Showing 78001 words to 81000 words out of 190738 words

Chapter 27 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17288

da komai nata akan shi. Ta rikice ganin yaƙi magana ta ɗauka ko bashi da lafiya ne? Tunda yake bai taɓa cewa wassh saboda ciwo ba...


Ta koma kitchen ta wanke hannunta tana bawa Dija umarnin ƙarasa wanke-wanke ta dawo gani ta yi baya parlourn da sauri ta nufi bedroom ɗinsa nan na baya ciki daga can ta ji sautin kiɗan jitan shi ta nufi wajan, ta tsaya saroro tana kallonsa ya tuɓe rigar sai training yake a gym ta ce


"Sadauki" Ya juya ya kalleta yana ɗaga mata hannu tare da juya yatsunsa alamar "What Mother?" Ta kashe sautin jitan kana ta rage gudun injin ya marairaice fuska sosai yana kallonta ta ce


"Ka bani tsoro Sadauki ba ka ji zuciyata ba, baka da lafiya ne? Mene ya sameka? Are you okay?"


"Mother" Sadauki ya faɗa yana sauka ya ce "Kin taɓa ganin Sadauki ya yi rashin lafiya?"


"To wannan kiran gaggawar na mene?"


"Just to see you Mother, na farka na leƙa bedroom bakya nan shine na biyo ki fa"


Ta dinga kallon shi ya ɗaga hannu ya ɗora a kafaɗarta suka fita waje ta ce


"Yaushe Sadauki zai girma ne ni Azizat?"


"Sanda na yi aure, ko na yi aure ban taɓa girma wajan Babata da Matana Allah idan ban muku shagwaɓa wa zan wa?"


Waje ta nema ta zauna ta ce "Wallahi da za ka yi auren da na ji daɗi sosai na samu jikokai kaga kai kaɗai Allah ya bani" Ya girgiza kai yana ɗaukan ƙafa ya ɗora saman table yana mai sauya channel zuwa kallon ball ya ce


"Da kowa zagewa zan yi nai ta haihuwa, matana ta haihu nima na haifa"


"Ikon Allah. To ka fito da matar auren mana"


Ya ɗan ɓata fuska sai kuma ya girgiza kai ya ce "To har yanzu babu ƴan'matan" Mother ta ware Idanu sosai ta ce "Duk tarin ƴan matanka Sadauki? Kiran yau da ban na gobe daban"


Ya yi mata shiru kawai don hankalinsa ya koma kan ball wasa ake bugawa sosai tsakanin Hala Madrid da Bercelona. Ta ce


"Ina magana fa"


Ya juya ya kalleta sosai tasan lissafin abinda zai faɗa yake can a nutse ya ce "Su duka ƴan matan suke so na, ina son samun wacce zuciyata ta nutsu a kanta Mother, ina son soyayya sosai, ƙauna, tattali da kulawa ina son macen da ni zan koya mata mene soyayya da yadda zata so ni, wacce zan sha wahala a kan ta sosai. Sadauki na son soyayya" Ya faɗa hankali kwance don har a ransa yake jin normal ne


Hajja Azizat ta riƙe haɓa ta ce "Naga abinda ya dame ni" Sadauki ya ce "A'a fa ki daina salati kamar na faɗi mugun abu, a duniya babu abinda yafi daɗi irin zama da wanda zuciyarka ke tsananin so"


Tana ƙoƙarin magana ya buga ihu ya miƙe yana "Go goooo!" Daidai nan wani ya shigo cikin parlourn Sadauki ya tafi da sauri ya bawa mutumin hannu ya ce


"Gooo Daddy mun cinye ku goo" Daddy ya girgiza kai kawai ya ce "Yau ɗaya Madrid sun abin ƙwarai" Sadauki ya ɗan rusuna sosai har ƙasa ya ce "Good morning Daddy"


"Morning Friend, ya jita? Ya kuma business?"


"Good" Daidai nan wayar Daddy ya fara ringing aka saka secretary a number bai ɗauka ba sai da yaga Hajja Azizat na kallonsa ya ɗaga ya ce


"Laminu ya akai ne?" Ya yi shiru can ya ce "Oh waje mai kyau please, ya yi tsari da ƙawa a shirya sosai don na daɗe ban yi ba, a fa shirya?"


Ya kashe wayar Hajja Azizat ta ce "Sannu da shigowa Prof"


"Yawwa wife, ya rigimar ɗanki Sadauki" Ta yi murmushi


Ƙara wayar Prof ta yi notification ya shigo Sadauki ya kalli screen ɗin wayar ya ce "Daddy wannan secretary ɗin baya ga jiya da turo maka pictures? I noticed that" Prof ya miƙe ya ce


"Yhhh pictures ɗin motoci ne sababbi da zan siya na bawa secretary aikin hakan yanzu ma can zani"


"Yanzu ka shigo tunjiya kuma yanzu zaka sake fita?" Ya ce "To ya za a yi ni kaina ina buƙatar iyalai na kusa dani, na yi kewarku sosai wallahi"


Jikinta a sanyaye ta ce
"To Allah ya tsare ya kiyaye ya bada sa a" Prof ya ɗan bawa Hajja Azizat side hug ya ce


"Love you wife soon zan dawo" yana ƙoƙarin fita Sadauki ya ɓata fuska ya ce "Daman baka so na ka fi son Mother"


"Banda ciwon baki me kake saka mutane Sadauki? Shekaru 30 ciff kake wannan shekarar fa, and idan ban so matata ba wakake tunanin zan so?" Ya haɗe rai shi dai ganin hakan ya saka Prof rungume Sadauki ya ce


"Stubborn friend i love You" Sadauki ya ɗage gira shi ma.


Bayan Prof ya shiga mota driver ya ja ya kira number secretary ɗin a hankali bayan an ɗauka ya ce "Sweetheart Lina ina bisa kan hanyar hotel ɗin...."


Zuwan Ustaz Kano uku bayan tafiyar Ridayya yana zuwa gidan Zainaba ta shaida kaf halin da Ridayya ke ciki amma ta ɓoye labarin data bata don gane abinda suka aikata tare da Zameer, ta kuma ce tun ranar da aka faɗawa Ridayya kowa ya mutu daga ciki har da Ustaz ɗin ta sulale a wajan ta suma, Zameer kuma ya saka aka yi mata allurar bacci mai ƙarfi ya ɗauke ta ya koma garinsu. Ta shaida masa bata san garin ba sam sai dai ya tambaya a lokacin kuma Malam iro Allah ya yi masa rasuwa kaf Almajiran ba wanda ya san asalin sunan Zameer balle garinsu hankalin Ustaz ba ƙaramin tashi ya yi ba. Ya je ya tambayi gidansu da Sadauki ya fara cin karo yana wasa da wani ƙaton kare.


Haka kurum Sadauki ya ji mutumin ya yi masa kwarjini ya tsaya yana kallonsa Ustaz ya faɗa masa dalilin zuwan Sadauki ya ja baya da sauri ya ce


"Thank you dear Lord, nemanta nake ido biyu ta hanani runtsawa so kai ne Abbiey ɗin da take magana?"


"Ta zo?" Ustaz ya faɗa a hankali yana cin surutun Sadauki har tsakiyar kansa ya ce


"Wacece ita? Muryarta daɗi amma kamar bata da lafiya?"


"Ta zo ne?" Ustaz ya sake tambaya cikin damuwa ganin yadda Ustaz ke ɗaga kai kamar ana masa dole Sadauki ya dawo da asalin halinsa ya ce "Ban sani ba"


Don a rayuwa ya tsani ɗagawa da faɗin rai yana sane ɗin kuma ya share Ustaz ya yi tafiyarsa.


Duk inda Ustaz ke tunanin neman Ridayya ya fassakara Wasiyyar Baffa kawai yake son cikawa ba wai wani dalili ya saka yake neman nata ba. Bayan ya shiga mota a hankali wanda yake ciki ya yi mata key suka fara tafiya ya ce


"Babu labari?" Ustaz ya lumshe idanunsa zuciyarsa na dokawa da matsanancin ƙarfi ga wani irin matsewa da zuciyarsa ke yi tana tattare masa waje guda a ƙirji tana ƙoƙarin haifar masa da wani irin ciwo.


"Ka bani dama na baka labarin matar dana gani mana please wallahi kullum da abin nake kwana a rai nake tashi" Ustaz ya yi shiru yana sunkuyar da kansa ƙasa wani irin numfashi numfashi yake futarwa da ƙyar, zanen photon abun ya kasa gogewa daga idanun zuciyarsa gani yanke tamkar yanzu idanunsa sukai masa mummunan ganin da har ya koma ga Ubangiji ba zai manta ba. Gefe guda sunan BILAL da Ridayya ta furta yana masa amsa amo! A kunne tamkar yanzu ne take faɗa


"Bilal ka taimaka ka saurare ni, idan na fasalta maka ita babu mamaki mu sameta gidan mahaukata"


"Tajj...please"
Ustaz ya faɗa da ƙyar yana ƙanƙame jikinsa tare da rirriƙe kansa yana jin kamar zai cire maimakon su shige airport kai tsaye sai ya nufi asibiti da Ustaz ciwon kan nasa yana bashi tsoro.


Tamkar mujiya haka Ridayya ta tsinci kanta a ƙauyen Batsari mai cike da tarin ni'ima da albarkar noma ga yalwar bishiyoyi da ƙoramaiw gwanin ban sha'awa. Da yawan lokaci barin gidan take ta yi nisa ga cikin ƙauyen ta zauna bakin ruwa ta ci kuka ta ƙoshi ta yi bacci a wajan ta tashi ga girman da cikinta ya yi haihuwa yau ko gobe. Bata da abokin hira sai cikin jikinta gefen zuciyarta kullum tana son tambayar Zameer ina ƙanwarsa Khairiyya? Tunda ya ce ya mayar da ita gidan mijin bata ƙara ji ya yi maganarta ba ko ba a garin take da zama ba?


Ganin yamma ta yi sosai ta miƙe ciki a gaba tana tafiya a hankali tana shigowa cikin mutane aka fara darewa ana cewa "gata nan gata nan" domin tuni ƙauyen ya gama ɗauka ita ɗin mayya ce kowa kaffa kaffa yake da yaronsa da an ganta za a tsiri kunna turaren mayu ita dai bata kula kowa hakan bai taɓa damunta ba, babu kalar tsangwama da tashin hankalin da bata shiga ba a rayuwa, daga iyaye ƴan uwa al'umma gari da miji. Yanzu kuma dangin miji da ƴan ƙauyen su duk dalilin Soyayya da kuma halittar da Ubangiji ya yi mata. Ƙauyen Batsari daman ba wani ilimi ne da su ba balle wayewa kowa ya yi believing cewa ita ɗin mayya ce.


Tunda ta ƙarasu take jin hayaniyya ƙofar gidan kuma cike da mutane ana ganinta aka dare ta shige dafe da ciki turus ta yi ganin Khairy tsaye ta tura ɗauri a gaban goshi ga Zameer ga Iyatu ga baban Zameer da babarsa da tarin yaran gidan da kuma Hanne dake ta kuka. Ridayya ba ta yi magana ba don ta ɗauka Khairy gida ta zo gani sai dai kukan da ta ji da kalaman da suka sauka a kunnenta suka haifar mata da murɗawar mara ƙafarta ta riƙe sosai, haka bayanta da ƙyar ta juya idanunta ya sauka a kan wata halitta wacce Ubangiji kawai ke da ikon samar da ita.


"Ni ba wahalalliyar matarka ba ce Zameer ga tsiyarka nan munafukin banza da wufi, wato ka ɗirka mini ciki shi ne ka watsar dani? Allah ya yi na haife ga kuma ɗanka nan"


A gigice Zameer ya ce
"A'a Khairy wallahi ke nake da muradin aure kece kala ta kuma ina da abinda nake jira dana samu za mu yi aure mu rayu da ɗanmu"


"Wa? Ni Khairiyya na aureka Allah ya kyauta mini idan duk duniya kai ne saura wallahi ban taɓa aurenka na faɗa maka" a gigice Ridayya ta ce "Khairiyya wannan kalaman fa? Wannan maganganun fa ina shi ɗin yayanki ne?"


"Tofar da yawon bakinki ni ba ƙanwarsa bace raina miki hankali kawai yake wallahi, ni budurwarsa tun muna University shi kuma ya ce na dawo gidansa da zama cikin da ya ce miki na mijina ne to nasa ne"




Ridayya ta juya ta kalli jaririn baƙin shi har ba a magana ga ƙaton goshi hanci kamar bana mutum ba suma ɗa babu a kan shi, ɗan tamkar bakwaini ta kalli Zameer da Khairy duka farare ne su gashi sun haifi baƙi kuma mummuna munin daya zarta na Ridayya.


Juyawa Ridayya ta yi ta kasa gane wanne yanayi take ciki tana Khairy na cewa "Gashi nan sunan shi Harazimi" Kafin wani ya yi magana suka jiyo salatin Ridayya tana durƙushe jini na zuba ta ƙasan ta cikin ikon Allah kafin su ƙarasa sun ji kukan jariri amma ba wanda ya taɓa Ridayya wai kar ta cinye shi. Ga wani jini ɗaya ɓalle mata idanunta ya fara rufewa ta fara ƙoƙarin danne jaririn dake kuka ta ƙasanta. Hanne ce ta ƙarasa tana kuka ta riƙe Ridayya ta zaro jaririn ta goge masa jinin jikinsa tas ta yanke masa cibiya. Hanne ta damƙawa Ridayya jaririn ta buɗe ido da ƙyar wani irin hawaye ya zubo mata abinda bata taɓa zato ko tsammani ba, abinda ko mafarki bata taɓa hasaso hakan ba. Kyakkawar halittar dake ƙirjinta kawai take kallo hasken fatarsa har kashe mata ido yake babu abinda ya firgitar da ita yadda take hango tsantsar kamannin Muhammad-Bilal Ustaz a kan fuskar jaririn data haifa kamar su ɗaya sak da Abbiey ɗinta.


"Allahamdulillah" Jikinta ya fara rawa saboda jinin daya ɓalle mata idanunta ya shiga ƙaƙƙafewa ta damƙi hannun Hanne ta ce "Ban san ki ba amma na yarda dake, na bar miki wannan ɗan nawa don Allah ki bawa Abbiey shi ki tambayi Giɗaɗo ya faɗa miki waye Muhammad-Bilal Ustaz na bar miki shi wallahi na bar miki Allah ya yi masa albarka" Idanunta ne ya rufe hanne ta riƙe jaririn ta fara salati cikin ikon Allah Ridayya ta amshi salatin da ƙyar tana mimmiƙewa tana faɗin


"La'ilaha illallahu Muhammadur Rasulullah......








Idan an yi comment zuwa dare a yi new posting






M. SHAKUR


‎KISSA TRAINING CLASS📢


MASU SO SU KOYI KISSA🎊


MASU SO SU IYA KISSA🎊


MASU SO SU SAN KAN KISSA🎊


MASU SO SU ZAMA HATSABIBAI AKAN KISSA🎊


GANE IDAN AN SHIRYA MIKI KISSA🎊


KISSAN IYA KWACE DANGIN MIJI🎊


KISSAN IYA KWACE MIJI🎊


BA BOKA BA MALAM BAKUMA MAGANI KAWAI KISSA KADAI🎊




ZOKI SHIGA AJIN KISSA DA NAIRA DUBU KACAL!!!


5DAYS TRAINING CLASS WANDA BABU YANDA ZA’AYI KIYI TRAINING DIN NAN BAKI IYA KISSA DA KISISINA BA.


KISSA SHİNE BABBAN MAKAMIN MATAR AURE❤️


ZOKI SHIGA KAFIN KISHIYARKI TARIGAKI SHIGA💃🥳


KISSA CLASS PAYMENT IS 1k


GUESS WHAT 5 LUCKY ACTIVE MEMBERS ZASU CI NAIRA DUBU ASHIRIN EACH💃💃💃 20k EACH


ANOTHER 5 LUCKY MEMBERS ZASUCI KYAUTAN SET NA TURAREN WUTA BY RUKY


ANOTHER 5 LUCKY MEMBERS ZASUCI KYAUTAN KAYAN MATA FROM HONEYDROPS KAYAN MATA


JOIN YANZU YOU MIGHT BE THE LUCKY WINNER




You can make payment here


3107021073 Aisha Muhammad first bank
KO


0895672695 AISHAT MUHAMMAD GT BANK


Send evidence of payment to 07032934950


MUNAFUKIN MIJI 25
Mikiya Writers Ass...


Bright pens free batch
Nimcyluv




Writer of
Moon
Mijin Malama
Idan ba ke
Sirrinmu
Uncle ne
Jidda
Zain Abeed
Kwaila ce e.t.c


*Masu son MUNAFIKIN MIJI daga farko ku je wattpad don Allah🥰*
https://www.wattpad.com/1425100722?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=nimcyluv








"A'a ke za ki raini ɗanki ba za ki mutu ba, kin ji?" Cewar Hanne wacce ke riƙe da babyn. Ridayya ta rufe idanu ita kaɗai tasan zafin da zuciyarta ke yi mata ga jinin da yaƙi tsaya mata da ƙyar ta riƙe hannun Hanne ta ce


"Mene ya yi saura a rayuwata? Gwara na mutu maybe nawa farin cikin sai a lahira zai tarbe ni" Idanunta rufewa suke sosai jikinta na rawa har yanzu tana riƙe da hannun Hanne.


"Matar Giɗaɗo... Matar Giɗaɗo" Shiru Ridayya bata amsa ba, hakan yasa hanne rikicewa ta kurma ihun daya jawo hankalin jama'ar gidan da suke ta ɗauki babu daɗi su da su Khairy.


Abinda tunda yake bai taɓa ji ba a tsakanin shi da Ridayya shi ya ruski Zameer, mummunan faɗuwar gaba wani abu dake nuna ban shirya rasa ki ba shi ne yake ji yana matse masa zuciya. Ganin idanunsa ya sauka a kan jaririn dake hannun Hanne ga Ridayya a kwance ga jinin dake zuba ta jikinta ya saka ya ƙarasa wajan da sauri ƙuri har lokacin yana kallon halittar Ubangiji wacce kamar a kan Jaririn na Ridayya aka gama kyau, wannan shi ake kira da baƙar tukunya mai fidda farin tuwo.


"Ke Hanne wannan yaron fa? Ina kika same shi?" Domin shi zaton shi ko jaririn da Khairy ta kawo ne ya yi masa kallon tsoro da farko? Wancan baƙi ne yanayin halittarsa har ta ɓaci sosai ga shimfiɗeɗen baki ƙaton goshi kamar irin yaran ruwan nan wannan kuma zaka iya cewa haihuwar Larabawa ne irin usul ɗin nan.

"Matarka ta haife shi yanzu fa Giɗaɗo, kaga da mun yi aure da tuni ni ce na haifa maka wannan kyakkawan babyn" Mamaki ya kusa kashe Zameer sai ya dake ya kama Ridayya ta yi saurin ƙwace hannunta da ƙyar ta buɗe baki ta ce


"Karka taɓa ni, Hanne kar ki kuskure ki bashi ɗa na don girman Allah"


Zameer ya ja tsaki sosai bai tsaya jiran me zata ƙara cewa ba ya sunkuce ta ya yi waje da ita zuwa can shargalan asibitin da suke da shi a gefen ƙauyen Batsari. Hanne ta rungume jaririn a ƙirjinta tana jin ƙaunar yaron na ratsa ta, dukda ta san zafin ciwo ya saka Ridayya cewa ta bar mata shi amma da gaske take ji inama ta bata shi? Amma ya za a yi mummuna kuma baƙar mace ta haifi wannan yaron?


"Ikon Allah" Hanne ta furta a fili. Ta juya ta kalli yaron da aka yasar a ƙasa yana ta tsala ihu da alama shima bai jima da zuwa duniya ba, ta juya ta kalli Iyatu ta ce


"Haba Iyatu kun bar yaro yana kuka a ƙasa? Akwai karara a gidan nan fa" a harzuƙe Iyatu ta ce


"Me ɗin zan taɓa? Wannan halittar Allah ya sauwaƙe, uwar Giɗaɗo ma bata taɓa shi ba sai ni da nake kishiyar uwarsa? Ai idan kin ganni a lahira wallahi kai ni a kai, gidan da kowa gashin kansa ya ke ji ya je can ya gama ta zubar ɗinsa a kawo shege ki ce na taɓa? Zunubin zan taɓa Hanne kema da zan ba ki shawara da kin haƙura haka nan kin yi auren ki, domin Giɗaɗo ba irin arziƙi bane tun yana ɗanƙaramin shi yake ƙoƙarin hakkewa yaran ƙauyen nan da gayya Malam ya kai shi bara ba? Ashe iskanci kawai yake zubawa a can birnin Kanon"


Wuff iya mahaifiyar Giɗaɗo ta fito daga ƴar bukka tana riƙe zani dake neman kuncewa ta ce "Baƙin ciki kike da ɗaukakar Giɗaɗo ya je birni ya yi ilimi na boko ya nemo mace mai ƙashin arziƙi ai ya bani labarin komai nan da ɗan ƙaramin lokaci jirgina zai ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki" Sai kumfar baki take yi ita ɗaya.


Iyatu ta buga cinya tana ajjiye abin kaɗin adudiga tare da yin shewa da tafi ta ce "Anzo wajan daidai wajan ma, ai ba girinrin ma ta yi ma, idan kuma kaga baƙin maciji ko baƙar leda ka gani ka shafawa hanyarka lafiya,ina ƙoda ina romansa?...," Wata shewa Iyatu ta sake yi tana juya ɗuwawu ta ce


"Riiiiiiii arziƙi kashi idan irin wannan arziƙin dana gani yau an kawo muku shi ne arziƙi to umma ta gaida assha, wai shi ɗan gidan mai dallla ne ko me?" Kafin ka ce me tuni sun hargitsa ɗan gidan nasu Hanne ta lallaɓa ta gudu da jaririn Ridayya zuwa gidansu domin ba zata iya da wannan azabar tasu ba, ko kunyarta sam basa ji.


Da ƙyar jinin ya tsaya aka ce za a ƙara mata wani dukda bata cikin hayyacinta furr cewa ta yi bata buƙatar jinin Zameer a jikinta bisa dole Dr ɗin ya haƙura akai mata allura ya bada magani kasancewar asibitin komai na masu haihuwa kyauta ne a haka bacci ya ɗauke ta. Dr ɗin ya dinga kallon Ridayya ko mutuminta ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login