Showing 60001 words to 63000 words out of 190738 words

Chapter 21 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

18765

ɓare ya saita a saman wandon ya bata ya ce "Shiga toilet ki wanke jikinki sai ki using wannan ok" hanyar fita zuwa bedroom ɗinta ta nufa ya damƙo hannunta ya tura ta cikin toilet ɗinsa yana tsaye ta fito sai raɓe raɓe take.


"I have been waiting for this day Ustaz ki kula, kina sauya kayan jikinki a kan lokaci, banda ƙazan ta ai kin san komai?"


"E, Abbiey" Cike da kunya dukda ba wani nauyin shi ta ke ji sosai ganinsa take babanta kuma babarta kuma abokinta kuma ƙawarta kuma Bestfriend ɗinta. "Lecture ɗin ki gobe ne zai fara, ki kwanta yamma zan nuna miki wani waje" Ta yi sauri ta batsa kusa da shi ya mata tsayi sosai ta kama hannunsa ta ce "Na gode sosai Abbiey uba na gari farin cikina, Allah ya saka da alheri ya ƙara buɗi" Kallon ta yi sai ya jinjina kan shi. Da sauri kuma ya ce
"Ki mini alfarma Ustazana kin zama babba ki nisanta kan ki daga maza please" Ta ce "In sha Allah, Abbiey me ya sa baka saka shadda kai ka saka bluetooth da irin kayan nan na ƴan gayu? Kullum hirami i doesn't like it" Ya haɗe fuska nan da nan ta shiga hankalinta bayan ya nuna mata sabbin kayan sallar da ya yi mata rabi duk abayas ne masu mugun tsada shoes backs atamfa lace kamar bashi da matsala haka ya zage ya yi mata siyaya daɗi ya ishe Ridayya ta faɗa jikinsa tana kuka "Thank You! Thank you!"


Washegari da kansa ya kaita makarantar a sabuwar motarsa ta zamani, tun shigowar su Moo ya daki kafaɗar Meer ya ce "Hee look" Meer ya juya iya motar kawai ta ja hankalin Meer lallai wannan mai kuɗi ne. Nasiha sosai Ustaz ya yi mata kana ya ɗauki sabuwar waya da sim ya bata saboda karatu ta fita ya juya yabar makarantar. A hankali take tafiya saboda hijab ɗin da Ustaz ya ce ta saka jakarta a hannu sai yatsuna fuska take kan ta a ƙasa, yadda take tafiya zaka ɗauka yanga take da ƙibar ta da tsayin ta daidai wadaida. Kamar an ce ta ɗago kan ta idanunta ya nutsa cikin na shi yana tsaye yana kallonta hannunsa zube cikin aljihu, wata harɗaɗɗiyar shadda ce ya saka a jikinsa Amy color iya haɗuwa ya haɗu sai kashe mata ido yake yana ɗan rausayar da kansa gefe hakan ya ƙara masa kyau a idanun Ridayya ita kam kwalliyarsa na matuƙar burgeta. Jin numfashinta sai tsaya ya saka ta yi saurin sunkuya wa zata ɗauki jakarta data faɗi ƙasa gabaɗaya jikinta rawa yake kokawa take da zuciyarta wajan ganin bata sake kallon shi ba. Ta ɗauki jakar ɗaguwar da za ta yi ta ganshi tsaye a gabanta......








Na'ima Sulaiman Sarauta
Nimcyluv
Share
Comment🌚🧚🏻‍♀️
*✿ MUNAFUKIN MIJI 20 ✿*
Mikiya Writers Ass...




BRIGHT PENS🤙🏼 free batch
Nimcyluv




Saurin ka baya ta yi jin numfashi da ƙamshin shi na sauka a fuskarta, ta kakkaɓe jakar tana juya idanunta, zuciyarta sai dokawa take saboda tsaiwar shi a wajan.


"Most beautiful lady in the world, what pretty!"


Da sauri Ridayya ta ɗago idanunta ba tare data shirya ba, jin kalaman da suka daki zuciyarta, wanda ba a taɓa danganta ta da su ba, ita da ake ce mata Zoo ko Kangaroo? _Most beautiful lady in the world?_ ta maimaita a zuciyarta


Yana sakin murmushi mai taushi idanunsa a ciki ya ce "Yes you're, please ko sau ɗaya ki fito takara ta Miss Nigeria" Ya ƙare maganar yana kashe mata Idanu ɗaya, tare da gyara tsaiwar shi da kyau fuskarsa ɗauke da yalwataccen murmushi wanda ya ƙirƙira bisa dole ya aza mata. Ridayya kasa magana ta yi domin ba ɗabi'arta ba ce musamman yadda rikicewar al'amarin da afkuwar shi ya wanzar da wani irin sabo abu daya gitta tare ɗar suwa a jaririyar zuciyar da bata san komai ba sai Abbiey.


Haɗuwar wasu ƴan sakanni na shirin shafe alaƙar shekaru masu yawa da sanya almakashi ta ƙarfin tsiya wajan yanke alaƙa da zumunta mai cike da shaƙuwa soyayya da kulawa haɗi da al'ƙawarin zuciya kuma halastacciya.


"Kar ki saka na dinga mafarkin waɗannan sexcy eyes ɗin, pretty" Meer a ransa ya ce "Kutumar uba, ji yarinya kamar irin gumakan Indian nan sai masifar girman kai" bai gama tunani ba ya tsinkayi muryarta cike da sangarta kamar mai shirin kuka ta ce.


"Thank you"
A ranta tana jinjina sabon kalaman cin mutumcin data ruska yau, tare da sanya ƙafa ta shure su nan take, babu inda ta ɗarsa zancen balle ya kwaɗaita mana wani abun. Gabaɗaya ta mayar da maganganun nasa amshin shata, tamkar kuma busar sarewar Audu haka muryarsa ke mata amo a kunne. Meer ya girgiza yana ɗaga shoulder ya ce
"Wow! Gaskiya muryarki akwai daɗi ma sha Allah, new student?"


"E, haka" Ta faɗa tana ƙoƙarin barin wajan domin da ƙyar take fusgar numfashi, ita kam hundred percent mutumin nan ya gama burgeta, his voice, his dress, the way he's talking, komai nasa daban ɗan gayu sosai da shi. Ya yi saurin shan gabanta ya ce


"Uhm kuma za ki bar ni bayan ban ga ji da kallon wannan black beauty ɗin nan fa" Sai a lokacin ya ɗan kalli idanunsa a ranta tana mamakin yadda bata iya nutsa ganinta a ƙwayar idanun Abbiey amma yanzu kai tsaye take kallon cikin idanun Meer. Kamar za ta yi kuka tana rausayar da kai ta ce.


"Don Allah kar ka ci mutuncin HALITTAR ALLAH, nasan tsananin munina ya sa kake cewa na zama Miss Nigeria, bani na halicci kai na ba, BAƘAR KALA da launin halitta na muni shi Ubangiji yaga ya cancanta dani, kuma na gode da ni'imar shi"


"Subuhanallahi!" Cewar Meer yana sauya fuska tare da jujjuya kai daga hagu zuwa dama, daga kudu zuwa arewa, daga gabas zuwa yamma ya ce "Who told you cewa ke mummuna ce, yanzu na zubar masa da haƙura, keep a joke aside Black beauty ban taɓa ganin colour mai kyau da ɗaukan hankalin mutum nan take kamar na ki ba"


"Uhm" Meer ya ce
"Ban son Uhm ɗin nan, ina nufin abinda na faɗa i never lie to you"


"Stop kidding me" _Ka daina tsona ta_ Ya girgiza kai yana ɗaga gira ya ce "Ko tsokar da kan ta, ta yi kaɗan ta tsoka ne ki"


Murmushi kawai ta yi tana bin gefen shi zata shige ya bi bayanta, gabaɗaya Ridayya jin ta take wata uncomfortable duk duniya banda Abbiey ba wani namiji daya nuna mata kulawa ya faɗi kalaman masu daɗi a kan ta sai wannan mutumin da ko sunan shi bata kai ga sani ba.


Ya sha gabanta idanunsa zube a kanta yana bin yadda jikinta ke motsa wa dukda ta saka hijab, da baya da baya yake tafiya ya lumshe idanu ya buɗe ya ce "Kuma ba ki tambayi sunana ba?" Nan ma ba ta yi magana ba ya sassauta murya cike da salo na yaudara wanda yake ƙara nutsar da zuciyar Ridayya na daga cikin abubuwan da suke burgeta da shi.


"Iyee irin wannan jan a ji? Well is allowed sunana ZAMEER MAHBOOB DOLLAR" Ta dai yi murmushi kawai wanda ya tabbatar da ta ji sunan. Ya ɗaga kafaɗa duk biyun yana ƙara yin baya ya ce "Sunan ba daɗi ko? Ai shikenan bari na gudu tunda am not welcoming"


Ya juya abinsa. Sai Ridayya ta ji duk ba daɗi tunda shi ne first person a maza daya fara nuna kulawa a gare ta, gashi yana da sauƙin kai da fara'a da kuma wasa bata kammala tunanin ba ta ji ya ce


"Ok see you later RIDAYYA" ya faɗa yana nufar inda ya faka motar shi. Mamaki ya cika ta a ina ya san sunanta? Me ya sa kuma zai ta fi? Ko ba a makarantar yake ba? Sai ta ji gabaɗaya kamar ya tafi da ƴar nutsuwar data fara samu.


Daman ta riga ta san a Department ɗin da zata ɗauki lecture yau ɗin kai tsaye ta nufa kan ta a ƙasa saboda kar wani ya ganta ya ƙara razana domin abinda Mahmud ya yi a kanta yana nan zaune a ranta bata manta ba. Tunda ta shiga cikin hall ɗin ake ta kallonta sai a tuntsire da dariya nan da nan idanunta ya cika da hawaye ta na jin wata na cewa "Ba za ki daina kallonta ba sai kin yi mafarki? Kila irin mayun dajin nan ne ko ƴan ruwa ai duk haka suke fa"


"Wallahi Ilham mamakin yadda aka samu mutum bai wannan baƙin nake, kima ture munin baƙin ya yi over zan sauya wajan zama gaskiya wannan ai illa za ta yi wa mutum" Hankalin Ridayya ya tashi ainun wannan shi ne ba'a rabu da Bukar ba an haifi Habu. Yadda ake aibata halittar da Ubangiji ya yi mata ya sanya babu abinda ta fahimta har lecture ɗin ta zo ƙarshe, zaman ya gundure ta sai kuka take na zuciya wanda ya fi cin rai. Ta riga kowa tashi ta fita ta yi nisa sosai har ta zauna kan kujera ƙasan wata bishiyoyi tunanin rayuwarta da yadda babu farin ciki ko kaɗan a ciki ya shiga kai kawo a ranta, tun daga haihuwa a yadda aka bata labari, fitar mahaifiyarta zaman ta wajan stepmother ɗin ta wacce tasha azaba kala-kala wanda shiru da miskilancin Ridayya yana daga cikin ƙona ta da a ka yi a saman harshe, tsanar mahaifi rashin jan jiki da Mami ke nuna mata dukda lukuta da dama ana ce mata wai don ita ƴar'fari ce a ranta ta san ba haka bane.


"So You are here?"
Ta yi saurin ɗago kan ta domin ta gane muryar. Suna haɗa ido ya kashe mata nasa idon ɗaya tare da langwaɓar da kai gefe "Wai guduna kike yi? Yasin to ba ki isa ba don ni naga wajan zama" ganin idanunta sun sauya sun kumbura ya yi ƙasa da murya ya ce


"Kuka? Kuka ki ka yi pretty?"Ta ce "A'a"


"Kuka ne mana ya zaki ce a'a bayan ga gaskiya nan a kan fuskarki, waye ya saki kuka wlh sai ya ci ubansa" A sanyaye a yanayin muryarta na zan yi da shagwaɓa ta ce


"Kai ne ke mini ciwo, thanks" Mamaki ya kashe Meer jin yadda ta ce wani _thanks_ a wulaƙance ya ce "Oh sorry, kin sha magani?"


"Azumi" Ya ɗan shafa kai ya ce "Oops yhhh haka ne, sannu kyakkawa" Ta miƙe tana shirin tafiya ya miƙe shima ya ce


"Kuma shi ne ba ki tambayi sunana ba, jan ajin ya yi yawa haka". "Ka faɗa mini ai"


"Na ce miki me?" A sanyaye ta ce "Zameer" Ya lumshe idanunsa cike da gwaninta ta samarin zamanin yanzu ya ce "Oh my dear lord, za ki kashe ni da golden voice Ridha" ta yi shiru har sukai nisa cak ta tsaya ganin motar Abbiey jikinta na ɗan rawa sosai ta ce
"Don Allah ka daina mini ga Abbiey na can zai ganni" Meer ya taɓa fuska yana laɓɓansa ya ce "Na je na gaida Abbiey na nemi ta barraki da albarka saboda watarana"


Ta yi rau rau da Idanu wanda suka cika da hawaye ta ce "Faɗa zai yi mini fa, please ka tsaya nan" Ya ce "zan tsaya muga wayarki?"


Kafin ta yi magana ya amshi wayar ya saka numbersa kana ya kira ashe har credit duk Ustaz ya saka mata bata sani ba, ya bata wayar ya ce "Matsoraciyya kawai, bye ki kula kar ki yi kuma ki taimaka mini" Bata kula shi ba ya zo daidai kunnenta ya ce "Take care of yourself for me, only me pretty"


Ta runtse idanunta tana jin wani irin, ban bara kwai wai namiji da suna Hajara haka take ganin al'amarin Zameer lokaci guda ya yi zaune daram a zuciyarta ko iya haka ne ita kam ba zata mance da shi ba, ya faɗa mata kalamai masu daɗi a lokacin da take tsananin buƙatar hakan, dukda ko sau ɗaya bata taɓa jingina kan ta da wani namiji ba balle ta yi kwaɗayin rayuwar aure da shi, babu lissafin hakan a ranta. Burinta ta yi karatu ta yi achieving muradanta, ko sauya ɗaya ta samu kusanci da iyayenta su jata su rungume ko da basu kira ta da sunan ƴa cikakkiya wacce kwayayayen halittarsu ya samar da wanzuwar ta a duniya ba. Daga nan kuma ta jirayi lokacin da ruhinta zai koma ga mahaliccinta.


Sauyin bugun zuciyarsa ya samu asali tun kusanto shi da ta yi, sannu a hankali zuciyarsa ke buɗewa wani abu na shiga tare da wanzuwa a zuciyarsa. Ƙoƙarin hana idanunsa abinda zuciyarsa le buƙata da muradin gani a kodayaushe, haƙar shi bata cimma ruwa ba, tsintar idanunsa ya yi kwance a kan ta. Ya zame idanunsa yana mai yin tasbihi har ta buɗe ƙofa ta shigo kan ta a ƙasa ta ce "Sannu da hanya Abbieyna na kaina" Bai yi magana ba ya tayar da motar suka fice a hankali kuma yake driving ɗin.


"Ridayya" ta yi saurin cewa "Na'am Abbiey"


"Kin tuna girman alƙawari Ustaza" ta kalli gefen fuskarsa yadda sumar sajan ya yi kwance yana ta kyalli sai duk ta ji ba daɗin ganin jallabiyya a jikinsa, da yadda ya naɗa hirami sai ta ɗauka kamar tsofa ne ya saka ko rashin waye na ohho. A hankali ta ce
"Al'ƙawari Abbiey?"


"Ustazana ke fa baushiya ce, na maimaita wa wasu magana kema, da gaske kema maimaici kike so shalale?" Ta girgiza kai ta ce "Ka yi haƙuri Abbiey ba zan karya ba" Ya sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya yana jin kamar ganganci ya yi a hankali ya ce "Mene al'ƙawarin?"


"Ka ce University ba irin primary school bane ta sha bamban da secondary school na riƙe mutuncina, na yi maka alfarma zuwa sanda zan kammala karatun, na jingine batun samari har zuwa lokacin, zaka share mini tantama a wannan zaka bani mamaki zaka tabbatar da sauyin matsayin dana samu"
Ya yi shiru yana hamdala a ransa ganin maganganun shi sun yi zaman tishin hadda a kanta jin ya yi burus ta ce


"Mene matsayin Abbiey?"
Ya juya sai a lokacin ya kalleta da kyau a hankali ya ɗauke Idanu kafin kamar an yi masa dole ya ce "Ba zan su furta su a yanzu ba Ustaz, kar ki tilasta mini faɗar hakan da gaske ba za ki ɗauka ba, bar lokaci"


Bata sake magana ba, har suka je gida bayan ya yi parking shi ne ya fara fitowa ya matsa yana buɗe mata ƙofa tare da kallon ta, ta marairaice ce fuska cike da gajiya ta ce "Wassh Abbiey na, ka ɗauke ni na ga ji" Ya girgiza kai ta sake cewa


"Ƙafana bayana cikina Abbiey ka taimaki ka ɗauke ni na ga ji" ya kame fuska da kyau yana gyara tsaiwa ya ce "Allah ya yafe miki Ustaza watarana haihuwa za ki fa, ki daina raki yanzu ai ba zan iya ɗau kar ki ba"


"Yee na zama ƴar lukuta Abbiey ba zai iya ba" Ganin ya nufu ta ta yi saurin fitowa tana gudu ta ce "Yanzu sai ka ɗauke ni Abbiey"


"Gudanawa kike? Goyaki zan daga nan har bedroom" Ta yi dariya tana jerawa da shi ta ce "Kuma na yi missing bayanka da gaske Abbieyna mai laushin nan" Girgiza kai kawai ya yi suna shiga ya nufi bedroom ɗinsa, ita ta fara zuwa ta gaida Umma da Baba ƙarami.


Wanka ta yi tare sauya kaya, bata son ɗan kwali gabaɗaya ta ɗaure kanta har baya ta fito parlour taya Umma yin abin buɗe baki, lokacin ta samu Abbiey suna ɗan magana da Baba ƙarami a hankali kalli ɗaya ya yi mata tare da haɗe fuska da sauri ta juya ɗakko hirami Baba ƙarami yana kallon yadda Ustaz ke zare Idanu da haɗe fuska. Bata sake fitowa ba sai da aka yi buɗa baki ta sha kunun gyaɗa da ƙosai sai fruits komai take tunaninta yana kan Zameer yadda yake lumshe idanunsa sa zubin halittarsa da adon da yake musamman yadda yake murza shadda _Pretty_ sunan ya yi mata wani irin it was so special to her. Ƙarfe 12 Ustaz ya kira ta bitar karatun Alkur'ani sosai yake mamakin baiwar iliminta abu ne mai matuƙar wahala ka ji ta kuskure amma yawan ya mata tilawa har sau biyu gashi tunaninta ya kaɗai ta tabbas akwai abinda yake faruwa a rayuwar shalalensa.


Har aka kammala azumi a B.u.k dai kullum suna tare da Zameer abinda ya bawa Mardiyya mamaki sosai, sai ta ce ta daina kula shi amma fur ta ƙi ita ba taga dalilin barin Zameer shi ne namiji na farko daya bata kulawa bayan Abbiey ya nuna mata itama mutum ce, ya bata lokacinsa ya nuna muninta is nothing tunda ba ita ta yi kanta ba, kuma shi colour ɗinta ya yi masa hundred percent. Aka sallame azumi akai sallah Mami ta dinga mamakin kaya masu tsadar gaske da Ridayya ke sawa domin ko Zainura albarka.


A zaune a parlour Ridayya ta samu Mami tana mai yin ɗari-ɗari ta tsuguna ta ce "Mami Zainura ta ce kina kira na" Mami ta jinjina kai tare da zubawa Ridayya Idanu, da sauri kuma ta share hawayen daya zubo mata har za ta yi magana sai Ammi ta fito ganin haka ya sa Mami miƙewa ta ce


"Zo mana" Abin ya bawa Ammi mamaki yau Fatima ke kiran Ridayya? Aikinta ya lalace kenan ko me? Ridayya ta bi bayan Mami har ɗaki ta tsaya bakin ƙofa. Ganin inda ta tsaya Mami ta ce


"Shigo mana" Ridayya ta ƙarasa ta nuna mata leda ta ce "Ɗauki naki ne" haɗaɗɗan lace mai kyau da tsada blue and white ɗinkin riga da skirt "Gobe akwai taron family, ki saka"


"Na gode Allah ya saka da alheri" Zainura ta ce "Wannan abayar ta yi miki kyau Ridayya" Ta ɗan murmusa ta ce "Bari na cire na ba ki, Abbiyena ya siya mini da yawa"


Kan Mami a ƙasa ta ce "Rabu da ita, ki je kar Abbiey ɗin ya jiki shiru ya yi faɗa" Ta ce "Ai baya nan" Fuskar Mami a ɗaure ta ce "Na ce ki je ko?" Jikinta na rawa ta fita domin har ta fara farin cikin jin muryar Mahaifiyarta. Tana murna ta nunawa Ustaz kayan ya dinga kallon kayan ya ce "Mun godewa Mami"


Taron familyn kowa ya bayyan har su Hajiya da mai ran

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login