Showing 21001 words to 24000 words out of 190738 words

Chapter 8 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17319

Ustaz ɗin


_Ka ci-gaba da zama a matsayin Uba kuma jigo a rayuwarta, Bilal don Allah don Allah ka duba girman Allah ka bawa Mamana rayuwa mai kyau idan har mijinta bai kasheta ba, ka bata karatun data rasa a baya ka tabbatar bata sake kuka ba, sai yanzu na fahimci ba Ridayya ta yi kuskure ba, mune mukai muna muka bata lasisin zaɓar wanda ya fi mata muhimmaci a rayuwarta, Bilal, Muhammad-Bilal, Ustaz Ridayya taka ce amace yanzu a wajanka na bar maka ita halak malak har abada, da zarar mun dawo daka Rano duk zan raba auren su wanda bai yi mini wata rana ba, zan bata mijin da yanzu fitila ta haska mini da cewa; shi ne ya fi cancanta da rayuwarta, ba zance umarni nake baka ba, ba kuma zance saƙon zuciya zuwa zuciya bane, ina da yaƙinin cewa wannan ɗin tamkar WASIYYA ce, rashin tabbaci kawai nake da shi, Na barka lafiya yanzu zamu ɗauki hanyar zuwa Rano duba kakarku_


Tunda Ustaz yake a rayuwa bai taɓa shiga halin daya shiga irin yanzu ba, rana mafi dana sani a rayuwarsa shi ne ranar auren Ridayya, sai yanzu da wannan ranar take bin bayanta suka zama tagwaye. Zufa ta dinga yanko masa jiri ya shiga ɗaukarsa. Da sauri ya fara dubawa ko zai samu jirgin da zai kai shi ya isa Ranon? Cikin dare ko gama kimtsa wa bai yi ba ya nufi garin Rano. Mamakinsa bai shige ganin babu wani ahhali ko guda ɗaya ba, sai Hajiya wacce jikin nata yake da sauƙi ta sa shi gaba da tsokana ya fara tsofa babu aure.
"Hajiya su Baffa?" Ta ɗan yi sak sai kuma ta ce "Mun yi waya da su, tun kwanaki biyu baya ya ce sun taho amma har yanzu shiru" Mai ran ƙarfe ya ce "Babu mamaki ɗaga tafiyar sukai domin umarni na bayar a tattaro mini kowa a zo da shi, har da wannan yarinyar mai kama da baƙar tukunya rabo na da ita tun tana shan nono babu wanda nake kwaɗayin gani sai ita" Ustaz ya ce "Baku sake waya ba?" Ta ce "A'a, mene damuwar wai suna nan tafe In sha Allah" Ustaz ya girgiza kai sai kuma ya miƙe ya fice, number maƙocinsu ya kira ka ce ai kwanansu biyu da yini da tafiya, tashin hankali ya ƙara shigar Ustaz duk inda zai bincika labarin hatsari wanda baya fatan ace haka ɗinne ya yi amma ba wani labarai da suke yawo ba hatsari daga Kano zuwa Rano, Asibiti zuwa asibiti ya dinga dubawa har mutuware amma shiru.


Watan uku da yunƙurin zuwan Ridayya gida wanda Zameer ya yi munafurci ta fasa kenan. Tana zaune banda mugwayen mafarkai babu abinda take yi. Kwaɗon kwaki ne a gabanta wanda ta baɗa masa gishiri ta kasa ci, Zameer ya ɗaga labule daga waje yana ƙare mata kallo ya ce "Ga kayan wanki na nan" Kai kawai ta jinjina ya ƙanƙantar da idanunsa cike da masifa ya ce
"Ba'a yi mini magana da kai, nikam ba a yi mini ban so" A hankali muryarta bata fita sosai ta ce "To, kuɗin Omo da ruwa" Ya ɓata fuska ya ce "Nan fa ɗaya, ki ranta mini ruwa kuma ki shiga gidan matar can ki ja a rijiya" Da jemammun idanunta kawai take kallonsa magana ma bata ƙaunar yi ko kaɗan "Kana gani bani da lafiya ka tausaya mini mana, Khairiyya ta ja ruwan" Ya zaro idanu waje sosai ta ce "Tamɗijam! Lallai kin samu matsala ki duba fatarki ki duba da baby Khairy ɗaya ce? Farar fata ai bata san wahala ba, kuma ke aure kike bautar aure za ki fa Ridayya ladanki yana wajan Allah"
Ya girgiza kai yana riƙe ƙugu ya ce "Kambu to na saka Khairy jan ruwan guga ai Ubangiji ba zai yafe mini ba, saboda na ci zarafin kyakkawar halitta, ko aure ta yi mijinta ya ce ta ɗakko wallahi ubansa zan ci" Yar da yake magana haka take binsa da kallo zuciyarta fal mamakin abu biyu, baby Khairy, ko aure ta yi zai ci uban miji cike da damuwa ta ce
"Aure baya nufin bautar da mace Rayuwata, biyayyar gidan miji ai ba bauta ba ce" Ya ɗaga kafaɗunsa ya ce "A to!" Ya zuciya sai fita ta ce


"Ashe Khairy baby ce kuma yanzu?" Ya tsaya turus gabansa na faɗuwa ya ce "E, haka babanmu ke ce mata baby saboda mugun kyan da take da shi, she's so romantic"
Duk da ilimin Ridayya bai yi zurfi ba ta fahimci me yake nufi ya ce "Ki aro iron ki goge mini"
Ya fita domin burinsa bai huce ya ciwo maƙudan kuɗaɗen da aka zuba a caca ba. Zanin wata atamfarta ruwan huda ta yafa ta ɗauki bokici ta shiga gidan Zainaba. Zainaba na zaune tana kaɗa miyar abincin dare ta ce "Wai ikon Allah yau kuma" murmushi Ridayya ta yi dugun bakinta ya washe haƙora suka fito kamar ƴar shekaru 50 don tsofa.


"Mara ba lallai yanzu muke maganarki ni da Baban hajjo, yana jira ki bani labari na je na bashi har da mafarki na yi jiya" Ridayya ba ta yi magana ba. Can ta ce "Ruwan zan ɗiba" Zainaba ta ƙura mata ido sai bata ce komai ta ce "Zan saka Almajiri ya kawo miki, zauna kici abinci" Ta girgiza kai "Allhamdulillah na ƙoshi" Zainaba ta miƙe ta zuba mata tuwon samo har da bushsshen kifi ta shimfiɗa tabarma ta ce "Yau banga abinda zai saka ki fita kibar gidan nan ba" Dole Ridayya ta zauna ta fara cin tuwon hannu baka hannu ƙwarya ta kawo mata kwaɗon zugala domin jinin jikinta ya dawo harda yanka mata dafaffen ƙwai kafin ta gama ci Almajiri ya fara kaiwa Ridayya ruwan.


"Ciki ne dake Ridayya"
Ridayya ta zaro Idanu waje ta ce "Ciki kuma?" Murmushi kawai Zainaba ta yi ta ce "Wallahi ciki gare ki na jima da fahimta, kamar yar da na fahimci Khairy ma ta haɗiyi wake" Ridayya bata gane irin wannan maganganun ta ce "Haɗiyar wake kuma? Kamar yaya" Zainaba ta ce "Za ki gani ai shi ɗan duma ne watarana zai fallasa kan shi, ƙwai zai fashe warinsa ya adabin uban kowa musamman mamallakinsa" Ridayya ta yi shiru "Ki bani labarin tunda kin shigo mini yau"


"Wannan labari" Zainaba ta ce "Shi fa, wallahi na ƙagu" Ridayya ta lumshe idanunta hawayen dake ciki ya sakko a nutse ta ce "Ta ina zan fara? Labarin Ridayya mai girma ne, girman da ko wacce ɗiya mace musamman budurwa da matar aure jinsa zai yi mata amfani" Ta yi jim "Rayuwata a wajan Amma zan faɗa miki? Ko zamana da Abbiey zan labarta miki? Ko kuma juya mini baya da mahaifina ya yi ne zai zama farkon labarin ko haɗuwata da Zameer?" Zainaba ta kawo kujera ta zauna ta yi taƙumi ta ce "Fara mini ta farko yadda zan fahimta" murmushi kawai Ridayya ta ce "Taya zan ba ki labarin abinda bana duniya ya faru sai dai abinda aka bani labari zan iya" Zainaba ta ce "Yawwa ai farkon zai fi citta ƙila shi ne soyayyar Baffa da Mami ko?"


Ridayya ta ce "Da farko dai...." Da sauri ta yi shiru zumbur kuma ta miƙe jikinta na rawa da ɓari ganin Zameer a kanta Zainaba ta ce "Ya zaka faɗo mini gida babu umarni kamar ana zaman bariki" Bai kula Zainaba ya finciki hannun Ridayya tana turjewa ya fara janta a ƙasa, maƙota duk suka fito har da mazajensu babu wanda ya iya dakatar da Zameer, Zainaba ta dinga ƙundumawa Meer zagi tana faɗin "Tsinanne haihuwar asara Allah ba zai bar ka ba, In sha Allah Ridayya ta kusa rabuwa da kai faƙirin banza cima zaune" Maganganun Zainaba kamar saukar dalma haka Ridayya take jinsu a zuciyarta, jin yar da take tsinewa mijinta da yadda take fatan aurenta ta mutu baƙin cikin haka ya saka Ridayya rushewa da kuka. Zameer ya rufe ƙofa baka jiyo sautin komai sai ihun Ridayya da saukar bulalar wayar caza "Iskancin banza da wufi ni za ki kawowa ɗan iska har gida, wato kema Idanunki ya buɗe abinda na gudu kenan na datse karatunki, shi ne za ki shigo mini da kwarto har cikin gidana?" Ridayya tuni numfashinta ya tsaya Khairy na tsaye ta ce "Shi ya sa ban taɓa faɗa maka ba ai wallahi kar ta ce sharri nake mata, yanzu ai ka gani da Idanunka" ran Zameer ya ɓaci domin baya wasa da duk wani abu daya shafi alaƙar gado tsakaninsa da Ridayya cikakkiyar gamsuwa a wajanta yake samu dukda bata tsinana masa da uwar komai, kamar ruwa haka take zama, she's not romantic at all. Amma baya jin zai iya sharing ɗinta da wani banza ya shige ɗaki Khairy ta bi bayansa suka rufe ƙofa Ridayya na shimfiɗe kamar gawa.


Hajiya da Mai ran ƙarfe ne suke jijjiga Ustaz amma ina ya jima da fita daga hayyacinsa, a gigice Bintalo ta shiga yayyafa masa ruwa amma ko motsi bai yi ba, Hajiya ta fara kuka wiwi don a duniya tana ƙaunar Ustaz ta jima bata taɓa ganin mutum mai zurfin cikinsa ba, taurin zuciya kafiya da na ci da kuma haƙuri da kawaici. Firfita take masa tana shafa kansa "Innalillahi! Mene shirin faruwa ne mun shiga uku" Mai ran ƙarfe ya ce "Maganin shiga uku Allah, ciwon Ustaz ne ya tashi yi ta yi masa firfita, Bintalo ci-gaba da zuba ruwa a kansa"
Gabaɗaya suka rufo akan Ustaz su shafe mintuna kafin ya sauke ajjiyar zuciya idanunsa rufe bakinsa na motsa wa shi kaɗai ya san me yake cewa "Bilalu lafiya,ina dalilin wannan ciwo naka?" Ya sake rufe idanu da tunani inama ya buɗe idanu yaga mafarki yake. Hajiya ta riƙo fuskarsa ta shiga girgiza shi ta ce "Yi magana Bilal buɗe Idanunka"


"Baffa, Abba, Mami, Amma, Junaid, Balkisa, Zuhura, Zainura, Aliyu, Usman, Umar, Abubakar...," Ya kasa ƙarasa maganar Hajiya ta ce "Mene ya same su? Suna ina yi mana bayani Ustaz" Nutsuwa ya tattaro ya aza bisa gangar jikinsa ya daure ya ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!"
"Ustaz wai mene haka?" A hankali yana fusgar numfashi ya ce "Ba a gansu ba, suna mace suna raye tsayin watanni..." Kafin ya ƙarasa faɗa Hajiya ta yanke jiki ta faɗi.


Zameer na zaune shi da Gaza ya ce "Zameer baka son yarinyar nan ka sakar musu ƴarsu?" Wani irin murmushi ya yi ya ce "Hauka ma kenan"
"Kamarya Hauka mene fa'idar zamanku aure ba soyayya ba kulawa" Zameer ya gyara zama ya ce "Tunda nake a rayuwa ko da second guda ban taɓa jin son Ridha ya gitta ta zuciyata ba, ban taɓa ji ba"


"Than, you have to divorce her" Ya ɗaga kafaɗa ya ce "Shi ne ba zai iya ba, domin akwai amfaninta yana nan zuwa musamman yanzu dana fahimci ciki gare ta" Gaza ya ce "Ikon Allah, mene shirinka sanar dani please" Murmushi kawai ya yi ya ce "Babar Ridayya na da kuɗi sosai da wanda aka bar mata gado da wanda ta mallaka nata na kanta, na saka an duba mini wajan ƊAN GADO, Malamin ya iya aiki"


"Kenan asiri ka yi wa ƴar mutane" Ya girgiza kai ya ce "Ko kaɗan wallahi ban taɓa yi wa Ridayya asiri ba, ai ba zan ɓoye maka komai ba nasan dai ina zuwa ana yi mini duba, plan ɗina shi ne da zarar iyayenta sun baza zata mallaki kadara nai yawan gaske, zan buƙaci ta bani na juya mata amma ko wanne ta yi sa hannu da sunana" Dariya Gaza ya yi sosai ya ce


"Saboda ita bata da ilimi" kai tsaye ya ce "Ina ta ganshi, ai dabara na yi na datse mata karatu saboda karma idanunta ya buɗe ta ce zata iya juya kadarorinta, tana gama secondary a ajinta na farko na jam'i na datse karatun idan ina raye ai ba zan bar Ridayya ta yi ilimi ba balle ta mallaki wani abu nata na kanta, soon rabata da garin nan"


"But You don't love" Ya ɗaga kafaɗa ya ce "Ita ai tana so na, zata iya mutuwa saboda ni soyayyarta a gare ni ita ce rauninta na fahimta, yanzu ma goga take mini" Sallama sukai yi tare nufar gida.
Kasancewar bata samun bacci sosai ya sa tana tsaka da goga bacci ya ɗauketa. Hayaƙi ya cika ɗakin da sauri Zameer ya shigo gani ya yi sabuwar shaddar shi ta babbake Allah ya sa dutsen bai buga ba. Ya kalli Ridayya ya kalli kayan cikin ɓacin rai dutsen da ya yi jajur da wuta ya ɗauka ya manna mata shi a fuska. Ihun a zaba ta saki da sauri ta shafa fuskarta sai fata ta biyo hannunta rabin fuskar ya kwailaye kafin ta dawo hayyacinta ya yi ball ta ita ya taka mata ruwan ciki azaba ta saka ta saki fitsari da tusa a wajan ya juya ya fice daga cikin gidan, kuka ta kasa ta riƙe cikinta sai birgima take a wajan har gari ya waye tuni kamanninta suka sauya. Ta fito da ƙyar zata shiga banɗaki ta ji Khairy na waya tana cewa "Na je likita ya tabbatar mini ciki ne dani" Ridayya ta nemi ciwo ta rasa ta saki butar hannunta ta nufi kitchen wata sharɓeɓiyyar wuƙa ta ɗakko kai tsaye ta nufi ɗakin Khairy da wuƙar a hannunta....




Idan naga comment gobe kuga posting da wuri.


Muna godiya da zaɓar BRIGHT PENS🫶🏼🤙🏼


*✿ MUNAFUKIN MIJI ✿*
Nimcyluv@Arewabooks


Page 9
BRIGHT PENS🤙🏼 free batch




*HAUSA AFFILIATE MARKETING🥰👇🏼*
https://chat.whatsapp.com/LvflCjMI3U5IfUHobHzudk








Khairy na kwance akan gado daga ita sai gajeren wandon Zameer, tana danna waya tare da ƙyaƙyacewa da dariya. Kamar daga sama taga Ridayya ta faɗo cikin ɗakin tana huci kamar wata mahaukaciya, jiri sai neman ka da ita yake neman yi amma ta turje.


Tsirarar wuƙar ta nunawa Khairy tana nufar wuyanta da ita, idanunta jajur hawayen baƙin ciki na zuba daga cikin idanunta, na tsananin kishi da soyayyar Zameer, imagining take ita cikin ya tabbata yana da kusanci da Zameer, to; a cikin biyu za a yi ɗaya, ko dai ta kashe Khairy ko kuma ta kashe kanta ta huta.
"Kar ki mini ihu a ɗakin nan, daga ni sai ke ba ki da wani mataimaki" Ridayya ta furta tana sake nunawa Khairy wuƙar. Ganin haka yasa Khairy rikicewa tsoro ya ɗarsu a zuciyarta. Bakinta na rawa da ɓari ta ce "Na shiga uku me na yi miki da zafi haka Anty Ridayya? Me ya sa kika tsane ni?"


"Riƙe kalamanki marasa daraja a wajena Khairy, bana buƙatar duk wasu shaci faɗe naki, idan yau ki kaga ban kashe ki ba, to wallahi gaskiya kika faɗa mini" Ganin al'amarin Ridayya da gaske ne domin ta fara ƙoƙarin fita daga hayyacinta, maganganun fitar da kansu kawai suke ba tare data shirya ba ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Kisa kuma? Kashe ni za ki yi, me na yi miki kina cikin hankalinki kowa?" Ridayya ta yi dariya sosai dukda cewa bakinta a waskace yake, fuskar ta tattare saboda ƙona ta da Zameer ya yi, muninta ya sake bayyana ƙarara idan ka kalli fuskar Ridayya ba za ka so ka sake kallo ba.
Ridayya ta ce "Idan na yi miki lahani, na saɓa miki kamanni tare da ji miki rauni na kashe ki za ki gane ban haɗa hanya da dawanau ba balle a laƙaba mini sunan mahaukaciya, Khairiyya ki faɗa mini cikin waye a jikinki, mene ya haɗaki zama da ɗakin mijina bayan ga naki can? Ina dalilin sanya sutturar mijina bayan ta haramta a gare ki, gajeren wandonsa, tsaraicinsa ne" Lallai daman an ce; mai haƙuri bai iya fushi da tara mutum ba. Khairy ta rikice ta rasa da wanne kalamai za ta yi amfani da su wajan shimfiɗa ƙaryar da zata tseratar da ita, daga haukan Ridayya domin ta gama tattarawa tare da azata a gurbin sabbin masu taɓin hankali.


"Ci...ci...ciki kuma? Ni mene haɗina da ciki? Wallahi....," Kafin ta ƙarasa maganar Ridayya ta sauke mata wuƙa a gefen hannunta, nan take wajan ya dare jini ya fara zuba. Khairy ta zunduma ihu tare da faɗin.
"Wayyo Allah, mahaukaciya ce wallahi mahaukaciya ce jama'a a kawo mini ɗauki" Ridayya ta sake sheƙewa da dariya ta ce "Ai na faɗa miki, kashe ki zan yi muddin ba ki faɗa mini cikin waye a jikinki ba"
Suka shiga zagaye ɗakin, Khairy na riƙe da hannunta tana ihu a kawo mata ɗauki, amma tsit kake ji, tamkar malam ya ci shirwa. "Khairiyya kenan ki daina ɗauka ban san me nake ba, na sani ni yarinya ce, you're smarter than me, tunaninki da nawa ba ɗaya bane ba komai nake ganewa ba idan, idanuna suka makance, wallahi a yau ko za a kashe ni, ko zan tafi gidan yari sai kin faɗa mini gaskiya ko na kashe ki a nan, idan ya so a yi jana'izarmu tare Ubangiji ya yi mana hisabi ya kuma tantance mai gaskiya" Khairiyya na kuka sosai, bawai don Ridayya ta fi ƙarfinta ba, saboda makamin dake hannunta ba a wasa da mai wuƙa.


"Bani da ciki, mene zai haɗani da ciki kuma? Ki yi mini rai ni gidanki ma zan zo na tattara na bar miki, idan hakan zai zama farin giki a gare ki, da nutsuwar zuciyarki"


"Hehehe ki je ina? Ai ni dake mai ƙarfi yau shi zai ƙwaci kansa lashakka, ki bar gidan Ridayya matar mijin Zameer ban miki lahani ba? Ai ƙarya kike, Har ka tuna mini, an ce da mahaukaci ba ka duka, har ke ce kike cire kaya a gaban mijina ko? To bari na cire miki nono ɗaya sai naga gobe me za ki nuna" A gigice Khairiyya ta ce "Na shiga uku wallahi kin haukace, banda haka ni da nake ƙanwar miji meye na ɗora zargin naki akai na?" Ridayya ta ware idanu ta ce


"Au, ba rami mene ya kawo rami? Kin ji na Amjat zargi? Haka tara, in ji kishiyar mai mageduwa, ai shi ɗa na kowa ne, ƙanwar miji ai ƙanwa ce, dole na ba ki tarbiyya saboda gudun bakin jama'a"
Khairy ta ce "Don Allah ki barni na fita, na je gidanmu babu wani ciki a jikina" Ridayya ta ce
"Kin san Allah, wallahi ba zan barki ba, kowa ya yi maka kan kara, yi masa na itace" Da gudu Khairy ta juya ta nufi wajan ƙofa ta sunkuya zata buɗe,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login