Showing 90001 words to 93000 words out of 166068 words

Chapter 31 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25412

hirarrakinsu.

Bata ji dadin yanda bai sanar da ita shirinsa ba, saboda ya za ayi tana nan yana shirin tafiya Saudiyya amma ba zai sanar da ita ba.

Ta dai kyale zancen ne saboda tana da nata shirin, kuma da bata ji yace zai wuce da Aishan Dubai ba bata da damuwa.

Ita din ma zata so ace baya gari zasuyi wannan tafiyar ita da Amina tunda zai zama babu wani sauri da takeyi ta dawo gida sai lokacin da ta ga dama kawai. Don haka a take ta yiwa Amina waya suka daga ranar tafiya, domin a lokacin dama Asiya bata dade da haihuwa ba.
__

Ranar asabar ce wadda gobe Lahadi jirgin Abban Sadik da Aisha zai tashi.

Duk wani shiri da take bukata ta gama shi; abu dayane a ranta yanda zata tsara Abban Sadik ya yarda ta biyawa kanta kudin zuwa Dubai ta bishi. Tunda yayi maganar ta sa aka bincika mata aka gama yi mata lisaffi; kudin jirgi, hotel har zuwa kudin da take so ta kashe ta lissafa kuma taga cewa tana da su zata iya biyawa kanta.

Jirgin safe zasu tafi don haka zuwa goman dare sun gama komai sun kwanta. Yana kwance rigingine tana kwance a gefensa sai dai basu kashe fitila ba tukunna don basuyi bacci ba.

Mirginawa tayi ta koma jikinsa, ta dora kanta a kan hannunsa sannan ta dora tafin hannunta a tsakiyar kirjinsa, tace

‘Yallabai za a wuce da ni Dubai din?’

Ya dan dago kansa ya kalli fuskarta

‘A’a. Ai na gaya miki babu kudi amma kada ki damu kiyi ta addu’a business din ya kankama zamu je Dubai in Sha Allah.’

Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan ta muskuta tace

‘Don Allah to ni zan biyawa kaina, kaga dama adashin da nace maka na dauka last month 250k suna nan kuma inada wasu savings sai na kara.’

‘Um, kiyi abinda kika tsara zakiyi da kudinki in Sha Allah next time sai muje Dubai din.’

‘To kayi tunani dai kafin muje, kudin suna dollar account dina Kuma kaga visa din Dubai bata wahala. Kafin mu gama aikin Hajji kayi shawara. Kaga kafin ma mu dawo gida mun huta, ko kwana biyun ne ina laifi.’

‘Saboda muje kiyi min addu’a, ki tsara ni kiyi min wayo ko?’

Ta kyalkyale da dariya.

Suka karasa hirarrakinsu suka yi bacci.

Gari yana wayewa karfe tara na safe jirginsu ya daga sai Saudiyya.
___

Ranar litinin karfe shida na safe Uwar Sadiku suka kama hanyar garin Doguwa; a motar Amina suka tafi sai dai akwai Alele yaronta shine yake tukasu.

Nisan garin ya bawa Zahra mamaki matuka, don gani tayi kamar za a fita daga garin Kano.
Ko da suka Isa Doguwa ma wucewa sukayi sai da suka kusa fita Kano sannan suka sauka daga kwalta suka fada wani daji, da ba don taga alamar motoci suna bi ba da zata ce babu wanda yake shiga wajen.


Hanyar tsakiyar daji take, babu koda gona a kusa.

Ta kalli Amina wadda suke zaune a bayan mota tare zuciyarta fal tsoro, Amina tayi murmushi tace

‘Kada ki damu, kina hawowa nan layin kin zama bakuwar Malam Jani, babu abinda zai cutar dake har ki fito ki kama hanya sosai.’

Ta dan gyara zama ta mayar da hankali ga kallon hanya duk da ba wani gani takeyi sosai ba.

Sun kai kamar minti goma sha biyar suna zura gudu a lokon nan kawai sai taga sun fado wani sarari mai fadin gaske; kamar wata karamar unguwa.
A gaban wani babban gida sukayi parking wanda yake kewaye da wasu gidajen tsilli-tsilli sannan ga yara suna wucewa jefi-jefi. Yanayin wajen yanayi ne mai dadi, babu sanyi kuma babu zafi sannan ko ina a share yake tsaf.

A kofar babban gidan sukayi parking kusa da wasu motoci guda biyu wanda ga dukkan alamu masu kudine sosai kuma suma bakin wannan gidan ne.

Tun kafin su gama fitowa daga mota yaro ya fito daga cikin gidan yayi musu iso. Madadin su shiga ta kofar gidan sai yaron ya zagaya da su ta wata kofar da take bayan gidan.

Daki ne ya sha shimfidu na jajayen daddumai, har labulayen dakin duka jajaye ne. Ya nuna musu wata bakar dadduma yace su zauna, bayan sun zauna yace

‘Za ayi muku iso idan Malama ya gama, yana da wasu bakin.’

Kafin su amsa ya fice daga dakin.

Suna nan zaune tun wajen karfe tara na safe har sha biyu ta gota babu wanda ya sake lekosu, idan suka taba hira sai su koma suyi shiru.

Zahra ta dubi wayarta taga lokaci, ta dago ta dubi Amina tace

‘Amina anya ba a manta damu a gidan nan ba kuwa?’

‘Nace miki yana sane, tunda naga motocin nan na san yana da baki sai ya gama da su zai sauraremu.’

‘To ya ya za ayi muyi Sallah kin ga dai daya tayi.’

Ta dan zaro ido

‘Sallah! Ki rufa mana asiri, ai sai dai idan mukaje gida ma hade. Wa ya gaya miki ana kallon gabas a nan?’

Kallon da Amina take mata ya sa tayi shiru, suka cigaba da jira.

Jimawa kadan wajen daya da rabi yaron da ya rakosu dakin ya leko yace shu shigo. Ya wuce gaba suka bi bayansa. Kofar da suka shigo ba ita suka fito ba, wata kofar ce a dakin ya shiga suka bishi. Siririn corridor suka bi wanda ya sada su da wani daki mai kawanya.

Kusan komai na dakin ja ne sai fari tsilli-tsilli. Bangon da yake kallo kofar an bi shi kaf an rataye tarkace kala-kala, kayuwan dabbobin ita dai Zahra kamar har shekar tsuntsu ta hango.

Jar dadduma ce a shimfide a gaban bangon wadda kallo daya zaka yi mata ka san ta hadiye datti da yawa. Yana zaune ya tankwashe kafafu babu wata sutura a jikinsa sai gajeran wando da bai karasa gwiwarsa ba.

Tun da suka saka kafa a dakin Zahra ta damki hannun Amina ta rike gam saboda tsoro, ita kuwa Aminan da yake ta saba kai tsaye ta wuce gaban wannan bakin katon suka gurfana.

‘Ki gayawa bakuwarki ba a tsoro a nan Hajiya.’

Ya fadawa Amina da kakkausar muryarsa.

Nan da nan Zahra ta dan gyara zama tana kokarin ta dake.

‘Me kike so ayi da kishiyar taki da ta hanaki walwala?’

Sai da Amina ta zungureta sannan ta tuna ita akewa tambayar

‘Um ni so nake kawai a rabata da mijina, su rabu har abada kuma kada ya sake auren wata mace.’

Aka kyalkyale da dariya wadda har dakin saida ya amsa, sai dai ko da suka kalli fuskar malamin da suke gabansa babu alamar shi yake dariyar.

Ya mika hannunsa baya ya zaro wata babbar tasa wadda kusan za a iya cewa hannu daya ba zai iya dauka ba. Ya dire tasar wadda take dauke da ruwa a gabansu, ya dauki wata bakar kwalba a gabansa ya diga wani mai a cikin tasar sannan ya fara motsi da baki kamar mai wuridi. Lokaci kadan ya gama sambatun ya busa a tasar sannan ya dubi Zahra yace

‘Duba min nan.’

Amina ta dan dungureta suka matsa gaban tasar suka leka; Aisha ce sanye da abaya suna tafiya tare da Abban Sadik a wani wajen kamar farfajiyar masallacin Madina. Sai dai ita Aishan wani abu kamar glass ya yi mata kawanya shi kuma Abban yana gefenta babu abinda yayi masa kawanya.

‘Sune wadannan ko?’

Da mamaki take gyada kai tana

‘Eh, sune, sune.’

Aka sake bushewa da dariyar nan da basu san wanda yake yinta ba, sannan mutumin mai kakkausar murya ya nuna Aisha a cikin tasar yace

‘Kinga wannan, ba zata tabu ba. Ko me za ayi mata ba zai yi tasiri sosai ba domin ta fi ki shiri.’

Dariyar nan ta sake karade dakin, bayan ta lafa ya nuna Abba yace

‘Wannan za muyi miki aiki a kansa amma sai ya baro wajen nan da yake, idan ya dawo gida sai ki sanar damu.’
Cikin in ina tace

‘To ba zasu rabu ba kenan?’

Dariyar ta sake karade dakin, bayan anyi shiru yace

‘Aikin da zamu yi miki shine; zamu shafe masa ita daga tunaninsa. Zai manta da ita ya manta ya sake aure, ke duk wani wanda zai iya fada a ji ma a auren zamu mantar dashi labarin Aisha. Idan aka yi haka to tabbas ita da danginta zasu raba auren don bazasu iya tuna masa da ita ba, don auren ma ba shi zai saki ba sai dai suje kotu alkali ya saki. Daga ranar da mukayi aikin ba zai sake tunawa da ita ba.’

Dakin ya kuma cika da dariyar.

Ita kanta saida tayi murmushi saboda wannan tsarin nashi yayi mata,tabbas idan Abba ya manta da Aisha zuwa wani lokaci ne ‘yanuwanta zasu raba auren. Shikenan ta huta da wannan alakakan.

Kamar daga sama aka jefo wata karamar bakar tasa gabansu, mutumin yace

‘Ku juye duk abinda kuka zo da shi a nan.’

Nan da nan Zahra ta bude jakarta ta fito da kudin da ta zo da shi naira dubu dari biyu ta saka a tasar, a take tasar ta bace.

Mutumin yace

‘Idan ya dawo a zo a sanar da mu, zuwa lokacin dan matsuruto zai sanar da ku kudin aikin da zaku ajiye masa kafin aiki ya fara. Ku tafi, ku tafi.’

Nan da nan suka mike, yaron da ya shigo da su ne ya sake shigowa ya wuce musu gaba. Ya bi da su ta wata kofar da ban da ba ta nan suka shigo ba, sai a lokacin Zahra taga sun fito ta kofar gaban gidan daidai inda suka ajiye mota. Motocin da suka tarar da safe basa wajen sai dai wata bakar mota wadda da alama bayan sun shiga ne masu ita suka zo.

Ba tare da bata lokaci ba suka shiga mota suka kama hanya, nan dinma hanyar da suka bi ba ta ita suka fito ba.


Babu wanda yayi magana sai da suka fito daga daji suka hau kwalta. Amina ta dubi Alele da yake tuki tace

‘Alele duk mai abun da ka gani ka tsaya mu siya mu dan sa wani abun a bakinmu, na manta ban yiwo mana guzuri ba yunwa muke ji.’

‘To Hajiya, mun kusa zuwa wajen masu mangoron nan ai.’

Ta dubi Zahra tace

‘Kawata kin ga inda za a magance miki matsalarki ko? Yanda yayi miki alkawarin haka zai yi miki aiki zaki sha mamaki.’

‘Hmmmn! Ai na ga alama.’

Suka yi shiru kowacce tana kora ruwan robar da suka taho da shi.


Jimawa kadan Zahra tace

‘Kawata naji yana maganar kudin aiki bayan kudin da na ajiye masa.’

‘Eh, ai in dai kin shiga da jaka wannan dakin sai kin ajiye duk kudin da yake jakar a wannan tasar ko an yi aiki ko ba ayi ba. Kudin aiki kuma da ban za a sanar dake. Kawai idan zamu dawo ki sake ciko jaka.’

‘Hmm!’

Suka sake yin shiru na dan lokaci, jimawa kadan Zahra tace

‘Ni abu daya ne yake bani haushi, duk inda naje sai ace wai mutuniyarki bazata tabu ba. Na rasa waye malaminta a garin nan da bamu san shi ba.’


Amina tace

‘To tunda dai an sami makarinta ba shike nan ba, duk ma wanda yake mata aiki su karata. Idan ta rabu da mijinki duk ma yanda tayi ba shikenan ba.’

‘hakane kam, a sauka lafiya.’

Sai daga baya suka sami masu rogo sun fito daga wani kauye, suka saya sukayi ta ci har suka rage yunwa.

Saida aka idar da Sallar Magriba sannan suka ajiye Zahra a gida suka wuce, a kan idan alhazai sun dawo zasu koma a gama aiki.


UWAR SADDIKU


Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)


30

Tunda suka dawo daga Doguwa kuma sai Zahra ta cigaba da harkokinta cikin walwala, musamman da yake yanzu gidan yana hannunta. Abu daya ne kawai bata sami yanda take so ba; ta riga ta tsara yanda zata yi yawon Sallah a motar Abban, sai dai kawai ranar da zasu tafi da motar ya fita ya kaita gidan Yaya Bello ya ajiye a can sanna Ali ya wuce da su airport.

Da ya sanar da ita wannan tsarin nasa da wuri da tabbas ta hanashi don da ya saba tafiya ya bar motarsa a gidan, amma dai wannan zuwa Doguwa ya wanke mata duk wata damuwa.


Nan da nan ta cigaba da shirin babbar Sallah da lissafin yanda zata kasafta naman san da ya bari a yanka.
__

Tunda suka isa kasa mai tsarki Aisha ta dukufa addu’a; duk abinda take so saida ta roka kuma ta yiwa Abbanta addu’a sosai.


Tare da Abba suke a hotel don haka ma bata sake tayi wata kawa ba tunda yawancin ibada ma tare suke zuwa, don haka ko kasuwa ma bata tunanin zuwa.

Saura kwana biyu arfa suna zaune ita da Abban sun gama cin abinci suna hutawa a dakinsu na otel suna dan taba hira . Kamar wadda aka tunawa ta dubeshi tace

‘Uhm, Dubai din zamu wuce ko Yallabai don ka ga shi yasa ba zan yi tsaraba a nan ba sai na je can.’

Ya harareta yana jijjiga kai

‘Wannan mata bata da mantuwa.’

Ta dan zaro ido

‘Da mijin zan manta ko kuwa da kaina?’

‘To zamu wuce kin ji dadi?’

Zumbur ta mike tsaye

‘Allah, dadi kai! Ai bari ma kaga nayi Sallah na yiwa Allah godiya tukunna.’

Sai da ta gama murnar ta tambayeshi nawa zata turo a kudinta da tace zata biya, yace ta turo dubu dari biyu account dinsa ya isa shi sai ya cika sauran.

Sai bayan ya nuna mata visa dinta sanna taga kwana bakwai yayi musu booking, ta ji dadi sosai don haka ta fasa duk wata sayayya ta mayar da hankali wajen ibada da kuma addu’a.
…………

Tunda suka tafi Saudiyya kusan kullum wayoyin Abban suna kashe, sai lokacin da ya zaba sai ya kunna suyi waya ta Whatsapp don ya ji lafiyar iyali. Tayi mita har ta gaji, don haka ya zama kawai sai dai ta bar masa sako a WhatsApp idan ya gani sai ya kirawota.

Tunda suka tafi ya ke shawarar tafiya da Aisha Dubai kuma yake tunanin yanda zai yiwa Zahra bayani ya rasa. Bayan Sallah da kwana hudu ya kama ranar zasu wuce Dubai kuma har ranar bai gayawa Zahra ba.


Kaf suka shirya kayansu ana yin sallar Magriba suka bi jirgi sai Dubai.

Sai da suka sauka a hotel suka huta sannan ya bude data.

Yana bude data kuwa kiran Zahra ya shigo kamar tana jiransa, a lokacin Aisha tana wanka. Ya amsa wayar ya fice daga dakin, ya dawo falon kasa wato reception na hotel din ya sami kujera ya zauna.

Bayan sun gaisa ya tambayi yaran, duka suna kusa da ita don haka ta bashi suka gaisa da kowa har Saddiku. Bayan ta karbi wayar suka dan taba hira, jimawa kadan yace

‘Yauwa ban gaya miki ba na wuce Dubai din fa, itama Aishan muna tare da ita a nan din tare zamu dawo.’

A dan razane tace

‘Um ban gane ba. Kace ita nan gida zata wuto?’

‘Eh. Na canza shawara daga baya tunda itama ta biyawa kanta kudin zuwa Dubai din kawai sai muka wuce.’

‘Um, Allah ya bada sa’a.’

‘Amin.’

Yanda yaji muryarta ta canza nan take ya san da sauran bayani, ya san idan ta fara mita abun zai daukesu lokaci don haka nan take yayi mata sallama ya kashe wayar.
…………

Kwanki biyun farko da sukayi a Dubai shi kadai yake fita tare da wanda aka hadashi don ya raka shi kamfanin da zai yi sayayya. Yana fita Aisha take komawa bacci, domin dama ta tara bacci a Saudiyya. Haka ya kwana biyu yana yawo ita kuma tana hutawa, don ko abinci har dakin ake kawo mata.

Sun riga sun gama magana da Aisha a kan ya saya mata waya in ya so ita kuma sai tayi tsaraba da kudinta; don haka fitarsu ta farko ya sayo mata Samsung hadaddiya mai tsadar gaske.

Suna komawa daki ta kasa hakura, saida ta kunna wayar nan. Suka hadu sukayi launching sabuwar waya.
Wayar ta hadu sosai kuma camera tana fitar da hoto don haka sai ya zama duk inda suka je haka zasuyi ta hotuna.

Sun hutu kuma sun ji dadi domin Aisha zata iya cewa bata taba jin dadin zama da shi ba kamar a wannan lokacin. Shi kansa yaji dadin tahowa da ita saboda yanda take jiyar da shi dadi kuma tana saka shi walwala, don haka ya saki kudi sukayi ta yawo suna sayayya. Hotuna kuwa Allah ne kawai ya san yawan wadanda Aisha ta dauka a sabuwar wayarta; wasu a dakin otel, wasu a wajen cin abinci, wasu a wajen sayayya wasu ma a kan hanya kawai. Ko wanne kuma sai ta makale a jikinsa take dauka ko ta sami masu wucewa tace a daukesu.

Ranar da suka kwana uku a Dubai rana suka je wani club na larabawa, wajen an yi masa tsari ne kamar a Sahara. Sanna ga rakuma da dawakai birjiki duk wanda kake so shi zaka hau, kuma abinci kala kala na larabawa. Wajen yayi matukar burge Aisha.

Tunda suka shiga wajen suke daukan hotuna.


Bayan sun gama hutawa rana ta fadi tace zata hau doki, suka karasa aka hada musu doki. Ita bata iya doki sosai ba don haka da ta hau wani balarabe ya ja linzamin dokin suka zagaya.

Daga baya Abba yace ta dawo su hau doki daya don su zagaya sosai.



Nan da nan ta sauka ta koma kan dokin Abba; ta zauna a gabansa ya rungumeta ta baya sannan ya ja doki suka kama hanya. Suna tafiya sunata hira da dariya.

Saida suka zagaye wajen tas.

Bayan sun dawo wani balarabe ya nuna musu hotunansu da yayi ta dauka a camera dinsa wanda idan suna so biyanshi zasuyi sai ya tura musu. Nan take ta mararaicewa Abba ya biya aka tura hotunan wayarta.

A gajiye likis suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login