Showing 66001 words to 69000 words out of 190738 words

Chapter 23 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17298

maganar soyayya tabbas ita ta fara cewa tana son Zameer kuma ya amince ba tare da san aibun hakan ba, ta shure duk wanda girma, daraja, baiwa, ni'ima da Ubangiji ya yi mata. A sanyaye ta ce


"Don Allah ka riƙe ni amana ka zauna dani tsakani da Allah nasan ba zan taɓa yi maka laifi ba, kar ka ce ka fasa aure na, kar ka ce zaka rabu dani kar ka ce zaka sake ni bana son zaman gidanmu ko kaɗan wallahi.....," Sai ta fashe masa da kuka a ransa wani farin ciki ya ji ya samu weakness nata available a fili ya ce.


"If you are never fallen madly in love, understand that God has done you a huge favour. Wallahi na masu na tabbatar dake matsayin matata kuma wannan Abbiey ɗin naki yana neman yi mana shamaki amma idan muka bi hanya ɗaya ba shi ba ko Baffa ba zai hana ba" Ridayya ta ce


"Shi Baffa da mai damu dani ba ya ce ni ba ƴarsa ba ce kaga ai ba zai hana ba" Zameer ya ce "To kice ba ki da wani gata ma kar ki damu zan maye miki gurbin kowa da kowa kin ji? Za ki yi farin ciki sosai Mrs Zameer Mahboon Dollar" Ta yi murmushi ta ce "Na gode" Ya kashe murya ya ce "I love you so so much my wife matata, ki zo makaranta gobe da wuri ina son ganinki"


"Ka ce baka ƙasar?" Ya yi saurin zare ido jin ya kwafsa ya ce "Ai soyayyarki ta motsa ta yi bake-bake a zuciya zan dawo da sassafe" Sallama sukai Ridayya na ji wata nutsuwa a ranta.


Sama da sati Ridayya bata saka Ustaz a idanunta, hankalinta duk ya tashi gashi Zameer yana ta tambayar yaushe zai ga Abbiey ɗin a lokacin sai ta ji bata damu da wayar Meer ɗin ba tunda tana da tabbacin zai aure ta ɗin. Nufar part ɗin iyayenta ta yi ta kuma ci sa a duk suna nan dake weekend ne har da su Zahura suka dinga kallonta haka Mami Zainura ta ce "Yaya Ridayya" Ta juya ta kalli Zainura a tsawa ce Baffa ya ce "Lafiya kika faɗo mana gida?"


"Aure nake so a yi mini Baffa" Maganar ta gigita kowa musamman Mami amma ta yi shiru hankalin Ammi ya tashi ganin plan ɗinta na aurawa Burhan Ridayya zai lalace "Aure wanne iri? Idan aure ne ki je ki yi magana da Babban mutum mana" In ji Balkisu domin ta jima da fahimtar tsananin son da Ustaz ke yi wa Ridayya ɗin ta ce "Na faɗa bai yarda ba, ni kuma aure za a mini bana son zaman gidan nan"


"Tab amma wannan yarinyar ba ki da hankali, yaushe kika san soyayyar wanne mara hankalin ne zai aure ki kuma? Ya taɓa ganin fuskarki?" Ridayya ta ƙi kula Zuhura domin ta san ba ƙaunarta take ba. Junaid ya ce "Kuma kika kasa yi wa Yaa Bilal ɗin biyayya ki jira yi uzurin shi?" Ridayya ta ce "Bashi da wani uzuri fa, kamar yadda Yaya Zuhura ta ce babu mai iya aure na to yanzu na samu aure nake so"


Baffa ya miƙe tsaye ya ce "Allahamdulillah ni na ji daɗi gwara na aurar dake na huta wallahi" Da sauri Ammi ta ce "Wannan ɗin zaka aurar? Me ta sani dangane da soyayya balle zaman aure wallahi ba za a aurar da ita ba ban shirya ba, ba kuma haka na tsara ba" Baffa ya ce "Zan aurar da ita sai dai idan yaron ne ya ce baya so ban kuma damu da dukkan wanda zata aura ba koda zai dinga taka ta a turmi ne"


"Kar ka yi wa aurar baki Baffa ka sanya albarka" Baffa ya ce "Ki rawo mini yaron" Da sauri Ridayya ta kira number Zameer ya ce gashi nan zuwa. Gabaɗaya wanda suke wajan sai la'antar auren suke musamman Baffa da Ammi da Zuhura Mami bata cewa komai tunani take wanda ya sha bambam da nasu.


A lokacin har Baba ƙarami yana wajan da Umma kowa ya hallara Zameer na zaune ya ci uwar shadda ta babbar riga ga ɗan makulin mota ga iphone a hannunsa. Balkisu sai kallonsa take ita da Mami haka kurum suka ji bai kwanta musu ba. "Kai ya sunanka? Waye ubanka a garin nan? Mene matakin karatunka?"


Sai kuma Baffa ya sake cewa kodayake ban damu ba idan zaka aure ta ɗin dukda na yi mamaki. Zameer mamakin yadda ake ta wulaƙanta Ridayya a kan idanunsa a cikin gidansu ya kama shi ya ce


"Sunana Zameer Mahboon Dollar, ina GRA dake Nassarawa da zama Daddyna bai fiya zaman ƙasar nan ba, na yi degree a Bayero University a nan na haɗu da Ridayya ƴarka, kuma ta kwanta mini kuna iya yin bincike domin ku tabbatar" Baffa ya ce "Ba wani bincike da za a yi, kawai ka turo a magabatanka sai a ɗaura aure ka ɗauki matarka" Zameer ya yi hamdala Baba ƙarami kallon Zameer ɗin yake shi da Mami da Balkisu harda Junaid.


"Yanzu kenan ka yi degree aikin me kake?" A ransa ya ce "Zaman banza mana" A fili kuma ya ce "Ina Business a wajan ƙasar nan ina tafiyar da harkokin mahaifina" Da gaske ya yi degree domin ya dage yaga ya yi karatu domin ƙarya da shiga sabgar manya sai da ilimi kawai ya yi alƙawarin idan ba aikin Gwamnati bane da zai dinga ganin kansa a office mai A.c yana juyawa yana saka hannu a manyan files na harkar maƙudan kuɗaɗe to zai taɓa wani aiki saɓanin wannan ba.


"Na baka ita"
"Ban amince ba, sai mun yi bincike a kan ka" Da sauri Baffa ya kalli Baba ƙarami Ammi ma ta ce "Ban amince nima" Haka Balkisu. Nan da nan Ridayya ta fara kuka hankalinta ya tashi "Ka je zan kira ka ko?" Cewar Baba ƙarami.


Kwana biyu tsakani Ridayya ta dinga neman Abbiey ɗin nata baya nan ta san shi kaɗai ne kawai zai ji tausayinta,number shi a kashe bedroom ɗinsa a rufe. Baba ƙarami ya dinga neman Ustaz shima domin abin ya zo saɓanin tunaninsa shin daman ba son Ridayya yake ba all this time?. Abinda basu sani ba Ustaz na gidan ya rufe kansa a ɗaki shi kaɗai sai rubutu yake a cikin diary ɗinsa cikin kwana biyu ya faɗa ga wani ciwon ƙirji komai ya dai na yi masa daɗi ya ƙara zama shiru-shiru Ridayya ta bashi mamaki ta gigita shi da kalamanta.


Yau tunda ta je makarantar ba taga Zameer ba yanzu ne kuma suka shiga second semester. Mardiyya ta ce "Dole na kalle ki ban ɗauka haka kike ba, wallahi za ki yi ladama idan kika auri Zameer I'm telling you Ridayya"


"Ki samun albarka kawai Mardiyya" Diyya ta ce "Ba kya tausayin Abbiey wallahi yana son ki duniya ma ta san haka"


"Ki aure shi mana Mardiyya, ai ke kina jin tausayin shi ko?" Da mamaki Mardiyya ta ce "Haka kika ce? Ni fa aminiyarki ce idan ban faɗa miki gaskiya ba waye zai faɗa miki? Ki nutsu sosai ki gane dalilin daya saka kike son auren Zameer na tabbatar ba soyayya ba ce, kamar yadda shima ba son ki yake ba, soyayyar gaskiya tana wajan Abbiey" Ridayya ta miƙe ta ce


"Mardiyya me kike nufi? Jallabiyya zan aura ko hirami ko carbi, ki auri Abbiey mana wallahi zan fi kowa murna idan na gan ku tare as husband and wife ni bana son shi ke kuma ya yi miki sai a haɗa bikinmu rana ɗaya ki zauna kullum ya dinga faɗa miki Asstagafirullah subuhanallahi ko kuma ya yafe miki" kalaman Ridayya kamar ka yi musu dariya amma gaskiya take faɗa. "So kina so ki ce he's not romantic? Jallabiyya baya burge ki ko? Kin san wani abu baki san su waye ustazai ba Ridayya lokaci ko na ce rana ɗaya idan ki kai soyayya da su wallahi sai kin hauka ce, su ɗin daban suke ba a banza ake kiran su da Ustazai ba sun karanta sun gani sun san mene soyayya da aure, ki rubuta ki ajjiye wallahi tallahi sai kin yi kuka akan Abbiey"


"Kuka? Duk kukan da na yi a rayuwa? Bari ki ji Abbiey ba irin mutanen ne ba daban Allah ya yi mini Abbiey na, kuma da na ke cewa ki aure shi wasa nake miki shi ba zai yi aure ba ai faɗa mini, kuma uba ne a wajena har abada ba kuma yadda za a yi ya sauya mini ba zai taɓa barina na yi kuka kuma ni ma bana son damuwarsa, ni kawai bana son shi kuma shi ma bai taɓa cewa yana so ba idan kina tunanin na yi ba daidai ba don Allah watarana na ji labarin aurenku ke da shi" Tana faɗin hakan ta ɗauki jakarta ta bar wajan. Mardiyya ta bi Ridayya da kallo tunda suke yau ta taɓa jin Ridayya ɗin ta yi magana mai tsayi dukda faɗa take amma sanyi ne a muryarta sosai idanunta da maganganunta na ƙarshe sun nuna zallar kishin Abbiey. Idan ta fahimta SO shi Ridayya ta ke wa Abbiey, BURGEWAR da Zameer ke yi mata ya danna son take ganin kamar shi zuciyarta ke buƙata da yawan lokaci ganganci da mata ke yi kenan da zarar anga farin namiji yana murza shadda za a ɗauki soyayya a aza masa.


Ridayya ta sake kiran number Ustaz cikin sa a ta shiga kuma aka ɗaga sai dai ba magana. Shirun Abbiey na taɓa zuciyarta ainun muryarta na rawa ta ce "Abbieyna don Allah kar ka yi fushi dani ka taimaka ka saka baki su Abba su amin na yi auren nan" Ya sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ta ce "Baka da lafiya? Please kar ka yi ciwo ka taimaka mini"


"Shalale just think about me, kar ki cutar dani please"


"Abbiey wallahi bana son ka wallahi baka taɓa burgeni ba ka tausaya mini" Ba zata tantance yanayinsa ba sun jima kafin ya ce "Ki yi tunani iya yau, a yanzu ba ruwana Ustaza" Ya kashe wayar. Ta yi ta kuka ta dinga neman Zameer da ƙyar ta same shi cikin tawagar su.


"Meer ga mayyarka can" In ji Moo ya ce "Wallahi duk ta daman gashi bana son Khairy ta fahimci da ita, kasan halinta amma yau zan kawo ƙarshen komai" Ta tsaya daga nesa da tunanin zai zo amma ya yi burus ya haɗe fuska ta ƙarasa kan ta a ƙasa ba wanda ta kuma sai shi ta ce "Ina son magana da kai"


Suka matsa ya haɗe fuska ya ce "Ki rabu dani kawai tunda bakya tausayina ba ki damu dani ba, kina kallo za a rabani da ke" Ta girgiza kai ta ce "Ba zan bari ba"


"Me za ki? Ai wannan Abbiey ɗin baya son farin cikin ki daya bari mun yi aure amma zan nemi wata kawai" Jikinta na rawa ta ce "A'a don Allah idan ka bar ni ba zan samu wani mijin ba"


"Kina so na?" Ya tambaya idanunsa cikin nata, ita ma cikin idanunsa take kallo kamar yadda yake kallon nata. "Ina son ka"


"Ki tabbatar mini da wannan son Ridayya ki bani dama mu raya yau, muddin na same ki yau babu wani abu da zai yi mana shamaki da aure, ki mallaka mini kan ki budurcinki yau ɗin nan idan ba haka ba kawai zan rabu da ke"


"Kana nufin mu yi iskanci?" Ya ce "Oh C'mn auren ki zan yi so babu wani batun kalma mai kama da iskanci, amince mini shi zai tabbatar da kina so na za ki iya yin komai domin ni, kamar yadda ni ma zan iya ka kalli yadda na rame ki duba ko abinci bana ci saboda tunaninki, idan na bar ki ba za ki samu mijin aure ba" Ridayya ta fara tunani da gaske idan Zameer ya rabu da ita babu wani da zai zo mata da kalmar Soyayya balle aure, domin har yanzu kalaman Burhan yana zaune a zuciyarta.


"Idan ban amince ba wata zaka aura?" Ya kashe ido yana kwantar da kai ya ce "Bisa dole, domin tun yanzu zan fahimci ba za ki iya sadaukar da abi domin ni ba, kuma ai daman haka ake soyayyar yanzu don dai ba ki taɓa yi ba, ni kam idan ba ki amince ba daga yau babu ni ba ke"


"Na amince" Ta faɗa ba tare da tunanin komai ba. Zameer ya zage ya dinga mata kalamai masu daɗi da sanyaya zuciya ya tabbatar mata ita da shi mutukaraba takalmin kaza. Haka ya ɗauketa zuwa hotel ta na ji tana gani ya yi fatali da budurcinta ya mayar da ita cikakkiyar mace a waje tun kafin ta je gidansa, ba tare data sani ba duk abubuwan da suka wakana a lokacin Zameer yana yin vedion komai a wayarsa tun daga zuwansu hotel ɗin har sanda ya rabata da budurcinta....






Ku jira ni zuwa dare idan naga comment.


Na'ima Sulaiman Sarauta
Nimcyluv
08164069385
*✿ MUNAFUKIN MIJI 22 ✿*
Mikiya Writers Ass.....




BRIGHT PENS🤙🏼 free batch
Nimcyluv




Ya juya ya kalleta jin yadda take ta kuka, zuciyarsa fes ya samu miliyan goma a caca ta sanadin yarjejeniyar soyayya ta samu budurcin Ridayya. "Kukan na mene kuma? Bafa dole na yi miki ba"


Kukan da bata san dalilin yin sa ba shi take a lokacin da ƙaddara ta yi fatali da dukkan wata kima da darajarta na ɗiya mace saboda ƊA NAMIJI, da soyayyar da bata tabbacin zahirin ta a cikin zuciyarta, ta wofintar da duk wata kulawa tarbiyar da Abbiey ya bata sun zama tarihi a yanzu. Shigowar Zameer cikin rayuwarta tsakanin wasu ƴan watanni ya rusa tarbiyyar shekara goma sha shida da watanni.


"Haba Pretty idan kina kukan nan ina jin kamar ban dace da ki mallaka mini komai a matsayina na wanda kike so kuma kike shirin aure ba"


Ta kasa magana sai sautin kukan dake tashi a hankali tana naɗe jikinta a bargo, haka kawai fargabar Abbiey ya san wannan abin mai shirin tarwatsa zuciya ya rusketa. Ta tsinkayi muryar Zameer dab da kunnenta yana kama hannunta da yanzu bashi da shamaki da shi ya ce


"Look into my eyes Ridayya, na yi miki dole? Ita fa soyayyar zamani haka take kina so na yi believing da haka, kuma wannan abin daya faruwa babu komai sai ƙauna kin bani kyauta mai muhimmanci wacce ba zan mance da ita ba, zan dinga tunawa a kullum, kin bani budurcinki na ba ki nawa kinga 50/50 kenan ko?"


"Idan har zaka aure ni shikenan hakan shi ne muradi na, i know nothing about the love.....,"


"Shi ya sa na fara nuna miki yadda soyayyar take yanzu ai, cikakken masoyi shi ne mai yin haka idan ban yarda da ke babu ta yadda za a yi na yi tarayya dake Ridayya" Ta jinjina kai a hankali ba tare da ta ce komai ba a hankali maganganun Zameer na yaudara ke ratsa zuciyarta ya ce


"Ki yi wanka na yi dropping naki gida baby" Da ƙyar ta ja ƙafafuwanta tana rufe Idanu saboda tsananin azabar dake ratsa gaɓoɓin jikinta yana kai wa zuwa jijiyar dake sadar da yanayin mutum a kwakwalwa.


Yana tsaye ya sauya kaya zuwa wani milk ɗin voyel mai manyan zane iya kyau da ɗaukar hankali Zameer ya yi, ya taje sumar kan da comb sai ɗaukar ido take komai nasa dabanne a idanun Ridayya ta yi tsaye tare da shagala da kallon shi.


"Ya dai? Wannan kallon fa Mai so na?" Ta ɗauke idanu sanyaye ta ce


"Ka iya kwalliya ko wanne kaya na yi maka kyau ina son yadda kake dressing" Ya ɗan taɓe fuska yana lumshe idanunsa can ya riƙe ƙugu ya ce


"Oh hello na fahimci ke kalmar _I love you_ wahala yake miki ban taɓa ji kin ce Zameer i love You ba, sai dai a ce na yi kyau? To ki riƙe yabon nikam yau kalmar soyayya nake buƙata wajan ki" Cikin yanayin da ya zame mata ɗabi'a ma rashin son magana da sanyin jiki ta ce


"To ai ban san me zan ce ba, Abbiey kawai nake iya cewa ina son shi" Ya watsa idanunsa cikin nata can ya ce "Say something different....,"


"Rayuwata"


Ya juya da sauri jin sunan da ta ce ya dinga binta da wani irin kallo can ya saka hannu ya cira ta sama yana zagaye da ita ya ce "Oh wow gaskiya I'm lucky person, irin wannan suna haka say it again"


"Rayuwata"


"Mai sona" Ya faɗa yana kallon idanunta da suke a lumshe komai nata a nutse yake hatta muryarta golden voice Ubangiji ya bata, idanunta sexcy eyes ne irin nasu kyau da tsari shi sam har lokacin a gigice yake da lamarin Ubangiji, yadda take da muni daban yadda Allah ya sanya ni'ima da baiwa a jikinta daban, ya kasa mance irin tagoma shin lagwadar daɗin daya kwasa, sanda ya fara kai hannunsa zuwa jikinta ya girgiza the real definition na jin daɗi fata mai kyau ita ce Ridayya's skin bashi da ƙarfin qiwwar faɗar taushi da laushi fatar ta, ko'ina ya taɓa lutsum yake nutsa hannunsa babu rama ko misƙata zarratan a jikinta. Lafiyayyen diri mai ɗaukan hankalin namiji gata a sangarce take komai kuka Abbiey ya riga daya lalata Ridayya a ɓangaren shagwaɓa ko tari baya so da ƙaunar yaga tayi hakan bai rufe masa ido wajan tsawatar mata ba idan ta kuskure.


Da ƙyar take jan ƙafar tana tafiya a hankali cikin ikon Allah ta shige bedroom ɗinta, tare da faɗawa kan gado ta kwanta idanunta lumshe, abinda ya faru tsakaninta da Zameer ba komai bane sai soyayya kuma zai tabbatar zata iya komai domin shi. Amma ta sha jin ana cewa cikar kima da darajar mace shi ne ta kai budurcinta gidan miji? Mene bambancin wacce ta bawa saurayi a waje da nufin nuna masa soyayya da wacce takai gidan miji? Ta mirgina wani irin zafi ƙafafuwanta ke mata wa zata faɗawa? Me zata saka ta daina jin zafin? Nan da nan zazzaɓi kuma ya rufe ta ta rufe jikinta sai rawar san yi take hawayen da bata da masaniyyar dalilin taruwar su suka shiga wanke mata fuska.


A hankali ya turo ƙofar domin ya kasa jurewa idan wani zai faɗa masa zai iya yin kwana biyu a gidan bai ga Ustaza ba zai ce ƙarya ne, sai gashi ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login