Showing 36001 words to 39000 words out of 190738 words

Chapter 13 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17322

salihar kishiya gwara muguwa, da makira gwara annamimiyya, green snake in the grass, Fatima Batool ba za ta taɓa dawowa gidan nan ba, idan kun ga dama a daren nan ku saka wuyan Ridayya gabas ku yanka" Hajiya ta ce "Ki yi haƙuri Kaltum, ɗa na kowa ne bawa sai mai shi, ɗan Fatima ai ɗan Maryam ne, tunda kike kin taɓa gani saɓani ya haɗa su? Kuma duk runtsi da Uba ake ado bada riga ba"
Kai tsaye Anuty Kaltum ta ce "Hehehe tab, ba girin-girin ba, ta yi mai wallahi da wata kishiyar gwara gidan marayu, Ridayya kuma Allah zai kula da lamarinta, sara da sassaƙa baya hana ganji toho" Tana faɗin haka ta juya suka kama Mami tare da ficewa daga cikin gidan domin daman farkawar ta kenan daga allurar baccin da likita ya yi mata ta fito a haukace da ƙyar suka gano ita ta nufa, dukda ikon Allah da ƙudirarsa ce ta kawo ta gidan.


Bayan fitar su Anuty Kaltum, Baffa ji ya yi ciwon kan da yake masa ya ragu ya samu peace of mind, ko minti ɗaya bai tsaya yin nazarin cewa Mami fa ya saka? Hakan na nufin za ta yi nisa da ganinsa, gefensa zai rasa komai nata sai ya ji tamkar daman bai taɓa auren wata mace ba face Ammi. Hajiya ta kalli Ammi da kuma Ridayya dake hannunta ta ce "Ke kuma Maryam na dawo kan ki, ki ji tsoron Allah ki riƙe wannan jaririyar tsakani da Allah ki ɗauke ta tamkar su Zuhura, idan har kika cutar da ita bayan a kan Idanunki aka raba uwa da ƴa to wallahi Ubangiji ba zai bar ki ba" Ammi dai bata kalli Hajiya ba sai cewa ta yi "In sha Allah"


"Mansur mu za mu shige, daga nan zani gidansu Fatima na sake basu haƙuri kuma In sha Allah watan gaba zan dawo gani Ridayya" Baffa ya ce "To" Ya miƙe ya ce
"Allah ya tsare ya kiyaye, Junaid zai kai ku ko kuma driver?"


"A'a Junaid zan aike shi ga Muhammad-Bilal nan" Cewar Ammi tana miƙewa tsaye idanunta kuma a kan Bilal ɗin daya kafe ta da Idanu.
Ya ɗan taka har tsakiyar parlon kafin ya tsaya ya ce "Nikam ban so, tsahirta miki nake idan ba za ki ce Yaya Bilal ba ko Babban mutum ki barshi" Ammi ta riƙe baki ta ce "To ba zan ce Yayan ba ba kuma zan ce Babban mutum ɗin ba, Muhammad-Bilal zan faɗa tunda haka aka raɗa maka"
Bilal ya ƙanƙance idanunsa rai ɓace ya ce "Baffa ka yi wa matarka magana yanzu ni idan na ce Maryam za ta ji daɗi"Ammi ta saki baki sai kuma ta nufi kan Bilal ta ce "Ungu wannan dan ubanka ka rama ka ji daɗi, ni kake cewa Maryam?" Bilal ya yi kicin-kicin da rai fuskar nan a ɗaure kamar zai ce ya shiga uku. Baffa ya kalli Bilal kawai sai bai ce komai ba, Hajiya ce ta ce
"Kai Babban mutum Maryam ai matar ƙanin mahaifinka ce, kar ka kuma ambaton sunanta mahaifiyarka ce ai"


Ya yi gaba cikin kamilalliyar nutsuwarsa yana bada faɗi har ya je bakin ƙofa ya tsaya ya ce "Ita ma ta dinga ce mini Yaya Bilal, idan ba zata iya ba ta kalle ni ta shige" Hajiya ta rafka salati ta ce "Uwar taka ce zata dinga ce maka Yaya?" Har ya buɗe ƙofa ya dawo da baya yana riƙe kansa dake juya masa sosai da sosai ya ce "Ta faɗi sanda ta yi cikina ta haifa, nikam bana son haka raini ne da gaske raini ne Granny"
Ya fice yana banko ƙofar, Ammi ta yi ƙwafa a ranta ta ce "Zan ci ubanka ne, shegen yaro me uban son girma ma rainin kowa da taurin kan tsiya" A fili ta ce "Ai kar ki damu Hajiya haka halinsa yake sai mu dinga cewa Yaya Bilal ɗin muna bashi girma kamar yadda yake so" Sallama sukai Hajiya ta fita zuwa harabar gidan, ta nemi Bilal ta rasa domin ya ji haushin yadda ta ce Ammi babarsa ce.


Wani irin shu'umin murmushi Ammi ta yi tana girgiza ƙafa wacce ta harɗe su ɗaya kan ɗaya kafin ta miƙe tsaye ta ce "Ni za a bawa rainon ƴar kishiya? Ni Maryam ko a gidanmu ba kishiya, na zo nan na yi zaman bora sannan a haɗani da rainon ƴar kishiya?" Dariya ta kece da ita sai da ta yi mai isarta kafin ta juya ta ƙura wa fuskar Ridayya kallo kana ta ce
"Barka da zuwa hannun kishiyar uwa, barka da zuwa uƙubar kishiyar uwa, zan fanshe duka haushin da ubanki ya gana mini da cikinki, zan fanshe fifikon soyayyar da ubanki ya nuna a kan majaifyarki, na rantse da Allah duk abinda na haɗiya na ɓacin rai da kishi a yanzu zan amayo da shi a kan ki, zan tabbatar muguwar azabar da zan miki sai ta ƙarasa rayuwarki, kamar yadda Mansur yake mugun sonki tun kina ciki, gashi yanzu a ranar da kika zo duniya tsana mai tsanani ta maye gurbin soyayyar, ai ɗan halak shi ya san idan an yi masa ya rama, tuwon girma, miyarsa nama"
Ammi ta girgiza kai tare da kaɗa hannu ta ce
"Ɗan kishiya ba zai taɓa zama ɗa ba, kamar yadda kishiya ba zata taɓa zama ƴar'uwa ba"


Hannu ta saka ta ɗauki Ridayya sai kuma ta saka zaftara-zaftaran faratanta ta gantsarawa Ridayya mintsini a cinya har sai da fatar wajan ta sutale, tunda a ka haifi yarinyar ba wanda zai ce ya ji kukanta banda wanda likitoci suka saka ta yi, sai kawai ta dinga zabura ita kaɗai. Tsananin azaba da yadda mintsinin ya ratsa jaririyar ƴar kwana biyar zuwa shida a duniya wacce bata san meke faruwa ba ya saka Ridayya sakin wata ƙatuwar shaƙuwa ita kaɗai gumi zai yanko mata yake, ta dinga zabura kamar wacce ake kaɗa mata gangi, dukda irin azabar da Ammi ta yi mata bai daka Ridayya yin kuka ba. Ammi ta duba taga fatar wajan ta sutale jini na zuba ta ƙarasa kitchen ta kwashi gishiri ta manna a wajan, ta kwashi ya ji shi ma ta manna, yarinyar ta dinga sakin ajjiyar zuciya fuskarta ta yi sharkaf da gumi. Ganin har yanzu ba ta yi kuma ba ya saka Ammi cewa "Tsinanniya gayyar tsiya, yadda ban taɓa ƙaunar uwarki ba wallahi ba zan ƙaunace ki ba" fuuu ta yi part ɗinta a tsakiyar parlo ta shimfiɗe Ridayya bayan ta cire mata kayan da Bilal ya saka mata ta ƙure a.cn dake cikin parlon kana ta yi cikin bedroom ɗinta. Wata number ta kira ana ɗagawa ta ce "Ki tura masa raguwar kuɗin, ki zo ina buƙatar ganinki" Tana faɗin haka ta kashe wayar.


Muhammad-Bilal na fita ya nufi ɓangaren iyayensa ya samu Umma zaune tana kallo, yanayin yadda ya shigo ya sa bata kula shi ba, duk da mutum ne shi mai zurfin ciki bai fiya shiga sabgar da babu ruwansa ba, sai a yi abu sau naya bai tanka ba ta rasa dalilin daya sanya ya damu da lamarin Ridayya? Ta girgiza kai tare da ci-gaba da kallonta. Wanka ya yi ya shirya cikin wata blue black ɗin jallabiyya mai kyau da taushi sai zabga ƙamshi yake komai na ɗakinsa a tsaftace yake, drawer ɗin littafansa daban tari guda duk na addini ne, Alkur'ani, hadisi, tafsir, azkar, ƙawa'idi, Dala'ilu, umdatul ahkam, zajidul zauj, hakƙun mubin littafai na addini kala-kala. Yana tsaye hannunsa ɗaya goye a bayansa takardun kammala karatunsa yake gani, bai taɓa sha'awar neman aiki ba sai yanzu. Kasancewar ɓangaren Accounting ya karanta fannin business, finance, and accounting ya sanya ya fita da sakamako mai kyau, baya wasa da duk abinda zuciyarsa ke so da muradi yana da naci, da ƙwallafa rai ga taurin kai ga duk abinda zuciyarsa ta kwaɗaitu a kai, ya dinga kallon takardun yana tunanin ta ina zai samu aiki? Ko bai samu ba, ta wacce hanya sai dinga neman kuɗi? Wayarsa ya ɗauka da takardun ya fita bakinsa ɗauke da addu'a ya haɗe rai sosai a dole baya son raini gani yake yawan magana da sakin fuska shike kawo raini.


Makarantar islamiyyar da yake koyarwa ya fara zuwa, ɗalibai na ganinsa suka shiga hankalinsu ya nufi aji shida ajin ƴan sauka gabaɗaya ƴan'mata da samari ne a ciki waje ya nema ya zauna suka gaishe shi, ɗaya bayan ɗaya suke bashi haddar Alkur'ani har aka zo kan Muwahif, duk sanda zata bawa Bilal karatu sai ta samu matsala gabanta ya dinga faɗuwa saboda tsananin kwarjininsa, haiba da mazantaka ta cikakken namiji.
A hankali ya tsaya da danna wayarsa ya yi mata kallo ɗaya jin haukan data rafka masa kowa ya yi nisa amma har yanzu a izu biyar take bata jima da zuwa Ali'imran ba. Kallon da ya yi mata da nufin ta gyara sai ya ga ta ƙura wa fuskarsa Idanu da kuma tsayayyen gemunsa mai kyau da sheƙi. "Keee" Ya kira sunanta amma ta shagala wata ta zungureta ta ce "Wahif Ustaz yana magana, Wahif" Firgigit ta dawo hayyacinta tun kafin ya yi magana ta fashe da kuka tana ƙoƙarin cewa "Ustaz ka taimaka mini wallahi ina...."


"Out" Ya faɗa a tsawa ce da gudu ta miƙe tare da yin waje tana rushewa da kuka, bayan gama karatun ya fita ya nemi aiki ko na hannu ne bai samu ba da ƙyar ya samu aikin jiran wani babban shago na wani Alhaji. Sai magriba ya dawo gidan.


Dr ne tsaye yana ƙare wa Dada kallo kafin ya ce "Mu je office" bayansa ta bi ita da Yaya A'isha ya ja kujera ya zauna idanunsa a kan Dada kana ya sauke ajjiyar zuciya yana zare glasses ɗin idanunsa a hankali ya ce
"Mun sauya mata ɗaki zuwa ICU" Yaya A'isha ta zare ido ta ce "ICU Dr? But why?"


"Eclampsia, dalilin jijjigar da ta yi kafin a yi mata Cs, binciken da mukai ya tabbatar tana da hawan jini kuma ta ɗauki lokaci tana naƙuda wacce ya haifar mata da zazzafan zazzaɓi da ciwon kai, sanda ta fara jijjigar mun su yi mata Loading dose mgso4 amma babu hali hakan yasa mukai aiki aka cire babyn" Likitan ya yi shiru can ya ce
"Ta farfasa bakinta sosai sanda ta yi jijjigar, babbar damuwar ta yi saurin farkawa daga coma da wuri kuma hakan hatsari ana iya samun rasa rayuwa ko hankali gabaɗaya"


Yaya A'isha ta fashe da kuka sosai ta ce "Amma dukda wannan baƙar azabar da Fatima Batool ta sha wajan haihu aka iya ɗauke jaririyar a bawa kishiya? Ko zafin haihuwar da wahalarta bai gama sakinta ba, ga saki ga ƙwacen dole da raba soyayya ina Alhaji Mansur zai kai wannan hakin don Allah?"


Likitan ya ce "Pardon, bangane ba an karɓi baby ba, kuna nufin babyn baya cikin asibiti under special care na likitoci? Ba kusan cewa Eclampsia na iya taɓa jariri ba?" Hajiya ta yi jigum saboda wannan tashin hankalin ta kuri Anuty Kaltum ta ce "Jijjiga na taɓa jariri ne Dr?" Ya jinjina kai ya ce


"Sosai ma, suna samun Cerebral palsy irin yaran nan Abnormal dolaye irin galahanga ɗin nan, babyn ma na iya rasa ransa, ko a haife shi yaƙi kuka kamar yadda itama babyn taƙi yi, idan baby ya samu Cerebral palsy akwai matsala, wasu suna kurmancewa ne, wasu basa gani sosai, ko kuma kaga gabaɗaya yaro baya gane karatu"


"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Shi ne abinda Dada take faɗa Yaya A'isha kuka kawai take ta ce "Don Allah don girman Allah Dada a dawo da Ridayya wajanmu, yarinyar ba cikakkiyar lafiya ta cika ba" Godiya Dada ta yi wa Likitan tunda ba za su samu damar shiga wajan Mami ba sai zuwa safiya tana addu'a a ranta Ubangiji ya sa kada sanadin haihuwa Mami ta rasa tunaninta ko ta haukace.


Wajan ƙarfe goma Ammi ta ruski Baffa a ɗakinsa yana ganinta ya ɗan saki murmushi ya ce "Uwar gida ran gida, idan ba ke ba gida" Ammi ta juya idanunta ta ce "Yau kuma kirarin na uwar gida ne, ina na amarya Fatima?" Nan da nan annurin fuskar Baffa ya ɗauke domin baya ƙaunar jin sunan Fatima ko da wasa.
Ya riƙe kafaɗun Ammi idanunsa cikin nata wanda suke ƙara rikita shi ya ce "Maryama kar ki kashe ni da raina don Allah" Ta ware idanunta kafin ta ce "Rufa mini asiri na kashe mijin Fatima baban Ridayya Uncle ɗin Bilal" ai gabaɗaya Baffa ya ji ɗakin na juya masa yana jin kamar ta caka masa wuƙa a zuciya ne ya riƙe ta da ƙarfi ya ce
"Ki tausaya mini Maryam, sunan Fatima azaba ne a gare ni ban so koda wasa,na tuba; na bi Allah na biki matata Maryam" Ta yi murmushi tana kashe mata ido ta ce "An gama ranka ya daɗe, angon ƙarni" Juice ta bashi ya kalli ruwan lemon jajur da shi kamar an kaɗa jini, bisa umarnin zuciya da abubuwa dake fusgarsa ya damƙi hannunta gabaɗaya mai ɗauke da kofin ya shanye lemon. Bayan ya shanye yana tsaye ta ce "Zauna mana Baffa?" Ya kalleta sai ya ce "Na zauna Maryam?"


"Zauna Baffana" Ya nemi ƙasan kujera saman carpet ya zauna ta yi wani kalar murmushi ta ce "A'a koma kan kujera magana za mu yi" Ya yi jim ya ce "Na zauna a kujera Maryam? Na zauna ba matsala?" Ta jinjina kai ya miƙe jiki na rawa kamar mazari ya zauna a kujera ta harɗe ƙafa ta ce


"Mansur kuɗin rainon ƴarka za mu yi magana, duk wata zaka bani dubu ɗari, dubu ɗari da hamsin kuma kuɗin siya mata madara da kaya" Ya kalleta ta ce "Ka ji?"
Ɓarin da jikinsa yake ya tsananta ya ce "Shikenan koda saura? Yanzu zan tura miki kuɗin ko sai anjima?" Ta yi murmushi ta ce "Da safe, sai abu na gama ko da wasa kar na ganka a ƙofar gidansu Fatima da niyyar zuwa biko" Ya girgiza kai ya ce "Ba zani ba" Ta ce "Good, bacci na ke ji yanzu da safe zan zo ka faɗa mini duka abubuwan daka mallaka, ka faɗa mini me da me ka mallakawa Ridayya tun tana ciki, ka faɗa mini irin abubuwan da Fatima take maka wanda kake so" Ya jinjina kai ta ce "Ka ji ko?"
"E, na ji Allah ya kaimu"
Waje ta yi bita da sauri sai da sukai nisa ta tsaya ta ce "Ya kake bina Baffa salon ka ja mini masifa?" Ya marairaice fuska ya ce "Tambayarki zan yi daman zan iya kwanciya a gado na yi bacci?" Ta ce "E mana jeka" Ya ce "Thank you" Ya juya.


Tana komawa part ɗinta ta samu Ridayya kwance inda ta barta ƙafa ta ɗaga zata taka mata ciki sai kuma ta girgiza kai ta ce "Idan na kasheta mene ribata?" Sai ta ɗauki Ridayya ta yi mata tumɓur har pamper ɗin ta cire ta zaga can baya wajan bola ta saka ɗan'kwali a ƙasa kana ta ɗora Ridayya a kai cikin bolar shirgin gidan ta juya, dare ya raba kafin ka ce me cinnaku sun yayyame saman fatarta sai gantsara mata cizo suke, sun cika gabanta hancinta saman laɓɓanta har cikin idanunta cinnaku ne sai gatsa mata cizo suke ga tsanyin dare tsananin azaba ya sanya jaririyar daddagewa ta yantsara uban ihu cikin tsakiyar daren sakaliyya....






Domin comment ko gyara yi magana ta gmail ɗina sulaimanshuaibunaima@gmail.com


Ko kuma ta WhatsApp number 08164069385


Na'ima Sulaiman Sarauta
Nimcyluv


*✿ MUNAFUKIN MIJI 14 ✿*
Mikiya Writers Ass.....




BRIGHT PENS🤙🏼 free batch
Nimcyluv




Fitowarsa kenan daga shashinsu domin yin shur na azumin Alhamis, tunda ya fito yake jin zuciyarsa babu daɗi, ya yi shiru yana jin yadda iskar gari ke kaɗawa tana bada wata amintacciyar ni'ima mai saukar da nutsuwa a zuciya. Saukar kukan jaririyar ya yi daidai da lokacin da ya ji kansa ya sara, ya yi jim yana son tabbatarwa da kansa abinda kunensa ke jiyo masa. Da sauri ya miƙe tsaye carbin hannunsa na ƙoƙarin faɗuwa zuwa ƙasa, gashi farar jallabiyya ce tas a jikinsa.


Direction na inda kukan ke fitowa yake bi, a haka har ya isa daidai inda bolar gidan take ya waiwaya a hankali, amma bai ga kowa ba zatonsa ya bashi yau ko rashin sa'a ya yi mutanen ɓoye ke son buɗe masa ido? Ya ci-gaba da tasbihi a zuciyarsa. A bin mamaki kuma lokacin jaririyar ta daina kuka, yana ƙoƙarin juyawa ya sake jin saukar kukan nata wanda yake shirin rusa nutsuwar daya gino a kanta, cikin sauri ya fiddo wayarsa ya kunna torchlight tare da haskawa. Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!


A gigice ya saki wayarsa dukda ƙasan zuciyarsa bai gama tabbatar masa daba gamo ya yi ba, ya saka hannu a fili kuma cikin kamilalliyar muryarsa ya ke azakar na neman tsari da kariyar Ubangiji. Da duka hannu biyun ya ɗauki jaririyar yana matsawa wajan haske, ya runtse idanunsa da sauri lokacin da ya yi tozali da Ridayya, fatar jikinta ta kumbura jini sai zuba yake tako'ina a jikinta, da sassarfa ya nufi ɓangarensa ya shiga bedroom ya rasa abinda zai yi duka wannan abubuwan bai san su ba, sai jaririyar ya gama sha'aninsa a gidan bai kalle shi ba, balle ya san yadda ake kula da su.


Ruwan shower ya kunna yana ƙoƙarin zuba mata sai kuma ya girgiza kansa ya koma ya kunna hiter kafin ruwan ya yi zafi ya nufi saman gado, ya ɗora Ridayya a ciyarsa. a hankali yake bin fatar jikinta da kallo, dukda kasancewarta jaririya amma sam bata da hasken fata gashi da cinnakun da fatar suna neman zama ɗaya ga jinin dake fita duk ya dagule fatarta.
Audiga ya ɗakko ya dinga share jinin yana marmasar da cinnakun amma tamkar na asiri sun kafe gashi sai tsala ihun azaba Ridayya ke yi. Ustaz ya inda zai saka kansa idan ya tsora mata idanu sai kawai ya sauke ajjiyar zuciya, da ace shi ma'abocin kuka ne da karaya da lamarin rayuwa da tuni ya raunata. Ya ci-gaba da gogewa har jinin ya fita a hankali ya dinga kaɗe cinnakun wasu su fita wasu kuma suna nan. Ya ajjiyeta sai kuma ya dawo ya ɗauketa gani yake tamkar wani abu ne zai sameta idan ya bar ta. Ruwan zafin ya haɗa daidai wa daida, ya saka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login