Showing 177001 words to 180000 words out of 190738 words
Chapter 60 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt
na ciwo sai ta yi masa dariya ya ce "Ki ce kina so na ko na ji sauƙi" kawai sai ta kashe wayar. Naƙuda ta ci ƙarfin Mardiyya ta sha wahala sosai bata taɓa sanin haka haihuwa take ba, ƙasan zuriyarta wani irin ɗaci take ji ƙarar saukar motoci cikin gidan ya yi daidai da kukan saukar jaririn duniya "Ma sha Allah yaro ya zo duniya a daidai kamar yasan zuwan ubansa" Yaya Balkisa dake taimakawa Umma ta jawo jaririn ta goge shi ta yanke cibiyar ta saka cikin zani cikin murna Umma ta ɗauki jaririn da ganin irin zubin kyan da Ubangiji ya yi masa idanunta rufe ta miƙa hannu jikin jaririn ta riƙo abu kamar hannu kamar kunne da sauri ta kalli zanin ta waro idanu waje ta ce "Balkisa mene wannan a jinin yaron?" Balkisa ta ce "Umma leɓen babyn nan a haka ya sakko kamar hannu kuma macace ba namiji" a gigice Umma tana girgiza abun da ya yi shaƙaf idanunta kamar ya faɗo ta ce "Leɓe kika ce fa Balkisa leɓe na jikin baki?....
Share share share Please with comments
*MUNAFUKIN MIJI*
Nimcyluv
47
Mikiya writers Association.....
*Masu tiktok kuje ku yi following profile ɗina domin mu dinga tattaunawa daku a can...*
https://vm.tiktok.com/ZMrhYsBQE/
Cikin tashin hankali Umma ta ce "Bakin jariri kika ce fa Balkisa? Leɓe na jin baki irin nawa da nake magana kike nufi ko kuma wata tsoka ce ta yi tozo take neman faɗuwa ƙasa haka?" Ita kanta Balkisa mamaki da kallon baiwa da hikimar Ubangiji wajan iya tsara halitta shine ya cika mata zuciya da ƙyar ta zame idanunta akan jaririn ta ce
"Zai fi kyau ki nutsu Umma jaririn na hannunki ki duba da kyau sosai"
"Wannan ba dai jariri ba, sai dai idan ɗan aljanu kawai Mardiyya ta haifa, na rantse ban taɓa ganin jariri mai munin wannan ba, kalli hanci a bulaƙe kuma ya nane ta fata kalli halitta a jikin baki wai leɓe ce ko fa irin hasken jarirai babu a tattare da wannan jaririn" yadda Umma ke magana zai tabbatar da tashin hankalin da take ciki da gaske bata taɓa tsammanin jinin Babban mutum zai kasance haka ba, tana da yaƙinin jinin Muhammad mai ƙarfi ne duk yaron da zai haifa tabbas kamanninsa zai ɗauka.
Balkisa ta juya ta kalli Mardiyya da ko zafin haihuwar bai gama sakinta ba, fama ake ta yi ta mahaifa ta faɗo amma abu ya ci tura, dukda an ɗaure amma neman yin sama take wajan ƙirjinsa, hakan ya saka innar Mardiyya ta fara shiga tashin hankali domin tas mahaifa kan kashe mutum jini take sha sosai. Innar ta kalli Umma ta ce
"Haba baiwar Allah ke baki da imani da tausayi ne, kamar ba ki san ciwon haihuwa da zafin naƙuda ba zai yarfawa yarinya magana kike ina laifin ki yi lale da zuwan mai gidan naki? Halitta ɗaya ce dai kuma an haifa"
Wani banzan kallo Umma ta watsawa Inna ta dire jaririn da take jin ranta yana ɓaci a kansa, amma bata isa ta nuna masa ƙi ba saboda jininta ne amma har ƙasan zuciyarta take mamakin yadda yaron sam bai kwanta mata ba. "To Allahamdulilah mahaifa ta faɗo mun gode Allah an rabu lafiya"
"Ma sha Allah, sannu Mardiyya" cewar Balkisa ta shiga goge jinin wajan. Mardiyya ta sauke ajjiyar zuciya idanunta akan jaririn ganin babu inda ya bar mahaifinsa ta runtse idanunta tana jin fargaba mai tsanani na ratsa mata zuciya haihuwarta sa zuwan yaron duniya na nufin abubuwa da dama.
"Me na haifa ne Inna?" Ta furta da ƙyar Inna ta ce "Jaririya ce mace kika samu Mardi"
A firgice Umma ta ce "Mace kuma ke Balkisa ba namiji kika ce ba? Ai da maza jaririn ke kama"
"A'a Umma mace daman na ce miki ai"
Umma dai ta kasa furta komai sai girgiza kai take Mardiyya ta ce "Na yi wa Umma takwara a sakawa babyn Hadiza" zanin Umma na faɗuwa ta ce "Wacce Hadizan za a yi takwara? Ba dai ni kike nufi ba Mardiyya"
"Umma mene laifina idan na saka sunanki jikarki ce fa? Ai farinciki ya kamata ki yi ko?"
Umma ta girgiza kai ta ce "A'a na yafe idan an haifi wani a saka, ga innarki nan a saka ko"
Kafin su yi magana Yaya Zuhura ta shigo cikin murna ta ce "Umma albishirin ki?" Ta haɗe rai ta ce "Goro"
"Babban mutum ya dawo yanzu, Yaa Bilal is now at home" ba Umma hatta Mardiyya ba ta yi tsammanin jin hakan ba, ta sauke ajjiyar zuciya mai nauyi na farinciki da kuma na tashin hankalin da take tunanin yana gab da rikito mata. Farinciki ya saka Umma ta kasa cewa komai ta riƙe Yaya Zuhura ta ce
"Da gaske kike Zuhura?" "E Umma, yana main parlon ma" Umma ta juya zata fita Mardiyya ta ce "Umma ki tafi masa da babyn na san zai yi farinciki"
Ita dai Umma ko ta kan Mardiyya bata biba ta nufi hanyar fita Yaya Zuhura ta rufa mata baya, Balkisa ta miƙe ta ce "To Mardiyya bari na je na gaisa da ɗan'uwan nawa nima kafin ya shigo"
Inna dake satar kallon Balkisa ta ce "A'a kekam ai sai son barka sannu da ƙoƙari, uwar mijin dai ce naga ta na yi wa jinjirar wani gani-gani ai halittar Ubangiji ce"
Bayan Balkisa ta fita Inna ta ce "Mardi anya ba ki yi gamo da aljanu a wannan cikin ba? Ko kin watsawa ƴaƴan aljanu ruwan zafi ba ki sani ba?"
"Inna me kika gani?"
"Uban uban me na gani, ga abinda na gani nan a cinyarki ki dubi yarinyar nan har wani maiƙon baƙi take yi ke fara ubanta ma jaririn da shi haka kakannin nata" cikin runtse idanu Mardiyya ta ce "Ai Ubangiji da yadda ya kewa kowa tashi halittar"
"Haka fa, na ga alama to Allah ya raya miki"
A can main parlour Ustaz na kishin giɗe yana ɗan lumshe idanunsa hannunsa ɗaya riƙe da hular kansa little Bilal na cinyarsa sai Junaid dake kusa da shi, dukda cewa Ustaz ba ma'abocin yin fara'a bane amma fuskarsa ɗauke take da lallausan murmushi wani daɗi ya ke ji da nutsuwa na saukar masa, musamman yadda yake ganin farinciki a fuskar kowa dalilin zuwansa da zuri'arsa,bai taɓa zaton haka ya yi kewar gida ba sai yanzu daman Ridayya tuni ta shige part ɗin Mami saboda jininta bai gama ƙwari ba, ƴan'uwan Mami sun yi caa a kanta ita dai sai murmushi take gashi kowa burinsa ya ɗauki su Al'hussan, hawayen farinciki ke ƙoƙarin zuba daga cikin idanunta ta sauri juyar da fuskarta ganin sun haɗa idanu da Mami Anty Kaltum ta saka a haɗawa Ridayya farfesu wanda ya ji daddawa da kayan ƙamshi tare da kunun kanwa.
Jikin Ustaz har rawa yake wajan miƙewa lokacin da Umma ta ƙarasu parlourn tsayawa ta yi tana ƙare masa kallo ta kasa yadda babban mutum ne ya zama haka, tamkar ba jikinta ya tsaga ya fito ba, hatta kwantaccen murmushin dake shimfiɗe a saman fuskarsa is very different dana baya, bata san hasken fatarsa ya kai har haka ba sai yanzu, har wani yellow fatarsa ke yi saboda tsananin hutawar da yake yi, zagayayyiyar fuskarsa ce kawai a bayyane da manyan idanunsa da suke farare tas sai kwantaccen sajen fuskarsa ya zagaye ya sauka tare da haɗewa wajan gemunsa, a hankali ya sauke hular kansa ya riƙe sumarsa ta sauka don dama tuni little Bilal ya zare masa ribbon ɗin. Ustaz ya kasa kallon Umma saboda ya san shi ɗin mai laifi ne, ya ƙarasa gabanta da tsananin girmamawa yana ƙoƙarin tsugunnawa ta yi saurin riƙo hannunsa ta damƙe a nata ta kasa cewa komai ta kasa jurewa kawai ta rungume shi cikin farinciki ta ce
"Your welcome Son, barka da zuwa" ya kwantar da kansa a shoulder ɗinta tunda ya mata tsayi da yawa a hankali ya ce "I am sorry Umma Please...."
"It's okay, zuwanka alheri ne Muhammad domin kana zuwa jininka na zuwa duniya" ya ware idanu da tunanin ko ta samu labarin su Sadauki yaransa ne? Kafin ya zurfafa tunani ta ce "Mardiyya ta sauka lafiya yanzu, kaga sai ka shigo ka yi mata sannu da samun kai ka yi wa baby huɗuba" da wani irin expression yake kallon Umma sai bai ce komai ba ta ce "Akwai matsala ne?" Ya girgiza kai a hankali ya ce "Zan zo" Ta yi murmushin sosai yanzu hankalinta ya kwanta ta ce "Bari na shirya maka favourite ɗinka yanzu, ka shiga ɗakinka ka huta yanzu sosai" ya ɗan juya agogon hannunsa ya ce "Ok tom" kafin ta yi magana Yaya Zuhura ta fito da sauri ta ce "Zuhura zo mana kawo mini wannan kyakkyawan babyn mana"
"Umma ai ƴan uku ne bari na kawo miki sauran" da sauri ta ce "Ba dai wanda Baba ƙarami ya saka mini frame nasu a parlour ba?"
"E, sune wallahi"
"A'a Ikon Allah, yi sauri Please Zuhura"
Har Ustaz zai tafi sai ya tsaya tare da jingina da jikin bango ya harɗe hannayensa a ƙirji waiting to see Umma's reaction Umma tunu ta zauna saman kujera tana riƙe da Sadauki da yake buɗe idanu yana rufewa alamar baya son haske tana zaune Yaya Zuhura da Zainura suka kawo mata sauran suka ajjiye a cinyarta, ita kanta Umma bata san meke damunta ba, wani daɗi ta ji yana ratsa mata zuciya ta ce "Ma sha Allah, fatabarakallahu ahsanunl kaliƙin Ubangiji ya raya wannan yaran ya yi musu albarka ya kau da idanu a gare su" Yaya Zuhura ta ce "Amin" Zainura kallon Umma kawai take Ustaz dai na tsaye shima idanunsa akan yaran idan kuma ya tuna daga jikin wa yaran suka fito yana samun tsoro a zuciya na rashin matakin da Umma zata ɗauka a wannan karan kuma.
Umma ta kalli Yaya Zuhura ta ce "To ina ruwar yaran na yi mata barka"
"Ridayya ce Umma" cewar Zainura Umma ta juya sai a lokacin ta kalli Zainura don ba wani shiri suke ba ta lura yarinyar surutu gare ta da rashin kunya "Wacce Ridayya kuma?" Zainura ta ce "Ridayya dai ƴar Abbiey yayata kuma yaranta ne ita ya haife su" cikin rashin fahimta ta ce "Zuhura me yarinyar take cewa ne?"
"She is right Umma, they are Ridayya's children yaranta ne ai tana part ɗin Mami"
Umma ta yi jim ta kasa cewa komai sai kallon yaran take da wani irin shock ya akai Ridayya ta haifi wannan kyawawan yaran? Masu kama da larabawa? Ta tuna yadda little Bilal yake ita kenan jininta na haifar fararen yara ne masu kyau? Ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Daman ta yi aure ne?"
"Kai ai bata bar gidan nan ba sai da ta yi aure Umma" Umma ta yi shiru bayan ta ji abinda Zainura ta ce shi dai Ustaz na tsaye lokaci zuwa lokaci yake ɗan goge goshinsa Yaya Zuhura ta ce "To kawo su a mai dasu"
"A'a ki bar su mana, ɗauki wannan mai tsotsar hannun naga yana da rigima" Ustaz ya kalli wanda ta ce yaga Sadauki ne bai san ya akai maganar ta fita ba sai ji ya yi ya ce
"Sadauki ko? Daman shi ne baya baccin dare haka muke ta fama"
Umma ta ce "Me ka ce?" Ya saurin lumshe idanu tare da tafiya zai bar wajan ta sake cewa "Taya ka sani kai to?"
"Saboda yaransa ne su ɗin ai"
Gabaɗaya suka kalli mai maganar Baba ƙarami ya ƙarasu fuskarsa ɗauke da murmushi cikin sauri Babban mutum ya rungume Abba ya ce "Abba....," Baba ƙarami ya ce "Barka da zuwa babban abokina uban ƴan uku" Ustaz ya lumshe idanunsa kawai ya gaida Abba kana ya matsa for the first time ya ji nauyin Baffa ya ce "Sanniyda zuwa Baffa" Baffa ya ce "Kai ne da sannu Babban mutum, an samu ƙaruwa Ubangiji ya raya ya saka musu albarka"
Kai tsaye Ustaz ya ce "Amin Baffa, thank you" Tajj dake shigowa ya ce "Shugaban marasa kunya ta duniya" Ustaz ya yi masa banza ya kame fuska musamman ganin su Zainura da su Khaliperh a wajan, amma dole sai ya ce uban Tajj akan irin haka. Umma ta kalli Baba ƙarami da tsananin mamaki ta ce "Abba ka yi magana ka yi shiru kuma ban gane yaran Babban mutum bane, yaushe ya samu yaran? Bayan yarinyar da aka haifa masa yanzu?" Baba ƙarami ya yi murmushin jin daɗi kuma irin na manya ya ce
"E, Hadiza Al'hussan, Al'hassan, Gambo yaran Muhammad Bilal Tahir Rano ne da Ridayya Muhammad Bilal Rano, bi ma'ana Ridayya Mansur Rano" Tashin hankalin Umma ya girmama zufa ta dinga yanko mata baki buɗe take kallon Ustaz irin You disappointed me ɗin nan bani da alfamar da zaka iya mini biyayya ko bin umarnina idanunta ya sauya da ƙyar ta ce
"Sakin da ya yi mata fa?" Ta faɗa a raunace labɓanta har rawa suke tana datse su. Baba ƙarami ya zura hannunsa ya ɗakko takarda ya ware ya ƙarasa wajanta tare da kamo hannunta ya damƙa mata ita ya ce
"Read it Hadiza, ka karanta da kyau Hadiza ya rubuta miki takarda bisa umarnin da kikai masa sai dai baki karanta ba na amsa, wannan shine abinda takardar ya ƙunsa, nutsu ki karanta" ta buɗe; tunda ta fara karantawa take jin ƙirjinta na yi mata wani irin nauyi bayan ta kama ta miƙe tsaye hannunta ɗaya riƙe da Sadauki haka ta shige part ɗinta without say a single word. Ustaz trying to follow her Baba ƙarami ya riƙe shi ya ce "Ba yanzu ba, ka bata lokaci ka kalli waye a hannunta ta bar parlon, in sha Allah komai zai daidaita yanzu ka huta ka ci abinci ka ji ko?" Jinjina kai ya yi kana ya juya zuwa asalin part ɗinsa dake gida walking slowly yana ɗan buɗewa sai goge goshinsa yake, Tajj ya biyo bayansa Ustaz ya zauna saman doguwar kujera yana ɗan ɓalle botiran gaban rigarsa.
"Japan ta yi maka mugun sabo duk a.cn nan ji yadda kake goge fuska" Tajj ya faɗa bayan ya ɗauki remote ya ƙaro gudun A.cn kana ya zauna yana kallon Ustaz ya ce
"Ya hanya ka dawo lafiya?"
Shiru Ustaz ya yi kamar ba zai magana ba, a hankali ya ce "Kana lafiya Tajjudeen?"
"Allahamdulilah, an samu ƙaruwa Ubangiji yasa albarka munga kara thank you?"
"For? Kara?"
"Sunan Sadauki da aka saka" siririn tsaki Ustaz ya ja yana watsawa Tajj harara ta watsa bai ce komai ba can ya nisa ya ce
"I love Ridayya Tajj"
Sosai Tajj ya yi dariya ya ce "Sai yanzu Emotions ɗin ke ɗibarka? Da zurfin cikin fa?"
Cije lips kawai Abbiey ya yi yana sauke nunfashi tunaninsa ya bambanta, ga Umma, ga Zameer, ga Mardiyya da abinda ta haifa ga matsalar siyasa sam baya son siyasar ƙoƙarin janyewa ma yake yi. Sun ɗan taɓa hira dukda rabin hirar Tajj ne Ustaz da kunne ya ke ji a haka Mami ta aiko musu da abinci, Ustaz ya kalli abincin sai ya ɗauki wayarsa ya kira number ba jimawa aka ɗauka.
A hankali a kuma taushashe ga ce "Waye ya yi girkin?"
"Mami" ya yi shiru yana lumshe idanunsa, daga can ɓangaren Ridayya ta miƙe bayan Yaya A'isha ta amshi Al'hussan ta shige bedroom ɗin Zainura murya can ƙasa ta ce
"What happen?"
Still ya yi shiru, Tajj kowa ko a jikinsa abinci kawai yake ci hankali kwance domin sakwara ce da miyar akusi ta sha nama sai tuwon shinkafa da miyar wake wacce ta ji kifi Abbiey yaƙi magana kamar za ta yi kuka ta ce
"Talk, do you need something"
"Mimi" ya kira sunanta a ɗan shagwaɓe wanda ya saka Tajj kallonsa cikin sauri domin tabbatarwa da kansa Ustaz Bilal ne mai narkewa mace haka? Suna haɗa idanu Ustaz ya buɗewa Tajj idanu murmushi kawai Tajj ya yi.
"Abbiey mene? You scared me"
"Ki zo mu tafi gidanmu" ya ce ƙasa ƙasa yana ƙara lumshe idanunsa sosai ya takura da haniyar gidan da kallon da ake yi masa ta ce "Wanne gidan kuma Nurul hayat?"
"My house, our house"
Ita abin dariya ya bata ma tai ta dariya a hankali ya ce "Come"
Yana faɗin hakan ya kashe wayar. Hannunsa ya wanke tas ya zame ƙasa saman carpet tuwon ya saka da kansa sai marairaice fuska yake da sun haɗa idanu da Tajj kuma sai ya sha kunu ya saka malmala ɗaya tare da yin Bisimillah ya saka yatsu ya fara ci.
Har wajajen magariba Umma bata fito ba, ko da Sadauki ya yi kuka rarrashinsa ta yi har ya yi shiru ya koma bacci, tana zaune da tunani kala-kala a ranta wato rabon yara har uku kuma duka maza ba wasa bane, rabo ya saka Ustaz ƙin yi mata biyayya, rabo ya saka ya bar ƙasar rabo ya kashe Sadauki, rabo ne ya saka ta gudu daga Katsina, lallai rabo abune mai girma yarinyar da take aibata muninta ita ta haifi waɗannan zuƙa-zuƙan yaran? Allahu Akbar, gabaɗaya ta rasa me za ta yi ita kunyar fita take tun bata san uwar yaran ba ta ji tana ƙaunar su sosai, hawayen tausayin Ustaz ya shiga cika mata idanu tana zaune aka buɗe ƙofar tare da shigowa.
Inna ta ce "A gaskiya ba zan ɓoye miki ba an wulaƙanta yarinya kuma anci mutuncin furfurata, ban taɓa ganin haka ba tunda nake a rayuwa wannan cin mutuncin haihuwa ne, da ya yi ciki ya ɗora mata ya kama hanya ya yi tafiyarsa yanzu ya dawo amma ko ya shigo ya ce me aka samu? Saboda ga mara galihu ta haihu ko? Ai yau Mardi ki ƴar iska ce tunda ta haifa muku a ce mata sannu, balle kuma tsarkakkiyar yarinya ce mai haƙuri, ko kuma saboda bake ce kika wage ƙafafuwa kika haihu ba shiyasa kike mana haka ohho" Da mamaki Umma ta ce "Muhammad ɗin bai shigo bane?" A fusace Inna ta ce "Ya shigo gashi cikin rigar mamata, ji wulaƙanci ƴar dabar ina ce ni daya shigo zan masa ƙazafi haka?"
"Ki yi haƙuri bari ina zuwa" ina ta dinga satar kallon Sadauki dake motsi kana ta fice Umma kuma bata san mene yake faruwa da ita ba, bata son fita bata kuma son ƙara kallon babyn da Mardiyya ta haifa dukda cewa Ridayya da yaranta sun zame mata ishara akan tsarin halittar Ubangiji.
Number Ustaz ta kira bai ɗaga ba, tana ƙoƙarin kira ya