Showing 129001 words to 132000 words out of 190738 words

Chapter 44 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17284

babu aure" Ta dinga kuka tana yarfe hannu tana diddire ƙafa ƙugunta sai rawa ya zubawa ƙugun idanu sai kawai ya miƙe.


Da ƙyar ta yi shiru a parlour ya ɗauki Little Bilal daman tuni ta daina bashi nono police station suka fara zuwa Ustaz ya cike komai. Ridayya na zaune ɗauke da Little taga mutum tsaye ta yi baƙi da duhu ta ji an ce "Mai sona?" A razane ta ɗago kai jin muryar da ba zata taɓa mantawa da ita ba a rayuwarta sukai Idanu huɗu da Zameer a gigice yake kallonta ganin kamar ba ita ba, ya ji duk wahalar daya sha a rufe ta kau ya ji wani abu da bai taɓa ji ba yana motsa masa a zuciya wani abu mai kama da zahirin so sadidan na gaskiya ya tsirga masa Ridayyan daya ce ta tashi daga aiki yaga kamar yau ya fara ganinta babu alamar ta yi aure ba balle a san da zaman Little ta yi ƙiba ta zama ƴar lukuta ya dinga kallonta zuciyarsa kamar zata ratso ta ƙirjinsa. Ridayya ta yi saurin ɗauke kai da sauri ya nufe ta BM USTAZ ya tare shi "Yawwa matata mai sona ke nake ta jira lovely mu koma gidanmu ga ɗanmu ya yi wayo" gabanta ya faɗi kar dai Abbiey mayar da ita zai yi? Officer ya ce "Hajiya kin shi? Wannan mijinki ne?" Ridayya ta haɗe rai ta ce "Gaskiya ban taɓa ganinsa ba sai yau bani da haɗi da shi" Gaban Zameer ya faɗi muryarta na rawa ya zube gaban Ridayya kamar zai yi mata sujjada bai taɓa jin abinda ya taɓa jin irinsa ba "Wallahi ke matata ta ce ga ɗana nan wajanta, ni ba ruwana da filayen ma matata kawai nake so" Officer ya ce "Hajiya kin ji?"


"Ban san shi ba, officer kaga wannan?" Ta nuna Ustaz dake zaune yana danna waya ta ce "Shi ne mijina kuma ɗana bashi da alaƙa da wannan mutumin ka duba kamannin ɗana ka duba na mijina Ustaz kaga ana zaka tantance ɗan waye, ku amsar mini takarduna ku sake shi kawai" Tana faɗin hakan ta ɗauki Little ta bawa BM USTAZ ya amsa ya miƙe a hankali ya ce "Officer let him go" Suka saki Zameer a gigice ya bi bayan motar su BM USTAZ amma ina bai gansu ba kuma bai san wanne gida suka sauya ba.


Anuty Kaltum ta shirya kayan Ridayya cif sai a lokacin Mami take faɗa mata kuɗin da BM USTAZ ɗin ya tura ta Accout ɗin Ridayya na tafiyar wai ta yi tsaraba sosai Anuty Kaltum ta yi mamaki ta ce "To Allah ya ƙara arziƙi da wadata ya bashi lafiya"


"Ridayya je ki yi masa sallama mu tafi ko?"


"Ai ba sai na yi masa sallama ba Anuty" Watsa mata harara Anuty Kaltum ta yi ta ce "Ji wawta za ki tashi ko sai na ci ubanki?" Ta miƙe da sauri ta nufi ɓangaren Ustaz lokacin Mardiyya na parlour ta ce "Ɗiyarmu da kin tsaya yanzu na taya shi yin wanka yana shiryawa ne"


Ridayya ta kalli Mardiyya zuciyarta na yi mata wani irin zafi sosai ta ce "Na san wanka ya yi ai mun yi vedio call da shi har yake nuna mini wajan ciwon shi yanzu na wajan zan gani, karki damu uwata ai Abbiey nawa ne ba wani sirri tsakanina da shi" Tana faɗin hakan ta buɗe ta shiga ta fashe da kuka a kwace yake tsakiyar gadonsa daga shi sai boxer ko riga babu sai farar fatarsa dake ta ɗaukan idanu ya juya ya kalleta ta tura masa baki taƙi kallonsa tana kuka ta ce "Anuty ta ce na zo na yi maka sallama zamu tafi" Sai ta sake rushewa da kuka idan ta tuna abinda Mardiyya ta ce ya dinga kallonta ya ɗauke kai ya ce "Miƙo mini wayata can" ya nuna mata saman stool ta ɗauki wayar ta miƙa masa wayar ya amsa ya cafke hannunta tare da fusgota saman gadon ya mirgina ta koma ƙasan shi fuskarsa a saman tata ya ce "Ni kikewa tsiwa haka ake sallama da miji?" Cikin rashin fahimta ta ce "Miji kuma?" Ya share ya ce "Ni bari na sallame ki my crazy darling wife" Baki ta buɗe za ta yi magana ta ji saukar nasa cikin nata ya saka hannu ya kashe hasken bedroom ɗin......


*ALLAHAMDULILLAH*
Ubangiji ya sanya muna ɗaya daga cikin wata zasu lazumci wannan wata, yadda za mu ga farko Allah ya sa muga ƙarshe lafiya. Ubangiji ka yafe mana zunubanmu ya sa mu yi karɓaɓɓe. Bana son labarin ya kai ni bayan sallah wannan dalili ya saka lokaci zuwa lokaci zan dinga posting a channel da wattpad wanda ya karanta yana iya zuwa group ya yi comment ko prvt ko ta can wattpad. A daure a yi sharing domin kowa yaga sanarwar🌚🥰ONE LOVE HABIBATIES.






*YI DOMIN ALLAH*
*SARAUTA CHARITY FOUNDATION*


Ciyar da marasa ƙarfi da almajirai lokacin azumi. Ta hanyar yin abinci, kunu, ƙosai da ruwan sha tun daga kan 200 zuwa sama na abinda Allah Ya a hure maka.


*Saboda wasu dalilai da kuma yadda wasu suka nuna basa so, a daina saka sunan wanda ya bada kuɗi saboda sun yi ne domin Allah*


Saura kwana biyu azumi har yanzu ba mu kai ga samun abinda muke so ba jama'a a taimaka.


1. Sa'idu Hafsat 1k
2. A'isha Gadanya 3k
3. Maman Khalid 1k
4. Someone 2k
5. Received from pos 1k
6. Fatima Kabir 500
7. Unknown 2k
8. Murtala Maimuna 500
9. Fauziyya Abdulsalam 500
10. Unknown 1000
11. Unknown 500
12. Unknown 500
13. Unknown 500
14. Unknown 2k
15. Unknown 500
16. Unknown 3k
17. Unknown 1k
18. Unknown 1k
19. Unknown 4k
20. Unknown 1k
21. Unknown 1k
22. Unknown 500


Total 28k


6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank


Ko kuma
8164069385 Na'ima Sulaiman Shu'aibu Opay


Ku taimaka saboda Allah kuma ku yi sharing


*RAMADAN FEEDING*
Sarauta Charity Foundation. Re-post and support. Share saboda Allah


THE LAST DAY. KA SANYA KO BIYAR NE ALBARKACIN WANNAN WATAN YA ZAME MAKA MAFARKIN BUƊIN AYYUKANKA NA ALHERI A WANNAN WATAN. CIYAR DA WANDA BASHI DA SHI WANNAN SHI NE ABIN FARIN CIKI.


KA YI SHARING SABODA WANNAN WATAN SABODA ALLAH


*MUNAFUKIN MIJI 36*
Mikiya Writers Ass


Bright pens free batch
Nimcyluv




“coward” ya ce yana ɗage mata gira da kashe Idanu ganin yadda jikinta ke rawa kamar ba a taɓa ya yi mata abinda ya yi yanzu ba, he just gave a little light kiss. Amma ya lura jikinta sai rawa da ɓari yake ta rufe Idanu kamar bata taɓa jin abu makamancin wannan ba.


Ya dungure mata kai ya ce "Lazy wife, buɗe idanun" Ridayya ta kasa saboda da wani dake masa yawo saman jikinta yana kai mata saƙo na musamman da ban kuma. Wanda a duniyarta bata san da shi ba, hatta babban yatsarta rawa yake wai Little? Abinda ya yi mata ya fi ƙarfin a kira shi da haka yin duniya Ustaz ya yi ta buɗe idanunta amma taƙi sai wasu hawaye da bata san na menene ba suka fara bin gefen hawayenta.


"Kuka Ustaza? To shikenan a fasa tafiyar" Ta yi saurin girgiza masa kai tana ci-gaba da shassheƙar kuka na rashin dalili abinda ya yi mata ya tsaya mata curr a zuciya.


Ya ɗagota zuwa gefensa tare da riƙe hannayenta duka biyun ɗayan ya tallafo haɓarta yana zubawa fuskarta Idanu da gajiyayyun idanunsa a hankali ya ce.
"Kukan fa? Na mene?"


"Why Abbiey?"


Ya juya Idanu yana ƙara mutuwa da kyau gudun kar ƴar mitsitsiyyar yarinya ta birkita masa lissafi. Dukda ya gane sai ya basar ya ce
"Me?"


"You ki....,"
Sai ta yi shiru tana shagwaɓe fuska still taƙi kallonsa kamar yadda yake son nutsa ganinsa cikin ƙwayar idanunta da son gano ai nahin abinda ta ji game da hakan.


"Uhm za ki me dalili"


"Me ka ce?"


Ya matse hannunta dake cikin nasa tare da yin ƙasa da bakinsa daidai kunnenta numfashinsa na sauka ya ce.


“Play the role of my wife and be my children's mom Mimi” Ta yi shiru sai duk ya damu da shirun nata, kuma a ɗabi'ance hakan ya yi mace mai alkunya a kamata kuma hakan damuwa ce a gare shi, ko ABBIEY ɗin zata ce yana son jin muryarta. Da ita ɗinne kawai ƙofar zuciyarsa ke buɗewa yake jingina da ita ya yi hirar daya jima bai yi da ita, shi kawai yana son ta kama hannunsa ta ja shi zuwa rayuwarta da kanta, samun damar haka zai bashi ƙarfin qwiwar share dukkan wani damuwa da baƙin cikin data wanzu da shi tsayin shekaru, zai bata cikakkiyar dama a matsayinta na matarsa, zai share mata hawayen data daɗe tana zubar wa. Babban rainonsa yadda zuciyarsa taƙi masa adalci wajan buɗewa ta faɗa mata ainahin menene SO da ƘAUNA da kuma bambancin da suke tattare da shi game da BIRGEWA so yake ya samu damar da zai faɗa mata dukkan abinda yake ji a zuciyarsa game da ita, sai dai ƙaddarar shi kenan zurfin ciki kuma a kan abinda ya fi so da bawa muhimmacin ya fi ganewa ya yi komai a zahiran ce ko za a fi fahimtar yaran nashi.


"Can you? Za ki iya?"


Ya maimaita a hankali ta buɗe idanunta ta kalli gefen fuskarsa ya riƙo ta ya ce


"Ƙwayar idanuna za ki kalla" Ta girgiza kai.


"Ok fine an fasa zuwa ko'ina ma"


"Ka yi haƙuri Abbiey ban iya ganin Idanunka" ta faɗa a kasalance wani abu na yunƙuro mata.


"Za ki iya Ustaza nutsu" Ya riƙe kafaɗunta duka biyun yana gyara zaman shi a gadon daya gama cukurkuɗa shi da ita. Ya matsa gare ta sukai kusa da juna speaking calmly ya ce


"Rufe idonki" Ta yi yadda ya ce "Ja numfashi" Nan ma ta yi ya ce "Ok breath out" a hankali ta sauke numfashi zata buɗe idanun ya ce.


"Noo, wait a moment ɗan jira" Ustaz ya jima yana kallon fuskarta ƴar jaririyarsa yau ta girma har ta haifi Bilal, wanda da Allah ya ƙaddara a ɗan shi zai zo, lallai wani baya haifar wani rabo kuma ajali. Idan rabo ya rantse sai a rabo da juna a je wajan wani a haifa masa, Ubangiji ya sanya yana da rabon samun zuri'a da Ridha.


"Buɗe Idanunki, kai tsaye ki kalle ni Ustaza" ya ce yana riƙe fuskarta da duka tafukan hannunsa.


Kamar mai shirin ganin sabuwar halitta haka ta buɗe idanunta wanda kai tsaye suka samu gurbin sauka a cikin idanun Ustaz, wani abu ta ji ya tsarga mata a zuciya wanda ya sanya halittar ƙirjinta buɗewa da kyau tana fahimtar wani abu na musamman, wasu launi idanun Ustaz ke dasu, wanda ta kasa tantance ko na mene a karo na farko da take son ganin jallabiyya a jikinsa domin taga kamar ma ya fi kyau da ita, kallon ido cikin ido suke Ridayya ta dinga gani kamar ba Abbiey ɗinta ba, ya sauya ya ɗan birkice ya kuma rame sai nutsuwa da kamala haɗi da daddakonsa suna nan.


“Love is not by meeting eyes but by uniting hearts Ridherh, ki nutsu ki cire ƙuruciyar nan you are no longer a child, ke ɗin Oum-Bilal ce, haba jaririyata ya kike so na yi?"


"Me zan yi Abbiey"


"Be my wife"


Runtse idanunta ta yi sosai lokacin data tuna kalaman Zameer sanda ya ce yana son ta zama matarsa ta har abada sai dai mutuwa ta raba, ya yi mata al'ƙawarin hakan, Had all his promises been nothing but lies. Datse bottom lip ɗinta ta yi bata san ya fashe ba sai da ta ji taushin yatsarsa ƴar manuniyya yana goge mata jinin dake fitowa.


"What about me? If i ware to ask you to marry me, what would you say?" Ustaz ya yi shiru yana binta da idanu zuciyarsa na bugawa da ƙarfi amma bai bari rauninsa ya bayyana ba sam. Ya kasa ce mata komai.


Ta girgiza mai hawayenta na sake yawa muryarta na rawa ta ce "What if i don't want you to love me? Abbiey....,"


Yatsarsa ya ɗora a lips ɗinsa alamar ya isa ya kasa maganar. Kukan Ridayya ya tsananta ta ce


"Kallon mahaukaciya ake mini, na yi mamaki daya kasance har da kai amai yi mini wannan kallon. Wallahi ina da hankali Abbiey ni ba mahaukaciya ba ce, kuma Umma ta yi maka zaɓan da ya fi ni ta baka budurwa fara kyakkawa, bana jin aure Abbiey ko zan yi aure Sadauki ne zaɓina Abbiey ka yi mini uzuri please"


Ta kasa ƙarasa maganar saboda kuka ta ɗora kanta a cinyarsa kuka take mai cin rai, duk wanda ya ce bata fahimtar shirun Ustaz, da kallonsa ko tarinsa ko maganarsa ya yi ƙarya, sam Abbiey bai dace da ita ba yadda ya ƙare rayuwarsa haka yana da kyau ya samu kyakkyawar mata budurwa mai budurci, ba ita data watsar da nata tun a gabansa ba, tun kafin ta yi aure ba, ba ita data aikata zina ba. Wannan dalilin ya sanya take masa fatan samun macen data fita komai na rayuwa, Sadauki ya sota ne a yadda take ya kuma san ta yi aure ta haihuwa ko gaskiya ce ta bayyana ba zai ji zafi da baƙin cikin da Ustaz zai ji ba, shi ne ya bata rayuwa, ya kula da maraicinta dukda tana da Iyaye a raye ya bata tarbiyya daidai gwargwado tsakani da Allah amma ta saka ƙafa ta shure hakan ruɗin shaiɗan da uƙubar gidan uba, da mugun fata na Burhan da tsangwamar jama'ar gari ya sanya ta ji barin gidan shi ne mafita a gare ta, ta yi believing idan Zameer ya bar ta ba zata taɓa samun mijin aure ba ta yanke hukuncin bashi abinda ya buƙata tunda ta yi imani idan ta yi hakan zai zama miji a gare ta, mai share mata hawaye sai dai kash! Aka yi rashin sa a ashe MUNAFUKIN MIJI ta aura.


Ranar data bawa Zameer kanta ya dawo sabo a tunanin a hankali shuɗaɗɗun abubuwa suka dinga maimaita kansu a idanunta da zuciyarta dama kwakwalwarta suka zama sabbi a gare ta.


"Shhhh ya isa"
Muryarsa bata ma fita har yanzu sunan Sadauki ne a kansa zaune. Ya ɗagota yana murmushi ya ce "To maganar ta shige ok? Bana son mu yi irin wannan sallamar"


Ta jinjina masa kai wayarta ta fara ringing ganin sunan Anuty Kaltum ya saka Ustaz ɗaga kiran ya yi shiru.


"Wai uwar me kika tsaya yi ne daga zuwa sallama?"


"Hakƙin mijinta ta tsaya saukewa"


Ƙitt Anuty Kaltum ta kashe wayar Ridayya ta zaro Idanu ya haɗe fuskarsa yana goga mata hanci a hankali ya sunbaci goshinta ya ce "Blessing women"


Ya sauka daga kan bed ɗin ta bisa da kallo wallahi ƙato ne shi bata taɓa ganin girmansa ba sai yau, abinda ya fi ɗaukar hankalinta farar fatarsa ga suma luf luf kuma daga shi sai boxer.


"Abbiey ciwon ya warke ne kake saka ɗan mitsitsin wandon nan?"


Ya juya ya kalle ta ba yabo ba fassala sai ya ɗauke kansa ya share kamar ba zai magana saboda ya ja lokaci ta ji ya ce.


"Maybe ke yake jira, do you like it?"


Ta ɗauke kai da sauri sai kuma ta sakko ta fara gyara masa bed ɗin bai kulata ba ya buɗe drawer ya ɗauki wasu abubuwa kana ya rufe.


Yana tsaye har ta gama gyara masa gadon ta saita komai tunda ta saba bayan ta gama ya ce "Jazakhilla bil khair Jaririyata, Allah ya yi miki albarka"


Kanta a ƙasa ta ce "Amin. Abbiey na bar Little a wajanka"


"Shi wai ba a shirya yi masa ƙanne bane?"


Ta yi murmushi kawai ta nufi waje ya bi bayanta suka jera a tare. Zaune suka samu Mardiyya da sauri ta goge hawayenta tas amma idanunta ya yi jajur har ya kumbura domin ta laɓe ta ji komai hankalinta ya tashi sosai wani irin son mijinta da kishinsa ne suka dinga damunta. Ta fara yarda Ustaz bashi da lafiya idan hakan ya tabbata akwai matsala amma dole ta sake gwada shi domin gano gaskiya.


"Kaga ƴar Abbiey ɗinta kun fito?"


Ridayya ta share ta yi kamar bata ji ba, Ustaz ya san mene hakƙin iyali baya son Ubangiji ya kama shi da wannan laifin ya fahimci Diyya da kyau a kame ya ce


"Lafiya? Akwai damuwa?"


"Babu kawai bacci nake ji ne ina jiran kuma mu yi sallama da Ridayya"


Ridayya yunƙurin tafiya ta yi Ustaz ya yi mata wani kallo da sauri ta tsaya jikinta na rawa. Mardiyya ta fara ƙoƙarin haɗa jikinta dana Ustaz sai suka ji Ridayya ta fasa ihu ta zube tana riƙe ƙafarta hakan yasa da sauri Ustaz ya matsa daga kusa da Mardiyya ya ɗan rikice da tambayar Ridayya lafiya mene meke mata ciwo wani abu ne?


"Abbiey ƙafana ya maƙale ba zan iya tafiya ba ka ɗauke ni"


Kuka take sosai hankali kuma tashe take riƙe ƙafar Mardiyya ta tsaya kamar statue. Ustaz ya ɗauki Ridayya cak ya nufi main parlour da ita. Tun daga nesa Umma ta fara salati tana "me zan gani ni Hadiza wai ɓatan nono a ƙirjin budurwa"
Hankalin Ustaz baya jikinsa balle ya fahimta kukan Ridayya kawai yake ji, Umma ta yi saurin shan gabansa ta ce
"Sauke ta almura munafuka uwar ƴan iya mitsitsiyya dake kin iya kissa daman zawarawan nan haka suke da nacin miji"


Ustaz ya kalli Umma ta ce "Yanzu zaka fara Allah ya yafe mini ko? Ka zama shanyaye na mace nan gaba ɗan Daudu zaka zama kama maƙale hannu da kashe murya duk a sanadinta sauketa ka juya"


"Bana gane komai Umma ki mini uzuri Ustaza ba lafiya"


"Ta mutu mana? Idan ta mutu ni na mutu"


Da wani tashin hankali ya kalleta ya ce "Gwara ni na mutu Umma"


Yana faɗin hakan ya yi gaba tana kwaɗa masa kira ya share. Baba ƙarami murmushi kawai yake yana mamakin Hajiya Hadiza da bata san mene mayen so ba. Anuty Kaltum ta dariya domin taga komai a ranta ta ce "Za kiga aikin bazawara soon domin ba kiga komai ba sai Ridayya ta ke Maiduguri ta dawo ganin ɗanki sai ya gagare ki tunda kina jayaya da hukuncin Ubangiji"


Suna nufar hanyar harabar gidan Ridayya ta yi saurin cewa "Sauke ni" da mamaki Ustaz ya kalleta ganin ta zame ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login