Showing 111001 words to 114000 words out of 190738 words

Chapter 38 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17323

ɗin shi suke kallo matsayin mataimaki. "Muhammad ka faɗa mini wacce kalar ƙofa kake so, wacce zata haska ɗakinka ko a ina take zan yi iya ƙoƙarina wajan ganin ka mallake ta, ko bata son ka zan saka ta soka" Ya yi shiru kansa na harbawa, baya son yi wa Ridayya dole ko kuma amfani da damar shi.
"Babban mutum ka yi magana shiru baya magani" Mai ran ƙarfe ya faɗa yana riƙe kan Ustaz shi kansa ya firgita da yadda jijiyoyin suke harbawa. "Zurfin ciki ba shi ne mafita ba, wacece? Ka faɗa, yi magana"


"Oum....," Sai kawai ya girgiza kai ya miƙe yana shigewa toilet. Hajiya ta fashe da kuka ta ce


"Mun shiga uku wanne irin hali ne wannan? Miskilanci da riƙe damuwa kar zuciyar yaron nan ta buga"


"Ba zata buga ba in sha Allah. Ƴar rainonsa yake so na jima da fahimta musamman a dawowarsu na so ya furta ya ce Ridayya yake so da wallahi tallahi a yau Ridayya ba zata kwanta ba sai da igiyar auren Muhammmmd a kanta". "Babbar magana wannan shirgegen ai ya mata girma, kuma duk shekarun daya kwashe sai ya auri bazawara kuma mai haihuwa? Ina masa kwaɗayin samun budurwa"


Mai ran ƙarfe ya ce "Mata mata ku dai tunaninku na musamman ne, shi so na gaskiya ba ruwansa da wannan idan kuma don wannan yake sonta ai daya haƙura yanzu. Ko a baya dan dole ya aurar da ita" Hajiya ta ce
"To yanzu mene mafita? Kawai tunda mu mun fahimta a aura masa ita mana ai ɗan'uwanta"


"Bana son Ridayya ta fahimci alfarma ta yi wa Babban mutum, ita a yanzu bazawara ce tana da ikon zaɓawa kan ta wanda take so ne, kuma ina son Muhammmmd ya san ba a komai zurfin ciki yake da amfani ba, mutum kan iya rasa abubuwa da dama idan har ba zai buɗe zuciyarsa ba, ki bari sai ranar daya furta da bakinsa ni kuma a ranar zan nuna masa gata kuma ya je ya gina soyayyarsa a zuciyarta, ya fara nuna mata akwai halarcin aure a tsakaninsu ya kuma nuna mata bashi ya haifeta ba"


Tun ranar Ustaz ya ƙauracewa ganin Ridayya baya zama a gidan sosai ita kuma kullum sai ta fito ko zata ganshi abin ya fara damunta ta yi ta kuka ita kaɗai saboda ya yi aure ya daina son ta? Ashe mata tafi ƴa daman? Wani irin zafin Mardiyya take ji a ranta ita har yanzu ta kasa yarda cewa matarsa ce wannan ai cin amana ne kuma tun ranar data gansu rungume da juna bata sake yarda taga Mardiyya ba, bata da abin faɗa mata. Gefe guda kuma suna waya da Sadauki sosai a wayar Hajiya.


Ustaz ya fara neman appointment da likitan kwakwalwar domin a tabbatar ko tana da Mental Illness. Hakan yasa cikin gaggawa ya fara neman hanyar zuwa asibitin Psychiatry domin samun ganin Neurologist a san mene matsalar.


Rana tsaka ya saka Hajiya ta kira Ridayya bai ce mata komai ba ko gaisuwarta bai amsa ba. Bayan tambayoyin da likitan ya yi mata ya buƙaci yi mata photo na ka da yin gwaje-gwaje na kamar su CT scan (Brain hemorrhage) MRI (Stroke, Brain tumor) da EEG (Epilepsy) bayan duk an yi komai ya ce Ustaz ya dawo shi ɗaya washegari Ridayya dai da idanu da kunne take jin komai, ya shige da ita shopping ta baza idanu tana kallon garin Legos gwanin sha'awa abayas ya siya mata underwears komai size ɗinta perfumes, kalar man da aka rubuta mata a bela dake ya ganshi a ɗakin dake gidansu Tajj ribbons, flat shoes. Har sun gama komai taga wasu saitin kaya na maza masu kyau amma ƙanana ta ce


"Abbiey ka siyi wancan zai maka kyau" ya kalli kayan kafin ya yi magana ta ɗakko ta haɗa da wata hula p.cap da wani baƙin glasses ya fahimci Ridayya ita kyalekyale kawai ta sani bai kulata ba ya biya kuɗin.


Har bayan mota aka kai musu ya nufi gida ko ciki bai shiga ba ya juya ya fita yana buƙatar shan iska da samun nutsuwa.


A can Batsari mahaifin Zameer Giɗaɗo ya nema masa auren Hanne cikin ƙaramin lokaci aka ɗaura aka ware mata ɗaki a cikin gidan ta tare kasancewar Allah ya jarabceta da son shi amma duk ya siri mata auren ma fin ƙarfinta akai kullum cikin dare rufe ƙofa take.
Da ƙyar cikin sa a ya samu ƙofar a buɗe, jiki na rawa ya nufeta ta yi saurin ja baya ta ce "Saurara meye haka kamar wani daƙiƙi zaka yo kai na haka dabba ce ni da zaka faɗo mini?"


"Ke kisan da wanda kike magana dole ta saka zan raɓeki a rashin matata ne"


Hanne ta yi shewa ta ce "Wacce matar bayan wacce ka saka kana da wata mata ne ko jikin karuwar taka kake marari? Ashe zuwa birnin na banza ne"


Ya haɗe fuska gabansa na faɗuwa ya ce "Yaushe na saki matar tawa? Kuma ko ki yarda ki karki yarda dole na amshi hakƙina sadaki na biya, ki yi a hankali kafin na tafa miki rasit"


"Ai na zame maka ciwon ido wallahi zama dani dole mutukaraba takalmin kaza, na zama ƙadangaren bakin tulo, ni ba irin Ridayya bace ina da gata yanzu za a ci ubanka hankali kwance"


"Zagina ki kai fa?"


"Allah ya yi mini tsari da zagin mijin karuwa"


Ya sauke murya ya ce "To na ji, amma mu je mu raya daren aurenmu, haba Hannene Hanneta"


Gabaɗaya laɓɓanta ke fusgarsa yadda suke jajur kuma bakin ƙarami sai ya ji yana sha'awar sumbatar bakin. Hanne ta ce "Ni wanka zan yi ma kuma ina buƙatar cin kaza"


Kaya ta cire gabansa ya faɗi Hannen da yake rainawa ita ce haka? Har wani yawu yake haɗiyewa daman a matse yake kullum sai ya yi mafarkin Ridayya da yadda yake jinta zam idan yana tare da ita sai ya ji kamar ba ita bace baƙa mummunan ba. Kawai baya ganin darajarta tun ranar data bashi kanta kuma daman ba wani sonta yake ba.


Hanne ya juya ta sake juyawa tana ƙara rura wutar dake tashi a jikin Zameer idanunsa a rine ya ce "Bari na je na kawo miki kazar, amma ki bari ko ɗan bakinki na sumbata"


Ta zare Idanu ta ce "Hoɗijam! Ni na haɗa baki da kai Allah ya sauwaƙa maza ka kawo kazar dai na baka hakƙinka" a gurguje ya je ya kawo kazar bayan ta cinye tas ta ce "Ya leɓo mata ruwa a tulo ya ɗan fi san yi" Kafin ya dawo ta rufe ƙofa ta sha ruwa abinta kaza ta kwanta ta bi lafiyar katifa sai bacci. A daren Zameer kasa bacci ya yi kamar ya haukace ciwon ciki dana mara banda gizau babu abinda jikin Ridayya ke masa, yasan kuma duk inda take tana hanyar dawowa gare shi. A suba ya haɗa takardu da nufin zuwa Kano siyar da ko filaye uku ne daga cikin filayen Ridayya tunda yanzu shi ne yake da iko da su. Bayan ya shirya ya baza shaddar daya zo da su ya haɗa komai ya duba inda ya ajjiye kuɗin mota suka je nemi inda ka ajjiye ba kuɗi babu alamar su sama sukai ƙasa sukai sai Allah gashi bayan su bashi da ko taro.


Gabaɗaya parlourn ya cika da mutane kowa na familyn yana nan banda mutane huɗu, Ustaz, Ridayya, Hajiya, Mai ran ƙarfe. Cikin fara'a da farin ciki Baffa ya ce


"Allahamdulillah komai ya yi farko yana da ƙarshe, na so ba yanzu zamu bayyana ba amma na kasa jurewa ina buƙatar ganin yarana gabaɗaya su biyun, farin cikin haɗuwar su waje guda ya saka na sa a ka yi mini saukar Alkur'ani akan Ubangiji ya kawo mana ƙarshen komai ya daidaita tsakaninmu har na rabawa kowa alawa da goro to bana komai bane sai na farinciki. Kuma gabaɗayanmu zamu haɗu muje Lagos zuwan bazata"


Junaid ya ce "Baffa ai bamu san ina suke a Lagos ba" Alhji Mansur ya ce "Tajuddeen ya sani"


Gabaɗaya suka kalli Tajj dake shigowa da mamaki Yaya Balkisu ta ce "Tajj ya san komai?"


"Babu abinda ya sani, infact bai san Ridayya ba bai kuma san muna raye ba, daga baya na buƙaci ganinsa da neman taimakonsa. Ni na bashi picture ɗin Ridayya a nan yake ce mini ya taɓa ganinta sau ɗaya mota ta kusa bugeta, har ya bata kuɗi taƙi amsa daman ita ce Ridayya ɗin? Shima ta tsaya masa a rai haka kurum yana son taimaka mata tun daga ranar ya tsananta bincike a kan Ridayya har zuwa sanda ya je Katsina ya bigeta nine farkon wanda ya faɗawa, kuma na shaida masa kar ya nuna ya santa ko yana da alaƙa da wani nata, duk kuɗin daya kashe mata ni na bayar har wayar daya siya mata domin ina buƙatar na fara ɗaukar ɗawainiyyarta tun yaushe, kuma na hana shi faɗawa Ustaz, nine da kaina na saka ya dinga ɗora photon ɗanta mai sunan Babban mutum a status, kuma ta hanyar ɗora photon muka jawo tunaninsa zuwa Kano akai-akai har mutuwar aurenta na sani, ban san dai abinda ya kaita Katsina ba shi ma Tajj bai sani ba, kuma shi ne ya faɗa mini Ustaz ya ɗauketa sun tafi Lagos to in sha Allah a gobe muma zamu ɗauki hanya gabaɗaya kuma ta jirgi domin ina fargabar shiga mota tafiya irin wannan akwai ban tsoro iyali guda"


Barrister ya ce "Wannan haka ne kuma na yabawa ƙoƙarin Tajuddeen sosai samun aminin ƙwarai kamarsa yana da wahalar gaske mun samu taimakon ƴansanda na rashin binciken mutuwar taku"


"Yanzu a kan ganin Ridayya zaka kashe maƙudan kuɗaɗe na jirgi har wajan mutum goma sha?" Baffa ya kalli Ammi ya ce "Wai Maryam lafiyarki lou ya ci a ce kinfi kowa murna da dawowar Ridayya tunda kunfi kusanci da ita a kan mahaifyarta, kuma ko nawa na kashe a kan Ridayya ban faɗi na yi mata abinda ba lallai ta yafe mini ba, kuma Ubangiji ya hure mini donna kyautatawa iyalina ba laifi bane"


"Haka ne murna ce ta mini yawa Allah ya ƙara arziƙi da wadata, na ce ka haɗa da Burhan shima zai yi farin ciki idan yaga Ridayya". "Babu komai a je da shi ɗin"


Tajj ne ya kira Ustaz ya ce gobe kar ya fita zai zo da mutane masu muhimmanci.


Ustaz ya shaidawa Hajiya zuwa Tajj don bai ɗauki baƙin wasu serious ba, bashi da appointment da kowa a ranar ma yake ƙoƙarin zuwan jin sakamakon gwajin da akaiwa Ridayya.


Yana zaune saman kujerar parlourn ɓangarensa system ce a gabansa yana ɗan operating ɗinta Mardiyya ta shigo sai baza ƙamshi take ya sha atamfa Valisco da ɗauri ta yi sallama bata da tabbacin ya amsa domin bata ji ba, amma ta san ba zai wofintar da sallamar ba. Ta ƙarasa ta zauna tana cewa


"Barka da yamma ka shigo ashe?" Ya jinjina kai bai kalleta ba. "Na kawo maka abincin nan? Tuwon Alkama ne idan ba zaka ka ci ba to ka faɗi abinda za a dafa maka"


"No" Kawai ya ce mata a hankali itama idanunsa har yanzu a kan system


Wani irin Mardiyya take ji ta ce "To shayi fa? Ko fura naga kana so"


"Injiwa?"


Sosai ta ji daɗin maganar tasa har ƙasan zuciyarta ta ce "Ai nasan duk abinda kake so a wajan ƴarka Ridayya na ji tun kafin ma ta yi aure kullum sai ta bani labarinka da abinda kake so na abinci da kayan sawa, ka san har cewa ta yi shigarka bai taɓa burgeta ba, kullum kana saka jallabiyya da hirami kana carbi Ustazai basu san komai a soyayya ba, gabaɗaya baku san mene soyayya ba shi ya sa ba zata iya auren Ustaz kamarka ba"


Ya ɗago kai ya kalleta sai ya ɗauke ganinsa zata sake manana ya nuna mata hanyar waje "Idan ina buƙatar abincin zan sanar"


Sai ta ji ba daɗi ta ce "Don Allah ko baka so na ka yi ƙoƙarin kallona a matsayin matarka Ridayya kake so kuma kaga yanzu ai ita bazawara ce, ka ji tausayina da gaske ni ina sonka"


Ya kashe system ɗin ya ture yana jingina da kujerar ya kalleta gabaɗaya ji ya yi hasken fuskarta yana shigar masa idanu ta masa dau da yawa ta saka wani jan jambaki ya ƙara haska fuskar baya son irin haka amma kalar nata halittar kenan.


"Kuma daga faɗa miki sai ta ce ki faɗa mini? Ko kin faɗa ne domin samun fada ko na ji zafinta? Look Mardiyya kar mu fara haka dake ok, kuma da ban yi accepting naki as my wife ba da kin jima a Kano na dai faɗa miki bani da lafiya ba zan iya amfanar ki da komai ba, na gode da soyayya i appreciate it"


Miƙewa ta yi zata durƙusa daidai nan Ridayya ta shigo hannunta riƙe da wayar Ustaz daya manta kuma a lokacin ta saka sabuwar abayar daya siya mata ta yi rolling ta yi kyau. Da sauri Mardiyya ta zauna saman cinyar Ustaz tana ɗora hannunta a ƙirjinsa dake buɗe.


Kalmar A ce ta maƙalewa Ridayya hannunta ya shiga rawa wani irin abu mai zafi ya shiga yawo a ƙirjinta numfashinta ya tsaya cak. Tuni idanunta ya cika da ƙwalla sai ta ji wani irin haushin Ustaz ya kamata daman tuni ta ji bata ƙaunar ganin Mardiyya, zata juya ya ce


"Ridha..."


Ta tsaya ta kasa juya ji take kamar zuciyarta ce zata fashe ganin Mardiyya zaune a cinyar Ustaz wacce rashin kunya ce wannan? "Ridayya ƴarmu kina ji Abbiey ɗinki na kira?"


Ta juya Ustaz yaƙi kallonta ita kuma shi take kallo Mardiyya ta miƙe tana shafa sumar Ustaz tare da sumbatar gefen fuskarsa ta ce "Bari na baku waje Baby ƴarka kunyar ganin babanta take haka, idan kun gama na dawo na shafa maka mai nima bari naje na sake sabon wanka"
Ridayya bata san yaushe Mardiyya ta fita ba, to daman idan aka yi auren haka ake? Ya ita bata taɓa sani ba kuma ba haka Zameer ke mata ba. "Kawo mini wayar ki je, kin kuri matata"


Wayar ta ajjiye saman madubi ta juya tana sakin kuka ya girgiza kai ya ce "Rigimammiyya"


Tunda ta fita take kuka da ƙyar Sadauki ya rarrashe ta ya ce "Haba Shanshan kamar wacce a ka yi wa mutuwa?"


Ta share ta ce "Ka zo lafiya? Ya mother da hanya"


"Allahamdulillah hanya kuma kamar wanda ya yi tafiyar mota?" Ta yi murmushin yaƙe ya zuba mata Idanu ya ce


"Wani ya taɓa ce miki colour ɗinki me kyau ce?" Ta yi jim sai ya ce


"Kamar an taɓa faɗa na manta dai" Ya kashe mata Idanu ya ce


"Ko an faɗa bari na maimaita i love your skin colour Shanshan, na jima ina sha'awar kalarki kin san yanzu mata duk sun lalace da shafa mai su yi ta wari sai ka rasa baƙa kuma ka fara farar asali amma ke normal komai naki abin so ne natural halitta ba fake ba, i love You my fiance"


"Na gode"


"Meye wani kin gode, ku Hausawa kuna da matsalar you can't say you love me too?"


"Kunya nake ji"


"Ridayya" ta amsa ya ce


"Ban san yaushe ne ba amma san nasan kawai ina son ki ina buƙatar rayuwa dake har ƙarshen numfashina kar ki mini wasa da hankali domin dana rasaki gwara kowa ya rasaki, na rantse miki da Allah sai na mallake ki"


Gabanta ya faɗi ta ce "To mene abin rantsuwa kuma?"


"Ki faɗa mini kina so na, zaki aure ni? Zan turo Daddy wajan Abbiey ɗinki"


"Kai ba naka bane" Ya yi shiru ta ce "Uhm"


"No karki mini wata fassara fa, nawa ne mana ai wajansa zani neman aurenki just tell me kina so na?"


Ta miƙe zata gudu saboda kunya ya yi saurin riƙo ta yana tashi tsaye hannunta duka biyun ya kama kamar za su haɗe daidai nan Ustaz ya fito da waya a hannunsa saboda Tajj da yake cewa suna bakin gate mai gadi ya hana su zuwa. Ustaz ya nemi iskar shaƙa ya rasa ya ja numfashi ya kasa wayar hannunsa ya suɓaci zuwa ƙasa idanunsa a kan hannayensu da suke riƙe da juna. Tari ya fara sosai yana riƙe ƙirjinsa yana ganin yana-yana a idanunsa hannunsa ya saka da niyyar rufe baki yaga jini ya ɗigo hannunsa tsoro da tunanin kar zuciyarsa ta buga ya saka ya yi ƙoƙarin nufar gate ɗin da ake ta horn babu adadi har lokacin kuma Ridayya bata ji tarin na Ustaz ba, ya nufi gate ɗin amma jiri ya kama shi tari yaci karfinsa ya riƙe ƙirjinsa da yake jin kamar wuta na tashi ƙoƙarin kiran sunan Ridayya yake yana ɗaga mata hannu amma ya kasa abu mai danshi ya biyo ta hancinsa sunan Allah kawai yake kira ji ya yi kawai yana buƙatar Ridayya kusa da shi ko mutuwa ce ya mutu a cinyarta ya samu damar faɗa mata abinda yake ransa tsayin shekaru amma ina ya gagara daidai sanda aka buɗe ƙaton gate ɗin ya yi daidai da sanya Ustaz ya sulale ya zube a ƙasa jini gabaɗaya ya ɓata farar shaddarsa a lokacin kuma Ridayya ta ji ƙirjinta ya buga da ƙarfin gaske komai nata ya tsaya....




*Soyayya gaskiya ce! Zurfin ciki halitta ne, ƙaddara zane ce. Kowanne bawa yana da marudai wanda yake son cimma, haka ko wacce zuciya da abinda take so, da kuma son kasancewa da shi. Ba komai kake nema kake samu ba a rayuwa, wani baya gane kuskuren da yake sai ya sake making mistake the same, wani rashin wanda zai fahimtar da shi abu shi ne matsalar shi. Rashin tarbiyyar uwa na taka muhimmiyar rawa wajan rugujewar yara, kuma ɗa baya taɓa girma a gaban iyayensa. Rayuwa da ƙaddara abokan juna ne, soyayya tafi talauci illa a zuciya rayuwa da wanda kake masa kallon uba mahaifi matsayin miji abu ne mai wahalar gaske*


Ku bi a hankali ba sauri muke ba komai a tsare yake waye zai zama RABAGARDAMA? A rayuwar RIDAYYA? Uba ko Sadauki ko kuma kome za ta yi gidan tsohon mijinta?


Share and share as so much as you can
*MUNAFUKIN MIJI 33*
Mikiya Writers Ass


Bright pens free batch
Nimcyluv




Koda ya je ƙasa bai bari ya sare ba, baya son ciwo Ustaz ya dinga ƙoƙarin tashi ya kasa jinin zai zuba yake ta hancinsa. Ridayya kam ji ta yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login