Showing 45001 words to 48000 words out of 190738 words

Chapter 16 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17325

"Afuwa kai na ƙasa, barka da zuwa Babban mutum, zuwan ba zata haka?" Ammi ta yi murmushi ta ce "Ustaz ya hanya, ashe kana tafe kana lafiya?"


"Ƙalau, Ridayya fa?"
Junaid ya juya ya ce "Ammi ina Ridayya? Ni tun jiya ban sata cikin idona ba" Ustaz ya nufi kitchen haka kawai ya samu kansa da duba CCTV ɗin daya saka ba tare da sanin kowa ba, ya shiga dubawa abubuwan tashin hankalin daya gani sun girmimi tunaninsa jikinsa har wata kakkarwa yake na ɓacin rai zuciyar ta motsa, idanunsa suka juye tare da rikiɗe wa tamkar bashi ba. Daidai lokacin kuma motar Baffa ta sauka a gidan, zuwan Baffa da fitowar Ustaz daga kitchen ɗin sukai daidai. Bilal na zuwa ya ɗaga hannu ya wankawa Ammi mari ta yi baya tana zare ido "Bilal are you out of your sense? Mari fa" Bai yi magana ba saboda gabaɗaya jikinsa rawa yake, ya sake ɗaga hannu ya sauke mata wani mai lafiya ta yi bata zata kifa ta juya ta kalli Baffa ta ce "Kana kalli a kan Idanunka ya mare ni....," Kafin ta ƙarasa magana shi ma Baffa ya sauke mata wasu tagwayen maruka a fuska, da sauri Ustaz ya juya da nufin ɗakko Ridayya daidai nan kuma Anuty Kaltum ta sauka a gidan tare da mijinta General.
Ustaz na zuwa ya kalli Ridayya ya san idan ya nufe ta a haka zata firgita wannan yanayin nasa ba nata bane, ba zata ɗauke shi ba, dole ya fara samun nutsuwa kamar yadda yake idan ransa ya ɓaci, ya nufi bathroom ya mance bai rufe ƙofar ba, ya cire duka kayansa gabaɗaya ba abinda ya bari ya tsaya a tsakiya tare da sakarwa kansa shower idanunsa ya juye ya daddafe hannunsa da jikin bango ruwa na dukan tsakiyar bayansa. Ba zato ya ji an turo ƙofar ana faɗin "Abbiye.... Abbiey" A gigice ya juya yana cewa "No, Shalale haramun ne jikina stop amma ina......






Abu ɗaya nake nema wajanku shi ne sharing fisabilillahi saboda Allah🥹😢🤲🏻 sai kuma comment. Wannan littafin free book ne masu tambayata ko free pages ya kusa ƙare wa, idan kuɗinne ya muka yawa sai na yi dropping Account number no wahala ai🤓.


Domin gyara ko sharhi
sulaimanshuaibunaima@gmail.com


Na'ima Sulaiman Sarauta
Nimcyluv
08119237616


BRIGHT pens na godiya


*PAGE 16*
Bright pens🤙🏼free batch




Duk saurin Ustaz wajan dakatar da Ridayya daga shigowa cikin toilet ɗin, haƙarsa bata cimma ruwa ba. Ya dafe kai yana murza goshinsa da zufa ke fesu wa ta tsakiyar wajan. Cikin saurin kuma ya saki labulen dake tsakanin jacuzzie da mirror wajan shigowa. Ridayya ganin bata ga Ustaz ba ya ɗan leƙa kanta cikin sanyin muryarta ta ce "Abbiey, nine, gani" Ta furta idanunta na rufe wa sosai srup ɗin da Ammi ke mata ya yi matuƙar tasiri a kwakwalwarta, she's always sleeping. "Abbieynaa!" Ridayya ta furta tana mai janye idanunta ta buɗe su da ƙyar, saboda wani irin maganaɗisun bacci dake ribatar idanunta. Ustaz dake tsaye dafe da kansa gabansa sai tsananta bugawa yake, da ƙyar ya samu ya zura jallabiyya a jikinsa ko hiramin bai samu zarafin ɗaurawa ba ya ɗaga laubulen ya fito, idanunsa ya sauka a kan ta, ganinsa tsaye a gabanta ya saka ta buɗe bakinta tare da yin murmushi. Ya girgiza kai a hankali ya sunkuya ya ɗauketa a kafaɗa suka fice daga toilet ɗin zuwa bedroom ɗin Ustaz.


Ƙoƙarin kai hannu take zata taɓa tsayayyen gemunsa dake zubda ruwa ya yi saurin riƙe ɗan mitsitsin hannun nata, idanunta zube a kanta ya ce "Na roƙe ki Shalale ki ce ba kiga Abbiey yanayin haramci ba..," Ta yi shiru tana kallonsa ya janye idanunsa sai kuma ya juya da sauri bayan wani abu ya zo ransa ya cafke hannayenta muryarsa a daƙushe ya ce "Me hakan ke nufi Shalale? Da gaske ban fahimta ba, nikam ban fahimta ya zan yi da al'ƙawarin dana ɗaukar wa kai na? Kin rusa komai kin rusa tunanin Abbiye Shalale" Ya yi baya tare da kwanciya yana rufe ido, kokawa yake da tunaninsa wanda ya rabu kashi-da-kashi. "Babu mai ganin tsaraicina sai matata!" Kalaman suka dawo masa, koda wasa ya faɗi abu to gaskiyar kenan, ya zai yi da wannan jirkitaccen al'amarin? Ya miƙe tsaye kamar zai fita ya dawo ya durƙosa daidai tsayin Ridayya duk ya gaji da magana, kuma da taimakon shi dole bakin Ridayya zai buɗe, ya kalli cikin idanunta da suke sauya masa kala a kullum a kodayaushe a taushashe ya ce "Shalale kin ga abin a halin da matarsa ce kawai zata gansa?" Cikin rashin fahimta Ridha ta kalli Ustaz, jin ya ambaci sunan Abbiye ya saka ta yi murmushi dimples ɗinta na lomawa kana ta ɗaga kai, Ustaz ya yi saurin girgiza kai yana runtse gajiyayyun idanunsa masu laushi, faɗuwar gaba na wanzuwa a ko wanne lungu da saƙo na ƙofofin zuciyarsa, ya tsune laɓɓansa a nutse ya ce "Subuhanallahi! Hakan na nufin...?" "Zata zama Matarka idan har da gaske al'ƙawarin zuciya ne, kuma zuciyar ta Ustaz Muhammad-Bilal"


Ustaz bai juya ba, domin ya fi kowa sanin mamallakin muryar. Umma ta ƙarasa shigowa cikin bedroom ɗin ta juya ta kalli Ridayya ta kuma kalli Ustaz kana ta ce "Sai ka ce rainon matarka kake bamu da labari" Ya yi shiru ta taɓe baki kana ta ɗora da "Da sake an bawa mai kaza ƙafa, ka gaggauta sauya tunani" Sai a lokacin Ustaz ya kalli Umma kamar ba zai yi magana can dai ya girgiza kai ya ce "Umma please, kai na ciwo yake" Domin bashi wata magana bayan wannan ɗin, bayan ita kuma bai san wacce magana zai furta Umma ta gane tsakaninsa da Ridayya zumunci ne kawai. Umma ta ce "To, ta dai haramta a gare kuma, she's not your type, kwailar ma?" Ya kalli Ridayya sosai kana ya kalli Umma ya ce "Mene kwaila?" Ta ce "Baka sani ba?" Ya yi shiru ta yi murmushi ta ce "Kwaila ana nufin ƙaramar yarinya, ƴar mitsitsiyya wacce bata fara irgan dangi ba, balle batun al'ada" Ya sake juya idanunsa duk a gajiye yake daga jiya zuwa yau "Irgan dangi?"


"Nono irin na ko wacce ɗiya mace nake nufi Ustaz" Ustaz ya yi saurin rufe ido yana miƙewa tare da toshe kunnensa ya ce "Ya Rasulullah Asstagafirullah, ba a kunnen Muhammad-Bilal ba" Umma ta ce "Tunda na yi saƙo ba? Shekarar ta shida kai kuma shekara ashirin da biyar, ƙanwarka ce babu wani zance bayan wannan" Har ta fita ta tuna abinda ya kawo ta, ta ce "Ana kiran ka a sashin Baffa" Tana furta hakan ta yi waje tana jan tsaki, halin Ustaz gabaɗaya a bauɗe yake ta rasa waya gado? Tana fita Ustaz ya juya ya kalli Ridayya da ta yi shiru idanunta a kasalance ya saka ƙafa tare da zungureta ta buɗe ido a gigice jikinta na rawa da ɓari tunaninta Ammi ce, domin komai yana zaune a ranta daram kamar yadda al'amarin ya nuna a karatu, haddar ƙaramin yaro, kamar rubutu ne a kan dutse ganin Ustaz ya saka ta kwaɓe fuska za ta saki kuka.


"Ni zan yi kuka ba ke ba Shalale, kin ga abinda kika jawo, zan nema miki gafarar Ubangiji ƙuruciya ce da rashin sani" Ya miƙe tare da ɗaukan ta ya nufi ɓangaren Baffa cikin takun nutsuwa da zallar kamala, dab da zai ƙarasa annurin fuskarsa ya ɗauke ya yi kicin-kicin da fuska tamkar ya ce ya shiga uku, ya tsuke girarsa har haɗe wa take saboda tsabar baya son raini. Yana zuwa Ammi dake dafe da fuska domin marin Ustaz ya gigita ta, kunya take ji ya sauke hannunta a ga zanen yatsun shi daya kwanta a fuskarta. Baba ƙarami ya kalli Ustaz ya ce "Muhammad-Bilal mene hujjarka na marin matar ubanka?" Ustaz ya yi shiru domin haka nan ya ji baya buƙatar wani surutu, ya tsaya iya shi da ita Ammin.
"Ina magana ka yi shiru?" A hankali ya ce "Abba!"
Ya faɗa yana nutsa idanunsa cikin na Baba ƙarami "Ba'asi nake tambaya, domin ba zan lamunta ba" Ustaz ya yi shiru Baffa ya juya kan Ammi ya ce "Ke me ki ka yi masa, ya ake neman haukata mini tunani ne a cikin gidana?" Ammi ta ce "Ni ni ni ce da laifi, amma ya shige ba komai na yafe masa" Anuty Kaltum ta buga shewa tare da yin tafi ta ce


"Ai daman duk ɗan tauren da ya je barbara ya kwana da sanin da ciki zai dawo" Baffa kansa sai juyawa yake ya rasa meke masa daɗi ya juya ya kalli Anuty Kaltum da mijinta General ya ce "Anuty Kaltum wai meke faruwa ne, can you help me?"
Ta yi dariya ta nuna jin daɗi da Allah ya gwada mata wannan rana ta ce "Me kowa yake faruwa banda girbar abinda ka shuka? Ai duk wani rami daka tsinci kanka a ciki yanzu, to kai ne ka haƙa abinka da kan ka Alhji Mansur" Baffa ya girgiza kai tamkar zai yi kuka ya ce "Bari na kira Fatima a ɗakinta nasan ba zata bar ni a duhu ba" Anuty Kaltum ta ce "Hanzarta"
Baba ƙarami dake zaune ya girgiza kai ya ce "Dawo nan ka zauna Alhji Mansur babu Fatima a gidan nan" Komai na Baffa ya tsaya cak, domin bai fahimci Fafima bata gidan ba, ko ya ji bata taɓa yi ba, ina zata bada izinin shi ba?
"Shekaru Shida da suka gabata, ka saki Fatima a kwana biyar da haihuwar yarinyarta, bayan ka aibata yarinyar ranar da aka haifeta ka ce ba kai ne ubanta ba, ba kuma zaka taɓa zama uban jaririyar Fatima ba,ka ce a je a nemi ubanta"
Zufa ta dinga yankowa Baffa jiri na neman kada shi wanwar a ƙasa. Anuty Kaltum dake tsaye ta ce
"A shawar ce daka nemi wajan zama, don zaka iya yanke jiki ka faɗi babu mamaki daga nan ka samu shanyewar ɓarin jiki tun a nan duniya"
Zuhura dake tsaye zuciyarta kamar zata fito don baƙin ciki, ga marin da Ustaz ya yi wa mahaifiyarta, ga cin mutumcin mahaifinta da Anuty Kaltum ke yi, cikin masifa ta ce
"Babu abinda zai same shi, kuma Mala'iku suna cewa walaaká ga duk abinda ka roƙa wa waninka" Anuty Kaltum dake jiran kaɗan ta ce
"Ji banza shasha, ki bari ki samu cikakken ilimin kawo fatawa, kuma idan har haka ne ki shirya ganin abinda kema zai same ki ta dalilin babarki" Zuhura zata sake magana ta ji an daka mata wata razananniyar tsawa a kiɗime ta juya ta kalli Ustaz da jijiyoyin kansa suka gama bayyana suna harbawa ya ce "Out!"
Da sauri ta fice daga parlourn zuciyarta na faɗawa cikin ƙiyayyar Ridayya domin ta san all this happened because of her, ita ɗin annoba ce!
Baffa ya kalli Anuty Kaltum ya ce "Anuty Kaltum da gaske na saki matata Fatima, kar ku yi mini wasa da hankali"
Anuty Kaltum ta ce
"Ya shige wai, amma ai ya zama tarihi domin Fatima tuni ta samu mijin aure, mun zo batu a kan Ridayya a bamu ita mu tafi, a wannan karan babu ɗaga ƙafa ina tare mijina General Buba Manti" Baffa bakin Anuty Kaltum kawai yake kallo kamar wacce ba Hausa take furtawa ba ta ce
"Faɗi ko wanne yare kake ji, ina da ƙarfin qiwwar yi maka shi ni ba irin makirar matarka ba ce empty head" Ammi ta ce "Kaltum ya ishe ki haka nan, Ridayya kuma babu inda zata ƴata ce har abada kamar yadda mijina ya bani ita"
Junaid dake tsaye ya ce "Ammi ki bar wannan maganar ki bari a tafi da ita" Ammi ta ce "Zanci Ubanka Junaid idan manya na magana kana saka baki, kai ki damuwa bakya yi za a tafi da ƙanwarka?"


"Kin nuna masa damuwa da ƙanwar ta shi ne? Maryam bata wajanki na zo ba, karki nemi tunzura ni, ƴar masifa ce ni babu wani kalar tijira da ban iya ba, da matar General Buba Manti kike magana ko a sojojin sanin irinsa zai yi matuƙar wahala"
General dake tsaye ƙiƙam! Kamar gunki ya dakawa Baffa tsawa ya ce "heyyy where is the baby?" Baffa ya yi shiru domin shi bai ba san a kan wa ake magana ba, shi tunaninsa da dukkan wata nutsuwarsa yana ga matarsa FATIMA ZAHRAAH. "Zan cire maka yatsun hannu a nan wajan, I said where is the baby?" Junaid ya ce "Ka yi haƙuri, za a kawo Ridayya"
Hankalin Ammi ya tashi domin tafiyar RIDAYYA MUHAMMAD-BILAL RANO tamkar rushewar plan ɗita ne. "Ni ban ma san inda wa ma kuka ce?" A zafafe General ya ɗaga hannu zai kifawa Baffa mari a hankali Ustaz ya ce "No please"
General ya juya domin bai san da zaman Ustaz a wajan ba. "Ridayyerh na waje na, zan riƙe ta In sha Allah" Da ƙyar Baba ƙarami ya shiga cikin rigimar ya bawa General Buba Manti haƙuri tare da Anuty Kaltum.


Hankalin Baffa ya tashi shikenan suntirin gidan su Fatima, ita kanta idan ta ce bata zumuɗin ganin ƴar cikinta ta yi ƙarya, ko a baya bata san mene ya hanata zuwa ganin Ridayya ɗin ba. Anuty Kaltum sai da ta rahama duk wani ta'addaci da Baffa ya yi mata, har yana cewa sun raba shi da matarsa ba wani laifi, shi kam ko haka ai sun gasa shi idan ma haukata shi za su yi ba. Ya kuma mayar da Fatima tuni, Dada ta shiga maganar a nan akai addu'a Baffa ya sauyawa Fatima komai na part ɗinta, jinsa yake kamar sabon aure zai yi har magani ya sha ya fam abinsa. A daren da Fatima ta dawo ko inuwarsa bata ishe ta kallo ba, wani abun ban malak duk yadda take zumuɗin ganin Ridayya da rungume ta a jikinta ta faɗa mata yadda take so da ƙaunar ta, amma Mami ta kasa har mance wa take tana da wata ƴa a gidan tsakaninta da ita idan ta ganta a parlour shima idan sun zo tare da Ustaz ne. Ridayya ko inda Mami take bata taɓa zuwa ba, ko gaisuwa sai Ustaz ya ce Shalale a gaida Mami sai ta maƙale kafaɗa.


A ɓangaren Ammi farraƙu ta saka aka yi mai tsanani tsakanin uwa da ƴar, ya zamana ko wuta Mami za taga Ridayya zata faɗa ba zata taɓa yin magana ba, haka kuma Baffa sam bai damu da Ridayya ba komai zai lissafa na yaransa babu ita, Ammi ke nan nan da ita ta nuna mata soyayya kamar zata cinyeta a gaban mutane har lokacin kuma bata bar bawa Ridayya maganin maye ba. Rayuwa na juyawa komai na sauyawa, Baffa ya dawo da halinsa a kan Mami sam bai damu da ita ba, itama rayuwar haƙuri kawai take biyar tasa ya daina shiga hannunta, lokacin zuri'ar ALHAJI MANSUR ta ƙara yawa, Mami nada Zuhura, Junaid, Balkisa, Abdullahi, Khaliperh, ta yi ƴan uku su ne Usman, Umar, Abubakar, sai autanta Aliyu. Daman kuma duk sun girmewa Ridayya Aliyu ne kawai ta girma. Ridayya nada shekaru goma a duniya Mami ta samu ciki, ba wanda ta faɗawa ko Baffa bai sani ba.


Muhammad-Bilal Ustaz ya dage komai na rayuwa shi ne ya kewa Ridayya, tuni ya kaita asibiti tana amsar magani, shigar Ridayya makaranta ya zama sabon babi na rayuwa a gare ta, bata fahimtar karatu sam, kullum cikin bacci take sai ta gama yini a makaranta bata fahimci komai ba, dalilin hakan ran Abbiye ba ƙaramin ɓaci yake ba sai ya yi kamar zai dake ta sai ta fashe da kuka tana faɗawa jikinsa tare da bashi haƙuri, ya zage yana koya mata wani ta fahimta wani sai addu'a. Suttura komai na rayuwa Ustaz ne duk wanda ya tambayeta waye babanta sai ta lumshe idanu ta ce "Abbiey" Bata da ƙawa kowa gudunta yake wai daƙiƙiya ce kar ta shafa musu, gashi wata jarrabawa ita kaɗai sai a ga ta faɗi tun ba a fahimci menene ba har aka gane ai Farfaɗiyya ce ke damunta.


Mami na zaune Abdullah ya shiga part ɗinta ya sameta a parlour ta yi shiru tana tunani ya kalli yadda ta caɓa kwalliya ko'ina na sai ƙamshi yake "Mami" Ya faɗa da ƙarfi ta yi saurin buɗe ido ya ce "Ina ta sallama lafiya kowa? Ko wani abun ne?" Ta yi murmushi ta ce "Lafiya Abdullah, zauna mana?" Ya ce "Ba sai na zauna ba ai, Ridayya ce ta faɗi" Ta ƙura masa ido sai ta ce "Ina zuwa" Yana fita ta miƙe tare da shigewa bedroom ta kwanta tuni ta manta da babin wata Ridayya.
Cikin jikinta ya saka mata wata irin kewa da so da ƙaunar kasancewa da mijinta. Ta duba lokaci taga wajan 10 na dare kuma ita ce da girki,ta miƙe tana nufar part ɗin Baffa da nufin kai masa ziyara ta sauke wani jan aji na ɗiya mace, tana shiga ta ji tsit sai ta nufi bedroom da sauri ta yi bays zuciyarta na bugawa da ƙarfi ganin Baffa tare da Ammi kuma a ranar girkinta babu abinda ya fi ɗaga hankalin Mami sai furucin Baffa da yake cewa "Dake kawai nake kasancewa na ji daɗi Maryam, Mairamu, Mero na, jin Fatima nake tamkar gidan biredi, ji nake kamar ana gasa ni, gabaɗaya azaba nake sha, Maryam kece mace ɗaya tamkar da dubu na baki naira dubu ɗari" Ammi ta ce "Fatiman ce kamar gidan biredi?" A gigice ya ce "Tama fi, haƙuri kawai nake da ita yadda kika san ruwan sha, Maryam na ƙara miki wata dubu ɗarin" Ammi ta ce "Ba dubu ɗari nake so ba, furnitures ɗin part ɗin Mami nake buƙata, da duk wani abu daka mallaka nata"
"An gama yadda kika ce haka za a yi" Wannan maganganun ya rusa duk wata sauran yadda da ta yi wa Alhji Mansur Rano, ta rasa me yake mata daɗi wani irin kalar cin mutunci ne wannan? Ta durƙushe a wajan tana kuka. Ammi ta gyara zaman jigidar data siya a ƙugunta ta shirya ta nufi hanyar fita, a parlour ta samu Mami, fuskarta ɗauke da murmushi ta ce "Mami kina nan?" Idanun Mami a kan wayarta ta jinjina kai, Ammi ta ce "Nima zuwana kenan ban samu Baffa ciki ba" Mami

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login