Showing 21001 words to 24000 words out of 166068 words

Chapter 8 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25385

ba ko daya. Kwana tayi tana tunanin yanda za ayi Yusuf, nata ita kadai, yaje ya kwana da wata mace. Kuma haka ta tashi tana ta wannan tunanin tana tsaki.

Tun sassafe Jummai ta zo don haka ta barta da yaran a kasa ta dawo sama ta zauna. Koda Jumman ta shigo saida ta tambayeta ko za a yiwa amarya abinci amma tace a’a. Ta san ya kamata tayi amma bazata yi ba, domin da ana so ta bata abincin ai da a nan cikin gidan za a saka amaryar su zauna tare.

Karar wayarta ce ta katse tunaninta, ta daga wayar ta duba, Abban Sadik ne.


Saida taja tsaki sannan ta amsa wayar ta kara a kunnenta

‘Uwargida ran gida, kin tashi lafiya?’

Ta wurkila kwayar idonta cike da takaici sannan tayi yake ta amsa

‘Lafiya kalau, ya amarya?’

‘Alhamdulillah. Gamu nan shigowa yanzu zan kawo miki kanwar taki.’

‘To Allah ya kawo ku lafiya.’
Ta jiye wayar ta dubi agogon bangon dake falon, karfe goma da kwata. Ta ja tsaki ta kawar da kai, bata ma san lokacin ya tafi haka ba don ko wanka bata yi ba.

A take ta tuno abinda ya kamata ta fara yi, inda ta tashi da hanzari ta koma dakinta. Ta san dai inda suka boye layar nan jiya tabbas Abban Sadiku ta nan zai shigo falon don haka gara ta nemo layar taje ta mayar ayi ta ta kare kawai.


Tana shiga dakin ta nufi wardrobe inda ta rataye rigar da ta saka jiya a saman wardrobe din, ta zura hannunta a hankali cikin aljihun rigar ta laluba taji babu komai. Ta koma ta daya gefen ta zura hannunta a dayan aljihun ta laluba a hankali bata ji komai. Mamaki ya bayyana a fuskarta, ta fizge rigar daga saman wardrobe din ta karasa ta bajeta a kan gado ta sake lalube aljihun duka biyun bata ji komai ba. Ta daga rigar ta zazzage babu a binda ya fado, ta zauna a kan gado tana kallon rigar tana mamakin inda layar ta shiga.

Tabbas ba mantuwa tayi ba, a hannunta Amina ta bata layar kuma tabbas a aljihun rigar ta saka. Bata cire ba ta barta a kan da safe ta dauke; to a ina layar zata fadi?. Gashi tsaf aka share gidan jiya kuma yau ma Jummai har tayi shara.


Ta mike ta koma gaban wardrobe din ta sake dubawa ko a kasa layar ta fado, bata sami komai ba. Ta dawo ta zauna a gefen gadon tana tunani; to ina layar zata shiga?

‘Ikon Allah!’

Ta fada a fili.

Motsin taba kofar ne ya dawo da ita hayyacinta, Yusra ce ta shigo da sallama tace

‘Mommy Abba ya zo da matarsa.’

Taja tsaki

‘Mtsewwww! Kice masa ina wanka.’

‘Ai ba aiko ni yayi ba na san yanzu zai hawo nemanki.’

Ta mike tana fadin

‘To bari ki gani.’

Ta fada bandaki ita kuma Yusra ta juyo ta fito.Tana jin lokacin da Abban ya shigo dakin ya fita. Har ta gama wankan nan bata gano inda layar nan tayi ba don haka ta hakura tunda Aishan ta riga ta shigo ta zauna a falon. Haka ta fito ta zabo leshi mai kyau ta shirya tsaf ta fesa turarukanta masu kamshi sannan ta sauko.

Tun kan ta karasa saukowa ta hangosu; Aishan tana zaune a kan kujerar zaman mutum daya shi kuma Abban yana kan kujerar zaman mutum uku. Sadik da Yusra tunda suka gaisheta suka bar wajen, don Yusra ma tunda ta gaisheta ta haye sama bata sauko ba. Rukayya ce a zaune a kusa da Aishan sai Ummi da take ta faman yi mata surutu.

Ta karaso da sallama, ta wuce kai tsaye ta zauna a kusa da Abban Sadik. Tana murmushi ta dubeshi

‘Yallabi Ina kwana?’

Yaji dadin yanda ya ganta da fara’arta don haka shima tashi fara’ar ta karu

‘Lafiya kalau, ya kuka kwana?’

Bayan ta amsashi ta juya wajen Aisha tace

‘Amarya bakya laifi, barka da zuwa.’

Tana murmushi ta mayar mata da amsa

‘Yauwa, ina kwana.’

Suka gaisa cikin walwala, Zahra ta umarci Jummai ta kawo muta ruwa da lemo, ta dubi Abban Sadika tace

‘Ka san kasa tashi nayi saboda gajiya shi ya sa ban samu na dafa muku abincin safe ba, ko a kawo muku yanzu ku karya.’

‘A’a, mun karya ma sai dai ko kanwar taki zata kara.’

Tace

‘A’a na koshi.’

Sukayi shiru na dan lokaci, Abban Sadik yace

‘To Zahra ga kanwarki nan, naga ma kun riga kun saba kuma ban ga alamar matsala ba. Allah ya hada min kanku. Na gaya mata duk abinda take bukata ta nemeki, yara kuma yanzu sun zama masu gida biyu, duk inda suka shiga daya ne.’

Zahra tace

‘Hakane, Allah ya bada zaman lafiya. Ai ga uwata sarkin kaudi har ta makale mata.’

Suka yi dariya gaba daya. Abban ya mike yana fadin

‘Bari na hau sama, idan na sauko sai mu wuce.’

Ya Haye sama ya barsu a nan falon.

Yana wucewa Zahra ta sha kunu ta bata rai, suna hada ido da Aisha ta dauke nata kana saboda yanda taga sauyin yanayin.


Ta harari Rukayya wadda take zaune a kujerar kusa da ta Aisha tace

‘Ku kuma kowa ya bace kuna zaune kuna biya bakin mutane, tashi ki bani waje.’

Nan da nan suka fice daga falon ya zama daga Zahra sai Aishan, tana ta faman bata rai ita kuwa Aishan ta ma kasa hada ido da ita tunda ta kula da yanda yanayinta ya canza.
Jimawa kadan ta tashi ta kashe talabijin din dake kunne a falon ta haye sama ya zama Aishace ita kadai a falon.

Ta cika da mamakin yanda kiri-kiri Zahra tayi mata fuska biyu a cikin abinda bai fi minti ahsirin ba .

Sai da aka yi wajen minti talatin sannan taji motsin saukowarsu, yana tafe Zahra tana biye da shi rike da jakarsa ta computer da litattafansa. Sai wani faman murmushi take suka jero suka shigo falon, ta dubi Aisha da fara’a tace

‘A’a, ina ‘yayan naki sukayi Anti Aisha shine suka barki ke kadai?’

Murmushi tayi tace

‘Yanzun nan suka fice ai.’

‘Kuma sai ki kashe TV, da kin canza channel din kawai.’

‘Uhm.’

Abban Sadik yace

‘To mu tafi ko?’

Ta mike ta dubi Zahra tace

‘To sai an jima, na gode.’

Ta mika mata 'yar karamar leda dauke da turaren wuta da wata karamar burner tace

‘To ga wannan amarya, sai mun shigo ni da yara.’

Sukayi mata sallama suka fice.


UWAR SADDIKU


Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)


10

Saida amarya ta kwana biyu sannan su Yaya Zuwaira suka kawo mata ziyara tare da Abdallah da Farha. Nan suka wuni ana ta hira, sai bayan la’asar sannan suka tafi, suka barta da kewarsu.

Haka Yusuf ya cigaba da kwantar mata da hankali har ta samu ta dan kara sakewa.


Ranar Talata ne ya kama kwana uku, don haka ranar ne zai koma kwanan Zahra. Ya riga yayi musu bayani da daddare zai dinga canza waje kwana don haka wadda zai kwana a wajenta ita zatayi masa abincin dare.

Bayan ya dawo daga sallar magriba ya sameta a falo tana kallon TV, bayan ya amsa sannu da zuwanta ya zauna a kusa da ita suna fuskantar juna, yace

‘Yanzu zan wuce wajen yayarki, amma gaskiya bana son barinki ke kadai. Kinga da a can kike da bani da wata damuwa.’

Tayi dariya ta dan kwanta a jikinsa

‘To ai ni ban ce maka ina jin tsoro ba, tunda idan ma wani abun ya taso zan iya kiranka ko na kirawo Mommy ko?’

‘Hakane, amma dai bari naje gidan sai na kawo miki Yusra ta zo ta taya ki kwana.’

‘To duk yanda kace.’

Sai da yayi da gaske sannan ya Kanye jikinsa ya tashi yayi mata sallama ya fice a kan yanzu zai dawo ya kawo mata Yusra.


A falo ya samesu gaba daya banda Sadik, bayan Mommy ta amsa sallamarsa duka sukayi masa sannu da zuwa. Ya karasa ya zauna a kan kujerar zaman mutum uku kusa da Mommy, ya dubeta yace

‘Wa zaki bawa kanwarki aro ne a tayata kwana?’

Ta dan tsuke fuska

‘To ai kaga dalilin da yasa nace a hademu kace tace bata so, ai na zata zata iya kwana ita kadai.’

Ya kalleta alamar tuhuma, ta kau da kai sannan tace

‘To ai gasu nan duk wanda ka daukar mata, sai dai Yusra itace take tayani kula da kannenta idan suna bacci.’

Nana da take zaune tana yin homework tace

‘Ni dai don Allah ba ni ba Abba nafi so na kwana a nan.’

Kafin ya amsa Rukayya tace

‘Abba bari na shirya muje, amma fa ban yi homework dina ba, ga hadda ma ina so Yaya Yusra ta biya min.’

Cikin fara’a yace

‘Kada ki damu itama Antin zata biya miki, kwaso kayanki kafin na sauko daga sama sai na raka ki.’

Ya wuce saman ya barsu a zaune.

Yana kulewa Mommy ta harareta

‘Ke wai wacce irin yarinya ce Rukayya, kin ji kowa ya ce ba zai je ba sai ke uwar sakarci ko? Idan ya kuma zuwa yace wa zai je kika amsa sai na ci mutuncinki wallahi, kin ji na gaya miki.’

Tayi tsuru-tsuru tana mamakin yanda kawai don tace zata kwana gidan amarya abun ya bata ran Mommy haka. Yusra ta harareta tace

‘Sai ki tashi kije ki hado komatsanki kafin ya sauko kuma.’

Ta tashi jikinta babu kwari ta nufi sama inda dakinsu yake.

Tare suka sauko ita da Abban tayiwa Mommy sai da safe suka wuce, yana kula da yanda yanayinta ya canza don haka ya tabbatar fada Mommy tayi mata.


Bayan ya rakata ya tabbatar Aisha ta kulle kofa sannan yayi musu sallama ya dawo.

Dakin baki Aisha ta nuna mata ta ajiye kayanta, sai a hankali Rukayya ta sake sukayi homework din kuma ta biya mata haddarta, suka dan taba hira suna kallo sannan wajen karfe goma na dare aka dauke wuta.
Aisha ta shiryo suka kwanta tare da Rukayya a dakin baki.
……

Saida ya gama duk abinda yakeyi, ya zauna a falon sama yana kallon TV. Bayan yara sun kwanta itama ta zo ta zauna a kusa da shi, jimawa kadan ya dubeta yace

‘Zahra.’

Da murmushi ta dubeshi ta amsa

‘Yallabai.’

Ya gyara zama ya fuskanceta sosai

‘Ban ji dadin abinda kikayi ba, don Allah ki bar yaran nan su yiwa Aisha duk abinda take so wanda bai sabawa addini ba. Ina laifi idan yara sun tayata kwana, amma nayi magana kince ai ita ta zabi haka. Kuma Rukayyan ma saida kikayi mata fada saboda kawai na sakata aiki tayi.’

Ta bata rai tace

‘To ni me nace, shikenan ba zan fadi ra’ayi na ba saboda matarka. Yara kuma ai naka ne, ni babu wanda na hana idan ma Rukayya ce ta gaya maka nayi mata fada to karya takeyi.’
‘Ni dai don Allah kiyi min alfarma ki bari a zauna lafiya, don Allah.’

‘Uhm.’

Sukayi shiru na dan lokaci, daga baya kuma ta tashi ta wuce dakinsa ta kwanta tana matse kwalla. Wato daga ya dana dadin amarya kwana uku kacal har ya fara nema yayi mata fada a kan matarsa, lallai zata gyara musu zama. Haka ta kwana zuciyarta babu dadi.

Daga wannan lokacin ya zama kullum idan zai kwana gidan Zahra to Rukayya ce take taya Aisha kwana, tun tana dagewa har ta hakura. Kuma sai ya zama jininsu ya hadu da na Aishan suka zama kamar wasu kawaye duk da dai Rukayyan tana shan gori a wajen Mommy da Yusra.
-----

Ranar Alhamis da magriba bayan ya gama shirinsa zai koma wajen Aisha Mommy take gaya masa ita da yara zasu je wajen Hajiya gobe Juma’a don sun kwana biyu basu je ba. Har ya fita ya dawo yace mata zai gayawa Aisha don haka idan sun shirya suyi mata magana sai su tafi gaba daya tunda driver ne zai kaisu. Yayi mata sallama ya wuce.
----

Itama Aishan yana shiga ya sanar da ita gobe da yamma zasu je gidan Hajiya da su Zahra, don haka da gari ya waye yana fita office ta kama hidimarta don tayi sauri ta gama. Ya riga ya gaya mata sai bayan masallaci amma duk da haka tana gama aikinta wajen sha biyu ta sa hijabi ta nufi gidan Zahran.

Babu kowa a gidan sai ita kadai da Jummai wadda take share tsakar gida, tun a nan suka gaisa da Jummai ta wuce ciki.

Tana zaune a falo tana ta faman latsa waya tayi sallama ta shiga bayan ta amsa mata. Da fara’arta ta karasa ciki ta zauna a kujerar mutum daya.

‘Ina kwana Mommy.’

Sai da ta kalleta ta gatsine fuska sannan ta amsa da kyar

‘Lafiya kalau.’

Sukayi shiru na dan lokaci, ita Zahra ta cigaba da duba wayarta kamar babu mutum a wajen yayinda ita kuma Aisha take mamakin wannan tsare gidan da muzuran da ake mata. Ta yi dan gyaran murya tace

‘Uhm, Abban Sadik yace zamuje gidan Hajiya da yamma shine na leko mu gaisa. Idan kun shirya ko yara suyi min magana sai mu tafi.’

‘To.’

Ta mike tsaye tayi mata sallama ta fice, ita kuma tabi bayanta da harara harda kwafa saboda kishi.

Ta tsani ganin matar nan, gashi dai an ce bazawara ce amma kamar budurwa. Kuma ta zata Malam Sule direbanta ne ita kadai amma za ace su wani hada fita.

Ta ja tsaki ta cigaba da abinda takeyi.
……

Sai wajen karfe hudu saura sannan Zahra ta shirya, ita da yaranta gaba daya banda Sadik, domin shi yace ba zai je ba. Suka fito gaba daya suka shiga mota, har Yusra zata shiga gaban mota Mommy tace ta dawo baya. Don haka suka shiga bayan motar gaba daya, ita da Yusra, Rukayya, Nana da kuma Ummi duk da wajen zaman Ummi bai kai na mutum daya ba.

Yusra ce tacewa Malam Sule

‘Malam Sule ka tsaya a kofar gidan matar Abba da ita zamu tafi.’

Suna fitowa yayi parking a gate din Aisha ya latsa honk, ya juyo yacewa Yusra

‘Ko kirawo mana ita zakiyi.’

Mommy tace

‘Kayi mata honk din zata fito ko kuma ka buga mata gate.’

Yanayin da tayi maganar ya sa babu damar musu don haka kawai sai ya fita ya buga gate din, bugu daya ta bude. Cikin girmamawa ta gaisheshi tace

‘Bari na dauko jakata a shirye nake.’

Ta koma cikin gidan shi kuma ya koma mota ya zauna.


Jimawa kadan ta fito ta mayar da gate din ta rufe ta karaso jikin motar ta bude ta gefen da Yusra take zaune tare da sallama tana fadin

‘Yaya Yusra dan matsa na zauna, ko Nana ce zata koma gaba sai mu zauna a bayan.’

Dukansu suka kara babbakewa Yusra ta banka mata harara yayinda Rukayya ta sunkuyar da kanta, Mommy tace

‘Basa shiga gaban mota.’

Ta kallesu da mamaki sannan tace

‘Umm, to ku dan gyara sai na shigo mu zauna nan duka.’

Mommy tace

‘Gurin ba zai isa ba ai baki gani bane, ki zauna a gaban mana ke.’

Mamakin Aisha ya karu, kafin tayi magana Malam Sule yace

‘Ina ga ai ko Ummin Abban aka miko nan ai wajen zai isa Hajiya.’

‘Malam Sule, ka san dai Yallabai baya barin yara zaman gaban mota ko? Ta shiga gaban kawai muje in ba haka ba ka kaimu sai ka dawo ka kaita.’
A tunzure tayi maganar don haka Malam Sule yayi shiru.

Aisha ta dan ja baya, nan da nan Yusra ta ja kofar motar ta rufe yayinda Mommy tace

‘Mu tafi.’

Ya tada motar ya leko ta taga yacewa Aisha

‘Ranki ya dade yanzu zan dawo in Sha Allah.’

Yaja motar suka barta a nan tsaye tana mamaki.

Ta juya zata koma gidan sai kuma tayi wani tunani; yanda taga yanayin matar nan bata jin zata bar Malam Sule ya dawo kuma idan taje bata san me zata fada a can ba idan kuma ya dawo bata je ba bata san irin sharrin da za tayi mata a wajen maigidan ba. Ta riga ta san gidan don yayi mata kwatance kuma a bakin titi ne, don haka ta juya ta nufi titi, nan da nan ta sami motar haya ta bisu.

Zuciyarta har tafasa takeyi saboda takaici, ya za ayi ta shiga gaban mota da direba bayan ga yara. Ko da ma yaran ba zasu shiga gaban motar ba idan suka mammatsa bayan motar ma zai ishesu har ita. Amma saboda an shirya sharri da wulakanci ace ta shiga gaban mota, kuma a ja mota a tafi a barta.

Nan da nan ta isa gidan, kafin ma tayi tambaya ta gane domin ta hango motar Malam Sule a kofar gidan, ta sallami mainmota tana juyowa Malam Sule ya fito daga motar yana rage tsawo

‘Ranki ya dade tahowa kika yi? Don Allah kiyi hakuri, Hajiya ce tace na jirasu idan na mayar da su sai na taho dake.’

‘Babu komai.’

Ta wuceshi ta shige cikin gidan.

Suna zaune a falon Hajiya ana ta hira.
Hajiyan tana zauna a kasa ta mike kafa su kuma Zahra da yaran suna zaune a kewaye da ita, sai Anisa wadda budurwace 'yar wajen Yaya Saratu sai kuma yaran Bashir kanin Abban Sadik din su biyu; Fawwaz da Nawal.


Sai hira akeyi yara suna kaiwa da kawowarsu.

Tuni Mommy ta riga ta yi musu bayani cewa Aishan ce tace bazata biyo su ba sai dai a kaisu a dawo a kaita don ba zata hada tafiya da su ba. Take Hajiya tace a gayawa Malam Sule kada ya koma wanda dama Mommy ta riga ta gaya masa. Zancen suke mayarwa ta shigo, Hajiyan ce ta amsa sallamar ta, ta karasa ciki jikinta babu kwari saboda kallon da akeyi mata.

Ta wuce ta zauna daga gefen Hajiya inda yake da dan sarari, cikin sanyin murya ta gaida Hajiya wadda ta amsa mata kamar a fusace.


Jikinta ya kara sanyi sosai, don haka ta gyara zama ta sunkuyar da kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login