Showing 81001 words to 84000 words out of 190738 words
Chapter 28 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt
bashi mamaki ko tsofan da ta yi shi kaɗai yasan abinda yake masa yawo a zuciya. Kwanan ta biyu cikin asibitin aka sallame ta ko inuwar Zameer bata marmarin kallo balle fuskarsa, sai yanzu kuma yadda ta samu Zameer ɗin shi da Khairy matsayin turmi da taɓarya ya dawo cikin tunaninta kamar mai cutar mantau haka abin ya kwanta a ranta sai dai wani irin zafi da ciwo da zuciyarta ke yi mata.
Tana shiga gidan sukai karo da Shatu, Shatu ta faɗi ƙasa tana birgima da ihu a gigice Iyatu ta fito daga ɗakinta ganin Shatu a kwance ga Ridayya a tsaye a gefe ta fasa kuka ta ce
"Ta kama mini yarinya mayya ta riƙe mini kurwar Shatu"
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Shi ne abinda Ridayya ta faɗa a zuciyarta shin wacce kalar rayuwa take ciki ne? Me ya sa al'umma da mijinta da ƴan'uwanta suka kasa yi mata uzuri ne me ya sa har yanzu bata ganin daidai ne? Yaushe za ta yi farin ciki kamar kowa yaushe za ta samu ƴan'cin kanta ne yaushe zata bar wannan rikitaccen ƙauyen dake neman kashe da ranta da nasu kalar ƙazafin.
Iyatu ta finciko Ridayya ta ce "Wallahi sai kin sakar mini kurwar ɗiyata shegiya mayya baƙar muguwa mai baƙar aniyya" Ridayya ta kasa kuka ta kasa cewa komai sai kallon Iyatu take tamkar zautacciyya ta saka hannu ta tsinka mata mari ta ce
"Dai na kallona makira danginki ma sun guje ki balle mu? Mayya kawai"
"Wallahi ni ba mayya ce"
"Ƙarya kike ai mu da baƙin mutum muke gane maye" Sai a lokacin Iya ta fito hannunta ɗauke da Harazimi dake ta wangale baki yana tsala ihu Ridayya ta kalli yaron ta ce
"To kenan bani kaɗai bace mayya ga wani nan ma" Iya ta ce "Jikina ba maye bane, ki ne mi can maye kuma ki zo ki faɗi uban ɗan da kika haifa ni nafi zaton ma mu can muna surutu kikai mata sauyin yaro ko aljanu sukai muku musaya"
Zameer dake tsaye ya jingina da jikin garo ya ce "I was thinking the same thing Iya, Ridayya baƙa ce kuma mai muni kamar dai ɗan hannunki, ni kuma fari ne kyakkawa haka ma Khairiyya fara ce tas haka iyayenta to tayaya za mu haifi wannan ɗan? No way ki bata wannan Harazimi yake ko waye? Ki amshi farin ɗan wajanta domin babu yadda za a yi ta haifi ɗa kyakkawa"
"Amma ban taɓa ganin zalunci irin wannan ba, a kan idanuna ta haihu na yanke cibiyar kar ku rabata da yaronta wallahi zan tuna muku asiri" Ta fashe da kukan tausayin Ridayya kamar jininta.
Zameer ya dakawa Hanne tsawa tare da ƙwace ɗan daga hannunta ya ce "Ki dai na yi mini shisshigi cikin iyalaina Hannatou"
"Su waye iyalan naka? Ni da nake matarka ko fasiƙar da kuka haifi ɗa babu aure kuma ta hanyar zina? Ko kuma ita data kasance tana son ka kuma budurwar daka yaudara waye iyalin naka daga cikinmu Giɗaɗo?"
"Ki daina ce mini Giɗaɗo ban so zan watsa miki tafi wallahi" Iya ta ce "Saurara ita kanti take ko kairi ai matarsa ce kamar yadda kike matarsa cewa ta yi dole sai an raba auren ba zata iya rayuwa a ƙauye ba shi ne yanzu data haihu ta kawo ɗan"
Ridayya ta kalli Zameer ya haɗe fuska ta kalli Iya ta ce "Ban yi mamaki ba tunda shi ɗin Munafikin miji ne, amma wallahi ba matarsa bace"
Nan da nan Zameer ya sauya fuska ya ce "Sharri Ridha? Duk zafin kishin ne za ki haɗa ni da laifin aikata zina?" Ya zaro wayarsa ya shiga nunawa Iya pictures ɗinsu da Khairiyya wasu a kwance wasu suna rungume da juna wasu suna kiss abubuwa dai na ma'aurats ya ɗora da cewa "Wallahi matata ce sharri zata ƙulla mini"
Ridayya ta kasa magana Iya ta hau masifa tana cewa "Ke dai ba matar rufin asiri bace ki dinga aibata mijinki, ai ya faɗa miki komai da Allah da Annabi kika haɗa shi domin ya aureki kin rasa mijin aure to Allah yasa yana raye balle ki yi masa sharri, wannan tsinanen baƙin ɗan naki kowa ba lallai ya yi albarka ba kuma ba zan taɓa amsar shi matsayin jikina ba wallahi, gona ɗaya tal Malam yake da ita idan ya mutu ita Giɗaɗo zai mallaka ko Giɗaɗo ya mutu ki rubuta ki ajjiya bashi da gado, mai farar ƙafa"
Ta taga Iyatu ta leƙo ta ce "Tunda shi kaɗai Malam ya haifa dole ki ce gonar gantalallen ɗan ki zai mallake ta"
Faɗan ya koma tsakanin Iya da Iyatu Ridayya ta shige ɗaki wani abu ya tukare mata. Tun daga ranar bata da walwala damuwarta ta tsananta tsakaninta da ɗanta wanda har yanzu bata san sunan da aka saka masa ba sai kallo daga nesa ko kuma idan zata bashi nono, a ranta ta jima da bawa ɗan suna Muhammad-Bilal. Harazimi kowa yana ɗan girma muninsa na ƙara bayyana bisa dole take shayar da shi domin ba zata iya barinsa da yunwa ba. Watarana iya idan ta ɗauke shi sai ta daddoke mazaunansa ta tallaƙe masa ƙewa, tana ji za a dinga yi wa Little Bilal waƙa ana irin arziƙi irin albarka haihuwar farar mace ko da ka sha nonon baƙar mace sai ka ƙara fari gwanin ban sha'awa. Iye iye kamo mini shi nan. Irin wannan waƙen ya kan sanya Ridayya ɗan mursawa kaɗan. Har yanzu kuma tabon ƙonar da Zameer ya yi mata yana nan wani lokacin ya yi kamar zai tashi wani lokacin kuma ya addaba mata da ƙaiƙayi. Hanne ta ɗauki ragamar dafa mata zugala ta ci ta sha ruwan.
Tana zaune Zameer ya shigo hannunsa ɗauke da Little Bilal kamar ana ƙara masa girma sumar shi babu inda ta bar ta Ustaz yadda kasan Ustaz ne ya yi cikin ɗan ko kuma ya yi kaki ya tofar ba inda ya ɗauki kamar Ridayya sai ta Idanu, amma girma faɗi hanci baki dimple sumar kai da jerin yatsun hannu gabaɗaya irin na Abbiey ɗinta ne Muhammad-Bilal Tahir Rano. Ta ƙura wa yaron Idanu wanda yake ta kallonta gashi da ƙiriniyya hannunsa baya zama waje ɗaya duk sanda Zameer ya ɗauke shi ya dinga kuka kamar zai mutu.
"Ridayya ki faɗa mini gaskiya ni na san da gaske wannan ɗan ki ne, kawai na yi hakan ne domin ki san har yanzu ni nake da iko a kan ki kuma ba zan taɓa bari ki zama wata ko ki ji daɗin rayuwa ba muddin ba ki mini yadda nake so ba" Ya yi shiru can kuma ya ce "Me ya sa kika haifi ɗa mai kama da wannan Ustaz ɗin? Ko akwai wani abu saɓanin abinda na sani kullum cikin firgici nake kwana kamannin Muhammad-Bilal dana wannan yaran kullum ƙara bayyana suke a Idanuna, kin taɓa tarayya da shi ne?....,"
"Zameer!" Ridayya ta kira sunan Zameer tana jin sunan har tsakiyar kan ta, jikinta na wata kalar Jijjiga da ɓari bata so tunaninta a kullum da kuma maganganun Zameer su samu tasiri da gasgata zuciyarta.
"Ai yadda kika iya bani kan ki a waje babu mamaki da auren naki ba za ki iya" Ridayya kallon Zameer kawai take ta kasa cewa komai, idan shi ɗan iska ne to Abbiey ɗinta mai tsafta ne ba zai taɓa shiga gonar da bashi da hakƙi a kanta ba. Ya gyara murya tare da fara zubar kalamai masu sanyawa ka yarda da mutum haɗi da kalaman soyayya "Bana jin daɗin yadda muke ba haka nasan ki ba, kina faɗar sunana kai tsaye saboda Kinga ina son ki ko? Ki bari mu dawo da rayuwarmu ta baya please ki bani wannan kadarorin na fara juya miki"
"Idan na baka zaka sake ni?" Domin sakinsa da warware igiyar auren kawai take muradi. Zameer ya yi tunani ai sai ka rubuta takardar sakin a rubuce ya zamana an yi sakin na halak bari ya yi da baki ya mata wasa da sakin, domin har ransa yake ƙaunar Khairiyya kuma yana da tabbacin ta yi masa nisa ba zata taɓa auren shi ba. Hanne kuma so yake kawai ta fahimce shi suyi rayuwa irin wacce sukai da Khairiyya. Ridayya kuma zata zama lover bed ɗinsa har abada ko baya sonta zai ci gaba da zama da ita yana samun ni'imar dake tattare da ita, ga dukiya ga farar mace a waje ta sawa a gaban mota, ga abokiyar gado shikenan.
"Idan sakin kike buƙata zan yi miki dukda ba a son raina ba rabuwa dake azaba ce a zuciyata" Ta miƙe ta warware wata atamfa tare da ɗakko takardun ta ajjiye a gabansa ta ce
"Ka bani ɗana ka sake ni ga takardun nan, ka sani dai dukiyata ce"
"Na sani ai juya miki ita zan yi dukda ba ki da wani ilimi balle qualifications masu kyau" Ya miƙa mata Little ta rungume shi tana sakin ajjiyar zuciya tana jin kamar Abbiey ɗinta take gani a gabanta. Zameer ya kwashe takardun ya ji daɗi babu wasu shaidu balle suga lokacin sakin da lokacin bada takardun.
Ya miƙe zai fita ta ɗan yi gyaran murya alamar tuni. Ya tsaya haka kawai faɗuwar gaba ta tsananta a zuciyarsa yana jin kamar wani abu mai mugun muhimmacin zai rabu da shi a rayuwarsa a hankali kamar zai yi kuka ya ce
"Na sake ki saki ɗaya" Ya nufi fita sai kuma ya tsaya ya ji bari ya ƙara ɗaya kawai ai duk cikin wasa ne "Na ƙara miki ɗaya, biyu kenan ki ke na sake ki Ridayya sai naga inda za ki je ki zaune wanda ya fi nan, naga wanda zai taimaka miki kuma ya zama jagoranki duk inda za ki dole waje na za ki dawo ni kuma na zama dolen ki my dear Ridayya! Ni ɗin nan ne ya zame miki dangi, ba za ki taɓa zama wata ba a duniyar ba za ki taɓa samun mijin daya kai ni kyau ilimi nagarta mai kuma jure zama dake ba"
Da sauri Hanne data raɓe a bakin ƙofa ta dafe ƙirji hawaye na zubo mata sai kuma ta yi waje da sauri daman jama'ar gidan duk suna gona. Tana fita Zameer ya fice zuciyarsa fari tas mafarkinsa yau ɗin ya cika.
Ko wacce mace na jin zafi da baƙin ciki da wani irin wani abu a zuciya idan kalmar saki ta gitta a tsakanin aurenta. Amma Ridayya zuciyarta fes dukda tana mai tunanin inda zata nufa idan bata da hakƙi tabbas Ubangiji zai nuna ikonsa zai bata miji nagari amma gabaɗaya a yanzu ta tsani MAZA gani kowa take tamkar Zameer kuma zai kasance MUNAFUKIN MIJI. Daman ita babu wani abu data sani don gane da so balle har ta ji ba zata iya rabuwa da miji ba. Bata san mene so da yadda ake gane shi ba, ba kuma tasan wanne namiji ne zai iya bata hakan ba koma waye dai bata buƙata wajen Abbiey ɗinta kawai da yana raye take son komawa.
Suna zaune cikin haɗaɗɗan gidan da suka sauya ya ɗan gyara zama fuskarsa a dame ya ce "Na yi wawta ban ɗauka haka ce zata kasance ba, na yi tunanin wannan plan ɗin shi ne zai dawo da rayuwarta cikin ta Babban mutum, na jima da gane su ɗin tamkar rayuwa da mutuwa ne, kamar kuma numfashin juna su ɗin ƙaddararsu tana tafiya ne da rayuwar ko wannen su, kamar yadda nake bibiyar rayuwar Babban mutum haka ta Ridayya sai dai na yi sake ta zilla mini garin gyara kuskuran da na yi na ƙara cilla rayuwarta cikin wani hali....,"
Kasa ƙarasa maganar ya yi saboda zafin da zuciyarsa ke yi masa ya sunkuya yana haɗe yatsun hannunsa. Can ya miƙe yana safa da marwa ya ce
"Ban zama uban ƙwarai ba, na yi dana sani a rayuwa wacce bata da wani amfani where is she?"
Abokin nasa ya ce "Kar ka ce haka Alhji Mansur ni na yarda plan ɗin nan zai yi working Ridayya zata neme ku da kan ta kamar yadda ta kuje muku, zata nemi Ustaz idanu rufe kamar yadda ta watsar da shi a baya, zata gane danginta da iyayenta sune gaba da miji a rayuwa, zata gane babu wani da yake son ta da gaske tsakani da Allah irin Ustaz"
Alhaji Mansur ya sauke numfashi ya ce "You are right Barrister, amma sai yaushe ne komai zai yi daidai wake da hannu wajan rabani da ƴata? A ina take yanzu ina tunanin zan nemi Babban mutum na bayyana a gare shi"
Da sauri Barrister ya ce "Mekenan akai? Baya ta haihuwa ai no no please don't do this. Idan Babban mutum ya san You are still alive ba zai saki jiki da dukkan zuciyarsa ya nemo Ridayya ba, kuma ba zai amince da ya aure ta ba, musamman da ka ce tunda yake bai taɓa faɗawa kowa yana son Ridayya ba ko?"
Ya yi maganar yana kallon Alhji Mansur ɗin da ya yi can ya ce "Haka ne"
"Ka yi haƙuri kamar plan ɗin mu ya yi going please na san da zafi but ka daure" Sallama sukai da Barrister shi daman Baba ƙarami bai ce komai ba jinsu kawai yake.
Alhaji Mansur ya mance ma wani girkin Ammi ne ya nufi ɓangaren Mami ya sameta zaune ta yi wanka ta shirya hannunta riƙe da azakar idanunta ya yi jajur kamar kodayaushe ya nemi kusa da ita ya ce
"Kukanne?" Ta girgiza masa kai ya saka hannu ya kamo fuskarta a tafin hannunsa ya juyo da ita suna shaƙar ƙamshin da numfashinta juna ya ce
"Haba Zara'una ya kike so na yi ne? Ni ma na yi kukan ne?" Ta kama hannunsa ta ɗora a ƙirjinta ta ce "Baffa bana jin daɗin zuciyata ina son ganin Ridayya na bata soyayya da kulawar data rasa ka taimaka mini"
Hawayen ya shiga goge mata ya rungume kawai ya kasa cewa komai a hankali ya yi magana a kunnenta ta yi saurin dukan ƙirjinsa ta ce
"Uhm ni ka bari"
Yau tunda ya shigo gidan ba sauƙi ko abinci bai ci ba, ya juya ya sake juyawa ya miƙe zaune a tsakiyar gadonsa ya koma ya zaune ya sake tashi ya nufi gaban madubin bedroom ɗin nasa. Ya zubawa kan shi idanu sai kuma ya langwaɓar da kai yana marairaice fuska da sauri kuma ya juya fara sakkowa daga strains ɗin benen mother da wata mata suna zaune ganin ba ita ɗaya bace nan da nan ya haɗe fuska ya koma armchair ya numfasa
"Sadauki ya aka yi ne? Yaushe ka shigo?"
Ya yi shiru bai yi magana ta juya ta ce "Atika ki dawo gobe mu yi magana ok?" Sallama Atika ta yi wa Hajja Azizat Sadauki ya zauna yana ɗora kansa a cinyar Hajja Azizat ya ce
"Ta ƙi barin idanuna me ya sa kullum take zuwa ne?". "Wakake magana ne?"
"Na san dole ta faɗa miki wace ita dole ne mother ki bani address na je ta faɗa mini dalilinta na shigowa bedroom ɗina?"
Hajja Azizat ta saki baki ta ce "Sadauki wata nawa da yin hakan baka manta ba?"
"Sai na rama zan manta fa" Ya koma ya kwanta a cinyarta yana tuna ɗazo kamar motar Prof ya gani ta shiga Bristol hotel ya share domin ai Prof ɗan business ne za a iya ganinsa a ko'ina.
"Ɗaga mini cinya malam" ya juya yana cewa "Allah ya kawo wacce zata kula da Sadauki"
"Amin. Domin na ga ji sosai da ganin haka kai baka girma kullum rikici da rigima da jama'a sai zuciyar masifa ga ɗan banzan kishi gwara ka yi auren macen ta lillisa mini kai ko ka nutsu"
Tun safe sai yanzu Sadauki ya yi murmushi wai mace ta lillisa shi ya lumshe idanunsa ya ce
"Duk sanda na yi aure ban ƙara kwanciya a cikiyarki sai ta matana, kike ta mini gorin haihuwa and kuma soyayyar da zan nunawa matana shi kaɗai ya isa ta nemi yafiya waje na ban iya son abu ba Mother ki mini addu'a ina da matuƙar kishi a kan abinda nake so"
Ta shafa kan shi ta ce "Allah ya yi maka albarka Hamzana Sadauki jarumin jarumai mai tarar zaki cikin dokar daji"
"E na tari zakanyya kin hanani mother. Amin Ya Allah love Allah ya ja da ranki kiga zuri'ar Sadauki"
"Allah ya amsa. Commissioner ya shigo Nigeria kasan watansa biyu baya nan, mun yi waya ya ce yana nemanka" Nan da nan Sadauki ya haɗe fuska ya ce "Gaskiya ba zani ba, ƴarsa masifar surutu ne da ita kuma ni bana son ka nemi juya ni"
A can ƙauyen Batsari yamma sakaliyya wasu mutane a babura sukaiwa ƙauyen tsinke kamar yadda suka saba hankalin jama'ar ƙauyen ya tashi domin sun san ƴan kidnaping ne ko masu kwashe musu shanu. Gida bayan gida suka dinga shiga suna kwaso yara da mata duk wanda ya yi yunƙurin hana su nan take suke kashe shi. Cikin rashin sa'a suna tsaka da al'amarin da kwashe jama'a manyan motocin jami'an tsaro sukaiwa ƙauyen tsinke suma daman sun zo bincike ne da kuma kawo musu taimako wanda kuma Commissioner da kansa ya buƙaci zuwa da jagorancin tawagarsa. Musayar wuta aka fara dukda ƴan sandan sun yi nasarar kashe wasu da kama wasu amma kidnappers ɗin suma sun yi nasarar tafiya da wasu.
Daga can kuma Zameer ne ke cewa "To ai sakin wasa ne bada gaske nake ba, BAN SAKE KI BA" kallon baka da hankali kawai Ridayya ke yi masa Allah ya bata iko ya riƙe Little Bilal a hannunta dukda jirin dake kwasarta saboda rashin jini ba ta yi ƙasa a qiwwa wajan barin inda Zameer yake ba da gudu.
Ya mara mata baya "Wallahi ban sake ki ba duk inda kika je za ki dawo ne sakin wasa ne ba" Kasancewar bata gani yasa gudu kawai take ta ƙanƙame ɗan ta duk yadda suke mata horn bata ji ba. Driven ya yi ƙoƙarin kauce mata amma ina bai ankara ba sai ihu da ƙarar faɗuwarta suka ji. Ya ajjiye wayarsa da yake tura information na gaggawa ya ce "Ya akai?"
"I am sorry DCP TAJJ MUJID BAITA mun kaɗe wata mata ne...
Nimcyluv sarauta
*MUNAFUKIN MIJI 26*
Mikiya Writers Ass
Bright pens free batch
Nimcyluv
*Masu wattpad a dinga following ɗin Account ɗina (profile) a kai ni 5k follower🌚 kunga ai kwana