Showing 66001 words to 69000 words out of 166068 words
mota biyu ma tayi zaton shi da Malam Sule ne suka dawo a lokaci guda. Sun gama magana da Abban yau Malam Sule zai bar aiki kuma bata so ya dameta da wata sallama don haka tayi zamanta a falo.
Basu gama gyarawa motocin tsayuwa ba Malam Sule shima ya iso, bayan ya gaida Abban ya mika masa mukulli yayi masa sallama a kan zasu hadu a office.
Malam Sule yana fita ya sallami daya yaron ya karbi mukullin motar.
A falon kasa ya sameta tana chatting a waya yayinda Sumayya take wasanninta a tsakar falon.
Bayan ya amsa sannu da zuwa ta ya mika mata mukullin motar yana fadin
‘Ga mota, Allah ya sa direban naki ya shirya ku fara fita gobe don na san kin matsu ki fara yawo a mota.’
Kafin ya rufe bakinsa tayi tsalle ta mike ta karbe mukullin dake hannunsa tana godiya. Ta fice ta barshi yana kokarin daukar Sumayya.
Tana hango motar jikinta yayi sanyi, taci birki kamar wadda aka tare. Ta sake karewa tsakar gidan kallo don ta tabbatar wannan itace kadai bakuwar mota.
Dukkan alamu sun nuna hakan ne; yanzu wannan ce motar da Abban Sadik zai bata don ta dinga tukawa? Ita da take son mota ta kece raini kamar ta Aisha ko kuma wadda tafi ta Aisha amma ya siyo mata wannan? Ta matsa kusa ta karewa motar kallo, Honda Civic ce kirar 2009, ba wai muni tayi ba ko tsufa da yawa don fes take amma dai tana ga babu girma ace ta hau wannan Aisha kuma ta hau dalleliyar Honda Accord kirar 2013. Ko babu komai yanzu a 2018 ake, ina ma laifi ya bata koda accord din ce itana kuma ta 2013 misali.
Ta juya ta kalli kofar falon ko zata ga ya biyota amma sai ta ga babu kowa, tayi kwafa a fili tace
‘Haba ai da kunya ma ya bani wannan yace ya bani mota.’
Ta wuce cikin gidan ta tafi nemansa.
A daki ta sameshi ya ajiye Sumayya a kan gado yana kokarin cire kaya, bayan ya amsa sallamarta tace
‘Naga motar, nagode Allah ya kara budi. Ni da na sa rai da wata dankareriyar mota, wannan ma ai ta Malam Sule ta fita kyan gani.’
‘To sai ki ajiyeta ki dauki ta Malam Sule, wannan din sai a dinga kai yara makaranta ko?’
So take tace motar bata ma kai ta Aisha ba amma bata son janyo matsala; 'yan kwanakin nan duk lokacin da tayi maganar Aisha to fa sai ta kwana biyu bata gane kansa ba, haka zai yi ta kunci yana muzurai. Don haka ta ja bakinta tayi shiru.
……….
Tana zaune a falon kasa yara suka dawo daga islamiyya, bayan sun yi mata sannu da gida Yusra tace
‘Mommy naga wata mota a waje.’
Ta tabe baki ta kawar da kai
‘Wai ita Abbanku ya siyo min.’
Ta dan zaro ido
‘Mommy gaskiya Abba ya raina ki wallahi, wannan motar fa ina jin '98 ce ko rabin kyan ta amaryarsa bata kai ba. Ya za ayi ace tana hawa wannan motar ke kuma kina hawa wannan. Shima dai Abba!’
Kafin ta rufe baki Rukayya ta karasa kusa da Mommy ta dafata tana fadin
‘Congrats Mommy! Wataran muma kya dinga zuwa daukarmu a makaranta ko na cewa kawayena Mommy ta zo yanda suke min. Bari naje na kara kallonta, wallahi Mommy ta min kyau ina son mota kalar silver.’
Kafin Mommy tace wani abu tayi waje da gudu, Ummi ta rufa mata baya sunata murna Mommy zata dinga kaisu school.
Yusra tayi tsaki tace
‘Ji ‘yar kauye Mommy.’
Ta tabe baki kawai ta kawar da kai, Yusra ta cigaba
‘Mommy ya fa kamata ma ki hannan wannan tayin kwanan da Rukayya take zuwa, ace kullum mutum yana faman yawo wajen kwana. Kawai kowa tashi ta fissheshi.’
Sai yanzu tunanin ya fado mata, don da tayi wannan tunanin da tuni ta hana tunda yanzu duk abinda ta fada shi Abban yakeyi.
Jimawa kadan Yusran ta sake cewa
‘Mommy kika ce Malam Sule ya bar aiki, yaushe za a kawo Sabon direba?’
Ya ma zo dazu kun tahfiz, gobe shi zai zo ya kai ku makaranta. Sunansa Balele, sai goben za ki ganshi.
………..
Yana zaune a a falo shi da yaran gaba daya bayan sallar isha’i. Yusra tana zaune a dining table tana karatu su kuma Ummi da Nana suna zaune yana yi musu homework.
Rukayya ce ta fito daga daki dauke da jakar makarantarta, ta wuce kicin inda ta jiyo motsin Mommy. Bayan tayi mata sannu da aiki tace
‘Mommy sai da safe.’
Tana shirin juyawa tace
‘Ke na gaji da wannan tayin kwanan, koma ki ajiye jakarnan an gama daga yau. Ai naga itama a danginsu tana da ‘yaya don haka ta dauko mai tayata.’
Ta sunkuyar da kanta saboda damuwa, sai dai ta san babu yanda zatayi don haka ta ja kafa ta fice daga kicin din.
Daga inda yake zaune yana jiyo abinda take fada don da karfi tayi maganar, ba zai iya hanata ba don haka ya tashi ya tsallake yaran ya haye sama.
Bayan ta fito ta dubi Nana tace
‘Ina Abban kuma?’
‘Ya tafi sama, yace ki karasa mana homework din ko ke ko Yaya Rukayya.’
Tayi murmushi ta janyo littafin Ummi; ta san ya jiyo abinda ta fada ne kuma babu yanda zai yi da ita.
………
Bai iya yiwa Aisha waya ba sai dai text kawai yayi mata ya sanar da ita ta rufe kofa don Rukayya bazata zo ba yau.
Batayi mamaki ba don tuntuni take tsammanin hakan; ita din ma hakan ya fi mata nutsuwa don gani take kamar za a iya amfani da Rukayyan a cuceta. Don haka nan take ta tashi ta rufe gidan tayi kwanciyarta; ta bari sai nan da sati daya sai ta dauko Amira ta cigaba da tayata kwanan suga abinda hali zaiyi.
--------
Kamar yanda Yaya Zuwaira tayi alkawarin zata nemi shawara a wajen malamai hakan kuwa tayi. Ta sami Malama Halima wadda bayan ta ji duk wani bayani ta ja ta suka sami Malam Muhammad.
Yayi musu bayani sosai, ya tabbatar musu tsafi ne tunda daga karshe Aishan tace Abban yace kamar daga jikinta yake jin warin. Sai dai ya tabbatar musu idan aka cigaba da addu’a abun zai karye. Ya tunasar da ita azkar sannan kuma ya tuna mata addu’oin karya sihiri, ya sanar da ita ta dinga karanta surarul baqara kullum dare a gidan kuma ta dinga yawan sadaka da sallar dare.
Ya sanar dasu kada suce zasu rabata da shi domin don haka akayi wannan asirin, idan suka bari aka cigaba da addu’a komai zai wuce.
Tun da Zuwaira ta sanar da ita ta mayarwa kanta ka’ida kullum kafin ta kwanta bacci sai ta karanta suratul baqara, idan kuma ta kwanta karfe biyu da rabi na dare tana yi zata tashi tayi sallar dare sannan ta koma bacci.
…………
Ko da aka hana Rukayya zuwa sai tashi ya dan fara yi mata wahala kasancewar dama cikin da yake jikinta yana sakata bacci sosai sannan kuma idan ta tashi kasancewar ita kadai ce a gidan bata jin dadi sosai. Idan tana jin motsin Rukayya tafi natsuwa, ta dai tabbatarwa kanta lallai gobe zata dauko Amira tunda ma an gama jarrabawa hutun makaranta za ayi.
Yau ma kamar kullum karfe biyu da rabi na dare alarm din wayarta ya fara waka, ta lalubi wayar ta kashe alarm din sai dai ta kasa tashi. Wajen karfe uku saura kwata alarm din ya kara daukan kara; ta daure dai ta mike zaune bayan ta katse alrma din. Ta kunna fitlar wayarta ta ajiye a kan durowar gefen gadon saboda babu wuta a lokacin. Ta zauna tana hamma tana muttsike idanu tana kokarin ta wattsake ta tashi tayi sallah.
Haka kawai sai taji tsoro ya shiga ranta, nan take baccin ya bar kanta. Ta karewa dakin kallo duk da dai babu wuta amma tana iya ganin komai dake ciki dakin saboda fitilar wayarta da take kunne. A hankali sai ta fara jin kamar ba ita kadai ce a dakin ba, sai taji kamar akwai motsin mutum a dakin kuma motsin ma a nan kusa da ita inda take zaune a gefen gado. Ta duba har tana shafa gadon ta tabbatar babu kowa amma kuma kamar tana jin alamar da wani a kusa da ita.
Ta kasa tashi ta bar wajen kuma ta kasa aikata komai, har jikinta ya fara rawa a hankali saboda tsoro.
Ta dan muskuta kadan ta janyo abun rufar da ta rufe kafafunta da shi ta rufe kirjinta da shi ta kankame jiki.
Motsi ta sake ji kamar an tsallake kafafunta sai dai bata ga wanda ya tsallake din ba, kafin tayi wani abu taji kamar an cafke cibiyarta wanda ya sa mararta tayi wani irin suka gumi ya karyo mata. Ko minti daya ba ayi ba taji an finciki cibiyarta kwatankwacin yanda ake balle murfin kwalabar lemo; da hanzari ta kai hannu ta dafe cibiyarta tana fadin
‘La ilaha illallah, wayyo!’
Gumi ya cigaba da karyo mata saboda yanda mararta take kara kartawa da ciwo. Ta dan muskuta ta gyara zama ta cigaba da ambaton
‘hasbunallahu wa ni’imal wakil’.
A hankali ta dan fara samun natsuwa, dakin ya dawo dai-dai sai dai mararta da bata daina murdawa ba.
Ta tuna sallar dare ma ta tashi yi don haka a hankali ta zuro kafafunta daga kan gadon don taje bandaki tayiwo alwala.
Yanda taji danshi a jikinta ta tabbatar fitsari tayi ko kuma jini ne yake binta, cikin hanzari ta karasa bandaki. Tana kwabe kayanta taga jini ne yake binta gashi mararta tana kara kartawa. Da kyar ta daure ta wanke jikinta sannan ta lallabo ta dawo dakin ta kwanta. Ta duba wayar tata taga karfe uku da minti biyar na dare, ta gyara kwanciyarta ta kashe fitilar wayar don yanzu babu wanda zata iya tashi daga barci.
Haka ta kwanta tanata juyi tana ambaton Allah ga mararta tana ciwo har akayi kiran asuba. Ta lallaba ta hada ruwan zafi tayi wanka sannan ta hada shayi. Ta dawo ta zauna a kan dining table ta saka kofin shayin a gaba tana kallonsa; karo na biyu kenan tana barar da ciki a gidan nan, to me yake faruwa? Ta san dai bawa baya wuce kaddararsa amma abun ya fara bata tsoro musamman na jiya da daddare da yayi kama da zuwa akayi musamman aka cire cikin aka tafi.
Kusan shekaru hudu kenan da aurensu amma bazata iya cewa sunyi wata shida cikin nutsuwa ba, fitna daga wannan sai wannan.
Yanzu gashi sati wajen uku kenan an shiga na hudu rabon da Yusuf yazo inda take, sai dai kawai waya. Wayar ma yanzu ba kullum yake kira ba.
Saida shayin nan ya fara hucewa sannan ta dauka ta sha. Ta sami Panadol ta sha saboda yanda mararta take ciwo sannan ta koma ta kwanta a kan doguwar kujera.
Sai wajen bakwai da rabi na safe sannan ta kirawo Yaya Zuwaira ta sanar da ita halin da take ciki, wajen takwas da rabi ta iso gidan suka kama hanyar asibiti.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
24
Suna zuwa asibiti suka wuce emergency, nan take likita yace suyi scanning. Bayan sun kawo sakamakon likita yayi musu bayani cewa cikin ya fita amma za a yi mata wankin ciki. A nan suka sami waje Zuwaira tace Aishan ta zauna zata je ta biya kudin ta dawo.
Bayan ta dawo kafin su koma waje likita ta dubeta tace
‘Wai kin gaya masa kuwa?’
Ta kau da kai
‘To me zan ce masa baya iya zuwa kusa dani, ni ban gaya masa ba.’
‘To bari na dawo sai na gaya masa, ai gara ya sani ko don ya san cikin jikinki ya bare.’
Ta wuce ta barta a nan.
Bayan ta biya ta dawo aka shiga da Aisha dakin wankin cikin, ita kuma Zuwaira ta zauna tana jiransu.
---------
Yana hanyar tafiya office wayarsa tayi kara, yana dubawa yaga Zuwaira. Da rawar jiki ya dauki wayar wanda shi kansa bai san dalilin hakan ba. Bayan sun gaisa ta sanar da shi Aisha tayi bari suna Asibitin Nassarawa.
Nan take ya juya kan motar ya kama hanyar asibitin.
Yana shiga asibitin yayi tambaya aka nuna masa inda suke, kai tsaye ya wuce.
Kafin ya karasa wajen ya hango Zuwaira a zaune a kan kujera tana jira a fito da Aisha daga wankin cikin.
Yana dab da karasawa nurse ta bude kofar dakin wankin cikin Aisha ta fito, nurse din tana mata sannu tana kokarin dafa ta. Zuwaira ta mike da hanzari ta nufota daidai lokacin da Abban ya karaso kusa da ita.
‘Aisha.’
Ya kirawo sunanta, ta kalleshi suka hada ido.
Ta dauke kanta tana kokarin mikewa sosai saboda yanda take jin jikinta babu kwari.
Kafin ta karasa mikewa ya tareta, gaba daya ya rungumeta yana mayar da numfashi. Suka dauki kamar minti daya bashi da niyyar sakinta. Yaya Zuwaira tana tsaye tana kallon ikon Allah ita kuwa nurse tuni ta wuce ta basu waje.
Bashi da niyyar sakinta don haka ta dan fara mutsu-mutsu tana son ta zare jikinta.
‘Akwai mutane fa.’
Ta rada masa.
Ya saketa, sai dai yana rike da hannunta yana kallon fuskarta. Cikin damuwa da tausayawa yace
‘Sannu.’
Ta daga masa kai.
Suka karasa suka zauna a kan kujera suna jiran a rubuta mata sallama.
Tana ta faman gyara zama don haka ya matsa ya janyota jikinsa ta kwanta.
Suna nan zaune likita ya fito daga dakin wankin cikin ya shige ofishinsa. Zuwaira ce ta mike ta bishi don shi baya jin zai iya barin Aisha a nan ita kadai ba.
Jimawa kadan Zuwaira ta fito rike da takardu, ta mikawa Abban takardun tace
‘Ga wanna magunguna aka rubuta, likitan yace zamu iya tafiya. Idan taci abinci ta huta zata ji kwari a jikinta, idan akwai wata matsala yace sai a dawo.’
Duk da tace masa zata iya tashi amma sai da ya riketa ya kamata sannan ta tashi, yana rike da ita har suka zo wajen motarsa. Sai da ya kwantar da kujerar gaban motarsa sannan ya sa Aisha ta dan kashingida. Ya rufe kofar motar ya matso kusa da Zuwaira wadda take tsaye jikin motar da direbanta ya kawota. Yace
‘Ina ga mu tafi a motata, in ya so sai direban ya sameki a can ko.’
Saboda haka gaba daya suka shiga motar Abban suka nufi gidan Aisha.
Sai da ya tsaya a super market ya siyowa Aisha kaji da yoghurt mai sanyi kuma ya hada da apple ya zuba a mota sannan suka wuce gidan.
A bakin gate yayi parking, kafin ya zagayo ya budewa Aisha kofa ta bude ta fito. Ya fito da ledojin da yayi sayayya ya mikawa Zuwaira yana fadin
‘Bari na rakaku ciki sai na fito na wuce office don ko isa ban yi ba na sami kiranki.’
Yana rike da Aishan suka nufo gidan, tunda ya bude gate din ya sako kafarsa cikin gidan ya fara jin wannan warin da yake firgita shi. Daga hannunsa da take rike da shi ta fuskanci abinda yake faruwa da shi, tana kokarin duba fuskarsa ya zare hannun nasa daga cikin nata.
Suna daf da taka barandar falon ya ja baya, yana juyowa ya fuskanci Zuwaira wadda take biye da su a baya wadda itama sauyawar da fuskarshi tayi yayi matukar bata mamaki. Kafin tace wani abu yace
‘Yauwa ku shiga, bari nayi sauri naje sai na dawo.’
Bata yi tsammanin ya ji a dawo lafiyar da takeyi masa ba don kamar a guje ya fice har yana yin tuntube.
Suka kalli juna ita da Aisha, ta matsa kusa da Aishan tana mamaki. Aisha tayi murmushi tace
‘Kin gani ko? Wallahi da ya shigo yake rudewa haka.’
Suka karasa cikin gidan.
Kafin wani lokaci Zuwaira ta gyarata ta hada mata abinci, bayan taci abinci ta sha magani ta kwanta a dakin baki sai bacci.
Kafin azahar dangi duk sun hadu a gidan don wannan karon Hajiya ma cewa tayi sai ta zo, don haka gaba daya suka taho da yaran da Anti Uwani. Sai da yamma suka tafi suka barta da Amira bayan da suka tabbatar ta wattsake.
-------
Kafin ya fita daga gidan har kansa ya fara sarawa, yana fita daga gate din ya kama hanyar ya nufi gidan Zahra.
Sai da ya kusa zuwa gate sannan ya kalli hannunsa ya ga mukullin motarsa, a take ya tuna da motarsa kuma ya tuna office ya kamata ya tafi.
A hankali ya janyo kafarsa ya dawo ya shiga motarsa ya kama hanyar office. Zuciyarsa tana begen Aisha amma ya kasa shiga inda take. Ya tuno kamar dai lokacin da suna asibiti bai ji wani wari ba, shi ya manta ma da wannan matsalar gaba daya.
Abun yana ransa kullum yana cewa zai nemi taimako ko addu’a a yi masa amma sai ya dinga mantawa, wasu lokutan ma yana rasa abinda ya sa baya magana a kan matsalar nan. Sau biyu yana zuwa gidan Yaya Bello don ya sanar da shi matsalar amma idan yaje sai suyita wasu hirarrakin gaba daya ma ya manta da abinda ya kaishi.
Yana tukin ma abinda yake ransa shine ya wuce wajen wani malami da ya sani mai Islamic chemist yaji ko zai sami wani taimako. Kafin ya gama tsara abinda zai gayawa Malam din kawai ya tsinci kansa a farfajiyar office anata faman yi masa sannu da zuwa.
Haka ya hakura ya shiga office din da niyyar idan ya tashi daga aiki ya biya ta wajen Malam din.
__
Tun ranar da Balele ya fara zuwa aiki suka fara fita da Zahra, da yake ta maida hankali kuma hawa motar tana ranta kafin sati hannunta ya fada. Tunda kuwa taga ta fara iya fita ita kadai ta bawa Balele tata motar ta karbi Fijo din da Malam Sule ya bar masa, don tana ganin ko Yaya dai wannan din