Showing 165001 words to 168000 words out of 190738 words
Chapter 56 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt
idanunsa akanta wajan mintuna 15 aka kira shi ya ɗauka ya ce "Su shigo" Polices ne mata guda huɗu ya kalle su ya ce "Arrest her" Ammi ta ce "Baffa police ne fa me na yi matarka ka saka a kama?" Ya juya baya ya ce "Take her out please na sake ki Hajiya Maryam, ta faɗa muku abubuwan data aikata mini nida yarana idan taƙi ku yi ta dukanta" Yana faɗar hakan ya fice Ammi ta zumduma ihu sosai tana kuka ihu da kururuwa kafin ta sulale a ƙasa ba numfashi haka suka ɗauke ta zuwa waje Baba ƙarami bai san meke faruwa ba haka Mami Yaya Zuhura daman ba ruwanta da Ammi Burhan ko a ƙafarsa ta Zainura kawai yake Baffa ya nufi ɗakin Mami tana riƙe da junior Baffa ya shigo kafin ta yi magana ya rungume ta tare da fashewa da kuka mai tsanani. Mardiyya ta dinga tunanin yadda BM USTAZ zai dawo har ta samu kusanci da shi kuma ta dangana masa alhakin zama uban cikin jikinta, dabara ta ƙare mata gashi tana gab da haihuwa ne a ranta kuma take jin yanzu ta fara zama da Muhammad Bilal ba zata ta bari kowacce mace ta raɓe shi ba.
Suna tsaye gabaɗaya a harabar makarantar Zameer na gujewa ganin Tajj burinsa ya sake samun dama ya koma wajan Baba ƙarami ya lafta masa wata ƙaryar da dole zai saka Baba ƙarami ya bawa Ustaz umarnin sakin Ridayya shi kuma ya saka ta dawo gidansa zai lallaɓata da soyayya irin wacce ya saba yi mata a baya. Daga nesa suka ji ana cewa
"Gashi can aradun Allah hene mijina ne Allah ya kawo ni Kano" Ta faɗa tana tisu kewar wani yaro wanda suke shekaru ɗaya da little Bilal ga wata yarinyar itama a baya ta yi yarkace kace zani na neman faɗuwa Moo ya ce "Wancan fa kika ce wancan ai mijin Ridayya ne"
Ta zabga salati tana yagalo yarinyar daidai nan Zameer ya fara ƙoƙarin guduwa ya ji an tare shi ta gaba ya buɗe idanu ganinsa ya sauka akan Khairy itama hannunta riƙe da wata baƙar yarinya ta sha bille taya-taya a fuska ga leɓen yarinyar ya sakko ƙasa suka saka Zameer a tsakiya......
A yi haƙuri a yi haƙuri Please...... A tsitsita haka nan a tausasa zuciya 🤓 ko editing ban ba bear with the errors and spelling mistake.
*_MUNAFUKIN MIJI_*
..... Nimcyluv
44
Ya kalleta ya ce "what brought you here Khairy?" Ta juya idanunta tana nuna shi da hannu ta ce "Lallai so are you questioning me? Ba ka yi expecting ganina ba ko?" Ya haɗe fuska ya ce "I have no reason da zan buƙaci ganin ki balle na yi expecting zuwan naki" Khairy ta yi wani irin ciji baki jin wani rainin wayo na Zameer ta ce "Oh really? Is that so haka ma za ka ce kodayake ban yi mamaki ba mutumin ƙauye kuma bakatsine ɗan Fulani ba tsiyar da ba zai iya tufkawa ba, musamman ta wajan mugunta" Ta juya ta kalli Hanne dake tsaye yarkace kace ta kalli ɗanta Harazimi wanda duk ya fice daga hayyacinsa ba zaka taɓa cewa rana ɗaya aka haife su tare da little Bilal ba. Yarinyar hannunta ta dire masa a gabansa ta ce "Kaga dalilin zuwana, bayan na haifeta ba zan iya ci-gaba da zama da ita ba, domin ko nono bata taɓa shaba ba zan iya dakon wahala ba" da wani irin expression Zameer ya dinga kallon Khairy without saying a single words, sosai kalaman Khairy suka saka masa wani irin gigita ya fara goge zufa domin shi rabon shi da ita tunda ta taka tun daga Kano ta iske shi har garin Katsina ƙauye Nahutu dake Batsari, amma shi ne zata kawo masa wata yaƙunanniyyar yarinyar kamar ƙarshen duniya ta ce ƴar shi ce? Mahaukaci ta mayar da shi kenan. Ya yi murmushi ya ce "Khairiyya Please ki faɗa mini mene ya kawo ki bani da lokaci"
"Hehehe sai ka ce mai aikin gwamnati ko wanda yake rolling babban kamfanin babansa, banda aikin banza da zaman kashe wando babu tsiyar daka iya, sai shegiyar ƙarya kamar me ga fake life kamar jinin ƙaruna, wai Zameer Mahboob Dollar ai kowa naga dollars ganin idanuna a gona, wallahi ka kiyaye ni ba Khairy daka sani bace, kuma ni ba irin Ridayya ba ce for sure don ma ka ji" Zuciyarsa ta buga tana neman tarwatsewa a ƙirjinsa da ƙyar ya iya controlling kansa domin bashi da wata power ga yadda friends ɗinsa suke kallansa ya ce "Ki yi komai ki ce komai amma karki sake sako sunan matata a nan wajan, domin ita ba irin ki bace Khairy kuma kika yi wasa yanzu zan sauke miki yatsun hannuna a fuskarki" Khairy ta ware idanu ta ce "Yau nake ganin ɓatan nono a ƙirjin budurwa wanne dare ne jemage bai gani ba? Wanne kalar cin mutumcin da cin fuska ne ba ka yi wa Ridayya ba saboda ni, ka dake ta, ka ƙona mata fuska, ka karyata a hannu saboda ta gane ina ɗauke da cikin da ka yi mini kuma a cikin gidan aurenta na sunna,har na gama zamana a gidan ta rayu ne da tunanin ni ƙanwarka ce, ranar da na kai maka shegen ɗanka dana haifa a Katsina ta san komai a take ta yanke jiki ta faɗi naƙuda ta kama ka, ina cewa a garin naku ma mayya suke ce mata saboda muninta da baƙar fatarta, wanne mataki ka ɗauka eh? Ai wallahi tallahi masifu yanzu ka fara gani ita kuma mayyar bata san darajar kanta bane shi ya saka ta manne maka har yanzu" Tana faɗin haka ta sake tura masa yarinyar dake kuka tana share majina baki har kusan kunne ga uban leɓe an yi mata wani tsagu a fuska fuskar nan sai naso take tamkar an shafa mata soda ta ce "Ƴarka ce uwarka na yi takwara gata nan ana ce mata Deluwa, and please daga yau babu ni ba kai har gaban abada bana son yaran ciki daman kai ka yi shi ina son na yi free domin ban son ƙaddararka ta shafe ni Giɗaɗo"
Kamar statue haka Zameer ke kallon Khairiyya yama kasa tunanin komai da ƙyar ya ce "Ki ji tsoron Allah Khairy na san cewa namijin ɗana ne amma wallahi tallahi bani ne uban yarinyar nan ba, ki dube ta ki dube ni babu ta inda mukai kama da wannan yarinyar, wallahi ki nemi ubanta tuntuni" Ta juya idanu ta ce "Matse maka ta yi wallahi ina da abinda zai saka ka tafi gidan yari for life har mutuwa, ba wai blackmailing naka zan ba, and this is my final decision bani ba kai" Zufa ce ta dinga yankowa Zameer ganin gininsa na neman rushewa shegu har biyu ya shiga uku ya zai yi dasu? Ya dinga kallon yarinyar da ƙyanƙyami a fuskarsa gashi kamar wacce ta san shi sai manne masa take Harazimi ma ya matsa kusa da shi, ga yarinyar wajan Hanne ya shiga uku! Yara har uku amma babu na zaɓe gashi yana ji yana gani an ƙaƙaba masa yarinyar da bashi da alhakin samar da ita.
"Wai Zameer meke faruwa? Daman abinda kuka aikatawa Ridayya kenan kai da Khairy? Taya Ubangiji ba zai jarabce ka ba, na sha baka shawara akan abubuwa da kake gashi yanzu wankin hula na neman kai ka dare, a cikin gidan aurenka ka yi zina da wata matarka ta sameka turmi da taɓarya har ta rufa maka asiri kuma ka ci-gaba da zaluntar ta? Akan karuwarka ka fifita matarka ta sunna? Yanzu ka dubi yaran da suke gabanka da sunan naka? Wacce kake ganin matsayin mujiya bora a cikin mata mummunan ita ta haifa maka kyakkyawan yaro, wanda kake ganin sun fita kuma ka abinda ka shuka nan ka girma, ba a kushe halittar Ubangiji wannan ya zama izina gare ka" Khalid ya ce "Wannan shi ake kira da baƙar tukunya mai fidda farin tuwo, ƴar baƙa mummunan da haifar kyakkyawa, sai na ji ni baƙar macen wallahi ta fiye mini fararen nan sosai" idanun Zameer ya sauya ya rini maganganu Shaba sun masa zafi kamar ya watsa wuta a ƙirji ya ce "Khalid karka sake aibata mini mata wallahi zanci uban daya kawo ka duniya yanzu"... "Ni kake zagi akan gaskiya? Ina cewa kai ka fara aibatata a gabanmu eh? Da sanda ta fara cewa tana sonka wanne kalar zagi ne baka yi mata ba? Kuma...," bai ƙarasa sauran maganar ba Zameer ya kai masa naushi a baki tuni bakin ya fashe jini ya fara zufa ya ƙara kai masa duka
"I love my wife, ina son matata Ridayya har gaban abada yanzu na fara son ta, ina jin kuma son ta ne zai zama ajalina wallahi akan ta sai na iya kashe ka muddin zaka ci-gaba da abinda kake faɗa a kan ta"
"Ni ka daka?"
Zameer ya ɗaga shoulder ya ce "Na daka ɗin ka ƙara cewa uffan akan mai sona" Khalid ya wani irin murmushi yana tare jinin dake zuba ya ce
"Ka yi kuskure baka san waye ni ba, you have no idea na abinda zan maka amma wallahi tallahi sai na yi bugu, bugun da zai taɓa zuciyarka ta fashe nan take ka mutu zaka san waye Khalid"
"A'a guys karku ɓata zumuncinku akan macen, kai Khalid ka yi kuskure kaima Giɗaɗo ka yi " Shaba ya faɗa yana riƙe dariyarsa musamman idan ya juya ya kalli yarinyar wajan Khairy ya dubu Hanne da har yanzu take tsaye. "Ba ruwan ka Shaba karka shiga abinda ba bai shafe ka ba" Khalid na faɗar ya yi gaba zuwa motarsa. Moo dai couldn't speak saboda al'amarin ya fi ƙarfinsa tunanin rayuwa kawai yake.
"Kece matarsa baiwar kenan ke kishiyar Ridayya ce?"
"Sharri! Kwarankwasa ƙarya ne a gabana a kunne na akan idanuna ya saki matarsa Ridiyya, bayan sun yi yarjejeniyar zata bashi takardun da aka bata na filaye shi kuma ya ce zai sake ta, yasan wai dole duk inda ta je ta dawo wajansa sata komo tunda bata da kowa a duniya sai shi iyayenta sun mace tuni, ita kuma ta ce aradu ta yadda ya sake ta, ya ce ya sake ko sako ɗaya ne? Na rantse da Alkur'ani mai girma ya saki Ridiyya ba tare da idda ba domin tana haihuwa hakan ya faru ji munafukin miji?"
Salati kawai Moo yake yana kallon Hanne zuciyarsa na tsinkewa tana wani irin rarrabewa a ƙirjinsa, ya yi saurin cewa "Haba Hanne ki tausaya mini wanne ce kaɗai hanyar da zan dawo da Ridayya zuwa duniyata wallahi ina son ta, ban san har haka son ta ya addabi zuciyata ba sai yanzu, zan iya rasa raina da ita kawai nake samun nutsuwa, ina jin zan rayu da Ridayya ko zata mini iyaka da taɓa yatsanta ne, bana iya bacci kullum sai ta mini gizau ki taimaka mini, karki bari ahhalin Ridayya su ji wannan batun" Kallonsa kawai Hanne take tana girmama son zuciyarsa ta ce "To shikenan mu je ka bamu wajan zama da abinci" da sauri ya ce "Ok jira ni a nan na samu napep ok" ya yi bakin gate ɗin makarantar da sauri. Moo tausayin Zameer ya ji amma ya san shi da Ridayya har abada.
Zainura na tsaye gefen motar driven gidansu watching them ta kalli komai da komai ta yi saurin yin saving VR ɗin na wayarta, ta nufi wajan Hanne cikin sauri tana mata magana.
Japan....
Kallonsa ta yi a hankali ta ce "Abbiey sai yaushe zaka dawo ne?" Ya dube ta ya ce "Soon" Ta marairaice sosai ganin yanayinta ya saka ya kama hannuna ya ce "What? Ba mun yi sallma ba daga nan airport zan shige"
"I will go with you"
Ya kalle ta da kyau sai ya nuna mata cikin jikinta ya ce "Sai kin haife mini wannan babin ɗin, na ƙara miki wani cikin ko ki mini" Ta tura baki cikin shagwaɓa ta ce "Tab, ni daga wannan ban kumawa ɗaukan ciki wahala dakon shi haka haihuwa kai duk me ka sani"
"Daɗi"
"Me ka ce?"
"Na san daɗi mana, kema haka ɗaukan ciki dai daɗi gare shi Ustaza" Cikin jin kunya ta ɗauke kanta gefe ya kai tafin hannunta zuwa bakinsa ya yi kissing so lightly in a romantic style "I need u" ta yi masa gwalo ta ce "Abbiey"
Ya yi ƙasa da murya sosai yana sake damƙe hannuna ya ce "Are You okay with me? Please Mintyna open ur heart ni mijinki ne kuma sirriki muna samun saɓani wannan duka nrml ne ga ko wanne ma'aurata but ban san zaluntarki ta wannan ɓangaren na san akwai alkunya" Ridayya ta sake yin ƙasa da kanta tana murmushin ya ce "Talk Ustaza"
"You are the best Abbiey, na gamsu sosai" ya saka hannu ya dungure mata kai ta ce "Auchhi"
"Allah ya yafe miki Ustaza ba ki taɓa appreciate ƙoƙarina ba, kin san ni ba inji ba, ur words make me feel enough and encourage my energy" Ta yi saurin ɓoye kanta a should ɗinsa tana dukan ƙirjinsa a hankali kuma ta fara shafa sumar da ta yi kwance jikinta ya saki ta ji mijinta kawai take buƙata wani irin son Abbiey take kamar rai kuma har yanzu bata taɓa mayar masa da raddin he loves him ba, tana jin kamar bata cancanci zama matarsa ba still har yanzu kuma hankalinta a tashe yake kullum cikin fargaba yake. Tana jin yana jan hancinta underneath his breath ya ce
"I love you Ya Rouhi"
Ta yi shiru can ta ɗago kanta, ya zuba masa idanu with different emotions dake cin ranta da zuciya, for the first time a rayuwarta ta matsar da fuskarta zuwa gare shi, hakan ya sa ya gyara zuwan al'amarin da kyau..... She just give him a hot and deep kiss on his lips sai kunya ya kamata tunda wannan shi ne karon ta na farko, sosai take jin kunyar Abbiey a wannan ɓangaren tana ƙokarin matsawa ya yi saurin riƙe fuskar nata ya shiga bata sumbata halattacciya ƴar sunna irin wacce aka halatta wacce kuma ya karanta. Sai abin ya zama na su biyun ita ma ta cire kunya aka koma ban gishiri na baka manda da sauri ta yi baya ta ce
"Zan yi test"
Ya yi miskilin murmushi ya kasa cewa komai can dai ya nisa ya ce "Thank you, Allah ya yi miki Albarka Ustaza, ya sauke cikin aminci ya kare ki bisa kariyarsa.... Jazakilla bil khair Nisful hayaat, i love you Miftaahu qalbiy"
Sosai ta ji daɗi ta kama hannunsa ta ce "Wasiymna, Allah ya kare ka da kariyarsa ya kare ka daga sharrin mutum da aljan, ya ƙara baka buɗi da arziƙi mai amfani ya wada taka da kyakkyawar zuciya ta taimako, ya kiyaye ka daga sharrin ƙarfe, Allah ya raba ka da haram ya haɗa ka da halak Allah ya tsare mini Qalbiy" Bashi da wani option wanda ya shige rungume ta sosai zuciyarsu ke bugawa da ƙyar ya cire ta, ya fita ya buɗe mata mota ta fito jingina ya yi da motar yana kame kansa da kyau fuska a kame ta ce "Abbiey zan shiga Allah ya kiyaye"
Kai kawai ya jinjina mata idanunsa na yawo a harabar makarantar kamar mai duban wani abu, har ya juya sai kuma ya tsaya kamar bai son magana ya ce "Ki kula ok?" Ta ɗaga masa kai tana tsaye har ya bar makarantar..... Hankali kwance ta gabatar da karatu da kuma test ɗinta sallah ke tayar da ita jikinta ya mata nauyi sosai ƙafarta ya kumbura ainun, ƙarfe biyar ta fito tana kiran number drive kamar daga sama ta ganshi ta yi saurin ja baya, sosai ta razana ganin kamar ba shi ba ya yi duhu sosai ya rame.
" I couldn't sleep shanshan, don Allah ki tsaya muyi magana idan tsoro kike sbd cikin nan ni ban ɗauki hakan a komai ba sai ƙaddara kuma ke ɗin nake so ba wani abu naki ba" Ta yi shiru Sadauki ya matso gabanta ta yi baya da sauri ya cafko hannunta a gigice ta saka hannu ta zabga masa mari ta ce "Ka dawo hayyacinka Sadauki ba cikin shege na yi ba, ina da aure ina da aure matar aure ce ni, cikin sunna ne a jikina"
Dumm!! Haka Sadauki ya ji a kansa tamkar a duka masa wani abu, ya dinga kallon Ridayya can ya ce "Zan so ki ƙara marina ko zan farko daga mafarkin da nake, wannan kalman naki na banza ne wasa kike mini, day by day haka nake rayuwa da tunaninki, soyayyarki, ƙaunarki a zuciyata ba za ki iya auren wani ki bar ni ba, ba cancanci hakan ba"
Kuka ta fashe da shi sosai tana girgiza kanta ta ce "I am sorry i am sorry Sadauki " da ƙyar ya ce "Is like something wrong with you?"
"Yes seriously I have something to tell you, i want to apologize for my actions. I realize now that i made mistake by prioritizing financial status over our relationship. I deeply regret hurting you and i understand if it's difficult for you to forgive me".
"Me kikai?"
"I choose someone over you "
"After a year? Duka wanna Ridayya da wanna maganar gwara ki ɗauki wuƙa ki caka mini a ƙahon zuciya Ridayya, gwara tun Fil'azal ki ce bani kike so ba da ki dinga wasa da feelings ɗina, me ya sa?..." Wani irin hawaye ne ya fara zuba daga cikin idanunsa wanda bai shirya musu ba, ƙirjinsa ya dinga ɗagawa jijiyoyin kansa suka firfito magana yake son yi amma ya kasa ya riƙe saitin zuciyarsu da ƙyar ya ce
"You broke my heart Ridayya, ki tausaya mini don girman Allah.... I love you Shanshan Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun! Wasbunalallahu wani'imail wakil Ubangiji ka ɗauki raina my heart hurts my chest is burning Ridayya why? Why don Allah why are you doing this to me?..." Cikin kuka tana durƙushewa ƙasa dafe da cikinta ta ce "Sadauki stop all this forgive me don Allah" Ya girgiza kawai tears running down to his face wasu na korar wasu ya ce "I just forgive.... But will never forget"
Kuka gabaɗaya suke da ace zata iya auren maza biyu tabbas