Showing 75001 words to 78000 words out of 190738 words

Chapter 26 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17296

ciki kuwa har wannan Manajan Bankin....," Wata shaƙa Ridayya ta yi masa idanunta ya firfito waje kamar mahaukaciya ta ce "Ƙarya ne Abbiey ya mutu ya barni, ƙarya ne na rasa kowa nawa suna nan a raye ka ce mini suna nan basu mutu ba"


Cak kuma numfashinta ya tsaya ta sulale tare da yanke jiki ta faɗi a sume.


____

Kuka take sosai kamar ranta zai fita ya kifa kanta a kafaɗar shi tare da damƙe hannunsa dake cikin nata, yadda take kukan zaka ɗauka ƙaramar yarinya ce tsananin damuwa ne ya yi mata yawa a zuciya.


A hankali yake shafa bayanta tare da ɗan bubbuga wa alamar rarrashi amma kamar yana zuga ta ganin kukan ba mai ƙare bane ya sanya ya jawota ya rungume ta a jikinsa, da sauri ta ƙanƙame shi domin da gaske tana buƙatar wajan da za ta yi kuka, kuka mai yawa ko hakan zai sassauta damuwar zuciyarta.


A hankali ya ce "Shhh ya isa haka, daina haka nan ni ma za ki sani kuka" Ta ɗaga masa kai kawai tana sauke ajjiyar zuciya


Ɗago kai ta yi ta kalle shi idanunsa sun yi jajur shima ta buɗe ba ki za ta yi magana ya saurin rufe mata bakin ya ce "Yi shiru, na san me za ki ce yau dai ki kwanta ki huta ki kuma samawa kan ki nutsuwa kin ji?" Ta ɗaga kai a hankali ta kwanta ya ɗora kanta a cinyarsa har lokacin hannunsa na cikin nata ta riƙe da ƙarfi a haka ya shiga shafa kanta shi ma yana sauke ajjiyar zuciya.




Kasancewar azumi dab yake da shigowa domin bai fi saura kwana ashirin da wani abuba ya saka ya nutsa tunaninsa ga mutanen da ya dace a bawa zakka wannan shekarar. Kodayaushe tunanin inda zai sameta shi ne burinsa dukda yana son ya samu zuciyarsa ta kaɗaita da tunaninta al'amarin ya girmame shi ita ɗin kula da ita hakƙinsa ne kuma wasiyya ce a gare shi, babu wanda ya rage masa a duniya sai ita ɗin INA ZAI GANTA?


Bai ji ƙarar buɗe ƙofa ba sai sautin murya ya ji a bayansa a hankali ya juya da kyau a kan ƙafafuwansa walwalarsa ta ragu faɗan shi ya ƙaro fiye da kima. Ya rame ya faɗa amma kamar ana ƙara masa kyau da hasken fata ne.


"by now it is appropriate that you stop thinking" Ya faɗa yana jan kujera ya yi wa kansa mazauni har lokacin wanda yake magana da shi ɗin bai kalle shi ba, bai kuma tanka maganar shi ba


"Na yi magana da Hajiya akan dawowar su Legas"


"Why?" Baita ya watsa hannu ya ce "Haka na yi niyya, have a seat"


Zama ya yi saman haɗaɗɗiyar kujerar shi idanunsa a lumshe sosai ga wani irin ciwon kai daya kasa barinsa Baita ya ce "Yau ka yi niyyar shigowa office kenan?" Bai yi magana ba sai hannunsa da yake kaɗawa yana matse yatsun alamar yana azabtar da kansa ta haka ne duk miskilancin Baita amma Ustaz ya ce shi babansa ne a wannan ɓangaren


"Kwana biyu na shigo na baka labari friend na sameka cikin wannan yanayin, naga kuma bai dace ba koda na je gidanka da ƙyar ka saurare ni kuma ka ji rarrashi na"


"Baka gajiya da magana Tajj?" Baita ya ɗaga gira ya ce "Saboda Ubangiji ya bani bakin, kuma kai dai baka isa ina maka magana ka yi mini shiru ba, serious magana nake da ita"


"Ina ji" Ustaz ya faɗa yana ɗora ƙafarsa ɗaya saman table ɗin dake gabansa, can kuma ya miƙe ya nufi duguwar kujera ya kishin giɗa a kai. Baita ma ya tashi ya dawo kusa Ustaz, takaici ya saka Ustaz kasa magana domin ba zai iya da neman maganar Baita ɗin ba.


"Ina cases ɗin da nake maka magana akai? Mun kusa yin nasara domin mun samu an yi tracking number ɗaya daga cikin yaran" Ustaz ya jinjina kai sosai yake jin maganar amma idan aka kalle shi zaka ɗauka bai ma san abinda Tajj Baita ke faɗa ba. "Na je Kano na yi kwana biyu gida a hanyata ta dawowa Legas na haɗu da wata"


"Maman Nadra za ka yi wa kishiya kenan?" Baita ya haɗe fuska ya ce


"Ka taɓa ganin an yi wa wanda baya raye kishiya?" Ustaz ya ɗaga kafaɗa tare da juyawa baya Baita ya ce


"Tana buƙatar taimako na tsaya, ka sanni bana ƙaunar ganin mace cikin wani hali ina da tausayi sosai a kan mace wallahi tunda na ganta na ji ina son taimakonta, zafa ka ɗauka tsohuwa ce irin sosai ɗin nan amma wallahi yarinya ce kasan ina da fahimtar abu ba a banza na shiga police ba, ina son taimaka mata"


"Ka yi mana"


"Ban san ina take ba, taƙi saurarata sam wallahi"


Tsaki Ustaz ya ja yana miƙewa tsaye a hankali ya ce "Yanzu ka zo ka faɗa mini naje na nemo maka ita ne? Tajj ka ɗan saurara mini ba ruwana da ita taimako ko ni zan iya taimakawa amma ka daina mini maganar ko wacce mace"


Baita ya riƙe baki ya ce "Wonderful! Ai wallahi sai na saka an yi maka aure da zarar ka san mece soyayya zaka riƙe mace hannu bibbiyu"


"Uhm soyayya, kune baƙin ta, daɗi da zafinta ba wanda ban sani ba" Ustaz na faɗin hakan ya fice daga office ɗin da sauri Baita ya bi bayansa yana cewa "Wait, tell me something about your first love kasa ka a kai wa ka taɓa so? Ka zama ragu a soyayya kenan?" Ustaz bai kula shi ba ya yi waje abinsa.




Tunda ta sulale ta suma a wajan bata san mene ya sake faruwa ba, bata san adadin data ɗauka ba a hakan balle kwanaki sautin muryar data tsana a rayuwarta fiye da komai ita ta firgitar da ita ta buɗe ido da ƙyar tana dafe kanta idanunta sun yi mata nauyi saboda kumburi da jimawa da ta yi da rufe su.
"Tashi mun ƙara su" Ya faɗa yana yin wani irin murmushi ganin hakan shi ne kawai damar data rage masa. Kafin ta sake buɗe idanunta ta ji ana faɗin


"Giɗaɗon ya zo Giɗaɗo ya zo, yee mijin Hanne ya dawo sannu da zuwa Giɗaɗo" Yaran da suka baibaiye motar suka shiga faɗa tsakar kuma basu taɓa ganin mota ba haka suke shafa ta ana leƙuwa tare da kallon Ridayya. "Waye kuma Giɗaɗo?" Ta tambaya a zuciyarta


"Ki fito" Ta ce
"Ina ne nan ɗin?" Kai tsaye ya ce "Katsina. Ƙauyen Nahutu dake yankin Batsari"


"Me za mu yi a Katsina mene ya kawo mu ƙauye"


"Saboda nan ne mahaifata cibiyata kuma daga yau zai zama garin mijinki" Ridayya ta girgiza kai bayan ta fito daga motar ta ce


"Wallahi ƙarya kake ba zan taɓa zama a nan ba ina gidan Alhji Mahboon Dollar ɗin?" Sai kuma ta miƙe da sauri da sauri ta ce "Munafiki macuci azzalumi wanda baya tsoran Allah bambancinka da shaiɗan kaɗan ne"


A gigice Zameer ke kallonta koda wasa aka ce masa Ridayya zata ɗaga masa murya ba zai taɓa yarda ba, yau Ridayya shi take kallon cikin idanunsa babu tsoro balle shakka bata tunanin gargaɗinsa. Wani abu mai kama da faɗuwar gaba ya gitta masa ganin komai na yayewa a idanun Ridayya Mai son shi, babu son, babu tsoron, babu biyyar babu tattali da wannan tausayin nata zuwa gare shi lokacin na farko wani abu mai kama da fargaba ya matse zuciyarsa kar dai ta daina son shi? Ya girgiza kai da sauri a fili ya ce "Never!"


"Ridayya ni kike jefa da wannan maganganun?"


"Na faɗa waye kai banda MUNAFUKIN MIJI? Ka aure ni a caca ka ce kana so na saboda kai MUNAFUKIN MIJI ne, ka kwashe kayan ɗakina ka siyar ka ce kasuwanci za ka yi saboda kai MUNAFUKIN MIJI ne, ka ce a kano kake sai gamu a Katsina saboda kai MUNAFUKIN MIJI ne, mene laifina da zaka munafurci ni har haka? Laifi na kawai don na nuna maka soyayya? Ashe haramci ne nuna kana son mutum ka wulaƙanta ni ka wulaƙanta rayuwata ka gaggauta mayar dani Kano, wallahi ko zan kwana bola ban zama tare da kai"


"Idan kina da kuɗin mota ki koma tunda ai na san kin san hanya" Ya faɗa a dage amma zuciyarsa wani kalar tsinkewa take kar dai Ridayya ta sauya


"Gidaɗo ka zo ashe? Meke faruwa nan ne ake ta ɗaga haƙarƙari?"


"Gidaɗo? Wani munafurcin sunanka Giɗaɗo?" Ridayya ta ji gabaɗaya ta sare da al'amarin maza kuma da tsani ko wanne namiji gani take zai zama kamar Zameer ya kasance MUNAFUKIN MIJI. Da ƙyar aka rarrashe ta tana kuka sosai ganin kuma yadda yaran ƙauyen suka baibaiye ta kamar za su cinye harda masu leƙowa ta katanga babu ɗaurin ƙirji. Ta yi kuka mai isarta taƙi fitowa daga ɗaki komai aka bata bata ci bacci ya gagari idanunta ga wani irin ciwon kai kamar kanta zai rabe gida biyu da gaske bata da kowa bata da sauran gata ita fa dole Zameer Giɗaɗo ya saketa.


Cikin dare tana kwance ba bacci take ba sai juya kanta dake bala'in ciwo yake kuma ta dinga ganin Abbiey yana mata gizau yana kuka sosai sai taga wani ya zo ya janye shi.


Kamar daga sama ta ganshi ta yi masa banza ya ce "Hakƙina za ki bani na kasa jurewa na fahimci ke kaɗai nake samun nutsuwa a tare dake" Ridayya ta cije bakinta ta ce "To Bismillah" Ya yi watsi da suttura shi kamar dabba haka ya faɗo idan take ta yi saurin ta shi ya ce
"Ya haka ina jin kamar zan mutu" Ridayya ta waiga can ta hango fatanya ta ɗauka ta zage iya ƙarfinta ta maka masa akan abar........




Share and share and share as you can! Giɗaɗon Batsari da alama za mu je Nahutu jinya🤣🤣🤣






Na'ima Sulaiman Sarauta
Nimcyluv
08119237616
*✿ MUNAFUKIN MIJI 24 ✿*
Mikiya Writers Ass....




BRIGHT PENS🤙🏼free batch
Nimcyluv




Mirgina wa ya yi gefe jikinsa na rawa yana ƙoƙarin kurma ihu ya ce "Akan hakƙina za ki nakasa ni? Ki cuce ni ki cuci kan ki?"


Gabaɗaya muryar Zameer rawa take ganin yadda har yanzu take riƙe da fatanyar idanunta sun yi jajur jikinta na wani irin ɓari kamar mai shirin tayar da aljanu. Ya dake ya ce


"Ki bi a hankali, ni mijinki ne kuma zan ci gaba amsa sunan hakan har gaban abada, idan kina tunanin wani abu saɓanin nawa kin yi kuskure"


Ridayya da ƙyar take riƙe kanta, ji take kamar za a wurgar da ita ne, duk da gabanta dake faɗuwa da kuma girman igiyar auren dake kanta bai hana ta nutsa idanunta cikin nasa ba ta ce


"Giɗaɗo"


"Giɗaɗo kuma? Ina kika ji sunan nan? Mene haɗina da Giɗaɗo?" Har lokacin yana damƙe da jikinsa da Ridayya bata samu damar idda nufinta akan shi ba sai gefen ƙafarsa data makawa.


Jikinta duka rawa yake gani take tamkar babban zunufi zata aikata faɗawa miji magana, mijin da a yanzu komai da take ji game da shi yake yayewa. Da ƙyar tana riƙe jikinta ta ce


"Giɗaɗo ba shi ne sunanka ba? Giɗaɗon ƙauyen nahutun batsari ko?" Ta girgiza kai ta ce


"Daga Almajiranci ka dawo Zameer?" Ta zube a kan ƙafafuwanta zuriyarta na yi mata wani irin zafi da tafasa ta haɗe hannayenta biyu ta ce


"Yau ɗaya ka faɗa mini laifina a gareka don Allah, soyayyar dana nuna maka? Zaɓarka da na yi na watsar Abbieyna? Ko fara furta maka kalmar Ina son ka? Ko kuma budurcina daka amsa kafin aure shi ne laifina? Ko kayan ɗakina daka kwashe ka siyar shi ne nawa laifin? Ciyar da kai da nake yi kullum, ko kuma fifitaka a kan iyayena shi ne laifina? Ka faɗa mini laifina dana cancanci irin wannan cin mutumcin wulaƙanci da ƙasƙanci a gidanka, me na aikata har haka daya dace ka zame mini MUNAFIKIN MIJI? ka faɗa mini mana"


Miƙewa ya yi ta yi saurin miƙewa dukda rashin ƙarfin jikinta ga ciki. Zameer bai bari kalaman Ridayya sun yi tasiri a zuciyarsa ba ya yi murmushi ya ce


"Wane ya faɗa miki haka? Wanne munafukin ne har haka Ridha tsakanina dake za a shiga?" Kallonsa kawai take da juyayyun idanunta ba tare da ta ce komai ba.


"Ridayya kar ki bari zuciyarki ta yaudare ki, ba ki da wani waje da yafi wajena, ba ki da wanda ya fini a yanzu dole ki yi mini biyayya domin Batsari kike ba Kano ba"


Ya nufi inda take domin baya jin zai iya rabuwa da ita, abubuwan da yake ji game da ita ƙara fusgarsa suke, a gare ta ɗinne kawai yake jin haka dukda wani irin tsoro da yake shirin ruskar shi a yanzu. Ya gyara tsaiwa ya ce


"Ni tamkar ƙadangaren bakin tulo ne, a gare ni a ɓata ruwa, a bar ni a ɓata ruwa, ni ɗin dai ya zame miki dole. Na tuna miki da babban murya iyayenki sun rasu baki da kowa a duniyar nan sai ni, kuma ki hanani abinda nake so ki gane Allah ɗaya ne"


Kallonsa kawai take duk yadda hawaye ke ƙoƙarin fita daga cikin idanunta ta kasa saboda kada ya gane a yanzu iyayenta sune rauninta da rashin gatan da take da shi. Hannu ya saka ya fusgota kamar yadda ya zama yi mata wanda hakan ya zama tamkar Sexual violence a gare ta ko shi mijinta ne idan ba da ra'ayinta bane to tamkar zalinci ne, CUTARWA ne.


Kokawa suka shiga yi duk ya gigice da tsananin buƙatar ta ita kuma ta yi alƙawarin har gaba da abada idan akwai ba zai ƙara morar jikinta ba. Ta zage iya ƙarfinta ta gantsara masa cizon daya kusan kwashe masa fatar wuya ya saketa ta yi saurin fitowa daga ɗakin tana nufar ɗaya ɗakin da yake da wata mata a ciki.


Wani baƙin ciki ya tukare a wuyan Zameer ganin yadda ya ga samu kuma ya ga rashi amma ko zata mutu sai ya fanshe duka sauran ranakun daya biyo ta bashi. Ya yi tsaki ya fita.


Kuka take tamkar ranta zai fita numfashinta na tsarƙewa saboda yadda zuciyarta ke mata zafi da raɗaɗi, idan ta tuna bata da kowa bata da wanda zata raɓa balle ya ƙwatar mata ƴanci sai ta ji komai ya sare mata ta ji tamkar ta yi giving up ko ta ji kamar ta kashe kanta. Rana zafi inuwa ƙona, ruwan daya dake ka shi ne ruwa ta yarda rayuwa da ƙaddarata a tare Ubangiji ya samar da su kuma sun zama jinin jikinta yadda ba zata taɓa iya guje musu ba.


Ridayya ta yi kuka mai isarta gashi tun tayin abincin da aka yi mata taƙi ci babu wanda ya sake sauraren ta da wani abinci tamkar gudunta suke haka suke mata acting. Kasancewar su gabaɗaya fulani kowa kyakkawa farin tas da shi zai ya zama ta kasance kamar baƙar tukunyar da aka tuƙa farin tuwo a cikinta.


A hankali ta lumshe idanunta tana shafa cikinta da yake ta zungurar mata mara wata iriyar ƙauna mai ratsa fata, jini da ɓargo ke ratsa zuciyarta ta ɗauki soyayyar duniya ta ɗorawa cikin tana jin shi ne kawai ya rage mata a yanzu.


"Idan kin gama kukan tashi ki fita daga ɗakin baiwar Allah" Ridayya ta kalli matar, wacce ta yi saurin ɗauke kai tana cewa "Bismillahir Rahmanir Rahim"


A sanyaye ta miƙe tana dafa bango ta fita ta nufi ɗakin tunda tana da tabbacin Zameer ɗin ya fita. Tana fita Iyatu ta ce


"Shatu maza ɗakko turaren mayun nan ki turara a ɗakin nan"


"Mayu kuma Iyatu?"


"Su fa, au wai ba ki san mayya Giɗaɗo ya auro daga Birni ba can? Ayya ai mayya ce saura ƙiris ta ci ɗari ba ɗaya shi ya sa kika ganta baƙa ƙirin wallahi tallahi"


Shatu ta yi zuru don a duniya tana jin tsoron maye an ce cinye mutane suke tare da soye naman shi su cinye. "Mun shiga uku Iyatu kar ta suɗe mu"


"A'a kurwa kurr namanku ɗaci gare shi, da kun ganta ku gudu ai kuna ji ko? Kar ma ta kira ku kuje"


Giɗaɗo na fita ya yi waje can dandali jikin Hanne na rawa ta zo wajansa ta ce "Masoyi ka dawo wai da matarka? Da gaske ba zaka aure ni ba?"


Kallon tsaf ya yi mata kana ya ɗauke kai yana danna wayarsa hankali kwance tunanin yadda zai amshi takardun wajan Ridayya kawai yake domin sune plan ɗinsa da burinsa a yanzu. Hanne ta fashe da kuka Allah yana gani tana son Giɗaɗo tun tana ƙarama kuma shi ma yana sonta tunda ya je birni ya dawo ya wargatsa duk wata shaƙuwa da sukai. Ta zube ta ce "Giɗaɗo ka tausaya mini ni ce Hannen Nahutun Batsari ni ce Hanneka fa Giɗaɗo ko ka manta ne?"


Ya ja tsaki ya miƙe tsaye ko inda take bai kalla ba ya yi gaba a wajan gani yake gabaɗaya ƴan'kauyen ba sa'aninsa bane shi ɗin dabanne a cikin su.


Rayuwa ta yi wa Ridayya zafi duk ana ɓoye mata har ta fahimci kallon da suke mata na mayya bata uhm bata un'uhm bata walwala bata sukuni damuwa sun yi mata tsaye a zuciya ko bacci bata iyawa yadda taga rana haka take ganin dare idan an sammata abinci ta lasa wani lokacin ta kalle shi a Idanu ta nutsu ta gane mene asalin so ya ake jinsa a ƙirji da zuciya? Amma kwakwalwarta ta gaza bata damar yin hakan. Ta zama tamkar wata sauna gashinta kullum ƙara yawa yake kamar buzuwa. Yatsarta da take sha tun tana ƙaramar yarinya shi ta dawo sha yanzu. A haka watanni suka shura mata har zuwa wajan wata uku da zuwanta cikinta ya shiga wata na takwas.




Da sassarfa ya shiga sakkowa daga strains ɗin benen idanunsa a ɗan lumshe daga shi sai gajeren wando da wata milk ɗin Armless daya buɗe zip ɗin gabanta a ɗan gurguje yake sakkowa ɗin bakinsa kuma bai fasa ƙwalla mata kira ba.


"Mother mother mother"


Tunda daga kitchen take jiyo muryarsa a narke rikicinsa bata tsoro da mamaki yake hannunta duk fulawa ta fito a ɗan gigice tana mai tsayawa ganinsa zaune a ƙarshen step ɗin benen ya tanƙwashe ƙafa ta ce


"Sadauki lafiya kake? Wannan kiran fa?" Ya ƙura mata Idanu


"Magana za ka yi Sadauki ba kafe ni da wannan idanun naka ba" Hajja Azizat ta faɗa tana kallon tilon ɗan nata wanda take ji har ƙasan zuciyarta zata iya sadaukar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login