Showing 114001 words to 117000 words out of 190738 words

Chapter 39 - MUNAFUKIN MIJI BOOK COMPLETE PDF ORIGINAL ONE TO END. .txt

24 Jul 2024

17324

gabɓanta sun yi sanyi duk maganar da Sadaukin yake bata fahimta kamar almara ta kasa juyawa kuma.


Tajj tun shigowarsa harabar gidan idanunsa ya sauka a kan Ustaz da sauri ya fito ko kashe motar bai ba cikin wani irin tashin hankali ya kira sunan Ustaz.


"Bilal Innalillahi Bilal"


Kiran sunan ya saka Ridayya juyawa da wani irin firgitaccen yanayi ta kwace hannunta daga na Sadauki har tana bangaje shi ta nufi inda Ustaz yake wanda Tajj ke ƙoƙarin riƙe shi amma ya hana a dole shi zai miƙe.


Tuni hawaye sun wanke mata fuska kamar yadda jikinta ke rawa haka zuciyarta ke yi daga kusa da ita ta ce murya mai ɗauke da tashin hankali ta ce "Abbiey"


Kallon da ya yi mata ya saka ta fahimci zuciyarta ce ta kira shi, raguwar halittar daya ya yi saura a cikinta shi ne ya kiranye shi.


"Kar ki zo mini nan kar ki taɓa ni" Ya furta da ƙyar yana numfashinsa na riƙewa zuciyarsa na tarwatse.


"Please Ustaz not here akwai Sadauki a wajan, ka bari mu je asibiti"


"Sadauki? Ka faɗa masa ya zo ya nemi aurenta waje na"


Yadda Ustaz ke maganar kamar baya nutsuwarsa kuma shi kansa bai san me yake cewa ba, taurin kai kuma ya hana shi ya kwanta yana miƙewa jiri kwasar shi. Ridayya kuka take ganin yadda Ustaz yake abu kamar zautacce


Tajj ya ƙarasa wajan Sadauki ya ce "Hamza jeka za mu yi magana"


"Where? Kana ji ya ce na zo na nemi aurenta a wajansa"


"Na ce ka je za mu yi magana ko Sadauki" idanun Sadauki ya yi jajur ya ce "Ba inda zani domin ba wajanka na zo ba, kai na nemi taimakonka ka share ni, bare ya fini...,"


Wani mari Tajj ya saukewa Sadauki a fuska ya ce "Ka shiga hankalinka kuma zanje wajan Daddy na ji da wanne irin abokai kake yawo"


"Babana babana ne ni ɗaya ka ce Prof zai fi daɗi a rai, daka ɗauke shi matsayin uba ba zaka wulaƙanta ni a kan wani ba, kuma ba zaka bari na rasa abinda nake so ba, so please stay away from me"


"Ok fine ka fita"


Sadauki ya nufi wajan Ridayya ta yi saurin yin baya idanunta a kan Ustaz da kansa ke ƙasa ya ƙarasa har gabanta idanunsa na zubar da wani rin hawaye mai zafi ya ce


"Zan tafi ba zan dawo ba sai da Daddy, i love You Ridayya don't ever ever trying to break my heart" Ya runtse idanunsa "Wallahi ina son ki, idan kika rabu dani abin ba zai mana daɗi ba ki saka a ranki bana yafiya saboda tsakani da Allah nake tsananin ƙaunarki duk abinda nake ina sane na san me nake yi, don Allah karki barni"


Sai kawai ya fashe da kuka abin har tsoro ya bawa Tajj don bai taɓa ganin Sadauki ya yi ko hawaye ba balle kuka, ko abu ne sai ya ce ya fi ƙarfin ya saka wannan ɗan abun a rai shi ya sa bai taɓa gwada yin soyayya ba.


"Ridayyerh i love You. Love isn't something you find. Love is something that finds you, ban san yaushe nake miki wannan son ban"


"Sadauki get out, ka rabu da ita ko?"


"Tajuddeen Baita shut up ok, ka rabu dani kai baka san komai ba tunda Maman Nadra auren zumunci ne haɗa ku akai, baka san ya mutum yake ji a zuciya ba idan hakan ya kasance"


Tajj ya jinjina kai ya ce "Ok" wayarsa ya danna magana biyu ya yi ya kashe sai ga wasu ƴan'sanda sun shigo cikin gidan sukai kan Sadauki da mamaki Sadauki yake kallon ɗan'uwan nasa ya juya ya kalli Ridayya wacce itama a ruɗe take gabaɗaya ta kasa fahimtar mene hakan?


"Ku je da shi"


Har aka fita da Sadauki idanunsa yana kan Ridayya yana jin kamar yanzu ne ma ya santa kuma ya fara sonta a cikin zuciyarsa. Jansa ƴan'sandan suke yana ji kamar ana saka abu ana cakar masa zuciyar gabaɗaya ji ya yi he just left himself wajan Ridayya there are millions of people in this dunia but all what he see is RIDAYYA no one can make him feel like her, and he will do anything to keep this feeling safe dole zai dawo kuma da iyayensa.


Sadauki na kallonta ita tana kallon Ustaz shi kuma Ustaz na kallon ƙasa Tajj kuma yana wayar a gaggauce. "Abbiey jini a jikinka mu je hospital ka ji kar ka yi ciwo"


Kallonta ya yi, wanda sai da hantar cikinta ta juya sai da ta yi ƙarfin hali wajan sake kallon cikin idanunsa amma abinda ta gani ya nemi ɗauke numfashinta, jinta ganinta murmushi taga ya yi tare da yi mata nuni da ta zo. Jikinta na ɓari ta ƙarasa ya yi saurin dakatar da ita ɗan nesa da shi ya ƙarasa miƙewa tsaye daman yana ɗan durƙushe ne gudun kar ya faɗi. A daidai inda take ya tsaya ya dinga murmushi sai kuma ya haɗe fuska ta ji muryarsa a saman kanta na faɗin.


"I don't hate you for not loving me anymore, but I hate myself for still loving you." Ya sake yin murmushi idanunsa jajur komai na zuciyarsa na buɗewa dukda ta gama yin rauni ya kuma sare da al'amarin bata isa ya mutu saboda ita ba "Abbiey don....,"


"Shhhh!" Ya faɗa yana ɗora yatsarsa a bakinta yana jin dukkan wasu feelings and emotions ɗin zuciyarsa suna tattarewa zuwa wuya ya ce "I've lived all this while for your happiness, but now, it is time I'll have to live for my own. I hope someday karma makes you suffer very much for betraying my trust. I hate you."


Komai na kan Ridayya ya zama fresh kuma new kamar an yi updating ɗinta da kwakwalwarta da tunaninta to the latest version ba a taɓa furta mata kalma mai zafi da ɗacin wannan ba, har maƙogaronta take jin ɗacin maganar ta dinga girgiza kai ina ma zata iya faɗa masa gaskiyar abinda take tsoro kuma take shakkarsa? Me ya sa rayuwarta take zuwa a haka ne ta ji dama bata zo duniya ba.


"I just hate you Ustaza"


Fitowar Mardiyya ya saka kai tsaye Ustaz ya nufi wajanta da yana da iyaye babu shakka wajansu za shi ko ya samu sauƙi yana ƙoƙarin ƙarasawa inda take ya yanke jiki ya faɗi ga wani dutse a wajan kai tsaye kuma mararsa ta sauka a kan dutsen.


"Abbiey!!!" Ridayyerh ta faɗa shout and soundly daidai nan itama ta yanke jiki ta faɗi a sume kafin Tajj ya motsa motoci wajan guda uku suka shigo.
Da sauri Alhji Mansur ya fito bayan Junaid ya yi parking suka, daga nan kowa ya fito hadda Barrister jikin Mami na rawa ta nufi wajan Ustaz Ammi kuma ta tsaya tana addu'ar Allah ya sa Ridayya mutuwa ta yi uban kowa ya huta don kar a ganota ta yi saurin nufar wajan Ridayya Baba ƙarami kallon tilon yaronsa ɗaya tal a duniya yake zuciyarsa na tsinkewa bai yi zaton a haka za su ruski yaran nasu ba. Tsoron rasa Muhammmmd ya saka shi rikicewa dukda kawaicinsa a kan Ustaz ɗin. Umma ta rushe da wani irin kuka tana cewa


"Shikenan ta kashe mini yaro ta kashe shi wallahi idan Muhammmmd ya rasu a kan ta ba zan yarda ba itama sai an kashe ta innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Babana baban mutum" kuka take tana jijjiga shi hankali tashe.


Barrister ne ya yi ƙoƙarin cewa "Asibiti ya kamata mu tafi da su ba mu tsaya kallon su ba"


Alhaji Mansur ya ce "Tajuddeen Junaid ku saka Babban mutum a mota" Suka kama Ustaz tare da sa shi a mota Baffa da kansa ya ɗauki Ridayya da hannunsa abinda bai taɓa yi ba tunda aka haifeta yana jin wani danshi na bin fuskarsa ya saka ta a mota, gabaɗaya basu lura da Mardiyya dake ta kuka kamar ranta zai fita ba.


Ta ƙasan Idanu yake kallon tafin ƙafarta da sukai fari tas ga dugwayen yatsunta gwanin sha'awa yadda aka gigice a kanta abin har mamaki yake bashi. Ya taɓe bakinsa tare da ɗaga kafaɗunsa cikin ko in kula ya zaro mandula yana murzawa tare da kunnawa ya shiga bata hayaƙi. Ammi data lura ta yi saurin dawowa baya ta ce "What rubbish? Mene haka shaye-shaye za ka yi anan wajan?"


"And so what? Ni fa gaskiya ba zaki kawo ni nan kuma ki takura ni ba"


"Amma Burhan kasan plan ɗinmu ko? Kai gabaɗaya kwakwalwarka bata faɗa maka gaskiya haka fa jiya na ji ance kun yi faɗa da wani ka saka wuƙa ka yayyanka shi yana asibiti da ban zo da kai nan ba da tuni police sun kama ka"


"Uhm" kawai ya ce yana girgiza kansa yana jin hayaƙin mandulan har tsakiyar kansa ga wani lafcecen yanka a ƙasan wuyansa.


"Ina magana kana sake hura mini hayaƙi bana son warin abar nan" zuƙar ƙarshe ya yi mata ya cillar a ƙasa ya saka ƙafa ya take sai yanzu yake ganin mutane tarr kuma daidai.


"Muje asibitin" Burhan ya girgiza kai ya ce "Kuje kawai" ya nemi waje can kusa da Maigadi ya zauna Maigadin duk a tsorace yake da Burhan.


Emergency a nan aka amshi Ustaz shi da Ridayya aka sanya su a ɗaki ko wanne daban nan da nan aka shiga kulawa da su har yanzu Umma kuka take Mami ta kasa cewa komai kasancewarta mace jaruma mai shanye abubuwa da yawa. Alhaji Mansur ya ce "Ban yi tsammanin ganin hakan ba, na ɗauka zanga Muhammmmd da Ridayya cikin farinciki suna tare ina jin kamar na yi kuskure wajan ɓoye gaskiyar komai akan cewa mun mutu, ban kyautawa kaina na ji ban cancanci zama uba a wajan Ridayya ba, na wulaƙanta ta na aibata ta, ta nuna wa duniya bata da wata daraja irin ta ɗa, ina tsoro kar ta mutu ban kyautatawa rayuwarta ba tunda aka haifeta bata yi farinciki ba...," Barrister ya riƙe hannun Baffa ya ce


"Alhaji Mansur mu bar maganar nan, fatanmu Allah ya basu lafiya bakiɗaya. Za su yi farinciki in sha Allah za a zama one big family"


"Na rasa wake da saka hannu wajan rusa farincikin iyalina, dole akwai dalili wannan dalilin bai shige ni ba"


"Kai Munafikin miji ba, daka fifita yarinya tun tana ciki ka nuna kamar ba a taɓa yi maka haihuwa ba, munafurcinka ya ja komai"


Cewa akai duk su tafi gida har zuwa sanda wani daga ciki zai farfaɗo Junaid ya kasa tafiya yana masifar ƙaunar Yaa Bilal kamar rai yana tausayin ƙaddararsa kamar yadda yake tausayin nasa ƙaddarar wacce har yanzu ta hana shi aure. Suka koma gidan Ustaz aka bar Junaid da Tajj da kuma Yaya Balkisu. A can suka samu Mardiyya mamakin ganinta ya cika masu rai, Hajiya tana ta kuka itama Mardiyya haka.


Farincikin ganin Alhalin Mai ran ƙarfe ya saka Hajiya da Mai ran ƙarfe yin kukan da basu taɓa yi ba, daman komai cuɗe musu sun kasa aiwatar da abinda ya dace, sun yi kuka har sun gaji bayan Baffa ya basu labarin komai.


Ammi ta juya ta kalli Mardiyya ta ce "Mardiyya tare kuka dawo da Ridayya ne domin idan anga zara za a ga wata, to ai ba kuka ya dace ki yi mata ba addu'a ya kamata ki yi ko?"


Hawayenta yaƙi tsayawa ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta ganta wajan Ustaz. Hajiya ta ce "A'a ai matar Ustaz"


Da wani irin shock Baffa da Baba ƙarami suka kalli juna hatta Barrister ya razana da jin furucin na Hajiya Yaya Zuhura ta ce "Matarwa kika ce Hajiya?"


"Matar Muhammad-Bilal matarsa ta sunna"


"Tamɗijam! Kuma ya san an yi auren shi ya ce yana sonta wannan dai haɗinki ne"


A fusace Hajiya ta ce "Dam ƙundun ubanki haɗin nawa ne, ba zuba idanu ya tsofe babu aure ba masifa ta ci ta cinye shi"


Yaya Zuhura ta ce "To a gaskiya ba ki kyauta ba, ita kuma ya yarda ta aure shi har da shimfiɗe ƙafafuwa?"


Baffa dai ya kasa magana ba'a rabu da Bukar ba an haifi Habu rikici kan rikici Allah ne kaɗai ya san manufar faruwar hakan. "To yana can Kano aka yi komai, kuma Allahamdulillah ya aminci bai bani kunya ba dukda har cewa ya yi bashi da lafiyar zama da mace wai nakasashe shi, bayan nasan ƙarya yake ni zai mayar karfa kullum yana cikin azumi ai tarr nake kallonsa lafiya lou yake itama yarinyar na faɗa mata ta kwantar da hankalinta"


Wani sanyi Mardiyya ta ji at the end zata san mijinta, za su yi tarayya matsayin miji da mata hope ɗinsa a kanta ya ƙaru tare da wata kalar soyayya mai zafi dole ita kaɗai zata kasance da shi babu wata ƴar mace da zata yi musu shamaki ko ta zama labule tsakaninsu.


"Alhaji Mansur mun makara" Baffa ya girgiza kai ya ce "Ya ce haba kafi kowa sanin komai"


"Ma sha Allah, na ji daɗi Allah ya sanya albarka ya basu zama lafiya daman Babban mutum mace ɗaya yake da muradi a rayuwarsa tunda an masa aure da Mardiyya magana ya shige su zauna lafiya su biyu abinsu ni kam Hajiya kin kyauta mini sosai"


Daga Baffa har Mai ran ƙarfe sun gane manufar Umma suka share. Ammi hamdala ta yi tunda Ustaz ya yi aure yanzu dole Burhan ya zama zaɓin Ridayya. Mami bata cewa komai tana jin zafin yadda Umma take nuna tsanar Ridayya idanu biyu Zainura ta yi shiru.


Can dare aka kira su Ustaz ya farka kuma Allahamdulillah da sauƙi amma akwai matsala zuwa safe suna iya zuwa a yi musu bayani. Har kuma gari ya waye Ridayya ko motsi ba ta yi suka fara shiga fargaba har likitoci har kawo lokacin Ustaz bai san su waye suke tare da Tajj ba.


Kokawa suke sosai shi da Hanne yana haki tana haki ta ce "Ba jaka bace ni da zaka dinga faɗo mini kamar dabba ko dabba ta san soyayya"


"Karki kuskura ki zage ni kuma ai ke matata ce ina da hakƙi a kan ki"


"Baka bani ci ba balle sha uwa uba abin ƙara lafiya da kuzari to baka isa ka zo mini da wata buƙatarka ba, shi ne ka wani kwaso ƙafa abujajen kai kaga mai mata ko? To wallahi ƙwalelenka malakar kare da hanzar kura, na farko dana bari na yi niyya ne"


"Don Allah don Annabi Hanne ki tausaya mini ni kaɗai na san yadda nake ji, ni ba haka na saba da matata ba, ita kullum bata gajiya dani baiwar Allah ce"


Hanne ta yi shewa tana tafa hannu ta ce "Haka na gani a ƙasa, daman taya zata ga ji da kai tunda ka zame mata munafikin miji banda ƙarya da haɗata da dangi ba abinda ka iya, ni daban Ridayya daban"


"Wallahi ita baiwar Allah ce ga haƙuri da tausayin miji ko na lokaci ɗaya ne ki bani dama ba zan sake tambayarki ba, da zarar matata mai sona ta dawo shikenan na miki al'ƙawarin ba zan sake tambayarki ba, kin san ina son ki you are my first love"


Zameer ya zage yana kwararawa Hanne kalaman soyayya masu ratsa zuciya nan da nan ta ji wani irin buƙatar mijinta Ubangiji ya bawa Zameer baiwar tsara mace gashi kyakkawa da iya ɗaukan wanka.


"Na ji amma ka fara wanke mini kaya ka kai mini ruwan wanka banɗaki ka kuma kawo mini tsiren Ayuba mai zafi sai ka zo mu satata" Ta faɗa tana fari da idanu tare da kaɗa jikinta


Jikinsa na rawa ta wanke kayan tas ya kai mata ruwa, ya saka Iya a gaba kalamai akan zai je ya siyar da fili ta bashi aron kuɗin mota "To ni bani da kuɗi amma a ɗaga shanuwa ɗaya a siyar na baka rance"


Nan da nan ya je ya amso zazzafan tsire na dubu biyu da biredi yana dawowa ya tarar Hanne ta caɗa ado daidai yanayin ko wacce mai wayewa ta ƙauyen Nahutun Batsari. Ta ci ta ƙoshi ta yi gatsa Zameer jikinsa har rawa yake domin sai daya tsaya ya sha tsumi a hanya yana ta faman baza riga.


"To jeka ka yi wa iya sallama" Babu musu ya fita kafin ya dawo ta rufe ƙofa ta ce "Zaka gane baka da wayo Munafuki"


Zameer bai iya bacci ba ya kwana tsaye yana firfita wando daga ƙarshe ya cire ya saka babbar riga ji yake kamar ana jan shi ya haɗa uwar zufa tsumin ya gama ratsa shi. Yana fita yaga ƙofar Hanne a buɗe ta manta sanda ta yi fitsari cikin bacci ta ji an faɗa mata kamar doki, ya fi ƙarfinta dole ta haƙura burinsa ya sumbaci bakinta ta datse taƙi bashi daman. Sanda ya ji daidai ya shaƙe mata wuya tamakr zai kasheta shi haka halittarsa take ta dinga kakarin mutuwa amma yaƙi sakinta faratansa duk sun shata a wuyanta sai dai ya ji daidai ya saketa ganinta a shimfiɗe kamar gawa ya saka nan da nan ya rikice tunaninsa ta mutu domin kullum haka yake wa Ridayya ya shirya ya kwashi kayansa da kuɗi da takardu sai tasha ya shiga motar Kano. Suna hanya ya kira Moo yake cewa nan da lokaci kaza jirginsu zai sauka a airport sun dawo daga Cameroon shi da Daddynsa.




Sanda labari ya je wa Prof Tajj ya kama Sadauki lokacin yana tare da wata sabuwar yarinya da ya yi Asabe reza tana ta masa yauƙi bai wani damu da iyalinsa idan ya sakar musu kuɗi gani yake basu da damuwar komai.


"Prof zan ce ko Hon?"


Ya ɗaga kafaɗa ya ce "Ko wanne zan amsa, ai da secretary ya tura mini pictures ɗin ƴan'matan na ji ba wacce ta yi mini sake" Ta yi fari da idanu ya tura mata kuɗi masu yawa ta ce "Thank you zama Ɗan'majalissa dole my professor"


"Anything for you baby"


Yana ta ganin kiran mother ya share can ya ɗauka ya ce "Sweetheart matata uwar Hamza Sadauki ya aka yi ina ta missing naki aiki ya sani gaba yanzu haka ina office"


Cikin kuka ta ce "Ba cewa zan yi ka dawo ba, Sadauki yana wajan ƴan'sanda ko ba zaka dawo gida ba ka taimaka ka shiga maganar"


Cikin basarwa ya ce "What? My son mene haɗin Sadauki da ƴan'sanda kuma ni ina nan ina ta fafutukar neman abinda zan rufa mana asiri shi kuma zai ɗakko magana? Aiki nake amma gabaɗaya tunaninku ya hanani sakat ji nake kamar na haƙura da komai na zauna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login