Showing 180001 words to 183000 words out of 190738 words

Chapter 61 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17314

shigo bakinsa ɗauke da sallama ta amsa ya nemi waje ya zauna ta ce "Yanzu nake kiranka"


Ya ɗaga kai ya kalleta sai kuma ya ce "Ina kusa ai" a hankali ya ce "Barka da hutawa"


"Yawwa. Amma na faɗa maka Mardiyya ta haihu ko? Tana hakƙi a kanka fa babban mutum, ashe daman baka shiga ba balle kaga yarinyar data haifa" shi dai ya yi shiru yana kallon ta idanunsa tuni suka shige ciki Gambo ta ɗauka ta miƙa masa ta ce "Tun ɗazo yake kuka ko abinci yake so"


Ya miƙe ya amshi Sadauki ya rungume shi, sosai yake da rigima kuma ya fi son a ɗauke shi ko irin kwanciyar jarirai bai so, saɓanin ƴan'uwan shi sam baya son haske yana buɗe idanu yake rufewa ɗan duhun daya gani a jikin Ustaz ya saka buɗe idanu yana gurun-gurun da baki.


"Bari na je"


"Yawwa sai ka yi wa yarinyar huɗuba" sai da ya je bakin ƙofa ya tsaya ya ce.


"Zani saboda je da kuma kasancewar ta matsayin matata, amma bani ne uban yarinyar ba" yana faɗin hakan ya fice Umma ta ji kamar Hausa kamar ba Hausa ba ta dinga maimaita furucin nasa a zuciya da fili.


Mardiyya na zaune bayan ta yi wanka ta shirya ta murza ɗauri tayi kyau ƙwarai abinta sai ƙamshi take wani irin daɗi take ji za ta yi tuzali da mijinta tana jin abinda Inna ke cewa ta ce "Ai kin san tun ina yarinya ba wani kirki ne dani ba, zuwa na yi fa nai mata tas ta dinga kuka tana bani haƙuri idan na yi shiru da baki aka wulaƙanta ki ai ban ma uwarki adalci ba"


Murmushi Mardiyya ta yi ta ce "kin yi maganinta ai yanzu"


"Amma naga wani kyakkyawan jariri a hannunta tubarakallah wallahi aka haɗa jaririn da wannan ƴar taki to cewa za a yi ba mutum kika haifa ba, to daman na ji ƙishin ƙishin wai mijin naki ya dawo tare da matarsa kuma ita ta haifa masa wannan yaran" Inna ta ce tana ƙifta idanu sai kallon ƙofa take. Diyya ji ta yi cikinta ya zuciya abu ya tukare mata a ƙirji idanunta ya yi jajur sai nishi take yi ta ce "Anya Inna daidai kika jiyo?"


Inna ta ce "Habawa ji ne dani kamar maciji wallahi haka akai kuma yara uku aka haifa duka farare idan haka ya tabbata kinga wancan ita ce da gida tunda maza uku ba wasa bane, ki dai kwantar da hankalinki kar jininki ya yi hawa 200 wallahi, kwana nawa ne ya yi miki wani cikin tunda naga baiwarsa kenan"


Hawaye ya cika idanun Mardiyya bawai tabbatarwa ta yi ba, kawai tana tunanin yadda zata iya haɗa Ustaz da wata ƴar macen. Tuna tana tunanin zuwan shi har ta fidda rai kuma Umma bata shigo ba, Balkisa kawai ta shigo sai Baba ƙarami da ya yi mata sannu.


Washegari duka suna Main parlor hadda Ridayya da ta yi wanka cikin wani dakakken lace ta yi masifar kyau, tai fresh sosai sai murmushi take tana kallon Little Bilal da suke ta faɗa da Zainura tana cewa "Ba za ka yi mini zaman ɗakin ba, tunda babarka ta dawo ita zaka bi"


Shi kuma sai ya maƙale kafaɗa ya ce "Uhm'uhm zani"


"Wai waye surukin namu ne?" Cikin Sauri Abdullah ya ce


"Wai Burhan"


"Burhan?" Ridayya ta maimaita tana sake kallon Zainura, Zainu ta haɗe fuska Khaliperh ya ce


"Ta kwafsa ai yarinyar nan, kuma na fahimci Tajj ma son ta yake ga mutumin kirki ta je ta ɗakko ɗan shaye-shaye"


"Wallahi ba ɗan shaye-shaye bane, kuma yana da kirki" ƙafa Aliyu ya kawo zai haure ta, ta kwasa da gudu ta bar wajan.


Shiru duk sukai ganin Ustaz ya fito cikin wani voyel mai laushi da manyan zane ya ɗora baƙar dara a kan shi ta ƙara fiddo kyawunshi Ridayya ta gefen idanu ta kalle shi ta ɗauke kai, Little ya tafi da sauri yana "Abbiey, Abbiey"


Ya ɗauke shi yana shafa kansa kamar zai shige ya dawo ya ɗauki Al'hussan a cinyar Ridayya, numfashinta na ɗauka a fuskarsa ya ɗaga kai suka haɗa idanu ɗan matsawa ya yi ganin kamar duk t.v suke kallo a hankali ya manna mata kiss a kumatu "Morning Mimi"


Ta yi saurin ware ido da sauri ya ɗago kansa suka haɗa idanu da Baba ƙarami, bai yarda ya sake kallon wajan ba ya nufi part ɗin Mardiyya ganin inda ya nufa ya saka Ridayya jin wani abu a ranta mood ɗinta ya sauya. Mardiyya na zaune cikin kwalliyar atamfa gilita babyn na hannunta ta ji ƙamshin Ustaz cikin sauri ta ɗaga kai ta ganshi tsaye bakin ƙofa hannunsa riƙe da baby, ta yi murmushi tana ajjiye jaririyar ta miƙe ta ce "Oyoyo sweetheart barka da zuwa" kafin ta rungume shi ya gefe tare da shiga cikin bedroom ɗin nata, ya zauna saman stool ta ƙarasa ta zauna ta ce "Good mrng"


Shuɗewar wasu seconds ya ce "Sannu, ya jiki?" Ta ce "Alhamd, ya hanya kana dawowa babynmu na zuwa duniya" ya ɗan yi mitsi-mitsi da idanu ta ɗakko yarinyar ta miƙa masa ba musa ya ɗora Al'hussan a cinyarsa ya amshi yarinyar ya zuba mata idanu can ya ce "Allah ya sa mata albarka"


"Sweetheart ya naga kamar baka farinciki, first born ɗinka ce fa kuma ba wani gift na haihuwa" tunda take bata taɓa ganin murmushin Ustaz irin yau ba, sai hakan ya yi mata daɗi sosai ya yi murmushi ya ce "Zan bada gift ai kin cancanci hakan ko dan riƙo da tarbiyya" bata kawo komai a ranta ba ta ce "Haba sweetheart ai ba komai don na haifa maka baby"


Ya miƙe tsaye ya ce "Zan je abu, ga wannan" ya miƙa mata envelope mai ɗauke da kuɗi ya ɗora akan jaririyar, ta ce "But is true?"


"For?" Ya tambaya yana ware mata idanu to be sure ya ji tambayar ya dai share ne ta ce "Da gaske wannan ɗanka ne? Kuma ka yi aure?"


Ya ɗan lumshe idanunsa yana rungume Al'hussan a ƙirji ya ce "E, daman ai ina da aure yara kuma nawa ne Mardiyya"


"Wace matar daka aura?"


"Ridayya Mansur Rano, Ridayya ƙawarki aminiyarki tun kuna yara" yana faɗin hakan ya juya a firgice kamar zata jawo shi amma tana shakka ta yi saurin shan gabansa ta ce "Ridayya ka ce? Wace haka wanann mummunar yarinyar she can't be your wife bayan ka sake ta?"


Ya dinga kallon ta duk yadda yake ƙokarin danne zuciyarsa yaga bai ci mutuncinta ba tunda da gaske tana hakƙi a kan shi kuma har zuciyarsa yayi niyya zama da ita idan ya so ya ji da rigimar Mimi shine take masa ihu aka, ko waye ya faɗa mata ana masa ihu a ka ya haɗe rai sosai a dake ya ce


"Ke bana son shirme matsa mini" bai zata ba ya ji ta cakumi wuyan rigarsa ta ce "Wallahi ƙarya ni,ni za ku ci amana bayan kowa ya san cewa ka sake ta sai dai idan zaman kasuwanci kuke tare a inda ka ɓoye ta" wani kyakkyawan mari ya sauke mata wanda ya sanya ta fasa gigitaccen ihu hakan ya saka Inna farkawa daga bacci a razane tana "Wanne ɗan mara wulaƙancin ne wannan"


Daidai nan Baba ƙarami ya ƙarasu tare da Umma da har yanzu bata fita daga shock ba ta ce "Muhammad ka bar ni cikin duhu ban gane cewa ba ƴarka bace"


Ya juya ya kalli Umma ya kalli Baba ƙarami kana ya kalli Mardiyya dake rusa ihu Inna na tsaye ya ce "To yaushe na yi cikin? Babu wata ƴa mace dana sani a duniya sama da Ustaz kuje ku tambaye ta ita ta amshi budurcina a can Japan, Ridayya kawai ta gani a halin daya kamata daman ace ita ta ganni, bayan tafiya ta da yaushe ta samu cikin? Ta muku bayani bani da lokacin hakan"


Umma ta saki baki Baba ƙarami girgiza kai kawai ya yi ya san daman za a yi hakan ya ce "Mardiyya an yi yarinyar huɗuba?"


Ta girgiza kai tana ta kuka fargaba ta cika mata zuciya tana fatan komai zai je ya dawo ta kasance da Ustaz har abada ta kuma raba shi da Ridayya da ta ci amanarta. Baba ƙarami ya amshi yarinyar bayan ya yi mata huɗuba ya ce "Wanne suna kike so?"


"Sunan Umma na ce a a saka Hadiza Umma na yi wa takwara"


"To ma sha Allah, Allah ya yara Hadizatul-kubra"


Umma ta yi saurin cewa "Wacce Hadizan? Wallahi bana so a ƴar shegen za a saka sunana wallahi na yafe a saka sunan tata uwar ko wannan" Ta nuna Inna. Inna ta zare idanu ta ce "Ni Mero ina ruwana? Bake kikai ta ɗawainiyya da cikin ba" Baba ƙarami ya danne dariyar dake cinsa ya ce


"Kina da gaskiya Inna, Umma ta yi ƙoƙari a cikin nan har fili ta mallaka masa fa? Ai dole a saka Hadiza" Yana faɗin haka ya sawa yarinya Hadiza Umma ta fashe da kuka ta ce "Allah ya isa wallahi, kuma ba ni Hadizan aka saka ba ki je ki fito mini da takardun filayena"


"Wallahi Umma ƴarsa ce sharri yake mini, wa aka aura mini idan bashi ba yawo nake yi ne?" Sai kuka take Umma ta ce "Ke rufa mini baki a nan, Ustaz kalma ɗaya yake idan ƙarya ne kai tsaye zai faɗa haka idan gaskiya ne"


Takaici ya haɗewa Mardiyya Inna dai na tsaye sai zare idanu take suna haɗa idanu da Mardiyya ta ce "Ashe tantiriyar ƴar iska ce ke?"


Duk suna zaune kamar daga sama Ridayya taga mace a gabanta ta ɗaga idanu ta kalli Mardiyya da take cewa "Shegiya munafuka Allah ya tuni asirinki mai ƙwacen miji wallahi ba ki isa ba sai kin bar mini mijina domin nawa ne ɗaya har abada"


Miƙewa Ridayya ta yi zata shige part ɗin Mami Mardiyya ta riƙo wuyanta, daman tun ɗazo zuciyarta ke yi mata zafi sosai bata tsaya jiran komai ba ta ɗaga hannu ta zabgawa Mardiyya mari ta ƙara sauke mata wani ta nuna ta da yatsa ta ce


"Kul karki kuma, ki haukan ki kan wanda ya ajjiye ki ba ni ba, wahainiyyarki ta kiyayi ramata, ke har ni za ki buɗe baki ki cewa mai ƙwacen miji? How dare you? Ni kikaiwa ƙwace ko ni na yi miki?"


"Idan kin manta na tuna miki, kin tuna sanda kika ce Abbiey ba tsarinki bane jallabiya za ki aura ko shi? Kuma kika ce idan ina da ra'ayi na je na aure shi? Ai tun daga wannan na sakawa raina sai na aure shi kuma ya zama nawa har abada, kin yar ni na ɗauka don haka dole ki bar mini mijina"


Maganganun da Mardiyya ta tunawa Ridayya sun mata zafi ta dake ta ce "Ohho dani dake za a ga mai fitar da wani, zama da mijina yanzu na fara kuma yanzu na shirya zan cika gidansa da tarin yara masu kyau irin albarka, zan ci gaba da son mijina don haka kowa ya iya allonsa ya wanke, ina son Abbiey yana sona" sosai suke faɗa ba zaka taɓa cewa sun taɓa zama aminai ba, Mami na ji ta yi shiru shi kansa Ustaz yana tsaye Umma ta ƙarasu ta ce "To wallahi sai kin barwa Ridayya mijinta, domin ita ce irin albarka" kalaman Umma sunwa kowa daɗi kuma sun bawa kowa mamaki ganin jinin Ridayya ya fara rawa idanunta yana wani kala ya saka Ustaz yin murmushi ya ƙarasu tare da kama hannunta ya ce


"No please Mimi" hannu ta saka ta doke hannunsa tana zabga masa harara ta suka ci-gaba da cacar baki "Banza wacce ubanta ya ce ba shi ya haifeta ba, wacce babarta ta gudu ta barta wajan kishiya uwar ƴar shaye-shaye kawai wacce ta auri ɗan caca.....,"


Caraf Zainura ta ce "E an ji ɗan caca ke kuma da kike yawan ta zubar fa? Mai shafe shafe kuma ita bata zalunci mijinta ba shi ne ya tauye mata hakƙi shi ya sa yanzu take ta ganin sauyi kala-kala, da kike maganar muni kuma ai ga ƙarshen muni nan kin haifa bayan ke ɗin fara ce kyakkyawa ita data kasance baƙa ki dubi nata kalar irin kiga? Ai babban goro sai magogin ƙarfe kuma da tsohuwar zuma ake maganin hakan kuma don tuwan gobe ake wanke tukunya" Burhan sai murmushi yake that's why she always love Zainura yana son mace mai tsiwa da baki wacce yana cewa ke zata ce kai ƴar drama like Zainura. Ustaz ya sunkuya ya sunkuci matarsa ya nufi part ɗinsa da ita sai rawar jiki take, Mardiyya ta juya fuuu bayan taci kuka ta ƙoshi addu'a take Allah yasa jaririyar ta mutu ma, ta dinga kiran number ƙawarta domin ita kaɗai tasan gaskiyar komai amma bata samu ta tuna gift ɗin da Ustaz ya bata hakan yana nufin yana son ta bai kuma yi fushi ba. Ta buɗe kuɗi ne ƴan 1k bandir uku sai ƙaramar takarda tana buɗe taga ya rubuta.


_Wannan kuɗin kyauta ne daga ni a matsayin mijinki, da gaske na so zama dake tunda ni bana buƙatar saki a cikin lamarina aurena dake ƙaddara ne, amma zunubin da kika aikata ya saka na janye nawa ƙudirin ba zan iya zama da macen dake bin maza ba.... Mardiyya na sake ki saki uku kuma ki nemi uban yarinyar da kika haifa_


Wani ihu ta saka tare da sulalewa a wajan babu numfashi. Waya yake yi yana cewa "Na ji ya dawo gari, ba zan taɓa haƙura da cin mutuncin da Zameer Giɗaɗo ya yi mini ba dole ne na baza bidiyon da sukai a jam'i kafin su yi aure, kowa ya gansu tsirara babu abinda ya shafe ni ba'a cin bashina na yi haƙuri wallahi, so zan jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya kenan, daman akwai wani ya bani kwangila ɓata shi Muhammad Bilal Tahir Rano ɗin domin jama'a suka baƙin shi, kaga yarinyar da sukai zina tare da Zameer ai matarsa Bilal ɗin ce da yake neman takarar Gwamna, kuma shi da kansa bai san cewa ta aikata abinda ta yi ba, so babu mamaki ganin bidiyon ya saka zuciyarsa bugawa ya mutu nan take" Khalid ya yi ɗan jim sai kuma ya ce "Ok bari na tura maka bidiyon yanzu da iPhone aka ɗauka ya yi clear sosai a fara posting a tiktok sai ya fi zama trending going in to viral ka yi hash tag sai a koma facebook da X da Instagram sai a turawa bloggers yawwa gashi nan zan tura bidiyon yanzu......




A yi haƙuri gobe zamu kammala
08164069385
*MUNAFUKIN MIJI*


Nimcyluv
48


Mikiya writers Association


Fitowa sukai daga ɓangaren emergency ɗin kana ganinsa zaka san yana cikin damuwa ya ce "Dr yanzu ya za mu yi da gawar? Kuma ba a samu labarin wanda sukai masa wannan rashin ɗa'ar ba?" Dr ya kalli Shaba da Moo ya ce "Ambulance za a kira sukai muku gawar, and wanda suka aikata hakan i think that is not part of my work, an dai samu labarin cewa ƴan daba ne suka same shi a bakin hanya, sukai ƙoƙarin amshe wayarsa ya hana su, garin haka suka soka masa wuƙa a ciki sai data ɓullo ta bayan shi, bayan wayar har motarsa suka gudu da ita shi kuma suka yasar da shi a ƙasa, kafin ma a zo asibiti ya cika" Moo ya sauke numfashi shikenan sun rasa Khalid? Yaushe za a daina ƙwacen waya? Yaushe ne za a daina shaye-shaye? Yaushe ne za a daina daɓa? Abin kullum ƙara girmama yake kamar cin ƙwan makauniyya? Faɗan sai ƙara yawa yake ba mai cewa komai babu mai ɗaukan mataki? Meke haddasa shaye-shaye da kuma daba? (Find out on MUTALLAB).


"Allah sarki Khalid Allah ya jiƙan shi bai so ya rasu bamu daidaita tsakaninsu da Zameer ba" cewar Moo kallon shi kawai Shaba ya yi without saying a single words. In few minutes rasuwar Khalid yaɗu cikin jama'a da kuma yadda ake Allah wadai da masu ƙwacen waya. Ambulance na zuwa aka saka gawarsa suka nufi gida, hankalin duka ƴan'uwa a tashe yake.


Zagaye yake cikin parlon nashi zufa sai yanko masa take ya juya ya kalli wanda ke tsaye a gabansa a hankali ya nisa ya ce "Kuma da gaske bai tura maka bidiyon ba kafin rasuwar shi? Bidiyon nan shine confidence ɗina kuma shinr hope nawa na ɓata farinjinin Muhammad Bilal, da kuma kawo naƙa su a takarar shi"


Guy ɗin ya girgiza kai ya ce "Oga bai tura mini ba, daman na baka shawara wannan aikin da mutum ɗaya kawai ya dace, baya tsoro, baya shakka baya damuwa da duk abinda zai biyo baya shi ɗin tamkar walƙiya haka yake, hagayi sa gabanka inda kake so, shi ɗin murucin kan dutse ne bai fito ba sai daya shirya, ɗan malam yaƙi halin malam, faɗa taka cikawa tashi kuɗi kawai shi ne a gabansa kaci amanar shi uwarka ta haifi wani, jan biro maganin daƙiƙin yaro..... Huhuhu kutumar uban nan wani aikin sai maza da an ganshi fitsari ake a wando, ya gagara matacce ne amma kullum firgita su yake mutum me aikin aljanu, mata maza wajan ƙin mata da sabgoginsu"


Nan da nan jiginsa ya fara rawa ganin haka ya saka Sakataren jam'iyar su Muhammad Bilal Ustaz mai suna Dr Ghali Uba ya ce "to waye wannan ɗin da kake ta yi wa kirari haka?" Shazali ya kalli Sakataren jam'iya ya ce


"MUTALLAB"


"MUTALLAB?"


Dr Ghali Uba ya maimaita sai kuma ta ce "Yanzu bamu da wani lokaci, amma idan ina raye ba zan bar Ustaz ya hau wannan kujerar ba, ni na nemi takarar kujerar wajan Uban jam'iyya amma saboda ya wulaƙantani ya ce ban dace da ita ba, ya je ya ɗakko wanda bai san darajar siyasa ba ya bashi? Na ci alwashin lalata jam'iyyar idan ya so na yi anti fati kawai"


"Oga kenan zagon ƙasa kake musu, sun yarda da kai fa? Shi ne kake ɓallo musu ruwa ta ƙasa? Ka daga oga"


Dr Ghali Uba ya ce "Shazali kenan siyasa sai ɗan siyasa, yanzu ka je ka yi bincike ka ji ko shi Khalid ɗin ya bawa wani kwafin bidiyon, kuma ka ce ina kiran shi yama sunan shi yawwa MUTALLAB TAHHB"


"Da ƙirinka oga ai MUTALLAB ko appointment ka nema da shi baza ka samu ba, saboda shegan ƙaro ne, innalillahi wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login