Showing 123001 words to 126000 words out of 190738 words

Chapter 42 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17302

gina gidansa da zai zauna da iyalinsa zamu bayyana ga wanda suke zaton mun mutu. Aure rai ne fa shi duk wanda yake ƙoƙarin ganin bayansa idan akwai rabo mai tsanani sai Ubangiji ya raba shi da duniyar bakiɗaya, auren Ustaz da Mardiya nufin Allah ne haka auren Ustaz da Ridayya rubutacciyar ƙaddara ce wacce ta jima a zane, kuma a bayanin Hajiya na fahimci Ridayya ita ce uwargida an riga ɗaura aurenta akan na Mardiyya domin mun jima da hakan mun su rufewa sai kuma aka yanke hukuncin rabawa dangi alawa da goro su saka albarka, ba wani wa'azi da zan yi sai ranar da aka yi biki Ridayya zata tare zan haɗa na yi musu wa'azi"


Hajiya ta ce "Hakan ya yi Allah ya saka Albarka a wannan auren ya tsole idon maƙiya. Oh ashe zanga wannan ranar jikokaina aka haɗa aure Allahu Akbar"


Ustaz ya watsa mata harara Junaid na kallonsa ya yi murmushi kawai. Baba ƙarami ya zaro kuɗi ya ce "Zainu kira mini Yaya Ridayya na bata sadakinta"


Sai a lokacin Ustaz ya ce "Sadakin baƙar mace daban yake Abba ka bari zan bayar"


"Gaskiya ne yanzu samun baƙar mace sai an bincka bincike mai tsanani" Mardiyya ta zo wuya.


"To In sha Allah gobe zamu koma tunda jikin da sauƙi sai ku zaba cikin shiri"


Ustaz ya gyara murya ya ce "Don Allah kar a sanar da Ustaza maganar auren nan zan faɗa mata da kaina"


Duk suka yi na'am Mardiyya ta tashi fuu ta nufi ɗaki zuciyarta sai wasiwasi take mata babu mamaki ciwon Ustaz ƙarya ne kamar yadda Umma ta faɗa mata plan ne don a raba auren a bashi Ridayya. Ta fara tunanin mafita dole a yau ta saka Ustaz ya kusanceta but how? A fili ta ce "Maganin saka feelings" da sauri ta ɗauki jaka da mayafi ta fice ba tare data tambaya ba.


Mami ta shigo ta samu Ridayya tsaye tana kallon madubi ta yi murmushi tare da kama hannunta suka zauna bakin gado ta ce "Bakya gajiya da kallon madubi? Ko kina shirya wani abu ne, Ridayya ke ta musamman ce ba za ki gane ba sai nan gaba" Ridayya dai ta yi shiru domin bata saba da Mami ɗin ba.
"Mene matsayin Ustaz a wajanki ne?" A hankali ta ce "Abbieyna"
"Baffa kuma fa?"


"Babana" Mami ta ce "To waye uban na gaskiya kenan Ridayya ga Ustaz ga Baffa kowa kuma uba dole akwai wanda yake amsa sunan daba nashi ba. Baffa shi wanda ya yafe miki kuma biological father naki, Ustaz kuma yayanki ne wanda ya raine ki"


"Kuma me ya sa ake kira na da sunansa?"


"Saboda shi ya buƙaci haka. Ridayya buɗe kunnenki Ustaz ba mahaifinki bane a rashin uba a kan yi ubanɗaki a rashin gata da uba kika samu Ustaz. Kamar yadda Junaid yake haka Ustaz yake a wajanki bambancin shi ne Ustaz nada ikon aurenki ki zama matarsa domin ɗan gidan Abba ne ke kuma ƴar Baffa ce akwai aure a tsakaninku"


Ridayya ta zare idanu tana rufe baki tana jin maganar wata kala ba tsari taya Abbiey zai zama mijinta? Wannan shafi abin kunya ne "Yanzu kika fara rufe baki na yi tunanin za ki fahimci cewa Ustaz yana son ki?"


"Mami na sani fa, i knew everything ina jin wani lokacin ai matsayin uba ne wani lokacin kuma sai na manta abubuwa ban taɓa kawo shi a matsayin miji ba. Mami Abbiey bai cancanta dani ba na yi zunubin da ba zai taɓa yafe mini ba idan ya ji, wallahi ba zan iya kallon Abbiey matsayin miji Mami ban dace da shi ba"


"Ya taɓa faɗa miki yana son ki?" Ta yi shiru koda ta nutsa tunani sai kanta ya fara ciwo Mami ta miƙe ta ce "It's okay. Mimi babu abinda yafi rayuwa da wanda yake sonka daɗi, ki tuna wanda ke zuciyarki wanda kike jin kishinsa idan kin ganshi da wata macen wacce kike jin dake kawai kike son ya rayu"


"Abbiey ne Mami bana son ganinsa da Mardiyya" Mami ta yi murmushi ta ce "Sai ki ƙoƙarin maye gurbin Mardiyya a zuciyarsa ki zama kamar ita da matsayinta a wajansa"


"To ki bani shawara, amma Sadauki fa?"


"Shawara kike irin ta uwa ko kuma irin ta Aminiyya? Sadauki ban ce ki daina tunaninsa ba nima"


"Aminai mugwaye ne, abokina ɗaya Abbiey ki bani irin ta uwa" ta faɗa tana kwaɓe fuska


"Da farko dole ne kina hira da Ustaz, ki kula da shi daga abincinsa har ruwan wanka kayan sawa ki dinga nunawa kina son shi hakan zai saka Mardiyya ki shi, kinga dai kin girma amma a wajansa ki nuna ke da Little ɗaya kuke idan kun yi faɗa kar ki bari Mardiyya ta gane, duk abinda zai ɓata ran Ustaz kar ki yi kina kwaliyya kina zuwa kuna hira amma kar ki kwana wajansa" Ta yi saurin cewa "Ai ba zan iya bama tunda kika ce zai iya aure na nake jin kunyarsa"


Mami ta miƙe tsaye ta ce "Sannu Mimi ke kam ko Zainura ta fiki wayo ki je yanzu ki yi masa sannu"


Fita Mami ta yi Ridayya ta miƙe daman ta yi wanka ta gyara sumarta ta ɗaure dake dare ya fara ta saka riga body short ta saka slippers ba zaka ce ita ta haifi Little ba domin jikinta har ya fi na Zainura kyau balle kuma na Mardiyya. Burhan na zaune a parlour ta zo ta shige ya bita da kallo yana hura hayaƙin tabar shi a parlourn.


Shiga ta yi bedroom ɗin a hankali bakinta ɗauke da sallama shiru babu kowa bedroom ɗin sai ƙamshi yake komai a gyare ta dinga kallon ko'ina ta nufi gaban madubi ta tsaya idanunta ya sauka a kan diary ɗin Ustaz ta buɗe ta ɗauka ta dinga dubawa ta buɗe shafin Farko idan aka saka _FIRST LOVE_ da mayan baƙi. Tana ƙoƙarin karantawa ta ji an ziro hannu ta saman kafaɗarta an ƙwace an dafa kafaɗarta da ɗaya hannun.


Ta cikin madubin ta gan shi yanzu ma dai jallabiyya ce a jikinsa mai ɗan faɗi ya faɗa ya ƙara fari ya cika mata Idanu ya mata kwarjini sosai sai duk kunya ta kama ta ta fara ƙoƙarin matsawa ya ƙara faɗi bakinta na rawa ta ce
"Abbiey ya jikinka? An ce ka ji ciwo a mara ko?"


"Injiwa?" Ta tura baki ta ce "Haka na ji wai ƙafarka nata jini yanzu ya daina ko? Da zafi wajan ciwon da yawa ne? Mu gani nuna mini wayyo Abbiey"


Ta faɗa tana ƙoƙarin ɗaga jallabiyyarsa zuwa sama ya yi saurin durƙusawa ya riƙe hannunta yana rufe Idanu saboda zafi ya kame hannayenta duka ya haɗe waje guda ya ce "Ustaza ba ki da kai sam, kin san me za ki gano?"


"Mararka zan gani mana wajan ciwon sai na yi maka addu'a" bashi da wani ƙwari gashi neman fin ƙarfinnsa take a dole sai taga wajan ciwon sai ƙoƙarin ɗaga jallabiyyarsa zuwa sama take. Cikin dabara ya janyeta yana tsayar da ita gaban madubi idanunsa a ɗan lumshe yake kallona yau Ridayya ce a gabansa take amsa sunan matarsa? Taya zai fara godewa Allah? A hankali ya ware hannunsa ya ce "Zo ki ji wani sirri" Ta ƙarasa har tsakiyarsa taƙi kallonsa a hankali ya zagaye hannunsu ya yi covering ɗinta tare da yi mata halal hug ya rungumeta a tsakiyar ƙirjinsa tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa kamar na rashin sabo ya sauke ajjiyar zuciya mai nauyi ya ce "Allahamdulillah ya rabbil alamin" Za ta yi magana ya damƙe hannunta tare da sumbatar tsakiyar goshinta irin na larabawa idanunsa a lumshe ta ji abu mai zafi na zuba a fuskarta kafin ta ɗaga kanta ya juyar da ita yana zama saman gado ya nuna mata lemon da Mardiyya ta kawo masa ya ce "Miƙo mini" jikinta a sanyaye ta ɗakko lemon ta ji san yi sosai ta ce "Abbiey na ɗan sha mu ji?"


Ya kalleta da kyau tana yin komai kamar yarinya shi bai ba san ame ta ɗauke shi ba. Mijin ko aboki ko kuma uba? "Na sha kar ka mini rowa"


"Sha" kawai ya ce kurɓa ɗaya ta yi ta ji daɗi sai ta zuƙe duka daga ƙarshe ta ji wani ɗanɗano nada ban ya ware Idanu ta kalli kofin shi ma kallon kofin yake kishin giɗa. "To wallahi daɗi ya yi"


"Allah ya yi miki Albarka Ustaza ya ba ki lafiya daga miƙo mini lemo sai shanyewa?" Da sauri ta ƙarasa ganin ya lumshe idanunsa ta yi saurin kame ƙafarsa ta ce "Yawwa ai wallahi sai naga wajan ciwon inda ka yi maka aikin.....




Karanta ka yi share
08164069385






*YI DOMIN ALLAH*
*SARAUTA CHARITY FOUNDATION*


Ciyar da marasa ƙarfi da almajirai lokacin azumi. Ta hanyar yin abinci, kunu, ƙosai da ruwan sha tun daga kan 200 zuwa sama na abinda Allah Ya a hure maka.


*Saboda wasu dalilai da kuma yadda wasu suka nuna basa so, a daina saka sunan wanda ya bada kuɗi saboda sun yi ne domin Allah*


Saura kwana biyu azumi har yanzu ba mu kai ga samun abinda muke so ba jama'a a taimaka.


1. Sa'idu Hafsat 1k
2. A'isha Gadanya 3k
3. Maman Khalid 1k
4. Someone 2k
5. Received from pos 1k
6. Fatima Kabir 500
7. Unknown 2k
8. Murtala Maimuna 500
9. Fauziyya Abdulsalam 500
10. Unknown 1000
11. Unknown 500
12. Unknown 500
13. Unknown 500


Total 14k


6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank


Ko kuma
8164069385 Na'ima Sulaiman Shu'aibu Opay


Ku taimaka saboda Allah kuma ku yi sharing


*MUNAFUKIN MIJI 35*
Mikiya Writers Ass




Bright pens free batch
Nimcyluv sarauta




*Ba zan ce na tafi hutu ba, ba zan ce ban tafi ba duk mai son jin ƙarin bayani ya duba ƙarshen page. Zan cigaba da posting iya wattpad da channel ɗina. Wanda suke buƙatar ci-gaba da karatu su yi following channel ɗin tawa, wanda baya buƙata shi ma yana iya joining bayan sallah ya karanta*


Follow my WhatsApp channel👇🏻
https://whatsapp.com/channel/0029Va5fqs7E50UpMpXolU1T






Sakin ƙafarsa ta yi ta fasa abinda ta yi niyya jin kanta ya sara da ƙarfi Ustaz ya kalleta kamar zai share sai ya ce "Sai dai fatan Allah ya bawa ƴar rainota lafiya, amma Ustaz tuni kin ci kai bayan tsaraicina da kika gani kina ƙarama yanzu kike son sake gani? Zunubi har haka Ustaza?"


Ta tura baki taƙi cewa komai kanta a ƙasa maganganun Mami na mata yawo a kunne kamar yanzu take faɗa mata. "Abbiey wai zan iya zama matarka?"


Ya ware idanu da kyau yana mai gyara zaman shi ya ce "Kuma injiwa?"


"Haka na ji" girgiza kai ya yi yana sauke idanunsa a kanta a nutse ya ce


"Kina son zama matar tawa ne?" Ta tura baki ta ce "Ni dai kawai na tambaya ne, kaga ni ai ba zan iya haɗa Idanu da kai ba idan ka zama mijina"


"Jiki ma za ki haɗa dani soon Ustaza"


"Ma ka ce Abbiey?"


"Ke na ce mana" ta fara lumshe idanunta da suka fara yi mata laushi ga wani abu dake mata yawo saman fatarta.


"Ni ban ji ba ka sake faɗa" ya miƙe daga kishingiɗan da yake zuwa zaune ya gyara da kyau hannunsa ya miƙa masa ya ce "Zo mu yi sirri" ta ɗauke kanta sai kuma ta runtse idanunta ta miƙe da ƙyar tana ƙoƙarin zama ƙasan carpet ɗin wajan ƙafafuwansa ya yi saurin tare ta, ta hanyar kama hannunta ya zaunar da ita a gefensa kafaɗarsu na gogar ta juna.


"Wassh Abbiey jikinka ya jani" wuyanta ya bi da kallo da mamaki domin bai taɓa lura ba sai yanzu wasu yanka yanka ya gani kamar wacce aka saka reza aka tsatsaga mata fata ko aka karce ta, ta kasa kallonsa ya saka hannunsa masu taushi a saman haɓarta ya juyar da fuskarta ɗaya gefen wanda ya ƙone ga ɗan raguwar tabo nan ga wani karcewar ne. Ya saka yatsunsa biyu ya fara shafa wajan da son tantance mene.


Ridayya kamar wata wuta haka take jin yatsun Ustaz jikinta ya fara rawa ɗakin ya shiga juya mata ga wani murɗawa da mararta ta yi ta kumburu nan ta nan ta fara fitar da numfashi.


"Ya aka yi kika samu wannan ciwon Mimi?"


Baki ta buɗe da nufin faɗa masa cewa Zameer tsohon mijinta ne silar komai shike shaƙe mata wuya a duk sanda suke tarayya. Nauyin Ustaz da girman shi da yadda kullum yake cika mata idanu da kwarjininsa yasa ba zata iya faɗa masa cewa mijinta na baya ke shaƙe mata wuya ba idan zai nutsu har suma take wani lokacin, ta yi ƙasa da kanta zuciyarta na bugawa.


"Bana son tabo bana so ko kaɗan ina kika same su?" Ya faɗa yana juyo da fuskarta zuwa dab da tasa numfashinsa na sauka a kan tata fuskar.


Kasa bashi amsa ta yi jikinta na rawa ta fashe da kuka tana kifa kanta a cinya tare da yarfe hannunta kuka take sosai ɗaya hannun tana riƙe mararta. Ta kasa daurewa da abinda take ji bata saba da wannan sabon yanayin ba ji ta yi akwai abinda take buƙata idan bata samu ba zata iya mutuwa.
Ustaz ya zuba mata Idanu shi dai babu abinda ya yi mata ya miƙa hannu zai ɗago ta a firgice ta ce "Don Allah kar ka taɓa ni Abbiey ƙara mini azaba kake" Ya jinjina mata kai ya rasa mai ma zai ce bai ɗauka taɓarar Ridayya ta je har haka ba.


Ya zame a hankali zuwa ƙasan carpet kansa daidai cinyarta a hankali ya ce "Ok meke miki ciwo? Jikin ne? Mu je asibiti"


"Abbiey wallahi mutuwa zan yi na shiga uku, wani abu ke mini yawo a jiki marata ƙirjina wani iri Abbiey" Kuka take har da majina ta fita daga hayyacinta nan da nan kanta ya fara ciwo wani irin zazzabin ya fara rufe ta saboda abin yawa jininta girma ya fi ƙarfinta. Shi kansa Ustaz ya fara rikicewa bai kulata ba yama mance bashi da lafiya ya saka hannunsa duka biyun ya jawota zuwa ƙasa saman cinyoyinsa ta riƙe hannunsa da kyau jikinta kamar an jona mata wutar lantarki ga wata uwar zufa data gama wanke mata jiki.


Addu'a ya fara yi mata yana ɗan buga kumatunta "Wifey, Little Mama, Angel buɗe Idanunki"


Buɗe Idanunta ta yi ta zubawa fuskarsa Idanu musamman laɓɓansa ta saki wata ajjiyar zuciya mai ƙarfi ta yi saurin rufe idanun "Ban san meke mini ciwo ba Abbiey ka taimaka mini ƙirjina marata, Abbiey ina son....,"


Idanunta da ya yi jajur yake kallo da kuma gargasar jikinta da suka mimmiƙe sai haɗe ƙafa take waje guda ya girgiza kai kawai ya jata jikinta kamar jira take ta yi saurin ƙanƙame shi tana jan numfashi jikinta ya yi zafi sosai.
"Shhhh ya isa it's okay"
Ta jinjina masa kai ta ce "Ka ƙara riƙe ni Abbiey wani abu ne yake mini yawo a jikina"


"Bari na duba jikin mu gani, can i?"


Kunya take ji amma gwara a duba mata kawai kar abin ya kasheta tana da sauran burika a rayuwarta. Ya ɗago ta ta dinga kallon bakinsa ya ɗage mata gira ya ce


"Go on; fell free to ask Little Mama"


Ta yi shiru ya mirgina ta ya fara ƙoƙarin zuge ziff ɗin zuwa ƙasa baƙar fatarta ta bayyana a fili fresh and natural skin ɗinta yake kallo sai kyalli yake daya taɓa fatar bayanta taushi da laushinta har tsoro ta bashi kamar ta yage bai ga komai a bayan ba ya ɗora hannunsa a saman bra zai yi unhooking ya ji an zabga salati.


"Me zan gani ni ƴar nan? Wacce ƙaniyyar ce haka"


Har lokacin hannun Ustaz yana wajan ya kasa ɗago kai ya kalli Umma kuma ya kasa ɗauke hannunsu, Ridayya kuma azaba ce ta yi mata yawa ta kasa tashi.


"Bariki a lalan gero an saba da gidan miji daman yaushe za a jure? Har kika kawo kan ki tare da sakar wa ɗa namiji jiki uwar mai zai tsinta a jikin bazawara, sai baƙar fata da mugun baƙi kamar kwal za ki tashi ko sai na yi ciki dake kika kwanta kamar ruwa"


Ustaz da idanunsa sukai wani irin sauya kala tun kafin Umma ta shigo ya ɗago ya kalli Umma cikin wata kalar murya ya ce


"She is my wife Umma, kar ki yi haka bata da lafiya"


Ta zabga salati ta ce "Muhammmmd ya na ji kana magana da ƙyar, to banga dama ba tunda kai baka san meke maka ciwo ba ga matar arziƙi zaka zauna ka ƙare a fanko"
Ya yi mata shiru ya riƙo fuskar Ridayya data gama caɓewa da hawaye ya saka yatsunsa ya share mata hawayen tas wasu na sake sakkowa ya ce "Mu je asibiti?"


"Uban uban uwar asibiti za ku" Ta saka hannu ta fisgo Ridayya ta tura ta waje ta ce "Li'ilafi kurash"


"Kai kuma shanyaye kake son zama har ni zan dinga magana kana mini kunnen uwar shegu Babana?"


"Wallahi ban ji me kike cewa ba"


Ta dinga kallonsa ta ce "To tashi ka fito waje" ya yi shiru ta ce "Zaka tashi ko sai na zo na miƙar da kai? Ka daina ganinka wani gansameme mai shekaru 43 wallahi ganinka nake kamar yanzu na haifo ka"


Yana daga zaune ya juya kama zai duba abu ya juya mata baya ya miƙe tsaye ba tare daya juyo ba ya shige bathroom yana dafe kansa.


Ta saki baki tana binsa da kallo ta shiga uku kar fa ɗanta ɗaya tal ya zama bita zai-zai. Ta yi ƙwafa dole ta kawo karshen wannan auren.


A gigice Ridayya ta fito daga part ɗin Ustaz idanunta rufe karo ta ci da abu warin taba ya daki hancinta cikinta ya hautsine ta shiga kwarawa amai a wajan kamar zata amayar da abinda yake cikinta ta tsani warin taɓa zata iya lissafa sanda ta taɓa jinta. "Kan uba!"


Ya faɗa yana daka mata tsawa da sauri ta buɗe idanunta ganin Burhan tsaye a gabanta daga shi sai gajeren wando yana busa taba gabaɗaya ta wanke masa jiki da amai ta dinga kallonsa ta kasa magana ya ce "Ke wacce irin mahaukaciya ce za ki mini wannan abun a jiki? Kin manta waye ni ko?"


"Ka ka yi haƙuri don...," Kafin ta ƙarasa ya saka hannu ya zabga mata mari wanda ya saka ta ƙara gigicewa kafin ta dawo hankalinta ya ƙara zabga mata wani marin wata ƙara da ihu ta fasa tana kifawa ƙasa daidai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login