Showing 69001 words to 72000 words out of 190738 words

Chapter 24 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

18731

shafe sati bai nutsa ta a idanunsa ba. Yadda ta rufe jikinta ya tabbatar masa akwai matsala a ƙarasa a nutse hannunsa a bayansa, kansa ko hirami babu duk ya hargitse gashi da yalwar suma kamar ita. Ya zauna gefen gadon ya jima kafin ya saka hannu ya janye bargon zuwa ƙasa ƴar body short ce a jikinta wacce ta sauya da ƙyar ya ɗan zame idanunsa daga kan cinyoyinta ya watsa saman fuskarta ta yi saurin rufe haka kurum kunyar Abbiey ɗin ya kamata sosai...


"Tashi zaune" Nan da nan idanunta ya kawo ruwa ta ce "Abbiey ba zan iya ba" Ya yi jim sai kawai ya saka hannu ya ɗago ta zuwa jikin gadon ya kalleta idanunta a rufe yana damƙe hannayenta cikin nasa ya ce


"Kalle ni Ustaza, kalli cikin Idanuna"


"Ba zan iya ba, Abbiey wasu abu ne a cikin idanunka ina kalla sai tsigar jikina ya tashi na ji wani abu daban" Ta faɗa da iyakar gaskiyarta ya girgiza kai maganar ma azaba ce a tattare da shi ya yi miskilin murmushi bisa tilas a nutse ya ce


"Kallon idanuna su ne zai ba ki damar mallakar wanda kike da buƙata a rayuwarki Ustaza, just look at into my eyes"


Ta ɗago a hankali ta kalli idanunsa kamar yadda yake kallonta, kallon kallo ake tsakanin Ustaz da Ustaza, abubuwa da yawa yake ganowa cikin maganganun da idanunta suke, yayinda ita kuma ta kasa me nasa Idanun yake faɗa jikinta ne dai ya fara rawa bata ankara ba ta ji fuskarta cikin tafukan hannunsa ya ce "Ki tabbatar mini mafarki nake a yanzu Shalale"


"Ba mafarki bane ba Abbiey ka taimaka ka yi mini abinda nake so idan kana so da gaske, ka faɗawa su Abba Zameer nake buƙata, Abbiey kalli sumar kan ka ba haka ta Zameer take ba, Abbiey kalli jallabiyyar jikinka shi kullum shadda yake sawa, yadi voyel masu kyau, nikam ka yi haƙuri"


"Idan na amince shikenan?" Ta jinjina kai ya saki fuskarta yana yin baya idanunsa rufe tana ganin yadda ƙirjinsa ke ɗagawa jijiyar kansa duk a bayyane. "Na Amince Ustaza Allah ya sanya albarka ya ba ki farincikin da kike nema a can"


"Na gode sosai na gode Abbiey best father in the world, i love You"


Cikin kulawa ya ce "Ban san yaushe ne har kika zama haka ba, shigar ki University ko kafin nan? Babu tabbaci. Allahamdulillah farin ciki na ɗaya iya yina na ba ki tarbiyar da ya dace a bawa ɗiya mace kuma na yi alfahari da mutuncinki za ki shiga gidan miji, babu wani abun aibu da miji zai goranta miki Ustaza dukda cewa soyayyar gaskiya bata da wani dalili, nutsuwar hankali da samun sauƙin zuciyata yadda kika kula da darajar ki na mace, za ki gidan miji da budurcinki Ustaza na yi ma Ubangiji godiya. Kema na gode da riƙe kan ki da kikai" Ya miƙe ya nufi waje sai kuma ya tsaya cak


"Ki sha magani, zan turo miki Zainura ta ba ki"


"Abbiey baka taɓa mini haka ba, kai kake bani magani fa? Kake tsefe mini kai ka yanke mini farce ka wanke mini sumata. Abbiey kai ne kake zaɓa mini kayan sawa kake mini magana a hankali me ya sa yanzu Zainura?"


"Ke kika zaɓa mana haka Ustaza"


"I am sorry Abbiey" Ya juya tare da ficewa.


Ustaz ya fahimtar da Baba ƙarami muhimmacin auren da Ridayya ke so, tunda ya fara magana kawai yake kallonsa kafin ya ce "Ok daman ba son ta kake ba?"


"Abba Allah ya yafe maka akan wannan maganar, ni mahaifi ne" Wani kallon baka da hankali Baba ƙarami ya yi masa kafin ya ce "Ya yafe maka dai a kan ƙaryar da ka yi wacce baka taɓa yi ba, Ubangiji ka yafewa Muhammad-Bilal Tahir Rano" Ustaz ya yi shiru fuskar Baba ƙarami babu walwala a ciki ya ce


"Babu laifi, na ji na kuma yarda baka son Ridayya a je a haka. Daman na zuba maka idanu ne da tunanin kana kiwo da kuma rainon matarka ne ashe wani kake wa, well is allowed ba zan zuba maka idanu haka ba shekara ɗaya ɗaya har shekaru arba'in kana gabana, yanzu ina buƙatar sarari da space ina son ganin jikoki burjik tunda kai ɗaya Allah ya bani, ka gaggautar fitar da matar aure Muhammad-Bilal tun muna mu biyu"


"Gori Abba, haba babu kyau gori fa ina buƙatarka sosai a yanzu Abba ka ɗan tsahirta mini da maganar aure" Baba ƙarami ya zame kan Ustaz a kafaɗar shi ya ce "Ba wasa nake maka ba, idan baka fitar ma a lokacin zan nuna maka ni na haifeka kuma kana amsa sunan Muhammad-Bilal Tahir"


"Allah ya bani iko" Ustaz ya ce yana kwanciya cinyar Baba ƙarami ya rufe idanunsa a yanzu iyayensa kawai yake buƙata hakan zai sanya ya ji sauƙin dake ransa. Ya tuna al'ƙawarin zuciyarsa duk macen data kalli tsaraicin shi babu shakka matarsa ce yanzu ya zai yi da Ustaza?


Hankali tashe Ammi ta isa wajan bokanta ta tarar ya yi mushe ba wanda ya sani gabanta ya faɗi domin ya faɗa mata watanni bayan mutuwarsa ko shekara duk wani abu da ya yi mata zai zama tarihi. Ta je wajan Biba ta nema mata wani malamin aiki cikin gaggawa amma Biba bata ƙasar tana can saurarawa abinta. Wani abin mamaki kamar an rufe bakin jama'ar babu wanda ya tsaya bincike a kan Zameer da sanin waye shi, asalinsa dama iyayensa.


Duk suna tsaye suna kallon Vedion Moo ya girgiza kai ya ce "Amma mene amfanin yin vedion please?" "evidence na amsar budurcin wacce ake ganin ba zan iya soyayya da ita ba"


Moo ya girgiza kai ya ce "Gaskiya ban ji daɗi ba, kuma har ka zo cikinmu kana nunawa? Yanzu tamkar tsirara haka muke ganinta innocent gril irin Ridayya ka wulaƙanta haka saboda kaga tana son ka? Ina da tabbacin itama bata san mene soyayyar ba tunda burinta kawai ka aureta"


"Ai matsalar ta fara cewa tana son namiji kenan, ya yi amfani da rauninta sosai. You see that madly in love situation is actually a mental health condition wallahi tallahi, birkita ƴan mata yake sosai, Balle kuma idan ya ketara obsession it comes with anxiety,depression, delusion. When God wants to test you, he makes you fall madly in love with an emotionally unavailable GAYE, your own don finish. Wallahi tallahi ina tausayin mace a zamanin yanzu wajan yi soyayya zuciyar mace mai rauni ce, ko yanzu da rauninta ka amfani wajan cimma burinka"


Zameer ya cije laɓɓansa ya ce "To Babana Shaba" Shaba ya ce "Idan na haifi ɗa irinka na tabbatar ban aikata abu mai kyau ba wallahi, Allah ya yi mini tsari Daddynka na Switzerland" Duk suka saki dariya Khalil ya ce "Muga vedion ko?" Zameer ya miƙa masa Khalil ya dinga danne danne a wayar ya shiga WhatsApp ya tura vedion ta number shi yana gama shiga ya saka delete for me yana murmushi ya ce "Oh" Ya miƙa masa wayar kana ya nufi bayan motarsa ya ɗakko ƙatuwar jaka a gabansu ya buɗe kuɗi masu jikin Zameer ya dinga ɓari ganin yawan kuɗaɗen kamar a mafarki ko sanda yake Nahutun Batsari ai bai taɓa ganin kuɗi haka ba, har su yi noma a girbe albarkar noman Khalil ya ce "Ga kuɗinka" Zameer ya amsa Khalil sai cije laɓɓansa yake suna tsaye kuma aka kira Zameer a kan an bashi auren Ridayya ya ture iyaye.


"Auren ta za ka yi bayan ka gama nuna mana tsaraicin ta?" In ji Moo "E zan aure ta In sha Allah"


Zameer tunda ya fahimci Ridayya nada wata kalar baiwa ta musamman wacce ba ko wacce ƴa mace Allah ke bawa ita ba, ya sanya a ransa zai aure ta, kuma zai yanke karatunta baya buƙata domin idan ta yi zurfi a karatu ilimin zai bashi matsala. Tunda Ustaz ya siyi komai da sunan Ridayya sannu a hankali zai dawo wajanta, kuma duk sanda iyayenta suka mutu Ridayya nada kaso mai girma daga ɓangaren babanta zuwa babarta, zata zama jarinsa ƙwarai da gaske. A cikin kuɗin ya cira aka kai kuɗin na gani ina so hadda sadaki, da Mijin Mama gidan iyayen gidansa da wasu mutane sune suka kai kuɗin Zameer bayan sun yi shiga ta alfarma wacce Zameer ya basu. Ba a tsaya lissafi da tambayar su waye su aka amshi kayan aka saka aure sati huɗu masu zuwa. A cikin sati aka kawo lefe na gani na faɗa masu a zabar kyau, Mami kallon komai take kuma ta ƙasa faɗawa ƴan'uwanta.


Cikin satin bikin Ridayya ta samu Mami a ɗaki ta ce "Mami zan yi aure lokaci ɗaya ki saka mini albarka a rayuwarta ba ki ce komai dan gane da auren ba, mijin ya yi ko bai yi ba ki faɗa mini komai ba"


"Allah ya sanya albarka" Shi ne abinda Mami ta ce tana ɗauke kai.


"Contractions Yaya Ridayya" Zainura ta faɗa tana murmushi jinjina kai kawai Ridayya ta yi ta miƙe ta nufi bedroom inda Mardiyya take. Ita dai ta san banda darajar Abbiey da bata auri Zameer ba tabbas shi ne ya sama mata wannan farin cikin. "Amarsu ta ango su Ridayya za a san kan duniya, dole Zameer ya yi farin ciki da tarbiyar Abbiey ya kare masa mutuncin matar daya aura"


"Uhm" Kawai Ridayya ta ce har yanzu ta kasa faɗawa kowa abinda ya faru Mardiyya ta miƙe ta ce "Bari naje tunda ba wani event sai ɗaurin aure ko? Allah ya sa albarka" Tana fita suka kusa cin karo da Ustaz wanda ya fito riƙe da trolley ta yi saurin ja baya ganin hannunta ya shafi nasa ya haɗe fuska sosai yana yarfe hannu ta ce "Ka yi haƙuri Abbiey ban gani ba" Bai kula ta ba ta ce


"Tafiya za ka yi? Ba zaka tsaya ɗaurin auren Ridayya ɗin ba?" Bai kulata ba ta ce "Bari na faɗa mata za ka tafi"


Hannu ya saka ya figo gefen hijabinta ya kafe ta da Idanu hasken fatar jikinta yana damun idanunsa ta masa haske da yawa da yatsa ya saita mata hanyar waje ta yi saurin ficewa daga cikin gidan. Ustaz ji ya yi ciwo na neman kwantar da shi domin ko tsaiwa ya gagare shi hakan ya sa zai bar Kanon bakiɗaya.


Ana saura kwana ɗaya ɗaurin auren Anuty Kaltum ta diro gidan ita da Yaya A'isha faɗa suke kamar za su daki Mami sai kuka take ranar an yi tashin hankali a gidan Alhji Mansur Rano ya ce idan har yarinya ta shi ce babu abinda zai hana a ɗaura mata aure gobe. Ya shiga ɗaki ya fito da tulin files ya damƙawa Ridayya ya ce


"Riƙe nan wannan kyautar da na yi miki ce" Yana faɗin hakan ya juya gaban Ammi ya faɗin ganin takardun abubuwan daya mallaka ya saka hannu tare da mallakawa Ridayya su ta bisa da sauri ta ce "Baffa ban gane ba, kasan me ka yi kowa?"


"Kina da tarihin ban taɓa yin hauka ba ko Maryam? Abubuwan dana mallaka na raba gida uku na bawa Ridayya biyu ya riƙe ɗaya shi ne mana"


"Ita kaɗai ce ƴa?" Ya ce "A'a, kawai haka nan na ji ita zan bawa" Za ta yi magana ya daka mata tsawa ya ce "Maryam fice mini a ɗaki kar ki ƙara mini ciwon kan da ban san dalilinsa na addabata ba shekara da shekaru" Ta fice a zuciya. Anuty Kaltum da Yaya A'isha har Mami suka dinga mamakin abinda Baffa ɗin ya yi a yanzu.


Washegari aka ɗaura auren Ridayya Muhammad-Bilal Rano da Zameer Mahboon Dollar auren da babu gata a cikinsa tunda babu Ustaz. Anuty Kaltum ta yi mata furnitures ƴan waje masu tsada haka Baffa da kayan kitchen an narka dukiya gashi kayan lefen ba abinda aka taɓa Ustaz ya bawa Umma komai da komai wanda Ridayya ɗin zata saka har kuɗin furnitures ma ya bata Baffa ne ya ce Umma ta bar shi duk abinda uba ya dace ya yi Ustaz ya ma Ridayya kafin ya tafi ta wajan Umma.


Aka kai kaya cikin wani dakakken gida tare da amarya sai santin gidan ake gwanin sha'awa iyakar haɗuwa ya haɗu. Mardiyya tare da amaryar sai Zainura a haka Zameer ya shigo shi ɗaya bayan sun gaisa ya ce "Ikon Allah har jere akai na manta ban faɗa musu ƙasar zamu bari ba yanzu haka"


"Ƙasar kuma?" Ya ce "E, a can zamu raya daren farko haka na tsara wa rayuwarmu ni da Mai sona" Mardiyya ta jinjina kalmar _Mai sona_


"Zan saka a kwashe kayan a kai ajjiya wani gidan idan mun dawo sai a dawo dasu yanzu haka a airport zaman jiranmu" Mardiyya ta miƙe tsaye ta ce "Za mu yi rakiya kenan?"


"No please hakan ma mun gode sosai" Ta kama hannun Zainura suka bar gidan Zameer ya sa aka kwashe kayan zuwa can wata unguwa wani ɗan ƙaramin gida aka jera kayan kitchen ɗin aka ƙulle. Ita da aka ce za a tafi airport sai ta gansu a wani gida ta dinga kallon gidan tana kallon Zameer ya haɗe fuska ya ce "Zan fara jarraba imaninki za ki iya rayuwa dani a duk yadda nake ko a'a shi ya sa na kawo ki nan idan kin cinye jarrabawa sai mu bar ƙasar"


"Idan har kana tare dani ai bani da wata matsala" Ta faɗa murmushi tana shiga gidan ta tarar da wata budurwa fara tas da ita sai danna waya take ya ce "Yawwa ƙanwata ce sunanta Khairiyya ana ce mata Khairy zata ɗan zauna damu"


"Sannu?" Cewar Ridayya Khairy ta ce "Sannu amarya zance ko bazawara ko budurbazar" Ridayya ta kalli Zameer ya kashe mata ido ɗaya ya ce "Tana da wasa sosai don mind her"


Cikin dare Zameer ya matsa gefe ɗaya yana tsaki sosai ta ce "Lafiya?" Ya ɗaga kafaɗa ya ce "Amma dai bakya kula wasu samarin don tsoro ya kamani yadda kika bani budurcinki suma za ki iya basu" Ta dinga kallonsa nan da nan idanunta ya cika da hawaye ta ce "Shiyasa ka matsa daga kusa dani?"


"To uban me zan yi idan ban matsa tunda ba wani ɗokin ki nake ba, abu ne ya yadda jiki an bani tun a waje yanzu bani da ra'ayi na riga na san shi, ai ba wani saura kin bani budurci tun waje"


"Me kake nufi?" A ɗan fusace ya ce "Ina nufin na gode mana, Allah ya sa ya tsaya iya ni kuma"


Bata ce komai ba, a daren ta yi kuka mai isarta ya ce kuma ya na da vedion abinda sukai ta yi a hankali. Cikin dare aka hauro tare da kwashe kayan lefen tas abu ɗaya ba a bari ba Ridayya ta dinga kuka, Zameer ya jata a jiki ya ce "Suna wahalallu ai talaka haka yake al'amarin shi akwai mugunta, zan mu je ƙasar waje ki zaɓi komai ta ɗauka ƙaddara ce" bayan ta kwanta ya ɗauki waya ana ɗagawa ya ce "Na gode da aron kayan lefe na gode sosai ka duba da kyau babu abinda aka taɓa" Ya kashe wayar. Gari na wayewa babu abinci ya baza wanka tare da yin waje daman ta zo da kuɗi ta yi cefa ne ta aza wuta idanunta sai hawaye yake sosai.


A cikin watanni biyu bayan auren Ridayya aka dawo da Ustaz gida rai a hannun Allah ciwon yau daban na gobe daban ya yi jinya zuciya data jiki kamar zai mutu hankalin family ya tashi aka faɗawa Ridayya Zameer ya ce ai basa ƙasar sai dai idan sun dawo. Ya yi haka ne domin baya so ya san halin da Ridayya ke ciki da gidan da take. Ta kira Ustaz a waya a ɓoye ta yi masa sannu bai iya magana ba kawai ya kashe wayar nan take ya tura mata kuɗi a Account ɗinta naira dubu ɗari. Bishasha ta samu Zameer sai da yaga bayan kuɗin.


Komai ta samu Zameer gani take tana kuskurewa zai saki vedion ta ga al'umma ya ɓata career ta. Ya kwashe kayanta ya siyar wai sabbin zai kawo mata ashe caca ya shiga da su bata sani ba, ganin hakan wahala ya yi mata yawa ta kira Mardiyya ta ce sun dawo sanda Mardiyya taga Ridayya hankalinta ya tashi amma basu ƙare lafiya, Mardiyya ta kwashe ta faɗawa su Ammi akai faɗa sosai Ridayya ta murje idanu ta ce babu abinda mijinta ke mata kuma. Ustaz bai ce komai ba domin ya jima da sanin inda Ridayya take rayuwa kawai ya zuba Idanu kuma shi ne dalilin daya saka yake tura mata kuɗi duk wata. A haka ta fara yin ƴar'tsala suka saba da Zainaba kullum ta yi zata bawa Zameer da Khairy. Lokaci ɗaya ta rame duk ƙibar nan ta zabge saboda wanki da gugar Zameer har ciwon baya ta fara, ba ci ba sha babu suttura sai dai idan buƙatar shi idan ta tashi ya neme ce a haukace haka zai faɗa mata tamkar dabba, bayan ya gama ya magance ta da kalamai masu daɗin gaske da nuna ita ce mace ɗaya tamkar da dubu duk wannan abun bai taɓa haɗa baki da ita a cewar shi wannan zuntumemen leɓen babu uwar da zai tsinana dai wari. Kwanci tashi ta samu ciki a lokacin kuma duk abinda ƴan'uwanta suka faɗa dangane da Zameer zai ta kwashe ta faɗa masa, hakan yasa Zameer ya haba uban kowa zuwa gidansa hatta Yaya Balkisu zuwanta biyu Zuhura sau ɗaya a lokacin Ridayya ta hana su shiga cikin uwar ɗakinta. Takaici ya saka Anuty Kaltum da Yaya A'isha ƙin waiwayar Ridayya kefe ɗaya kuma Ammi bata da burin daya shige taga auren Ridayya ta mutu ta haɗa ta da Burhan saboda kadarorin da suke wajanta. Zameer na ya san da kadarorin amma bai taɓa sanin inda ta ajjiye ba idan ya tambaya sai ta ce suna nan. A lokacin Baffa baya zama sosai kullum cikin tunani Ridayya yake kuma ya sakko akan Mami ita ko kallo bai ishe ta. Huɗuba sosai Zameer ya yi mata a kan ƴan'uwanta ya ce ko gidan basa barinsa shiga wai shi talaka bayan karayar arziƙi iyayensa suka samu. Har cikinta ya tsofa bata taɓa zuwa asibiti ga rashin abinci ta kwana da yunwa ta yini da ita ko abincin ta samu sai ta bawa Zameer wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login