƙirji. A kusan tare wasu manyan motoci guda biyu sukai parking a gefen Ridayya da kuma Sadauki dake kwance baya ko motsi, ta cire idanunta gabanta ya faɗi ganin bata gane mota ko ɗaya ba, a hankali aka buɗe motar farko wacce ta kasance ash wani matashi ne wanda zai iya girman Sadauki ya fito daga motar, fuskarsa sosai ta nuna tashin hankali ya ƙarasu wajan yana kallon Ridayya da Sadauki kafin ya ce


"Me ya sa ya kwanta a ƙasa what happened to him?" Ridayya ta kasa cewa komai idanunta duk ya jime saboda fargaba Riyad ya nisa ya ce "Kece Ridayya? Naga lafiya ya fito ya ce wajanki zai zo, daman hankalina bai kwanta ba tunda kwana ya yi jiya bai runtsa ba, ya kira number Mother sun yi magana, ya kira mahaifinsa kuma more than 30 miss calls bai ɗauka ba, don Allah ki sassauta kukan ki mini bayanin abinda ya faru in briefly" da ƙyar ta ce "Ka fara duba nunfashinsa ka ji ko yana raye" sai a lokacin Riday ya lura da rashin bugawar zuciyar Sadauki ya nufe shi kasancewar shi Dr ya fara duba shi hankali tashe.


Tsaye ya yi a kanta tun bayan fitowar shi daga motar, hankalinsa ya ji yaƙi kwanciya har ya je airport kawai ya saka aka dawo da shi, sai dai bai yi tsammanin ganin abinda yake gani ba, ya shanye damuwar dake ƙoƙarin bayyana a fuskarsa ya ce "Ridha.." jin muryarsa ya saka ta miƙe har tana ƙokarin faɗuwa ya yi saurin taro ta gefensa tana ganinta kusa da shi ta faɗa jikinsa ta fashe da kuka sosai "Abbiey na shiga uku na shiga uku Abbiey na kashe Sadauki" Ustaz ya kasa cewa komai sai bayanta da yake bubbugawa a hankali alamar rashin, deep down na zuciyarsa addu'a yake ta yi ga Ubangiji ya tashi kafaɗun Sadauki sosai al'amarin ya shige shi ya kasa furta komai Dr Riyad ya goge zufa ya ce "Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, Allah gare ka muke kuma gare ka zamu koma Ubangiji ya sanya can tafi nan sannu da aikin bauta Hamza Allah ya yafe maka" kalaman shi suka daki Ridayya da Abbiey ta ƙara rikicewa ta riƙe Ustaz da kyau shi ma ɗin riƙe ta ya yi gudun kar a yi biyu babu. Abbiey wayarsa ya ciro ya kira number gidansa wacce ta sada shi da Maid Ilhas, magana ya yi a gajarce kana ya kashe kiran. Hannun Ridayya ya kama zuwa mota ya yi wa Dr Riyad alamar ya jira shi a nan wajan, rarrashin Ridayya ya fara cikin kulawa da soyayya dukda kasancewar jinta a jikin Ustaz yana yaye mata abubuwa da yawa amma yanzu ta gagara nutsuwa gani take idan Sadauki ya mutu tamkar ita ta kashe shi. Addu'a ya shiga yi tana maimaitawa suna a haka mota ta sauke Ilhas ya fito ta yi saurin cewa "Good day sir!" Ya jinjina kai yana ɗauke idanunta can ya ce "Ki kula da ita, ku kasance tare ok"


"Yadda ka ce in sha Allah" motar ta shiga driver ya ja su zuwa gida shi kuma kai tsaye ya nufi wajan Dr Riyad ya ce "Me kake son cewa? Who are you?"


"Sadauki's friends" Dr Riyad said yana goge hawaye ya ɗora da "Allah ya yi masa cikawa kuma ina da tabbacin bugawar zuciya ce na farat ɗaya amma zamu je asibiti na ƙara bincikawa" MB USTAZ ya ja numfashi ya fesar "No need, zamu shige Nigeria yanzu" daga nan ya fara neman number wayar Tajj Baita gabaɗaya bai san yadda iyayen Sadauki da shi kansa Tajj za su fahimci wannan al'amarin ba. Kasancewar abu ne na manya ya sanya cikin awa guda suka samu jirgin da zai ɗaga dasu, da BM USTAZ da Dr Riyad sai gawar Sadauki daman tuni ya yi waya da Tajj ya masa bayanin komai kasancewar Abbiey bai iya ƙarya ko ɓoye magana ba, yana da zurfin ciki amma ba a komai ba.


Hajja Azizat na zaune ta yi zuru tana sauraren yayarta mahaifiyar Tajj tace "Yaya ban san meke damuna ba, kawai na ji bari na kira ki ko zan ji sanyi a raina, gabana faɗuwa yake sosai wallahi, gidan ya mini girma idan na kira Professor bana samun shi sama da sati ina son na faɗa masa al'amarin Sadauki" daga can ɓangaren Mahmah ta ce "Hajja Azizat ki yi haƙuri komai zai zama tarihi in sha Allah, yaushe Sadaukin zai dawo I'll talk to him zan masa bayanin yadda zai gane ya fahimta ya kuma yi tawakkali" Mother ta sauke ajjiyar zuciya tare da goge hawayen idanunta ta ce "Nothing goes well Yaya, Sadauki yana da ƙulafuci, kafin ya fita sai da ya bi mahaifinsa office domin ya ji matsalarsa da rashin son zama cikin iyalansa, lafiya ya fita amma daya dawo ban gane kansa ba, ya dinga ce mini na yi haƙuri da rayuwa da amshi ƙaddara a yadda ta zo mini da Prof da babu duk zan iya rayuwa, kuma karna bari wani abu ya sake shiga tsakanina da Prof, Yaya hankalina ya tashi na rasa gane me Sadauki yake nufi ban san kuma mene ya je ya gani wajan mahaifin nasa, main reason ya haɗu Ridayya kuma kin san tana da aure, ina guje masa fushin Ubangiji Yaya kuma ina jin tsoron faɗa masa gaskiyar lamarin na gaji na gaji Sadauki shi ɗaya nake da shi, zaman gidan babu daɗi" Sosai Mahmah ta tausayawa Hajja Azizat ƙanwarta cikin rarrashi take ce mata "Azizat kin yi haƙuri komai zai shige kowa da tasa ƙaddarar mumunin mutum Ubangiji baya barinsa haka nan. Ni da kaina zan fahimtar da Sadauki da zarar ya dawo Prof kuma ki masa uzuri ai kince ayyuka sun masa yawa, ga sabgar siyasa banda an ɗaga Elections ɗin da tuni an yi komai mai rabo ya samu, ba ki rasa komai ba"


"Yaya buƙatun ƴa mace ba iya ci da sha da suttura bane, kawai dai abar tunawa zan ta addu'a shi kuma Hamza Allah ya yaye masa son Matar auren, ai masifa ce wannan kuma jarrabwa babba" Mahmah daga nata ɓangaren da take zaune a saman kujera Nadra na kusa da ita tana bacci, ƙoƙarin magana take kamar daga sama taga Tajj ya shigo yanayinsa ya mata daban ta ce


"Ya zaka faɗo mini a gigice kamar kurarre lafiya? Wani abun ne kuma Deen?" Ya kasa magana sai zufa yake sharewa idanunsa sun yi jajur, dukda rashin jituwa da suke da cousin brother ɗin nasa amma sosai yake jin Sadauki a zuciyarsa, ya sha ɗaukar waya da niyyar kiransa just to find out if he is ok, daya tuna rikicin shi sai ya fasa, babban dalili a maza bashi da ɗan'uwa wanda ya shige Hamza, taya zan iya fuskarta Anty ya ce mata Sadauki ya rasu sanadiyyar bugawar zuciyar farat ɗaya, dalilin mace kuma a ƙasar daba ta shi ba? Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun! "Wai lafiya ina magana zai zufa kake ji idanunka kamar zasu shige don tashin hankali"


"Ƙaddara ce ta same mu wacce daman tana kan kowa Mahmah"


"Ƙaddara? Aikin ka rasa ko asarar dukiya ka yi" a rauna ce ya ce "Gwara na rasa aiki da dukkan abinda na mallaka da na rasa abinda na rasa a yanzu Mahmah, iya faɗan da muke da Sadauki ya wadatar dani yanzu dawa zan dinga yi?...," Mahmah ta ji cikinta ya juya gudawa na neman zubo mata ta yi baya kamar zata kifa ta ce "Mene ya samun Sadauki"


"Allah ya amshi abinsa, a inda bashi da kowa sai wani jinin nada ban, mun rasa Sadauki Mahmah Sadauki ya rasu" Salati kawai Mahmah take idan ta kamo wannan sai ta saki ta gigice ta fita hayyacinta lokaci guda, Tajj ya rasa ya zai yi ya ce "A'a Mahmah wannan bai dace da Sadauki ba, addu'ar da kika fara ita za ki ta yi in sha Allah yana cikin aminci zai kasance ɗaya daga cikin samarin Aljanna wanda Ubangiji yake alfahari da su"


Ta share hawayen da yaƙi tsayawa ta ce "Taya zan faɗawa Azizat wannan al'amari? Ya za mu yi?" Tajj ya ce "Faɗa mata ya zama dole, amma nima ba zan iya ba wallahi tsoro kallon idanunta nake na ce Hamza ya rasu" Da ƙyar Mahmah ta iya controlling kanta ta kira Mother tana ɗagawa ta ce "Ki zo gidana yanzu"


"Yaya lafiya?"


"Ki zo na ce"


"Ban tambayi Prof ba Yaya, bari na kira shi idan ya barni sai na zo"


"Ƙarama meke damunki ne? Wacce kalar biyayya ce haka? Kin san girman dalilin daya saka na kira ki? Sai kin tsaya kiran Prof?"


"Yaya you are always telling me cewa Aljannata na ƙarƙashin mijina, biyayya kuma ke bada ita, kin ce mini haƙurin shi ne maganin komai a rayuwa, abinda haƙuri bai baka ba, rashin shi ba zai baka ba, yaya na gino akan wannan kalaman naki. Na tuna keda kan ki kike bani wata kissa lokacin Annabi Muhammad S.W.A kin ce; wata mata mahaifinta ne ko mahaifiyarta babu lafiya, amma taƙi zuwa dubiya saboda mijinta baya gari kuma babu al'amarin waya a zamanin, har daga ƙarshe kika ce an aiko mata cewa mahaifin nata ya rasu, ta yi aike wajan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce mata ta yi haƙuri ta nemi izinin miji, haka ta haƙura ta yi wa mahaifin nata addu'a tana daga gida, a kaiwa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama wahayin cewa wannan matar Ubangiji ya bata Aljanna.... Me ya sa ba za mu yi koyi da mutanen ƙwarai ba, da bana haƙuri ba zan kawo yanzu cikin gidan Prof ba Yaya ki yi haƙuri na nemi izinin shi" A sanyaye Mahmah ta ce


"Okkk"


Ta juya ta kalli Tajj ta ce "Yaushe zasu ƙarasu da gawar?"


"Not too long, don sun jima da tashi bari na faɗawa wanda ya dace" ta jinjina kai ta ɗauki hijabi ta saka ta gyara parlon da za a saka gawar Sadauki. Tajj ya kira Baffa da Baba ƙarami da Junaid duk ya sanar musu, ya kira ƴan'uwansu na kusa da kuma na nesa ya kira abokan mahaifinsa ya saka aka wallafa rasuwar Sadauki a social media da gidajen rediyo. Da kansa ya kira Prof amma bai ɗauka ba ya masa kira sautarin shurin masaƙi but not respond.


Cikin ƙaramin lokaci gidan Murgayi Alhaji Baita ya cika da jama'a ƴan ta'aziyya hatta Mami da Sisters ɗinta suna gidan da kuma Dada, hadda Zainu da little. Daga baya Balisa da Yaya Zuhura suka shigo tare dasu Abdullahi da Khaliperh su Usman har lokacin kuma Hajja Azizat bata ƙarasu ba. Gida ya cika zuwa su BM USTAZ kawai ake jira.


Sama sama ya fara jin news dalilin breaking news da aka fara sanarwa nan take Allah ya yi wa Hamza Sadauki rasuwa ɗa a wajan Professor ɗan takarar ɗan'majalissa ya rasu ne a ƙasar Japan kamar yadda sanarwa ta je musu, za a yi jana'izarsa idan jirgin dake ɗauke da gawarsa ta ƙarasu aka maƙala photon Sadauki da yake tsaye da voyel fari tas ya yi murmushi idanuna na kallon wani direction ɗin daban ba camera ba. A gigice Prof ya yi cilli da wacce ke kusa da shi ya jawo jallabiya ya saka jikinsa sai rawa da ɓari yake yana ƙokarin ɗaukar key ya fita ta riƙe shi ta ce "Malam ina kake ƙoƙarin zuwa ai ha haka mukai alƙawari da kai ba" idanunsa na shigewa ciki ya ce "kina da hankali kowa? Kina jin ana news cewar ɗana gudu ɗaya tal da na mallaka ya rasu maimakon ki mini jaje sai ki kawo mini rubbish?"


"And so what don ɗanka ya rasu? Ba zai taɓa zama ciwon kaina ba" wani irin mari ya sauke mata yana kaiwa bakinta naushi ta fasa ihu ta ce "Wallahi ka yi kaɗan ka dage ni kamar baka san wacece Ladi ƙarin kunama ba, da kuma abinda zan iya yi?" Idanuna rufe ya zare Belt ya shiga lafta mata tana kururuwa itama ta shiga kai masa duka, suka fara dukan juna kamar rayuwa bariki kodayake bambancin kaɗanne ya mata lilis tare da mata jina-jina ya zari wayata da key ya fita. Duk a hanyar ya fara duba miss calls na jama'a babu adadi ya yi mamakin ganin Hajja Azizat ta kira kuma har an ɗaga yaushe to? Bayan ya san yau gabaɗaya bai waya da ita ba? Yaga kiran Tajj dana shugaban jam'iya har kiran yan'uwansa kiran kowa ya share ya kira number Hajja Azizat yana kira ta ɗauka ta ce.


"Thank God, ina kiranka ka yi mini izinin zuwa gidan yaya ta mini kiran gaggawa ban san meke faruwa ba" Wani irin tausayin matarsa ya kama shi, innocent mace ya cutar haka? Har ɗanta ya rasu amma ta kasa fita ji ya yi hawaye ya cika idanunsa wani irin sonta ya ninku a zuciyarsa da ƙyar ya ce "Jeki yanzu Azizat, Allah ya yi miki Albarka"


Tana shirin fita notification na shigowa wayarta dake gidan nasu akwai Wi-fi bata tsaya duba pictures ɗin da aka turo mata ba da sabuwar number a WhatsApps ta shiga mota, da kanta take driving tunani fal zuciyarta hannunta kuma sai rawa yake. zuwanta da yin parking ɗin motarta ya yi daidai da shigowar motar Ambulance ta tsaya tana kallon ikon, akan idanunta aka fito da gawa rufe da farin yadi a kan wani gado, can taga Dr Riyad ta gane shi sarai babu jimawa wani magidancin mutum ya fito fari tas dashi farinsa ya shige misali ko'ina na fatarsa lub yake da gargasa fuskarsa rufe da mask ya saka baƙin glasses a idanunsa, da kansa ya ja gawar Sadauki zuwa cikin gidan Mother ta bi bayansa da kallo ta kasa tunain komai da ƙyar ta ja ƙafarta zuwa cikin gidan, tana shiga parlo ya ruɗe da koke koken jama'a ta dinga bin kowa da idanu sai kawai ta shiga cikin bedroom ɗin Mahmah ta kwanta Mahmah da Tajj suka biyo bayanta nasiha sosai sukai mata can ta ce "Me ya faru ne?"


"Allah ya amshi Sadauki, Ubangiji ya amsa ran Sadauki ya rasu"


Mother ta rasa gane waye Sadauki wacce kalar mutuwa kuma "Sadauki? Wanne Sadauki?"


"Hamza Sadauki ɗanki Azizat"


"Kamar bani da ɗa mai suna Sadauki Yaya, wanne Sadauki yaya take nufi Deen?"


Tajj ya ce "Ki yi haƙuri don Allah Anty Sadauki dai ɗanki ɗaya tal ke da Prof"


Ta jinjina kai a hankali ta yi baya ta ce "Allah ya jiƙan shi ya yi masa rahama" daga haka bata kuma cewa komai ba, ta juya baya tare da kwanciya saman gadon babu hawaye ko tashin hankali a tattare da ita amma zuciyarta cak take kwakwalwarta nata processing tuna waye Sadauki? Mene haɗin ta da shi nata sadauki dai baya ƙasar gabaɗaya ai.


Haka al'amarin Ubangiji yake komai da lokacin shi, haka kuma mai rai dole ya ɗanɗani ɗaci mutuwa. Har akai arba'in ɗin Sadauki babu wanda ya ji kukan Hajiya Azizat ta kaɗaice daga cikin jama'a bata son kowa ya raɓe ta. Sau ɗaya suka ji ta fasa ihu a gigice Tajj ya shiga ɗakin ya ganta tana fisge-fisge ta fita hayyacinta idanunta rufe jikinta na rawa Tajj ya ƙarasa wajanta tuni ta doka wayarta da ƙasa wayar ta fashe ta yi fari baka ganin komai, kokawa suke sosai da Tajj da ƙyar ya rungume ta a jikinsa yana hawaye tare da kiran sunan Allah ya fara mata addu'a yana tofa mata, Mahmah ta yi tsaye ta kasa cewa komai makamin yadda Hajja Azizat bata ƙaunar Prof ya zo kusa da ita take, ko ta'aziyyarsa taƙi amsawa ta tambayi dalili ta ce "Me zata cewa wanda ya kashe kiran yaro?" Tun daga lokacin bata kuma cewa komai ba sai sanda ta yi ihun a hankali ta sauke numfashi jikinta ya saki a jikin Tajj ta riƙe shi da kyau kuma. Gabaɗaya sun rasa meke damunta mai kuma ta gani? Suka kira Malami ya fara mata rubutun don gana amma abu ya ci tura.


Umma ta kalli Mardiyya da duk ta yi wani zuru-zuru sai ciki a gaba ta dire mata kuɗi ta ce "My daughter gashi 200k ne ki ƙaro abinda kike so na fitar suna, tunda haihuwa ta zo gab gamu cikin watan haihuwar edd kawai muke jira" Mardiyya ta kalli kuɗin ta ce "Ok thanks"


Ta ce a yatsune kafin ta ce "Hadda Ustaz a masu zuwa ta'aziyyar Sadauki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login