Showing 33001 words to 36000 words out of 190738 words

Chapter 12 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17290

cewa take ya je ya ganota kar tunaninta ya haukata mata miji cike da zulaya take furta haka, sai kawai ya harereta irin ai na fiki sanin me nake.
Baba ƙarami yayan Baffa ya jinjina kai ya ce
"To ya kake so a yi kenan Mansur?" Kai tsaye ya ce


"Kawai a nemi uban yarinyar, wallahi tamkar na saka hannu na murɗe wuyanta haka nake ji, wannan ai baƙar kadara ce, annoba, kuma wake ɗaya mai ɓata miya Fatima fara ce tas, ni ma fari ne tas, yarinya kuma da sharɓeɓan leɓe harshe a waje? Hanci zai yi goman nawa? Jibi suma duk saman fatarta? Wallahi ƙila aljana ce ba" Murmushi kawai Baba ƙarami ya yi ya ce "To wa za a nema matsayin uban nata? Ko zaka taya mu lalube ne Mansur?" Baffa ya yi shiru.


"Wanne suna kake so a saka mata?" Aka faɗa a taushashe cikin sanyin murya, Anuty Kaltum ta kalli wanda ya yi maganar domin tunda ya zo wajan gabaɗaya maganar da ya yi ba takai huɗu ba. Rai a matuƙar ɓace ta ce "Tambayi mahaukacin ubanta gashi nan" A fusace Baffa ya ɗaga hannu zai kifawa Anuty Kaltum mari, Mai ran ƙarfe ya yi saurin riƙe hannun. Anuty Kaltum ta fashe da dariya tana tafa hannu ta ce
"Basshi, basshi ya taɓa ya taɓa wa kansa masifa da bala'i, da matar soja kake magana, wallahi sai na saka a ɗaure ka ka yi life in prison, kaf zuciyarmu babu faƙiri matalauci, kuma mai ƙarancin ilimin addini, aikin banza nifa daman tun farko wannan mutumin bai mini ba"


Ganin hayaniyya na neman tarwatsa masa kai, da kuma yadda jaririya ke saurin firgita ya sanya ya ƙara rungume ta a ƙirjinsa a hankali numfashinta mai zafi ke sauka, bakinsa ɗauke da addu'a yake ɗan tofa mata sama-sama. "Muhammad-Bilal" Baffa ya kira sunan Bilal a harzuƙe, cak ya tsaya kamar ba zai juya ba sai kuma ya ɗan yi baya tare da kafe Baffa da kallo na ya akai? Wannan tsawar fa? "Ka basu tsiyar su, su nemi ubanta"


"Ni ne ubanta, yarinyata ce, zan kula da ita a matsayin uba" Bilal ya faɗa idanunsa cikin na Baffa. Wata dakakkiyar tsawa Baffa ya yi wa Bilal ya ce "Ka basu ƴar su na ce"


"Ka dai na yi mini tsawa, nikam ka daina bana so, a gaban yara Baffa kalli yara kake mini tsawa a gabansu?" Babban ɓacin ran Bilal har da mutanen da bai taɓa ganin su ba sai yau, amma Baffa zai masa tsawa a kan idanunsu salon su raina shi? Bayan kowa ya san da shekarunsa a ka. Baffa ya ce "Sannu gyanbo, Bilal ka basu shegiyar ƴar su na ce"
Idanun Bilal ya shige ciki saboda ɓacin rai, suka yi jajur jijiyoyin kansa duk suka fito, ba matsalar ƴar ce gabansa ba, damuwarsa faɗan rainin wayo da rashin tubalin yinsa, shi ba wanda ya yi masa faɗa sai shi za a yi wa? For God sake!


"Bilal ni Baffanka ka ke yi wa haka? Ni?" Bilal ya ƙara nutsa idanunsa a cikin na Baffa ya ce "A kan idanuna kake musayar yawo da Hajiya, Hajiya fa, ashe ba daɗi?"


"Me kake nufi da ɗaukan yarinyar nan?" Kai tsaye ya ce "Rainonta zan yi, zan kula da ita, kyautar da ubangiji ya baka ka wofintar ni ina so, zan kula da ita da izinin Ubangiji zan kuma aurar da ita da ƙudirar Allah" Murmushin takaici Baffa ya yi ya ce "Ok, bada kuɗina ba, ba kuma da abinda na mallaka ba zaka ciyar da ita ba, kuma ka tattara kayanka ka bar part ɗina" Bilal ya jinjina kai don baya jin zai iya magana har yanzu idanunsa cikin na Baffa, ganin yana shirin juyawa ya saka Baffa cewa
"Ka basu ƴar nan na ce, Muhammad-Bilal"


"Baffa?" Bilal ya faɗa a rikice yana jin tsawar har tsakiyar kansa, ya taka har inda Baffa yake ya kama hannunsa ɗaya ya damƙe sosai ya ce
"Na roƙe ƙa da ka tsahirta haka nan, ban so da gaske ban so, nikam ban son tsawa, ka bar daga ni sai kai ka yi mini" Baffa ya ce "Sannu ubana" Bilal ya sake runtse idanunsa gam kamar ya nutse a wajan ganin yadda Baffa yake shirin zubar masa da girma "Kashe ni kawai Baffa zai fi wannan" sanin Bilal da masifar taurin kai da son girma ya saka Baba ƙarami cewa "Babban mutum jeka, Allah raya maka ɗiyarka ya sanya mata albarka" Bilal ya lumshe jiƙaƙƙun idanunsa da sukai laushi ya jima kamar ba zai magana ba ya ce "Amin Ya Allah, na gode ƙwarai Baba ƙarami"


"Wanne suna ka saka mata?" Ya yi sak domin bai yi mata huɗu ba sam, yana buƙatar tantance sunan da zai saka mata a hankali ya ce "Zuwa gobe zan saka mata suna" Baba ƙarami ya jinjina kai ya ce
"Allah ya kaimu" Yaya A'isha ta ce "Babba mutum kawo ta, zuwa anjima sai ka amsheta" Bai kalli Yaya A'isha ba, ya ɗan kalli fuskar jaririyar yana sake ƙanƙameta a ƙirjinsa ya jima sai kuma ya miƙa mata ita da ƙyar yana bata yabar cikin asibitin. Yaya A'isha ta juya zuwa cikin room ɗin da Mami take kwance tana hutawa hannunta ɗauke da baby. Anuty Kaltum kuma ta kalli Baffa ta ce
"Muna jiran takardar sakin Fatima, domin gida zamu shige da Ita"
"Ban niyya ba, ban shirya rabuwa da matata ba, kuma kar a kuskura a tafi da ita idan har nine mijinta" Yana faɗin haka ya fita, Anuty Kaltum za ta yi magana Dada ta hana. Kuka sosai Hajiya ke yi Baba ƙarami na bata haƙuri, kana suka dinga bawa su Dada dangin Mami haƙuri akan komai zai shige. Zuhura da sauran yaran suka tafi gida. Zuciyar Baba ƙarami babu daɗi takaicin abinda ɗan'uwansa ya yi, ya masa tsaye a zuciya.


Har kwana biyu jikin Mami bai yi daidai ba saboda jijjigar da ta yi, sai a kwana na uku ta dawo hayyacinta bayan ta buɗe idanu ganinta ya sauka a kan Dada dake zaune hannunta riƙe da azkar, motsin da Mami ta yi ya saka Dada juyawa cikin farin ciki ta ce
"Ma sha Allah autata ta farka" Ƙuri Mami ta mata kafin ta ce "Me na haifa?" Kai tsaye ta ce "Ɗiya mace Allah ya ba ki Batool ɗina" Mami ta yi ajjiyar zuciya ta ce
"Ki yafe mini Dada haihuwa akwai wahala, Allah ya saka miki da alheri da kika haife mu kika kula da mu, bamu da abin saka miki wallahi na ɗauka mutuwa zan yi haihuwa da wahala Dada" Dariya Dada ta dinga yi ta ce "Su Autana an girma an son zafin haihuwa da ciwon uwa, ba ki mini komai ba Allah ya raya mini ke da jikata cikin aminci da kwanciyar hankali" Mami ta yi murmushi, sai rarraba Idanu take taga ta ina za a bata babynta? Ta faɗa mata azabar data sha kafin samuwar ta. Ta kasa haƙuri ta ce


"Ina babyn?" Daga bayanta aka ce "Kima cire ranki daga ita Fatima" a rikice ta kalli Anuty Kaltum ta ce "Saboda me Anuty Kaltum?" A fusace ta ce"A saboda ubanta ya ce shegiya ce ita, bashi ne mahaifinta ba, ki nema mata uba wani wajan" Mami ta dinga kallon bakin Anuty Kaltum kamar zautacciyya, hawaye na zuba daga cikin idanunta ga wani azabar ciwo da nononta ke mata ya cicciko alamar babyn na buƙatar abincinta "Ban gane ba ƴarsa ba ce? Wallahi tallahi tunda nake a duniya babu namijin daya taɓa riƙe hannuna, Baffa ne wanda ya raya daren aurenmu, me na yi masa da zai haɗani da wannan masifar? Anya Baffa ne?" Kuka take kamar ranta zai fita ga ɗinkin dake cikinta nan da nan jikinta ya nemi rikicewa, Dr ne ya shigo yana yi wa su Anuty Kaltum faɗa da ƙyar akai mata allura bacci ya ɗauke ta.
Faɗa Dada ta shiga yi wa Anuty Kaltum a kan a matsayinta na babba don ranta ya ɓaci ba haka ya dace ta yi ba, idan bata kwantar wa da Mami hankali ba waye zai taushe ta?


Bilal na zaune idanunsa ƙuri a kan yarinyar fuskarsa baka tantance yanayin da take ciki. Mahaifiyarsa kallonsa kawai take yi har yanzu bata ce masa komai a kan al'amarin daya faru ba, domin ya tattara ya dawo shashin iyayensa da zama. Ya ɗago idanunsa wanda kullum suke a ƙasa a nan yaga kallon da Baba ƙarami da babarsa suke masa, ya yi kicin-kicin da fuska
"Baban baby har yanzu baka faɗi sunan ƴar taka ba" Bilal ya zubawa yarinyar ido can ƙasa ya ce "RIDAYYA"


"Ridayya" Baba ƙarami ya maimaita kana ya ce "Ma'ana?" Bilal ya miƙe tsaye ya ce "Zuciya, shi ne ma'anar sunan" Ɗakina ya koma ya dawo da wasu ledoji manya manyan guda biyu ya ce "Kayan dana siya nata, gobe za a kawo rago" Baba ƙarami ya ce "Kai, Ma sha Allah har da Ragon yanka? Lallai uban Ridayya mai zuciya ne, ina ka samu kuɗi?"


"Aiki na yi, zan nemi aiki saboda ita tunda na kammala karatuna" Baba ƙarami ya jinjina kai. Ya miƙe tsaye zai shige ɗaki sai a lokacin mahaifiyarsa ta ce "Ina zaka da ita? Ko kana da nonon shayar da ita, ka kaiwa A'isha ita" Sak Bilal ya yi domin ya manta da batun shayarwa ya dinga tunanin wanne nono kuma? "Zan siyo a kanti"
"Shi nonon kenan? Riƙon yarinya na neman sawa ka zauce Babana? Daman nonon a kanti yake ko a jikin uwarta? Bilal ya gwalo ido ai shi ya mance da wani abu a jikin mace kuma a ce da shi ake shayarwa? Juyawa ya yi ya fita kawai tare da barin parlon don yau da yarinyarsa yake son kwana ta ji ɗomin uba kamar ko wacce jaririya.


Washegari da safe Ammi na zaune sai kuka ta ke a kan Baffa ya ji tsoron Allah ya amshi Ridayya, ko ita ce ta amince zata riƙe ta da amana zata kula da ita kamar su Zuhura da Junaid. Tausayin Ammi ya kama Hajiya wacce take shirin tafiya Rano, bata taɓa ganin kishiya mai tausayi kamar Ammi ba, har tattara kayanta ta yi ta ce zata bar masa gidan tunda haka ne. A haukace Mami ta shigo gidan kai tsaye ta yi wajan Baffa ya ce "Baffa ina soyayyar? Ina tattalin ina yardar? Ka tausaya mini kada ka aibata ƴata, bayan ita halastacciya ce, ka da ka yi mata baƙin tabon da zai dinga bibiyar rayuwarta, kada ka yi abinda za ka yi ladama, wallahi ban taɓa kusanta kai na da zina ba, ban taɓa ganin wani namiji bayan kai ba, shin Ubangiji ba shi ke halittar bawa a yadda ya su ba? Baka halitta bana halitta balle mu zaɓi kalar yaran da muke so mu haifa, kalar halittar Ridayya har ya kai ka nisantaka da jininka? Har ya kai ka laƙaba mata kalmar shegiya? Kada ka gurɓata rayuwar ƴarka tun ƙuruciya Baffa ba roƙe ka" Tana kuka Ammi na yi kuka, Anuty Kaltum ta cika ta yi fam ganin kukan Ammi take tamkar na munafurci.
"Fatima wallahi tallahi na rantse da Allah ba zan amshi yarinyar nan ba, bana buƙatar sanin uban nata ki shige cikin ɗakinki ki zauna"


"Ɗakin ya ci uwarsa da ubansa, wallahi wallahi Fatima ba zata zauna da kai ba, ka sauwaƙe mata" Baffa ya jinjina kai ya ce "Na sauwaƙe miki?"
Mami ta ce "Muddin ba zaka amshi yarinyar da Ubangiji ya halatta maka ita matsayin jininka ba, ni kam ka sauwaƙe mini zan raini yarinyata in sha Allah, Ubangiji zai mini sakayya" Baffa ya jinjina kai ya kalli Ridayya dake hannun Bilal kana ya kalli Mami ya ce "Tunda haka kika zaɓa shikenan, na sake ki saki ɗaya Fatima na sauwaƙe miki"
Saki babu daɗi musamman idan da soyayya, ta dinga kallon Baffa sai ta ji komai na yayewa na soyayyar da take masa daga ƙirjinta, wani abu ya tsaya mata sai kuma ta miƙe tsaye ta ce "Babban mutum bani Ridayya" Kafin ta amsheta Baffa ya yi caraf ya amshi Ridayya daga hannun Bilal ya juya ya damƙawa Ammi ya ce "Riƙe ta na bar miki ita halak malak Maryama, na bar miki ita Ammi"


Cikin tashin hankali Mami ta ce "Kamarya ka bata ƴata? Ina saboda ita na zaɓi ka sauwaƙe mini domin rayuwa da ita? Da raina ina raye ƴar dana haifa zaka ce mini ka bawa kishiyarta Baffa, kishiyata ita zata raini ƴar dana haifa, ƴar da ka ce ba taka ba ce?"
Baffa ya ce "E, yanzu kuma na amsheta matsayin ƴata, kuma na bawa Maryam ta raineta bana buƙatar ku rayu tare tunda kika ɗanɗana mini baƙin ciki, to kema za ki ɗanɗana naga kina mugun son waccan mai kama da dalma ɗin ko? To na raba uwa da ƴa na zaɓi kishiya ta kula da ita, ke kuma ki bar mini gidana yanzu yanzu?"
Jiri Mami ta fara gani a idanunta kanta na juyawa ta nuna Baffa da hannu kana ta miƙawa Ammi hannu ta ce "Bani ƴata Maryam" Ammi ta yi murmushi ta ce "Zan bi umarnin mijina zan kula da ita tamakar ke"


"Ƙarya kike baƙar munafuka makira, macuciya azzaluma" Anuty Kaltum ta faɗa tana yin kan Ammi, Ammi ta fashe da kuka,jin kukan Ammi ya saka Baffa rikicewa kansa ya fara juyawa baya ƙaunar jin kukan nata kafin Anuty Kaltum ta ƙarasa wajan Ammi Baffa ya fincikota tare da sharara mata maruka wani ihu Mami ta yi sai kuma ta sulale a wajan babu numfashi.....








Imagining kana raye a duniya kana numfashi mijinka ya ɗauki jaririyar da ka haifa ya bawa kishiya ta raina, anya?






Share fisabilillahi🤲🏻💔
Na'ima Sulaiman Sarauta
Nimcyluv
08164069385
sulaimanshuaibunaima@gmail.com
*✿ MUNAFUKIN MIJI 13 ✿*
Mikiya Writers Ass.....




BRIGHT PENS🤙🏼 free batch




Masu tambayar ko ina yin paid Advert? Ina yi ga wanda suke buƙata su yi magana 08164069385


Don Allah a yi following WhatsApp channel ɗina🥹😢👇🏼 faka-faka
https://whatsapp.com/channel/0029Va5fqs7E50UpMpXolU1T








Yaya A'isha ce ta nufi kan Mami dake zube a sume tana kuka da ihu domin zaton ta Fatima Batool ta rasu ta ce "Anuty Kaltum ki rabu da su ki zo Fatima, ina jin ta rasu Fatima ta mutu Anuty"
Idanun Anuty Kaltum jajur a haka take bin Baffa da kallo dafe da kuncinta, zuciyarta na yi mata zafi da raɗaɗi ta ce "Alhaji Mansur ni ka mara a kan wannan azzalumar wacce daka gani babu Allah a ranta? Ni matar General ka daka?"


"Zan miki abinda ya fi duka, muddin za ki shiga hurumin da bai shafeki ba, ƴa dai na ce bana so, yanzu kuma na amsa na yarda ƴata ce, na kuma dawo na amshi ƴar daga hannun uwarta na bawa kishiyarta ta raina, ita na fi gamsuwa data raini yarinyar idan kuna ganin hukuncin dana yanke bai yi ba, sai ku yi abinda kuke ganin shi daidai" Ya ƙare maganar cikin ƙonar kaifin ya juya ya kalli Ammi ya riƙe hannunta ya ce "Sorry, bata dake ki ba ko? Bata ji miki rauni ba?" Kuka Ammi ta fashe da shi tare da zubewa gaban Baffa ta durƙoshe ta ce "Baffa nikam na yafe wallahi ba zan iya rainon Ridayya ba, kana kallon kallon zargin da ƴan'uwan Fatima suke mini, ba zan taɓa cutar da wani rai dake numfashi a duniya ba, balle kuma na cutar da jinin Mami, ban taɓa ɗaukan Mami matsayin kishiya ba, saboda ta yi mini karamci a rayuwa, ta bani kai na aura ba tare da ƙyashi ba, na haifi Junaid ta kula da shi ba cuta ba cutarwa, don Allah don Annabi ka bawa Mami Ridayya ta kula da ita ta ji ɗumin jikin uwa mahaifiya, kar ka raba soyayyar gaskiya raba uwa da ƴa tamkar ka kashe mutum wa'adinsa bai yi bane ka tausaya mana, ba lallai ka fahimci haka ma amma ni ma uwa ce na san zafin haihuwa"
Anuty Kaltum kallo Ammi kawai take, Hajiya ma haka hatta Mai ran ƙarfe tausayin Ammin ne ya kama shi.


Muhammad-Bilal jingina ya yi da jikin bango idanunsa zube a kan Ammi, tunaninsa ya bambanta dana sauran jama'ar dake wajan, a hankali ya girgiza kai a zuciyarsa ya ce "New Episode" Ya harɗe hannunsa zuciyarsa na bugawa na rashin sanin haƙiƙanin hujjarta ta yi hakan. Baffa ya kalli Ammi sosai da kyau cikin kakkausar murya ya ce "Maryam ke na yi niyyar ki raini Ridayya, ke nake da muradin ki yi hakan, ai ita ma ta yi miki rainon ɗan'ki Junaid, sai a ramawa kura aniyyarta"


Ammi ta girgiza kai sai kuma ta sunkuyar da kan ƙasa ta ɗan jima can ta ɗago ta ce "Ba zaka fahimci kuskuren da kake shirin yi ba sai gaba, Allah yana kallo tun kafin Mami ta haihu nake ƙaunar abinda ke cikinta, bana jin zan iya cutar da jikinta, idan ni na san haka ai ƴan'uwanta ba za su lamunta a ce kishiya ta yi rainon ƴar'ƙanwarsu ba, ita kanta Fatima ba zata aminta ba, Ridayya ita ce jininta ita ce haihuwarta ta fari ka bari su rayuwa tare" Baffa ya ce
"Kar ki mini haka Maryam, muddin ba ki amshi Wannan ƙazamar yarinyar ba, to wallahi tallahi za ki sha mamaki na, kuma ba zan taɓa bawa Fatima ƴar ba"
Sunan Fatima da Baffa ya kira sai ya ji kamar an saka guduma an daki tsakiyar kansa, ya yi baya da sauri yana riƙe kansa.


"Ni ma ka sauwaƙe mini kamar yadda ka sauwaƙe wa Mami, sai ka zauna da yaranka kawai" A gigice Baffa ya zube gaban Ammi idanunsa a ƙanƙance yana riƙe ta kamar zai yi mata sujjada ya ce "Na tuba, na bi Allah na biki Maryama kar ki kuskura ki sake furta kalmar saki, azaba kike gana mini a zuciyata, aure na dake kamar auren zobe ne, auren alƙawari, auren yarda da juna da aminta muddin na barki zan iya rasa raina" Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Ammi ta sauke. Hajiya dake tsaye ta ce "Duk ba za a yi haka ba, matsalarmu ɗaya ce shi ne, sheganta yarinya da Mansur ya yi. Allahamdulillah yanzu kuma ya amshi ƴarsa da Maryam da Fatima duka ɗaya ne, ko a wajan wa Ridayya ta tashi ba za ta yi assha ba, Ke Maryam ki riƙe Ridayya Allah ya rayata har zuwa lokacin da Mansur da Fatima za su daidaita kan su, ta dawo gidan"


Anuty Kaltum ta ce "Ai da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login