Showing 111001 words to 114000 words out of 166068 words
bai dawo ba kuma da ya zo nan shekaranjiya bana nan, amma idan bai zo ba zan kirawoshi kafin mu tafi.’
Tayi gyaran murya tace
‘Uhm! To ai munyi magana ba zaki koma gidan Yusufa ba tunda ko kin koma dake da wadda bata da miji duk daya kuke. Ki zauna a nan, ba zamu kashe miki aure ba, duk lokacin da ya dawo hayyacinsa sai ya zo ya daukeki ku koma.’
Tuni idonta ya cicciko da kwalla tace
‘Hajiya don….’
‘Ba shawara na zauna yi dake ba, idan ke baki san ciwon kanki ba mu muna kishinki. Na gama magana babu inda zaki koma har sai Yusufa ya zo nan da kanshi sai ku tafi.’
Da kyar ta bude bakinta tace
‘To.’
Ta tashi jikihta babu kwari ta koma cikin gidan, kai tsaye dakin Anti Uwani ta wuce ta fada kan gado ta sa kuka.
Tana shigewa Anti Uwani ta dubi Hajiya tace
‘Yaya don Allah ku bar maganar nan, ku bar yarinyar nan ta koma gidanta tunda ita ta ji ta gani. Idan tana can ma sai tafi dagewa da addu’a amma yanzu idan an rike ta a nan ba zata nutsu ba tunda ta fi son can din. Idan babu hali ma ni sai na koma can na dinga tayata zaman zuwa lokacin da komai zai warware.’
‘Uwani ki kyaleta, ai ba sallamarta mukayi ba kawai don mun mata aure.’
‘Ni dai Yaya gaskiya ki barta ta koma, shima Abubakar din zai zo ya same ni.’
Bata saurari Hajiyan ba ta tashi ta bi bayan Aishan.
Kai tsaye dakinta ta wuce don ta san a nan ne zata sameta. Ta zauna a gefen gadon ta dafa bayan Aishan tace
‘Yi hakuri Shatu, Abubakar din zai zo ya same ni. Wannan abun ba komai bane face jarrabawa kuma da izinin Allah zai wuce, mu da muka je har kasa mai tsarki muka roki Allah a kan wannan lamarin ai ya kamata a ce mu barki ki zauna a dakinki zuwa lokacin da komai zai warware.’
Ta share kwallarta da zanin gadon ta mayar da kanta ta kwantar a kan cinyar Anti Uwani sannan tace
‘Gara na zauna a can ni dai, kuma ina ji a jikina wannan matsalar ta kusa zuwa karshe in Sha Allah. Kuma Anti Uwani ita matarsa so take na bar gidan kin ga yanzu idan ta bude ido taga bana nan ai ta ci nasara ko?’
‘Kada ki damu ki cigaba da shiri in Sha Allahu don ranar Juma’ar zaki koma, idan ma sun ki saurarata har gidan baffanki zan je na kirawoshi ya mayar dake don na san ba zai goyi bayan wannan aika-aikar ba.’
Haka ta dauki lokaci tana lallashinta.
………..
Washegari da yamma suna zaune sai ga Baffa, Suhail ne babban yaronsa ya kawo shi saboda shi tun tuni ya hakura da tuki saboda baya gani sosai daga nesa, don haka idan zai fita sai ya jira yara.
Bayan sun gaisa da Hajiya da Anti Uwani yace
‘Kwana biyu, kin san idona ya ki ina ta so nazo na ganku to yara duk kowa ya bazama nema babu lokaci.’
Tace
‘Babu komai Baffa, ai dama komai lokacine. Allah ya kara lafiya ya ja kwana.’
‘Amin ya Allah.’
Suna nan zaune suna hirarrakinsu Aisha da su Abdallah suka shigo, sun dawo daga gidan Anti Zainab.
Bayan ta gaida Baffa yace
‘Yanzu kika zo Shatu da magaribar nan, ba kya gudun kiyi dare a hanya? Ya maigidan naki? Ina fatan dai komai ya warware.’
Ta sunkuyar da kai tace
‘Lafiya kalau.’
Anti Uwani tace
‘Ai tunda muka dawo daga Umra dama bata tafi ba.’
‘Garin yaya? Ina fatan dai ba matsalar nan ce ba.’
Hajiya tace
‘Itace dai har yanzu babu wani cigaba, don shi yasa ma nace ta zauna a nan idan ya dawo hayyacinsa ya zo su tafi.’
Da mamaki Baffa yace
‘Ikon Allah! Ko da yake malamin da na sa yake addu’a ya gaya min abun zai iya daukar lokaci amma komai daren dadewa zai yi karshe.’
Ya kalli Aishan yace
‘Shatu da kinyi hakuri kinyi zamanki a can tunda ance min an baki mai tayaki kwana, jarrabawa ce ta ubangiji kuma idan kina can din ai sai abun ya fi saurin warwarewa.’
Ta sunkuyar da kai, Anti Uwani tace
‘To ai Yayan ce ta hanata komawa ita da Abubakar, amma ita ai tana son ta koma gidanta kuma nima na goyi da bayan hakan an dai fi karfinmu ne kawai.’
Baffa ya kalli Hajiya yace
‘Gaskiya a barta ta koma Hajiya, ai hakuri akeyi. Kuma wannan abun in Sha Allah zai warware in Sha Allah.’
Ya kalli Aisha yace
‘Ki koma Shatu kiyi zamanki, sai dai idan shine yace ki tafi to tabbas muma ba zamu barki ki zauna ba. Amma yanzu hakuri zakiyi ki zauna gaba daya mu cigaba da addu’a.’
Anti Uwani tace
‘Dama gobe tace zata koma, tunda an yi haka in Sha Allahu goben sai muje na rakasu ita da Amiran.’
Baffa ya dubi Hajiya yace
‘Ayi hakuri Hajiya in Sha Allah komai zai wuce.’
‘Um,shikenan Baffa. Dama gani nayi tana can tana zama kamar me zaman kanta shi yasa nace ta dawo gida, amma in Sha Allah goben zata koma.’
‘Yauwa.’
Aishan ta tashi ta wuce daki inda su Abdallah suke can suna wasansu.
Hajiya da Anti Uwani kuma da Baffa suka karasa hirarrakinsu, sai dab da magriba Baffa yayi musu sallama ya tafi.
Yana fita Hajiya ta dubi Anti Uwani tace
‘Kun sami yanda kuke so ai sai kije ku fara shiri ke da ‘yar taki ko?’
Ta mike tana dariya tace
‘Eh, bari muje mu hada kayanmu ai zaman aure ba wasa bane kuma kowa da jarrabawarsa.’
Ta wuce daki tana dariya.
Cikin daren nan Anti Uwani ta taya Aisha suka hada kayanta. Washe gari Juma’a wajen karfe goma suka kama hanya tare da Anti Uwanin suka tsaya suka dauki Amira sannan suka wuce.
Sai da suka gama gyara gidan tsaf sannan Anti Uwani ta hau mota ta koma gidan Hajiya, ta bar Aisha da Amira.
Gaba daya Aisha ta manta basu siyo burodin karin kumallo ba gashi kuma basu da indomie a gidan. Don haka da safe wajen karfe takwas da rabi Aisha ta bawa Amira kudi ta siyo musu burodi da kwai su karya.
Tana fitowa daga gate din gidan su kuma su Yusra sun fito daga gidansu zasu tafi tahfiz don ranar aka koma hutu. Yusra ta balla mata harara, ita kuwa tayi dariya ta dagowa Rukayya hannu wadda ta mayar mata da murmushi ta daga mata hannu itama. Ta wuce ta barsu a nan Yusra tana ta faman hararar Rukayya.
--------
Tun bayan da ta haifi Sumayya bata sake yin wani tsarin iyali ba, ba wai ta damu da haihuwar bane amma tabbas a halin yanzu idan ta zo ba zata Hana ba. Duk da har yanzu Aisha bata haihu ba amma dai tana so ta haifi da namiji sannan Kuma tana so ta cika gidan da ‘yaya.
Tun cikin azumi take jin jikinta babu dadi, lokacin da ya kamata tayi al’ada har ya wuce bata sha azumi ko daya ba don haka zuwa yanzu tana da yakinin ciki ne da ita. Lafiya kalau take daukar ciki ta haihu don haka ta yanke shawarar ba zata je asibiti ba har sai cikin yayi wata hudu, zuwa lokacin idan aka yi scanning za a iya gaya mata mace ne ko namiji.
Tun kafin yaran su tafi tahfiz Jummai ta zo, don haka suma tafiya ta sallami Jummai da ayyukan da zata yi mata ta haye sama ta kwanta a dakinta. Bata Dade da kwanciya ba Shima Abban yayi mata sallama ya wuce gidan Hajiya.
Yana fita bacci ya kwasheta.
Bata farka daga wannan baccin ba sai wajen Sha biyu da kwata lokacin da yara suka dawo daga tahfiz wanda shigar Sumayya da Ummi dakin shine ya farkar da ita. Bayan sun gama yi mata sannu da gida tace su sauko wajen Jummai su ci abinci sannan su kunna TV suyi kallo. Suna fita daga dakin ragowar yaran ma suka shigo sukayi mata sannu da gida sannan suka fice
Yusra ce ta karshen shigowa ta sami waje a gefen gadon ta zauna, ta dubi Mommy din wadda har yanzu take kwance tace
‘Mommy kika ce matar Abba ta tafi?’
Cikin halin ko in kula tace
‘Eh, tun cikin azumi ma kuwa.’
‘To gaskiya Mommy ko dai bata tafi ba ko kuma ta dawo don gaskiya yau na wannan mara kunyar ‘yar tata ta fito daga gidan, don har hannu ma ta dagowa Rukayya.’
Ta tashi zaune ta kalli Yusra yayinda mamaki ya bayyana a fuskarta
‘Ikon Allah, to dama tana nan ko kuwa dawowa tayi?’
‘Ina ga dai Mommy azumi taje tayi a gida shine ta dawo.’
Ta jijjiga kai
‘Um! To shikenan idan kin sake ganin motsi a gidan kiyi min magana.’
Ta amsa sannan ta tashi ta fice daga dakin.
Duk da Yusra ta san cewa uwarta tana bin malamai amma bata san itace tayi abinda Abba ya daina kula Aisha ba, ba wai ta dauka bin malaman kuskure bane. Hasali ma a wajenta shine dai-dai tunda Mommy tace tsari ne ake nema musu. Lokacin da taga Abba ya daina kula Aisha tayi zaton asirin da Mommy tace musu ta yiwa Abban ne ya karye shi yasa ya manta da ita, don haka yanzu da ta ganta tsoro take ji kada ta sake yiwa Abbansu wani asirin duk da ta san Mommy a tsaye take a kansu.
Yusra tana fita daga dakin ta gyara zama ta kafa tagumi; Aishan nan wai me take nufi ne? Kusan shekara guda miji baya zuwa inda kike amma kin ki fita daga rayuwarsa? Wannan din wanne irin naci ne? Gashi zuwa yanzu matan unguwar da take harka da su sun fara tambayarta labarin Aisha a kan sunji a unguwa cewa auren Aishan ya mutu; duk da dai ta gaya musu itama bata san me ake ciki ba domin da ta tambaya ma Abban yace kada ta sake yi masa maganar.
Tabbas dole ta koma Doguwa; tunda dama akwai maganar Yaya Bello da take so a rabashi da Abban. Dama azumi ne ya hanata zuwa da aka sallace kuma bata da aiki sai bacci saboda cikin da take dauke da shi; ko da yake lokaci zata saka taje gidan Amina su tsara yanda za ayi don watakila ma Aminan zata iya zuwa mata Doguwan.
Haka ta karasa wunin ranar tana tunanin mafita.
--------
Ita kuwa Aisha tunda ta dawo gidanta sai ta sake mayar da hankali wajen addu’a, ranakun aiki taje aiki ta dawo ranakun Asabar da Lahadi kuma sai taje islamiyya. Rashin kulata da Abban yakeyi yana damunta sai dai da yake dinkin mayafai da takeyi yana rage mata zama haka nan sai abun yayi mata sauki;kuma ta samu ana sayen mayafan sosai don haka kusan kullam cikin aiki take Amira tana tayata.
---------
Ranar Alhamis ce don haka yara babu islamiyya da yamma, tun safe ta gayawa Saddiku kada ya fitar mata da mota don zata fita da yamma amma ga mamakinta sai da ya fita; koda yake yanzu ta kula ko sauraron maganarta baya yi, yanda yayi niyya haka yake aikatawa. Malam Ali yana kawo yara daga makaranta tace ya tsaya zai kaita unguwa don haka nan ya zauna ya jirata.
Saida ta gama abinda takeyi tayi sallar la’asar sannan ta fito suka kama hanyar gidan Amina.
Duk da gidan Amina bai kai girman na Zahra ba amma shima ya tsaru, domin maigidanta ma ya fi Abba Saddiku dukiya. Cikin walwala ta sauketa ta ajiye mata lemo da cake sannan suka gaisa.
Bayan sun gaisa Aminan ta dubi Zahra wadda damuwa ta bayyana a fuskarta tace
‘Ya na ganki duk kinyi yaushi ne kawata, meye labari?’
Ta tabe baki ta kawar da kai
‘Mtseww, wallahi kin san na ce miki Aisha ta tafi gidansu ko?’
‘Eh kwarai kuwa.'
‘To wallahi yarinyar nan ta tattaro kayanta ta dawo.’
Ta rike haba tana mamaki
‘Ikon Allah, to amma dai Abban bai ce komai ba ko?’
‘Bai ma san da ita ba komai normal, kawai dai bana son zamanta a gidan ne. Nifa na fi so ace babu igiyar aurenta a wuyansa shine kawai zan huta.’
Ta dafa cinyarta
‘Ki daina damuwa, ki bawa banza ajiyarta kawai tunda dai maigidan yana hannunki. Kuma na gaya miki aikin bokan nan ba zata iya karyashi ba ko waye malaminta a garin nan.’
‘Hmm! Kin san kuma da maganar Yayansa da nace miki yana mun shisshigi, duk da dai na sa Yaron Malam yayi min aiki amma dai naga alama aikinsa bai yi ba. Ni wallahi Doguwan ma nake son zuwa don dai kawai cikin da yake jikina ne ya sa bana son zuwa.’
Ta dan zaro ido
‘Ciki uwar Saddiku? Lallai matar nan himmarki tana da yawa.’
‘To na sani ko shine namijin da nake ta nema, ai kin ga dole na tattala.’
Ta mika mata hannu suka tafa
‘Da kyau kawata. Nima wallahi ina son zuwa Doguwa saboda mijin Asiya, ya fara kawo mata wargi gara na nema mata taimako. To amma gaskiya sai an dan kara kwana biyu, in kina so idan na shirya sai muje ko kuma na tafi da sakonki mu gani ko zai karba. Sai dai shi kinsan fa baya aiki da sako sai dai kai da kake da bukata kaje da kanka, kuma gaskiya ba zan baki shawarar zuwa wajen nan da ciki ba.’
Ta dan yi tsaki
‘Wallahi nima abinda nake ji kenan, to amma bari mu gani a kwana biyu tunda ma yanzu babu wata major matsala.’
‘Gaskiya dai. Idan kuma wani abun ya taso ai sai kiyi maleji da Yaron Malam tunda shi ko ta waya zaku gama komai.’
Suka karasa hirarrakinsu sai gefin magriba sukayi sallama Zahra ta shiga mota Malam Ali wanda yake jiranta ya mayar da ita gida.
Haka ta hakura ta cigaba da rainon cikinta tana fatan ya zama namiji; tunda ko babu komai yanda bokan nan yayi mata alkawarin babu wanda yake maganar Aisha. Domin har dangin Abba ma babu wanda yake maganarta kamar ma babu ita, kuma tana da yakinin kwanan nan kudin hayar gidan zai kare ta san dole Aisha ta tashi tunda babu mai biya mata.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
35
Duk yanda Aisha ta kai ga son boye damuwarta game da rashin ganin mijinta abun yana mata wahala; lokuta da dama ta kan kwana tana kuka. Wasu lokutan kuma idan ta yi sujuda da nufin ta roki Allah sai kuka yaci karfinta, haka zatayi mai isarta sannan ta dago daga sujudar. Tana zuwa aiki da islamiyya ga kuma cinikin mayafanta amma duk wannan bai isa ya debe mata kewar mijinta ba.
Yau din ma haka ta tashi cikin yanayi na damuwa, gashi ranar hutu ce don haka babu aiki kuma gashi da wuri Amira ta fita saboda ana bikin babbar kawarta; don haka ita kadai ce a gidan.
Duk yanda ta so ta kawar da damuwar daga ranta abun ya faskara, haka tayi ta faman aikace-aikace, har aikin ma da batayi niyyar yi ba. Sai wajen karfe biyu ta gama goge gidan, ta dauko tsumman ta fito ta wanke a faffon tsakar gida ta shanya. Har ta kama hanyar shiga gidan sai kuma ta zauna a kan dankalin da fulawoyi suke ciki; ta karewa tsakar gidan kallo kamar mai neman wani abu.
Haka kawai kuma sai ta ji kamar ita kadai ce a duniyar; ya za ayi ace tana zaune a gidan mijinta amman saboda Zahra babu mai kulata? Makota gaba daya basa harka da ita gashi mijin ma yanzu ya daina kulata. Ta manta rabon da a buga mata gate don daga ita sai Amira suke rayuwarsa, sai dai da yake duk sati sai Anti Uwani ta kawo su Abdallah. Ta share zazzafar kwallar da ta zubo a kan fuskarta.
Tabbas ba zata taba yafewa Zahra ba da ma duk wani wanda yake da hannu wajen sakata a wannan halin.
A da ta yiwa kanta alkawarin zata zauna tayi jiran har mijinta ya dawo hayyacinsa amma kawo yanzu bata sani ba ko zata iya cika wannan alkawarin. Domin zaman ya fara isarta, ta fara rasa walwala gaba daya tunda komai ya daina bata farin ciki. Tabbas bata san zuwa yaushe zata iya jira ba amma dai ta fara tunanin yiwuwar ta koma gidan Hajiya kawai ko jiran ne tayi a can.
Ta share hawayenta lokacin da ta tuna la’asar ta kusa kuma bata ma yi azahar ba, ta mike cikin sanyin jiki ta shige cikin gidan domin yin sallar azahar.
___
Da yake tazarar dake tsakanin karamar Sallah da babbar Sallah babu yawa har har an fara lissafin babbar Sallah.
Kamar yanda ya saba haka yayi wa kowa kayan Sallah; baiyi maganar Aisha ba wanda wannan ya kara kwantarwa da Zahra hankali ta kara sakankancewa lallai aikin boka na Doguwa ya kama.
Sa ya siyo da rago daya wanda aka yanka Uwara Saddiku tayi yanda take so da shi cikin walwala. Cikinta ya fara girma domin ya shiga wata na hudu don haka ba da ita akayi aikin suya naman ba, masu aiki ne su uku sukayi. Sai dai kawai tana zaune daga gefe a kan tabarma tana nuna yanda take so ayi.
Haka suka gama aikin suka tattare mata naman aka saka a cikin gida.
Ita kuwa Aisha tun ana i gobe Sallah suka tafi gidan Hajiya, a can aka yanka mata ragonta aka gyara aka soya. Saida suka gama yawon Sallah lokacin bayan Sallah da kwana biyar sannan suka koma.
Haka rayuwa ta cigaba.
__
Ranar Talata ce tana zaune a staffroom, bata da aiki a daidai lokacin don haka take ta faman duba wayarta tana kallon status; daga kan wannan ta koma kan wannan. Suna ta wucewa har tazo kan status din Anti Karima, matar Yaya Bello.
Hotuna ne na yaronta