Showing 153001 words to 156000 words out of 190738 words

Chapter 52 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17279

haife ki bata son haɗa inuwa dake, ko wanne yaro gudun ki yake saboda kasancewar ki baƙa mummuna. Ridayya kin faɗa tarkon ɗa namiji saboda ki gujewa azabar da masifar gidan iyayenki, kin nuna masa so sa tunanin ya dace dake da tunanin kina son shi ba ki san birgeki kawai yake ba, kin yi amfani wahalar da kike sha wajan ganin kin bar gidan hakan yasa kika amincewa MUNAFIKIN MIJI, ruɗin zuciya, dana kalaman soyayya da tunanin idan Zameer ya bar ki ba za ki samu wani ba, ya saka kika amince kuka ai bata abinda a yanzu yake ƙoƙarin tarwatsa rayuwarki. Kin yi rayuwar aure a gidan Zameer kin zama baiwa kina rayuwa da karuwar mijinki da tunanin ƙanwar mijinki ce, kin sami mijinki turmi data ɓarya, ya aure ki a caca ya raba ki da kowa naki ya miki duka ya karya ki ya ƙona ki a fuska. Ƙaddarar auren MUNAFIKIN MIJI bai barki haka ba, ya mai dake mahaifarsa kika fuskance wulaƙancin ƴa ƙauyen Nahutun Batsari, suka jingina ki da sunan Maita saboda halittar da Ubangiji ya miki, wannan bai gamsu ba aka wayi gari an kawo ɗan shege da mijinki Zameer ya haifa. Ki duba girman abubuwa nan duk kika jure kika shanye saboda kina neman rabauta da Aljanna, kuma kika ɓoye wasu hallayen namijinki saboda ɗan da kuka haifa da shi da kare mutuncinsa har zuwa girma, ba ki da laifi Ridayya ƙaddara ke ɗawainiyya da rayuwarki kuma babban abin farinciki Ubangiji ne ya hallace ki ni'imomin da ya yi miki suna da matuƙar yawa....."


Miƙewa ta yi jin yadda zuciyarta ke faɗa mata abubuwa ta zubawa kanta idanu ta cikin madubi wasu hawayen na sake biyo saman fuskarta a fili ta ce


"Kenan ba zan yi farinciki ba? Komai yake faruwa dani ƙaddara ce ko kuma don na kasance mummuna?"


"Mu kira hakan da ƙaddara" rufe idanunta ta yi da saurin tare da ƙoƙarin shigewa cikin bedroom ya kama hannunta ɗaya ta juya masa baya ya saka hannu ya juyo da ita suka fuskanci juna idanunsa zube a kanta yana ƙanƙantar dasu ya nutsa ganinsa sosai da kyau


"Fushi Ustaza akan wannan abin?"


"Wannan abin?"


Ta sake maimaita wa a zuciyarta ƙoƙarin shanye hawayen take muryarta na karkarwa ta girgiza masa kai, kanta a ƙasa ya tsare ta da manyan gajiyayyun idanunsa masu kaifi da sawa ta manta wasu abubuwan ta san baya amsa magana da ka


"A'a ba komai ni ba.....,"


Sai kawai ta fashe da kuka da sauri kuma ta shige bathroom tana sakin wani irin raunataccen kuka shikenan wanda ta saka ran zai bata farinciki ana shirin rabata da shi. Tana buƙatar mai bata shawara tana buƙatar wani kusa da ita ji take at anytime zuciyarta zai iya bugawa. Ustaz ya ja baya ya zauna saman gadon yana mai sakin yalwataccen murmushi abubuwan daya gani cikin idanun Ustaza sun saka zuciyarsa nutsuwa, he didn't see anything yet but an enternal love da wani irin pure heart zuciya cike da kishi. Ta shi ya yi yana rage kayan jikinsa.


Ridayya bayan ta yi kuka sosai har zuciyarta ta yi sanyi ta fara saukarwa da kanta ruwa a shower mai zafi daidai jiki ta saɓa sabulu kenan ta ji tsaiwar mutum a bayanta.


"Innalillahi Abbiey please out" gabaɗaya jikinta ya ɗauki rawa tunda take a duniya bata taɓa sanin sa irin wannan lamarin ba, jikinta ya dinga rawa kamar ta yi ihu tai ta kurmawa haka take ji


"Don Allah ka fita ba kyau ganin tsaraici Abbiey"


"Ko?" Ta yi saurin ɗaga masa kai a hankali daidai ita ya ce


"Today is the most suitable day for you to fulfill your heart's promise"


"What promise Abbiey?"


Ya mata shiru yaƙi magana ita kanta shiru ta yi tunani take anya wannan Abbiey ɗinta ne ba a sauya mata wani ba, baki ta buɗe da niyyar yin ihu jin wani abu ya yi saurin rufe bakin ya ce..


"Tukunna akwai sauran time, remember? Sanda kike ƴar mitsitsiya kin leƙa ni a toilet tun daga ranar na sawa raina da zuciyata na samu matar aure, na ɗauki hakan matsayin promise of the heart, yanzu ke ɗin tsagina ce"


Ta runtse idanunta kunya mai tsananin girma ta kamata dukda da ya hanata wanke sabulun ta dinga jan numfashi ba ƙaramin jarumta ta nunawa Ustaz ba, har mamaki ya yi for some minutes ya wanke su tare sai a lokacin ta buɗe idanu kanta na zubar da ruwa ya tallafo haɓarta


"Allah ya yi miki albarka"


"Uhm uhm ka yi shiru ni"


"Da na yi magana ne? Tsayin shekaru nawa ina rufe da bakina da zuciyata? Ki bar ni na faɗa kin ji ina da abubuwan cewa"


Ta maƙale kafaɗa tana narke fuska ta ce "Abu ɗaya"


“I LOVE YOU ”


kalmar ta saukar mata har cikin ƙasan zuciyarta,ta dinga jin wani iri kanta a ƙasa ya girgiza kai kawai yana ficewa bakinsa ɗauke da furucin


"Ustazu mijin ƴar baƙa"




Zameer na tsaye shi da Moo da Shaba sai Khalid kowa cikin shadda matasa masu jini a jika Shaba ya kalli Zameer ya ce "Na yi mamaki fa?"
"Name?" Cewar Moo idanunsa akan wata kyakkyawar yarinya dake cikin kyakkyawar shiga abaya ce jikinta amma ta saka irin baby hijab ɗin nan,sai wani mayafi ta yi covering jikinta tafiya take fuskarta a haɗe babu alamar wasa.


"Ban taɓa ganin Daddyn Zameer ba always baya ƙasar nan, mu a cikinmu waye ba a san dadynsa ba don Allah?"


"To mene matsalarka ne wai Shaba?" Shaba ya ɗaga kafaɗunsa ya ce "Kawai ina son ganinsa naga how rich he is yadda Zameer ke feeling kansa wani daban a cikin mu da alama Alhaji Mahboob Dollars is richer than my father, don haka ina neman appointment please Zameer"


Zameer dai bai yi magana ba, Khalid girgiza kai kawai ya yi yana murmushi hankalinsa na kan waya Moo ya ce "Akwai ƙamshin gaskiya sai ka ƙara girmama Zameer akan wanda kake" gabaɗaya suka saka dariya wasu na saman mota wasu jingine da mota Zameer gabansa sai faɗuwa yake yanzu babu mamaki Baffansa yana can gona ma, ga Hanne matarsa ta can ko ta haihuwa ohho ma ko ta kan lamarin baya bi Ridayya ce kawai a gabansa ita ke masa yawo a zuciya.


"Kunga wata Beb"


Gabaɗaya suka kalli direction ɗin da take hankalin Khalid ya karkata sosai a kanta "Wannan hannuna ce"


"Amma kamar babyn can nata ne ka duba hasken fatarsu mana" cewar Shaba. Cikin sauri Zameer ya cewa


"Zainura? My son"


"Ɗanka ne?" Ya jinjina musu kai ya ce "Ɗan da Ridayya ta haifa mini ne Zainura kuma ƙanwar matata ce"


Gabaɗaya suka kalli little Bilal wanda yake tsananin kama da MB USTAZ kyakkyawan yaro mai shiga rai ga wayo kamar ba haihuwar Ridayya ba, ga baki irin na Zainura magana yake sosai hatta sumar kansa irin ta Bilal ce.
A wannan karan Khalid ne ya ce "Karka raina mana hankali tayaya wannan baƙar matar taka mummuna zata haifi wannan yaron?"


Kalmar baƙa mummuna ya caki zuciyar Zameer ya ce "Idan ka kuma cewa matata mummunan sai na ci uwarka a wajan nan"


"Me za ka yi? Na faɗa baƙa mummuna wacce baka taɓa yi wa ko kiss ba, wacce ka tsana saboda ta baka budurcinta" da sauri Shaba ya rufe bakin Khalid ya ce "Haba Khalid this is not good, bai kamata kana aibata masa matarsa ba, kuma ai ba zai ga yaro ya kira sunansa ba Ubangiji ke halitta fa, don uwa ta kasance mummuna kuma baƙa ƙirin ba shi yake nufin ɗanta zai zama kamarta ba"


"Ikon Allah, baƙar tukunya mai fidda farin tuwo" cewar Moo ya kalli Zameer sai kawai ya girgiza kai, Zameer wani irin ƙaunar ɗansa ya matsa masa amma shakkar yi wa Zainura magana yake ya lura suna da bambanci da Ridayya mai son shi.


"Hi jimana" Khalid ya ce yana shan gaban Zainura ta ja ta tsaya tana tsare shi da idanu ta juya ta kalli Zameer ta ce
"Oh sawa ka yi a tare mini hanya ko me? Saboda na faɗa maka cewa karka ƙara zuwa ƙofar gidanmu? Wai kai wanne irin mutum Please?" Ta yi dariya tana cije bakinta Zameer ya ce


"Me ya sa ke baki da kunya ne? Ki koyi haƙuri da kunya da kawaici irin na ƴar'uwarki mana"


"Zameer kake ko? Koda yake bari na kira ka sa sunan da zaka gane Giɗaɗon ƙauyen Nahutun Batsari ta garin Katsina"


Shaba, Moo, Khalid da mamaki suka kalli Zainura ta riƙe ƙugu tare da yin fari da idanunta ta ce "Meye kuka tsare ni da idanu kamar yau kuka taɓa jin sunansa ba, ko kuna nufin yau kuka taɓa ji?"


A gigice Shaba ya ce "Wait; keep a joke a side Giɗaɗo kika ce fa?"


"Yes haka na ce, oh baku san cewa Almajiranta ya zo Kano ba daga Katsina shi ne ya zama ɗan fake life? Ku je ku yi tunani ko kuma baya ku yi nazari da kyau"
Wata zufa ce ta shiga yankowa Zameer kana ganinsa kasan ƙarya ta ƙare buri ya kar boka da tashin hankali yake kallon Zainu ita kowa sai murguɗa baki take hankalinta kwance, Khalid ya dinga murmushi Moo ya kasa cewa komai Shaba kallon Zameer yake from head to toe ya ce


"Amma da gaske wannan cute boy ɗin nasa ne? Ni kama yake mini da wanda ya fito takarar Gwamna ɗin nan Muhammad Bilal Tahir kamar ya yi kaki"


Watsa masa harara ta yi "E ai duk inda magana ta je ta dawo gaskiyar ba zata ɓoye cewa bashi ya haife shi ba, Muhammad Bilal Giɗaɗo sunansa muna ce masa Little, amma a yanzu na raba wannan alaƙar ya je can ya nemi ɗansa, little ko zaka je wajansa?"


"No Abbiey" ya ce yana maƙale kai "Well-done my son za ka yi albarka irin ta uwarka"


Duk wannan tashin hankalin Zameer bai dame shi ba, ganin yadda ɗansa yake ƙoƙarin gudunsa da gaske shi ke firgitar da shi, kar dai Ridayya ta karantar yaron nan komai? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Ya shiga uku ga wani masifar son Ridayya dake ƙoƙarin haukatar dashi tattausan laɓɓanta ranar da ta je police station yaƙi barin idanunsa ya biyo bayan Zainura da sauri ya ce
"Ki faɗa mini Ina matata take ina mai so na, ni ne rayuwarta Please Zainura ina kika ɓoye mini matata?"


"Tana cikin Aljihuna na ce gata cikin Aljihuna wai kai wanne iri ne, Yaya Ridayya ta maka nisa har gaban abada muna nan da kai akan son ta zai zuciyarka ta buga,kuma idan baka rabu dani ba Wallahi zan saka a sassaraka a mayar da kai Nahutu a ƙarye useless useless" baki sake ta bar Zameer ga kunyar su Moo ga zuciyarsa da take masa wani irin tsalle ko wacce gargasar jikinsa idan ta buɗe da muradin samun Ridayya take yin hakan baya iya bacci wani irin MAHAUKACIN SO ne ya kama shi.


Bai tsaya ba ganin Shaba na zuwa inda yake ya saka cikin sauri ya faɗa cikin wata napep dake harabar jami'ar.


Zainura na zuwa gida ta tarar parlorn Mami cike da su Anuty Kaltum da Yaya A'isha da sauran jama'a ana ta hira ta dinga mamaki cikin sauri ta shiga bedroom baki ta sake ganin Baffa zaune hannunsa ɗauke da jariri ta juya ta kalli Mami, Mami ta watsa mata harara tana ɗauke kai daga ita har little Bilal wajan jaririn suka nufa, ta taɓa babyn taga yana motsi ta fasa wani ihu ta faɗa kan Mami ta ce


"Is true Mamina ta mini ƙani wow Zainura you are so lucky" Ta ƙanƙame Mami Baffa ya ce


"Maza yi ƙoƙarin danne mini matata sahibata"


"Haba Baffa murna ce fa, Mami ko na ji miki ciwo ne" Mami ta ranƙwashe ta ita kam ta riƙe Mami so take ta ƙara taɓa Babyn Baffa ya ce "Idan ba ki ɗaga mini mata ba idan na zo ni da ke ne, ga wahalar haihuwa ga taki ke bakya girma ne"


Little ya ce "Baffa wannan" Baffa ya ce "Ɗan kyakkyawan jikina kalli Madam ce ta mini kyautar baby say thank you granny"


"Thank you granny"


Mami ta yi murmushi ta ce "Wato little surutun uwarsa Zainura ya ɗauka" Baffa ya ce "I see, like son like mother kenan"


"Uhm ai yau na sake ganin tsohon mijin Yaya Ridayya wai ina matarsa ji banza fa? Na kowa ci masa mutunci ya ɗauka ban san shi ba, Giɗaɗo sunansa fa a Katsina yake can ƙauyen Nahutu daga yankin Batsari ai Almajiranta aka kawo shi nan kuma.....,"


"Zainura!"


Mami ta kira sunanta da ƙarfi har sai da ta ji tsoro ta ce "Zameer ɗin kika faɗawa haka?"


"Mami to mene? Wallahi na tsane shi criminal ne gabaɗaya ya wahalar da Yaya Ridayya" Mami zata ƙara magana Baffa ya ɗaga mata hannu ya ce


"Baya saki Ridayya ba? Meye na kiran ta da matarsa "


Zainura ta tura baki ta ce "Ɗan wahala ne hadda rantsuwa bai sake ta wai guduwa ta yi matarsa ce yen yen yen ni ko jin zancen ban yi b saboda warin bakin ƴan ƙauye yake ai yama faɗawa Yaya Junaid everything "


Hankalin Baffa dana Mami suka tashi bada aure akan aure Ridayya ta yi ba? Nan da nan Baffa ya kira Junaid ya ce duk inda yake ya je.


Ammi kusan zaucewa ta yi bata taɓa ganin cikin Fatima ba sai kukan jariri ta ji? Ya akai bata taɓa lura ba mai ya ɗauke hankalinta har haka? Kenan Mami zata ci-gaba da haihuwa har ta kamo ta a raba gado daidai kenan gashi wannan karan namiji rawar kan da Baffa yake akan haihuwar har ya ɓaci ta rasa ya za ta yi koda ta samu Yaya Zuhura ta mata magana cewa ta yi


"Ammi matar na da zuciya ɗaya take zaune dake idan kika ce za ki mata baƙin ciki mutuwa za ki yi a tsaye bayan kin aure mata miji tun kafin ta aura amma ki dinga ƙoƙarin rabata da mijinta, abinda ka yi wa ɗan wani shi za a yi wa naka ni kin cucu ni ji nake dama bake ce uwata ba mugun abinki ya miki yawa"


"Ni kike faɗawa haka Zuhura " Yaya Balkisa girgiza kai kawai ta yi wannan shi ne ƙaiƙayi koma kan masheƙiya.


Mardiyya burinta bai shige Ustaz ya dawo ba, ta samu tarayya da shi ko sau ɗaya ne kuma ta yi evidence, wanda zai tilastawa Ustaz amsar cikin jikinta wannan shi ne plan ɗinta kuma ko kiranye ne zata saka a yi masa domin ya dawo ta cimma burinta.
Gefe guda kuma Umma sai ɗawainiyya take da cikin Mardiyya ta fara siyan kaya tana ajjiyewa har fili ta bawa Ridayya akai shaidu da saka hannu matsayin tukuci na cikin da haifa mata jika da zata yi a ƙalla kusan kullum tana kashe kuɗi sama da dubu goma zuwa sha biyar na kayan kwaɗayi ga yawan fita da take wai asibiti take zuwa.


Kuka sosai Hajiya Azizat ke yi tana kallon Prof ta ce "Yanzu ya zan yi da damuwarka zan ji ko data Sadauki? Anya Prof wanne kalar rayuwa ne na kasa gane maka dani da photo ɗaya muke a wajanka a matsayina na matarka yaushe rabon daka sauke mini haƙƙina? Ci da sha ba shi ne aure ba Professor al'amarin naka kullum ƙara girma yake sai ka yi wata baka gida?


Prof ya girgiza kai yana tattaro kalamansa ya ce "Madam plates try to understand me, ke shaida ce ina son ki kuma duk abinda nake yi ina yi ne saboda ku, bani da burin daya shige zama daku yanzu muna maganar fara kamfal ne takara ta sako ni a gaba addu'arku nake buƙata"


"I wish you all the best dear amma ka je wajan Sadauki talk to him ka ji damuwarsa"


"Right now my love"


Kwance ya samu Sadauki daga shi sai gajeren wando idanunsa yana kallon sama faffaɗan ƙirjinsa a buɗe ya rame saboda sam tunda yake bai taɓa saka damuwa a rai ba, bai taɓa tunanin a duniyarsa akwai abinda zai raunata zuciyarsa ba sai gashi Shanshan na neman kashe shi da ransa. Prof ya kalli kwalbar srup ɗin dake kusa da hannun Sadauki a karo na farko ya ji bai kyautawa ɗan shi ba.


"My love tashi mu yi magana" Sadauki ya share shi ya shanye kwalbar srup har uku saboda ya samu bacci ya ɗauke shi daman mai jima da tashi ba.


"Akan wacce ka shiga halin nan za mu yi magana, zan tabbatar data zama martarka idan har Ridayya ce"


Da sauri Sadauki ya juya ya kalli mahaifinsa Prof ya ce "Da gaske i am with you wannan karan ba zan bari soyayya ta kashe mini kai ba, yaran yanzu akwai saka damuwar soyayya musamman irin madly love ɗin nan yana rusa muku rayuwa, da yawa wasu na samun depression idan sukai heartbroken, wasu ma su fara shaye-shaye duk a sanadin soyayya"


Ya kama hannun Sadauki ya ce "Please my son ka kwantar da hankalinka ban san mene Hukuncin Allah ba, amma tabbas kai da Ridayya zaku kasance ma'aurata"


Ya kalli mahaifinsa sosai a raunace ya ce "Prof Shanshan bata tsautsayi na me na yi ba? Kullum cikin bata haƙuri nake, mace ƴar rarrashi ce da kulawa suna buƙatar a dinga supporting nasu komai ta ce zan yi obey, but bata so na she doesn't love any more, i love Ridayya Daddy"


"Na da kai na shaida hakan kuma na samu ganawa da mahaifinta"


"Are you sure Daddy?"


"Of course my son amma ban faɗa maka komai sai ka kwantar da hankalinka ka dawo asalin Hamza Sadaukina"


"Abba Ridayya fa?"


"Oh Sadaukin Ridayya, makaranta ta koma kamar yadda aka shaida mini kuma bata mance da kai ba, tana buƙatar ta kammala karatu yadda idan kun yi aure zata samu ciakken kula da kai as she said. Ridayya loves you Hamza bai kamata ka damu ba ka yi mata uzuri ka ji ko"


Sadauki ya yi shiru can ya ce "Kamar na yadda kamar ban yadda ba, well is allowed zanta yi mata uzuri zan ci-gaba da sonta kuma zan jira rata har zuwa ƙarshen numfashi zan bata lokacin da take buƙata, i love Ridayya Daddy help me ko gidansu na je na gaisa da iyayenta Tajj mugu ne ya hanani da ƴarsa ce Nadra ba zai bari ta dinga wahala ba ya san yana da maganin damuwarta"


Prof ya yi murmushi ya ce "Babba babba ne my dear respect your cousin brother ka ji?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login