Showing 1 words to 3000 words out of 166068 words
UWAR SADIKU
WRITTEN BY
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
1
A kicin ya sameta tana wanke-wanke, motsin shigowarsa yasa ta juyo. Ta kare masa kallo tana murmushi, shima kallonta yake yana murmushi. Yace
‘Daina motsa baki ki fadi abinda yake ranki.’
Ta kyalkyale da dariya ta cigaba da dauraye kwanon da ta wanke tana fadin
‘A’a! Gani nayi an ce Bichi za a je a gaida Baffa amma kuma naga an dau wanka kamar za aje wajen bazawara.’
‘Au ashe fa ban gaya miki ba akwai wata budurwa ce ma da zan dan abinnan....'
Kafin ya karasa ta katseshi tana dariya
‘Babu abinda zakayi, daga ni sai kai nawan ni kadai.’
‘Idan na dawo nace ki kwashe kayanki daga daki daya ai zaki gane.’
Ta kyalkyale da dariya.
Suna ta zolayar juna suka yi sallama tayi masa a dawo lafiya ya kama hanyar Bichi; inda zai je ya gaida kakanninsa na wajen uba.
Haka suke rayuwarsu cikin walwala da kaunar juna tare da yaransu biyu Abdallah da Farha masu shekaru hudu da kuma biyu.
…….
Wunin na yau baiyi mata dadi ba, gashi su Abdallah da zasu debe mata kewa suna gidan yayan babansu Baba Sani. Babu abinda yake damunta amma dai bata jin walwala, tunda sukayi sallama ya tafi Bichi take fargabar da bata san dalilinta ba. Haka har akayi sallar la’asar.
Tana zaune a falo ta kunna TV tana kallo; duk da hankalinta baya wajen; taji ana buga gate. Ta saka hijabinta ta nufi gate din, tana zuwa ta leka ta gefen gate din ta hango Baba Sani a tsaye rike da mukullin mota. Ta karasa da sauri ta bude gate din ta matsa don ya wuce
‘Sannu da zuwa Yaya, Bismillah.’
Ta fada tana kama hanyar cikin gidan da nufin ya biyota su karasa ciki. Ya ja ya tsaya a bakin gate, ganin haka itama ta juyo ta tsaya tana dubansa. Kafin tace wani abu yace
‘Ai ba ma sai na shiga ba, Umma ce dama tace na taho dake can gida yanzu.’
Gabanta ya fadi, dama tayi mamaki da ta ga Yaya shi kadai; musamman da yake su Abdallah suna gidansa.
Ta kalleshi ta dafe kirji ta fara Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun a ranta. Fata take Allah ya sa ba wani abu ne ya sami su Abdallah ba don watakila shi yasa gabanta yake faduwa tun safe. Ta kasa magana kallonsa kawai takeyi tana kokarin fassara damuwar dake kan fuskarsa, muryarsa ce ta katseta
‘Rufo gidan kawai ki zo muje, mu ake jira.’
Ya juya ya koma waje don ya jirata.
Da kyar ta ja kafa ta koma cikin gidan zuciyarta na faman bugawa da karfi kuma da gaggawa, dole ta sa hannunta ta dafe kirjinta.
‘Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.’
Ta fada a fili.
Mukullin gidan kawai ta dauko sai wayarta ta jefe a jaka ta fito ta shiga bayan motar Yaya Sani ya ja suka kama hanya ba tare da sunyi magana ba. Fata take Allah ya sa ba yarantane wani abu ya samesu ba don wannan shine karo na farko da suka taba zuwa gidan Baba Sani ba tare da ita ba kuma har aka barsu su kwana.
Suna shanyo kwanar gidan Umma ta hango mutane a tsaye cirko-cirko, ta dafe kirji cikin matsananciyar fargaba; tabbas ta san Abdallah ne ko Farha wani ya mutu; Allah ya sa ma ba su duka ne suka mutu ba.
Tuni hawaye ya wanke mata fuska yayinda ta balle murfin kofar motar ta fito ta nufi cikin gidan da sauri tana ketare mutane.
Babu wanda ya tare ta har ta kai tsakar gidan, kafin ta karasa kofar falon ta hango Umma a zaune a kan baranda ko shimfida babu. Mata ne a kewaye da Umman, duk da bata da natsuwar da zata tantancesu amma ta san duk kuka sukeyi. Da sauri ta karasa har tana cin tuntube, tan zuwa matan suka dan buda mata ta wuce har gaban Umman. Tana zuwa gaban Umma ta zube, Umma ta goge hawayen dake fuskarta ta kama hannunwanta duka biyun ta matse tana fadin
‘Hakuri zamuyi Aisha, haka Allah yake ikonsa.’
Tuni hawayen Aisha ya kara tsananta, ta kalli Bushra wadda take zaune a gefen Umma tana share hawaye suna hada ido Bushra ta kara rushewa da kuka tana fadin
‘Yaya ya tafi Anti Aisha! Yaya Mustafa ya tafi mutuwa tayi mana yankan kauna.’
Take Aisha ta daskare, hawayenta ya bushe ta bude baki tana zare ido; idan ta kalli Umma sai ta kalli Bushra. Ta bude bakinta cikin in-ina tace
‘Mustafa! Shi ai yana Bichi ko? Na zata Abdallah ne ko Farha, Abbansu ai yana gidan Baffa ko?’
Babu wanda ya amsata sai kukansu da ya kara tsananta. Cikin rawar jiki ta fara kokarin bude jakarta tana fadin
‘Bari na kirashi ai Bichi ya tafi dazu fa.’
Anti Rakiya kanwar Umman ita ta dafe hannun Aisha wanda take kokawar bude jaka da shi ta kalleta suka hada ido tace
‘Aisha hakuri zakiyi, Allah ya karbi rayuwar Abban Abdallah. Yana daf da shiga garin Bichi yayi hatsari a motar sai gawarsa aka kaiwa su Baffa.’
Ta fasa bude jakar ta bude baki tabi Rakiya da kallo yayinda bugun zuciyarta ya sake karuwa. Cikin rawar murya tace
‘Abban Abdallah ya rasu?’
Ta dafe kirjinta da hannuwanta yayinda numfashi ya fara yi mata nauyi. Bushra ta matso ta dafeta ta dubi Anti Rakiya tace
‘Anti Rakiya duba jakarta ki dauko inhaler dinta, kada asthma dinta ya tashi.’
Nan da nan Rakiya ta zazzage jakar sai dai babu inhaler a ciki, daga waya sai mukullin gida.
‘Babu fa inhaler a nan, babu ma komai a jakar daga waya sai key.’
Bushra ta mike ta dubi ta kusa da ita tace
‘Ku dafeta bari na fita don dole a samo inhaler.’
Tayi waje da sauri tana share hawaye, kafin ta kai farfajiyar gidan wajen rumfar motoci tuni numfashin Aisha ya fara sama. Tana dab da kaiwa gate Abba wanda shine dan autan gidan ya taso ya sha gabanta
‘Ya Bushra ina kuma za kije?’
‘Asthman Anti Aisha ne ya tashi gashi bata taho da magani ba ko inhaler.’
‘Subhanallah!’
Ya fada yana share kwalla, ya dubeta yace
‘Koma yanzu zan kawo in sha Allah. Ventolin ko?’
‘Eh, inhaler ko tabs duk wanda ka samo.’
Ya fice ya barta inda sauran ‘yan uwansu maza dake wajen har sun taso sun kewayeta tana musu bayani.
Ko minti goma Abban baiyi da fita ba ya dawo, ya samesu a tsakar gidan nan a kan baranda Aishan ta jingina da bango tana hawaye tana numfashi da kyar. Kafin ya karasa Anti Rakiya ta mike ta karbi ledar hannunsa, nan da nan ta balle kwalin inhaler din ta mikawa Bushra wadda ke kusa da Aishan. Haka aka dinga fesa mata inhaler din har numfashinta ya dawo dai-dai.
Can wajen karfe shida saura Baffa Tijjani wanda kanin mahaifinsu Mustafa ne ya shigo tsakar gidan ya sanar da su Umma zasu iya zuwa suga gawar Mustafa don an kawota daga Bichi har sunyi masa Sallah da yake a can din an riga an wanke shi anyi masa sutura.
Umma ta mike a hankali, itama Aisha ta mike yayinda su Bushra suka rufa musu baya. Falon baki wanda yake da kofa a bakin gate nan aka shimfeda gawar Mustafa, tsaf an yi masa sutura kuma da yake ba wani ciwo yaji ba fuskarsa tayi fes kamar ka kirawo sunansa ya amsa.
Umma ce ta fara isa kan gawar ta tsuguna, ta bishi da kallo tana fitar da hawaye yayinda Aisha ta zagaya ta daya bangaren ta tsuguna itama tana kallon fuskarsa wadda tayi kama da ta me bacci kuma yana murmushi a lokaci guda.
Umma ta daga hannu sama tayi masa addu’a na tsawon lokaci sannan ta mike cikin sauri ta fita daga falon tana share hawaye.
Aisha ta mika hannu ta shafa fuskarsa, ta bude baki a hankali tace
‘Mustafa.’
Babu amsa. Ta dan kara matsawa kusa tana shafa fuskarsa, kawai sai ta fada jikinsa ta rungumeshi tana rusa kuka. Duk mutanen da suke wajen saida sukayi mata kuka; tabbas mutuwa tayi musu gaggawa.
Shekaru biyar kacal da aurensu wanda aka yi shi cike da soyayya da kaunar juna yanzu gashi mutuwa ta raba su; tabbas dole a tausaya musu.
Sai da aka yi musu magana za a dauki gawar don a kai kafin magriba sannan aka kamo Aisha suka fito daga dakin; zuwa lokacin gaba daya gidan ya gama cika don har Maman Aisha wato Hajiya da yayarta Zuwaira duk sun iso.
Haka aka fita da gawar Mustafa zuciyoyi suna begensa, musamman Aisha wadda ta kasa gane yanda za ayi ta iya rayuwa a duniyarnan ba tare da Mustafa ba.
…….
Duk mutanen Bichi ma nan suka tare a gidan Umma ana zaman makoki; radadin mutuwar Mustafa ya taso musu da na mutuwar mahaifinsa wanda shekarunsa shida kenan da rasuwa.
Ranar da aka kwana uku ranar Baffa yace kowa ya tafi gida an gama zaman makoki, washegari aka mayar da Aisha gidanta inda a nan ne zata karasa takabarta.
Anti Uwani kanwar Hajiya itace wadda ta dawo gidan Aisha don ta tayasu zama ita da yaran zuwa lokacin da zata gama takaba; kullum sai an zo daga gidansu da kuma gidan Umma don a duba su ga kuma ‘yan uwa da abokan arziki da suke ta zuwa gaisuwa musamman da yake Mustafa mutum ne mai mutane ga kuma yawan kyauta.
_____
Satin da Aisha zata gama takaba aka raba gadon Mustafa. Gidan Umma suka hadu gaba daya har Baffa da wasu ‘yan uwan nasu na Bichi.
Abubuwa da yawa da ya mallaka Aisha ma bata san da su ba, Yaya Sani haka ya dinga lissafi yana cewa na Mustafa ne. Aka hada da gidajensa guda biyu ga motarsa ta hawa da makudan kudade a accounts dinsa da filayensa guda uku, kuma ga gidan gona wanda nasu ne su biyu shi da Yaya Sani.
Nan akayi lissafi aka fitarwa Umma nata sannan aka bawa Aisha nata da na yaranta; tayi zaton ma zasu ce a bawa Yaya Sani kason yaran ya ajiye musu amma taji Baffa yace duk a bata tunda ita din ma da iliminta kuma tana aikinta.
Aka bata zabi ko zata tafi da su Abdallah ko kuma a barsu wajen Yaya Sani, tace zata tafi da su.
Baffa ya sake yi musu nasiha suka yiwa Mustafa addu’a suka yi mata sallama suka tafi suka barsu ita da Hajiya da Zahida kanwarta da kuma da kuma Anti Uwani.
A ranar suka fara hada mata kayanta ita da yaran, gari yana wayewa suka tattara suka koma gidan Hajiya gaba daya.
Gidajen guda biyu da suka fado kasonta ita da yara ta sa Yayanta Abubakar ya sa mata ‘yan haya, ta ware kudi kuma ta bayar a samu wani waje da suke wahalar ruwa a Bichi a yi musu borehole Allah ya kaiwa Mustafa ladan. Musamman Baffa ya kirawota yayi mata godiya yayi ta saka mata albarka da Abba ya kai masa wannan labarin, haka itama Umma har gidansu ta zo tayi mata godiya kuma ta duba su Abdallah.
Haka suka cigaba da rayuwa a gidan Hajiya; kullum da safe Baba Abba zai zo ya daukesu ya kaisu makaranta idan an tashi kuma ya dawo da su.
……….
Yau satinsu biyu da komowa gidan Hajiya, bayan yara sun tafi makaranta Hajiya ta sami Aisha a dakinta wanda aka gyara mata bayan sun dawo. A kwance take a gefen gado bayan ta amsa sallamar Hajiya ta tashi ta zauna, Hajiya ta karasa ta zauna a gefen gado ta dubeta cike da kulawa tace
‘Aisha.’
Ta dago suka hada ido sannan ta sunkuyar da kai.
‘Yaushe zaki koma aiki? Kinga dai sati biyu kenan da fitarki daga takaba, ai ya kamata ki koma ko?’
Ta kawar da kai cike da damuwa
‘Hm! Wallahi Hajiya nima ban sani ba, aikin ma duk ya fice min daga rai wallahi.’
Ta share kwalla.
Hajiya ta gyara zama ta kama hannun Aishan tana kallon fuskarta
‘Zaki koma aiki gobe in sha Allah Aisha.’
Ta kalli Hajiya da mamakin jin maganarta ta zare hannunta daga na Hajiyan ta share kwalla, kafin tayi magana Hajiya ta cigaba
‘Tabbas mutuwar miji tana da ciwo tunda kafin naki mijin ya mutu nawa ya jima da mutuwa ya barni daku gamu Allah ya raya mu. Ki godewa Allah Aisha, domin dama Allah bai yi wa kowa alkawarin dauwama ba, mu din ma da muke raye lokaci muke jira. Ki cire komai daga ranki ki cigaba da rayuwarki; ko babu komai yaranki suna bukatar ki kuma walwalarki ce zata basu kwarin gwiwar cigaba da tasu rayuwar. Ki hakurkurtar da zuciyarki ki cigaba da rayuwarki Allah zai kawo miki mafita in sha Allah, ki cigaba da yiwa Mustafa addu’a Allah ya hadaku a Aljanna.’
Ta share hawaye tayi ajiyar zuciya, ta dubi Hajiya tace
‘Na kasa daina damuwa Hajiya, ki dinga yi min addu’a.’
‘Ina nan ina yi, kema kuma sai ki dage ki bawa kanki hakuri.’
Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan Aisha tace
‘In sha Allah gobe zan koma aikin Hajiya, shima yana son nayi aikin shi yasa ya samo min.’
Hajiya tayi murmushi ta dan kara bata hakuri sannan ta fita daga dakin ta barta tana tuno lokacin da ya samo mata aikin lokacin saura baifi wata hudu ba ya rasu ma ashe:
A kwance ya sameta a falo tana kallo, yaran duk sunyi bacci don har taran dare ta gota. Bayan tayi masa sannu da zuwa ya wuce daki ita kuma ta tashi ta jera masa abincin darensa a dining table. Ta bishi dakin suka fito tare, har ya zauna ya mike ya koma dakin ya dauko takardar ya fito ya sameta a zaune ya mika mata takardar sannan ya zauna ya fara cin abincin da ta zuba masa.
Karanta takardar takeyi tana murmushi, ta riga ta gaya masa bata son aiki amma shi ya dage tunda ta karanci education to ya kamata a samar mata koyarwa; ko babu komai ta sami abinda zata kula da kanta da shi. Ya kalleta bayan ya cinye lomar bakinsa yace
‘Sai ki bani tukwici Malama Aishatu ga offer nan kin zama malamar gwamnati.’
Ta kalleshi tana dariya tace
‘Gashi nan na baka tuwo harda nama. Allah dai ya bani ikon yin aikin nan don ka san ni da son jiki.’
‘Dagewa zakiyi fa, ki rike aikin nan kinga ko bayan raina kina da abinda zaki kula da kanki da yara kuma ko ina rayen ma bamu san abinda gaba zata haifar ba don haka aikin nan security ne a gare mu. Ki dage kawai Malama Shatun Musty.’
Wannan maganar tasa kwakwalwarta ta dinga maimaita mata tana share hawaye; gaban da yake nufi kenan ashe. Ai dole ma ta koma aikin nan, kuma in sha Allah goben zata koma.
UWAR SADIKU
WRITTEN BY
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
2
A hankali rayuwar Aisha ta fara dawowa dai-dai, sai dai kawai tana nan da tabon rashin Mustafa a zuciyarta. Ga yaranta suna walwalarsu amma duk lokacin da ta kallesu sai tayi kewar ubansu, musamman Abdallah da yake matukar kama da shi.
Gashi yanzu har an shekara da rasuwar Mustafa; duk abinda uba zai yiwa da ‘yan uwan Mustafa basu taba fasawa ba, kuma suna yawan zuwa duba su ko kuma su zo su kwashesu su yi musu kwana biyu.
Tuni an canza musu makaranta sun dawo kusa da gidan Hajiya amma Umma ta saka dole kullum sai Abba ya zo ya kaisu, in ya so sai Aisha ta dauko su.
………..
Suna zaune a falon Hajiya ita da su Abdallah da kuma Afnan ‘yar wajen Zuwaira sunata wasa, Afnan ce take bawa su Abdallah labari
‘Ni kullum Abbana ya dawo sai ya siyo min ayaba wataran ma harda apple.’
Farha tace
‘To muma dai kullum sai Mommy ta siyo mana duk abinda muke so, kuma Baba Abba yace mu Abbanmu ya tafi can yana Aljannah don ya gina mana gida kafin muje.’
Tace
‘Iyye, ‘yan gidan Aljannah.’
Abdallah ne ya tashi ya koma kusa da Aisha ya ya zauna a jikinta yace
‘Mama.'
Ta kalleshi cike da kulawa
‘Abdallan Mama.’
‘Da ma Abba ya jiramu ko? Ai da sai mu tafi aljannar tare, amma shi yayi wani sauri ya tafi.’
Tayi murmushi ta danne kwallar da ta taru a idonta
‘Watarana muma zamu je in sha Allah.’
Ya kwanta a jikinta yayi shiru, itama tayi shiru tana shafa kansa tana kuma kallon Farha wadda take wasa da Afnan.
Yaro ne ya shigo falon da sallamarsa, bayan ya gaida Aisha yace
‘Wani mutum ne yace na kirawoki Mama.’
Da mamaki ta kalleshi tace
‘Ni kaina Sule?’
‘E haka yace min.’
Ta bude baki zata sallameshi Hajiya ta fito daga daki inda take jiyosu tace
‘Tafi kace tana zuwa Sule.’
Nan da nan ya juya kamar wanda daman ya gaji da tsayuwar.
Hajiya ta karaso ta zauna a kan kujera kusa da Aisha, kafin ta zauna Aisha tace
‘Hajiya nifa ban ce kowa yazo ba kawai ki barshi yayi tafiyarsa.’
‘Ba zai yi tafiyar tasa ba, tashi zakiyi kije. Babu wanda zai yi miki auren dole ai sai an jira yardarki, idan kin saurari mutum ba shine yake nufin zaki aureshi ba. Ki godewa Allah a hakan ma, kuma ki tashi kije ki ga mai kiran naki.’
Kallon da Hajiyan takeyi mata ya tabbatar mata ba zata saurareta ba don haka ta mike ta shiga dakin ta sako hijabi ta zo ta wuce.
Hajiya ta bi bayanta da kallo tana jijjiga kai cike da tausayi; ta san dai Aisha so take tace ba zata sake aure ba, ita kuwa bata yi mata wannan fatan. Har yanzu da kuruciyarta domin shekarunta ashirin da biyar kachal, ba zai yiwu ba kuwa ace a barta babu aure. Addu’ar Hajiya daya Allah ya bata miji nagari wanda ma zai so ta fiye da yanda Mustafa yake sonta.
……..
Motar da ta gani a bakin gate din gidansu ta sakata mamaki.