Showing 57001 words to 60000 words out of 166068 words

Chapter 20 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25429

da dai suna da rufin asirinsu amma ya san tabbas babu mamaki idan Farha ta iya zagin.

Ba tare da ya cewa kowa komai ba ya tashi ya fice.

Yana fitowa daga gidan aka fara kiran sallar magriba don haka kawai sai ya wuce masallaci, sai da aka idar da Sallah sannan ya dawo ya shiga gidan Aishan.

Rukayya ce a falo ita kadai tana homework, bayan ya amsa sannu da zuwan da tayi masa ya wuce dakin Aishan inda ya hango fitila.

Tana zaune a kan dadduma da hijabi, da alama Sallah ta idar. Farha tana kwance a kan daddumar gefen Aishan yayinda Abdallah yake zaune a kusa da ita da alama tare suka idar da Sallar.

Ya karasa ya zauna a gafen gado, kallon da take masa kallone me cike da tuhuma domin tana so taji dalilin da yasa aka mari Farha.

Yayi gyaran murya yace

‘Yusra tace Farha ce ta zageta, kin san su basu saba zagi ba shi yasa zata ji haushi har tayi over reacting. Kin san basu saba zagi ba mu a nan amma tace Farha tace mata me siffar karuwai, kinga wannan ai ko wa aka gayawa zai ji haushi. Ki dinga yi musu fada, itama Yusran nayi mata fada.’

Cikin sanyin murya tace

‘Toh.’

Ta sunkuyar da kanta tana kallon daddumar da take kai, ya san ba zata sake yi masa magana ba don haka ya tashi ya fice daga dakin ya shiga dakinsa.

Mikewa tayi ta fara hada musu kayansu; gara ta mayar dasu inda ake kaunarsu. Ya za ayi ace Farha ta san karuwa kuma har yana wani fada yaransa basa zagi saboda nata yaran ne ba a musu tarbiyya don haka su suka iya zagi. Ba tun yau ba tana kula da yanda Yusra ta tsani Farha; shi kanshi Abban tana kula da yanda yake nuna kishinsa idan su Abdallah suka zo. Idan yaga tana hidimarsu ya dinga nuna kamar shi ta share shi kenan, gaba daya dai ta kula ya fi natsuwa idan basa nan.


Ta dai kau da kai ne ga abun saboda bata so aure ya rabata da yaranta; yanzun ma kuma bazata bari aure ya shiga tsakaninta da su ba.
Jimawa kadan ta gama hada musu kayansu ta janyo karamin akwatin ta fito falo yaran suna biye da ita. Ta ajiye akwatin a bakin kofa ta wuce kicin ta sami roba ta juyo kazar da ta soya musu tazo ta ajiye a kusa da akwatin. Ta shige dakin Abban tana rike da mukullin mota ta tsaya bayan ya amsa sallamarta tace

‘Zan je na mayar da su Abdallah gida.’

Ya tashi daga kashingiden da yayi ya dubeta da mamaki

‘Daga dan wannan abun da ya faru, ki barsu su gama kwankinsu ranar Lahadi sa tafi. Yusra nayi mata fada ba zata sake dukan kowa ba.’

‘Babu komai, sun fi so su tafi. Zan mayar dasu din ai yanzu zan dawo.’

Bai ga alamar zata fasa ba kuma baya son rigima da ita don haka yace

‘Allah ya tsare, sai kiyi sauri kafin dare yayi sosai. Bari na taso na fice sai ki rufe gidan tunda ba nan zan kwana ba.’

Kusan tare suka fito falon, ta dubi Rukayya tace

‘Ki bi Abbanki Rukayya, idan na dawo zan masa waya sai ki dawo.’

Sai da ya rufe mata gate sannan ya kama hannun Rukayya suka nufi gida. Yana mamakin irin wannan fushin na Aisha, ita idan akayi abu ko magana bata fiya son yi ba sai dai kawai ta yi shiru tayi ta faman fushi. Yanzu ya san sai ya kai sati yana lallabata kafin ta bari su dawo yanda suka saba.

Suna dab da shiga gidan ya cewa Rukayyan

‘Wai da gaskene Farha ta cewa Yayarki Mai siffar karuwa?’

Da sauri ta bude bakinta ta rufe da tafin hannunta tana zaro ido, ta ajiye hannun tace

‘Tab, wallahi Abba babu wanda yayi zagi a falon nan. Tana taka ta ma tace sorry, kafin ta gama magana ta mare ta, gaskiya bata zageta ba. Farha ma ai bana jin ta iya zagi wallahi.’

Shiru kawai yayi saboda takaici; to ya akayi Yusra ta iya karya haka, gashi har Mommy tana goya mata baya?

Zuciyarsa a jagule ya shiga gidan, suka rabu da Rukayya a falo ya haye sama.


UWAR SADDIKU


Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)


21

Babu kowa a falon saman don haka ya wuce ya zauna a kan kujerar zaman mutum uku ya zuba tagumi. Wannan abun da ya faru yayi masa ciwo, yanzu Yusra har ta san ta kirawo kanta mai siffar karuwa saboda tana so tayi wa Farha mugunta? To me ya hadata da Farhan da har ta mare ta haka; don tabbas shi kansa yaga yanda yatsun Yusra suka kwanta a kan fuskar Farhan. To Mommy ce ta tsara musu wannan karyar ko sune suka tsara mata?

Ya tuno fuskar Aisha lokacin da yake ce mata ta dinga yi musu fada; tabbas bai kyauta ba. Yanda Aisha tayi ya san taji zafin abun amma ya zata son zuciya ne kawai saboda yanda take son yaranta.

Sai a lokacin ma yaga rashin kyautawarsa da bai je ya kaita gidan ba; take ya fara nadamar barinta ta fita gashi baya son fitar dare.

Sallamar Mommy ce ta katse shi, bayan ya amsa sallamar ta wuce ta zauna a kusa da shi. Bayan tayi masa sannu da zuwa tace

‘Na gama abinci fa, ko sai kayi Sallah.’

‘Eh, bari nayi sallar a daki don masallaci ma kafin na kai sun idar.’

Ya tashi ya shige daki ya barta.

Sai da yayi Sallah ya fito yaci abinci ya gama, ya dawo tsakiyar falon ya zauna yana kallon labarai a Aljazeera. Mommy tana zaune a kusa da shi tana rike da Sumayya ya dubeta yace

‘Kirawo min Yusra.’

Ta tashi ta fice ta tsaya a kafar bene ta kwalawa Yusra kira,nan da nan ta hawo saman. Abban ya dubeta yace

‘Kirawo Nana ku zo tare.’

Ta juya jimawa kadan suka dawo tare da Nanan.

Nan suka zauna a gaban Abban, saida ya dan dauki lokaci sannan ya dubi Yusra yace

‘Kika ce Farha ta ce miki mai siffar karuwai ko?’

Cike da tabbas ta ce

‘Eh Abba.’

‘Me yasa kuka yi min karya?’

Yusra ta zaro ido tana kallonshi

‘Abba ba fa karya bane wallahi haka aka yi.’

Yayi gajeriyar dariyar takaici da mamakin yanda Yusra ta kware da karya haka. Yace

‘Akwai CCTV camera a falon, da na duba ba haka na gani ba. Ta fito daga kicin ta takaki kuma kamar ma tace miki sorry shine kika mareta kamar kina marin sa’arki shi kuma Abdallah yana tasowa kafin ya karaso kusa dake ma kikayi fatali da shi kuma kika zage su. Ko na gaya miki zagin da kika yi musu?’

Cikin sanyin jiki ta sunkuyar da kai yayinda Nana ta fara kokarin buya a bayanta itama tana sunkuyar da kai.

Ya nuna Yusra yana fadin

‘Kika sa naje ina yiwa yara fada ashe kece makaryaciya kuma kece me yin zagin sannan kika zo kika kirawo kanki mai siffar karuwa, ke kin san meye karuwa kuwa? Ki rasa abinda zaki siffanta kanki da shi sai karuwa?’

Sukayi tsamo-tsamo babu wanda ya iya magana. Yayi shiru yana sauraronsu, Mommy tace

‘Au yanzu dama ba haka aka yi ba Yusra kuka zo kuka tsarawa mutane karya?’

Nana tace

‘Mommy wallahi Yaya Yusra ce.’

Ya kalli Mommy kallo na takaici, ta dauke kanta.
Ya dubi Yusra yace

‘Allah ya shiryeka, amma dai ki sani wannan abun da kika yi karya ce da annamimanci kuma kin kai shekarun da komai kikayi Allah zai tambayeki a kai. Duk hakkin wanda kika dauka kuma idan bai yafe ba sai kin biya.’

Ya mayarda dubansa ga Mommy; wadda itama jikinta yayi sanyi saboda bata taba zata karyane abunda suka gaya mata ba, domin suna shigowa suka gaya mata haka itakuma tacewa Yusran tayi dai-dai; yace

‘Wannan shine abinda ya kamata ki mayar da hankali a kai ba shirme da sa idonki a inda bai kamata ba, Allah ya shirya.’

Ya tashi ya wuce daki ya barsu a nan itada yaran.
Cikin fushi tace

‘Yusra me ya sa kuka fadi karya kuka sa nima na hau kai?

Ta zumbura baki tana kawar da kai tace

‘Mommy yarinyar ce wallahi take bani haushi, bana sonta.’

‘Kada ki sake yi min irin wannan, sai ki gaya min ainahin abinda ya faru in ya so sai na san yanda za ayi. Ku tashi ku bani waje.’

Suka fice suka barta a nan cikin damuwa.
…………..

Wajen karfe tara na dare saura kwata suka shiga gidan Umma. Waya tayiwa Umma don haka tana danna horn Anti Uwani ta bude kofa, bata shigar da motar ba tayi parking a nan bakin gate.
Ta dauki Farha wadda ta fara bacci shi kuma Abdallah yabi bayanta, suna shiga farfajiyar gidan Anti Uwani ta karbi Farha tana fadin

‘Allah ya sa dai lafiya, me ya sami Farhan? Ko bacci ne?’

‘Eh bacci ta fara.’

Suka karasa ciki.

Umma tana zaune a falo don haka suka zauna nan. Bayan sun gaggaisa da yake da wuta Anti Uwani sai ta kunna musu cartoon, suka zauna har Farha wadda ta tashi daga baccin suka fara kallo.

Aisha ta tashi ta shige dakin Hajiya, tana shiga ta zauna a gefen gado ta zuba fuskarta a tafukan hannunta tana ajiyar zuciya. Jimawa kadan Anti Uwani ta shigo dakin, takarasa ta zauna a kan kujerar gaban mudubi tana fadin

‘Ikon Allah, wai lafiya kike Aisha naga dazu kika tafi da yaran nan kuma Lahadi kika ce zaku dawo wai me ya faru ne?’

Ta sauke hannuwanta ta bude baki zatayi magana sai hawaye, Anti Uwani ta mike ta leka falo ta kirawo Umma. Suka saka Aisha a gaba suna tamabayarta tana share hawaye, saida ta gama share hawayen sannan ta basu labarin abinda ya faru.

Umma tace

‘To ai wannan ba abun kuka bane, suma su Farhan ai da gatanasu ba gashi kin dawo da su ba. Kuma kin san halin yaran yanzu tunda dama ke da kanki kince yarinyar nan uwarta take tayawa kishi ai kuwa kinga zatayi abinda yafi haka ma.’

Ta sake share kwalla sannan tace

‘Nima abinda tayi bai bani haushi ba, abinda ubanta yayi ne ya fi bata min rai. Ai dama ba tun yau ba na gaya miki baya son su Abdallah suje don idan suna nan yayi ta muzurai kenan yana faman saka ni aiki. Da zarar na mike zanyi hidimarsu sai ya san abinda yace nayi masa, har gara ma idan ba kwanana bane sai mu sake ni da su. Yanzun kuma yana kallon shatin yatsun Yusra a kan fuskar Farha amma bai wani damu ba, bayan yaje sun tsaro masa karya da gaskiya ya dawo yace min wai Farha ta cewa Yusra mai siffar karuwa. Don Allah Umma yaushe Farha ta san karuwa, ai ko kalmar siffa ma bana jin Farha ta san ma’anarta; shekarunta hudu fa kacal.’

Anti Uwani tace

‘Ai ce masa zasuyi ke kika gaya mata shi yasa zai hau kai ya zauna, idan dai son kai ne ai kika sami namiji kin kure.’

Umma ta harari Anti Uwani sannan ta dubi Aisha tace

‘Duk wannan ba wani abu bane, wannan ya wuce ai sai ki tashi ki koma dare yana yi.’

Aishan ta kalli Anti Uwani tace

‘Shi da kansa yake yaba tarbiyyata amma yanzu da yake yaso son zuciya ce min yake yaransa basu iya zagi ba nawa ne suka iya.’

Tayi kwafa.

Anti Uwani ta dawo kusa da ita ta dafa kafadarta tace

‘Yi hakuri kin ji Shatu, sai dai su gani a kansu ba dai mu ba.’

Haka suka sakata a gaba sunata bata baki, zuwa tara da rabi ta taso ta fito ta kamo hanya.

Bayan ta fita Umma ta dubi Anti Uwani tace

‘Uwani ki daina taya yarinyar nan rigima fa, kin santa da taurin kai ga fushi.’

‘Yaya wallahi dole na tayata, duk taurin kanta da ake gani amma tana da hakuri. Ba karamin kureta akeyi ba kafin ta fara fushin da taurin kai, Allah ne kawai ya san abubuwan da take hadiyewa a wannan gidan don haka duk abinda ta fada ai dole na tayata Yaya.’

‘Ai shikenan.’
…………
Har karfe goma na dare yana zaune shi kadai a dakinsa, babu abinda yakeyi kawai tunani kala-kala suke yawo a kwakwalwarsa. Tunda ya zauna yake kallon wayarsa yana jiran Aisha ta kirawoshi tace masa ta dawo amma har yanzu shiru. Ya sake kallon lokaci nan take ya lalubo lambarta ya danna mata kira. Wayar tana dab da tsinkewa ta amsa, yace

‘A’eesh, kin dawo kuwa?’

‘Eh, tun dazu har ma na kwanta.’

‘Ok bari na rako miki Rukayyan.’

‘Ka barta kawai dare yayi, ma hadu da safe.’

Sukayi shiru na dan lokaci kadan, ya ma rasa me zai ce don ya san tabbas bai kyautawa Aisha ba. Ya gaji da sauraron numfashinsu yace

‘Zaki iya kwana ke kadai to?’

‘Eh.’

Ya fahimci gajiyawa a cikin muryarta kuma shima bashi da sauran abinda zai ce mata don haka yayi mata sai da safe, suka ajiye waya.
Yanda Aisha ta kwana tana fushi da shi haka ya kwana yana fushi da Zahra, duk yanda ta kai ga shisshige masa ya ki ya saurareta har ta gaji ta kyaleshi.

Ko da gari ya waye tun wajen tara saura ya gama shiryawa don yana da daurin aure, yana fatan kafin lokacin Aisha ta tashi; don bata tashi da wuri ranakun Asabar da Lahadi; in ya so sai ya shiga wajenta kafin ya wuce.

Yana tsaye a gaban mudubi yana gyara karin hularsa Mommy ta shigo dakin, ta wuce ta zauna a kan gado don ta kula har yanzu fushi yakeyi.

Ya gama gyara hular ya daura agogonsa ya dauki mukullan motarsa tare da wayarsa da suke ajiye a kan mudubin ya dubeta yace

‘Kada ki ajiye min abincin rana a gidan Hajiya zan ci, sai da yamma zan dawo.’

Da murmushi a fuskarta tace

‘To, ka gaida Hajiya da mutanen gidan.’

Ba zata iya hakura ba don tana ganin wannan itace damarta ta karshe idan bata yi masa magana yanzu ba abun yana kara wucewa haka za ayi ta cutarsu ita da yaranta. Don haka har ya juya ya nufi kofa ta tashi ta murmushi ta biyo shi, sai da ta zo dab dashi ta kirawo sunansa

‘Abban Sadik.’

Ya juyo ya bita da kallo alamar yana sauraronta, ta dan bata rai sannan tace

‘Mu sai yaushe za a kawo mana namu kajin ni da yarana?’

Da mamaki a fuskarsa yake kallonta yace

‘Kaji kuma? Wannan watan da akayi cefane ba a kawo harda kaji bane? Ko da yake idan ma sun kare ai sai kuci nama ko kifi tunda duk an kawo ko?’

Ta kara shan kunu

‘Kajin da aka kaiwa Aisha ta soyawa yara su nake magana, wadannan ma ai sun gani ko ladan ganin ido ai sai a bamu.’
Binta kawai yake da kallo yana mamaki, ya gyara tsaiwa ya kare mata kallo. Ya ma rasa me zai ce mata, yace

‘Allah ya sauwake. In dai kajin da Aisha ta soyawa yara ne ba ni na saya mata ba, kudinta ta sa ta siyo don ta soyawa yaranta kuma da ta soya duk yaron da yake cikin gidan saida ta bashi. Idan kina da kudi kema ki bayar a sayo miki kaji ki soya ku cinye ko kuma ragowar na miyar ki soya muku idan kun cinye sai kiyi miyar lami.’

Kafin tace wani abu ya juya ya fice; idonsa har rufewa yake saboda takaici da mamakin Zahra; Yaushe ta zama haka ne? Dama tura yaran take su gano mata abinda akeyi a gidan Aishan kenan?

A can gidan Aisha ma bai sami yanda yake so ba don haka ranar dai haka ya fita zuciyarsa a jagule.
_

Duk wanda Zahra take bi bashi wannan watan saida ta kirawo su, don haka sosai aka biyata bashi. Sai dai duk yanda ta so kudaden da ta hada su kai dubu dari uku basu kai ba, gashi bazata iya tambayar Abban ba don har yanzu bai koma kamar da da ita ba.

Ta riga ta tsarawa Abba cewa akwai kawarsu ita da Amina wadda mijinta ya rasu, don haka zasu je mata gaisuwa can Gaya. Ko da yace mata Malam Sule ya kaita sai ta ce masa da motar Amina zasu je don su uku zasu je. Don haka ya bata izinin zuwa.
__

Ranar Lahadi suka yi shirin tafiya Gaya, tun karfe takwas da rabi na safe tasa Malam Sule yazo ya kaita gidan Amina. Daga can suka kama hanya a motar Aminan.

Idan aka shiga Gayan ma sai an nufi can bayan gari kamar za a fita daga garin sannan a hau wani kwararo. Dan karamin kauye ne, duk da gidan ba wani babba bane amma dai yafi duk gidajen da suke kewaye da shi girma.


A share farfajiyar gidan take tsaf ga rumfuna kamar guda hudu wanda kowacce cike take da almajirai ana ta karatu.

Malam ya san da zuwansu don haka motarsu tana tsayawa wani matashi a cikin almajiran ya taso da hanzari ya taresu. Ya jagorancesu cikin gida.
Suna shiga soron farko ya nuna musu kofar wani daki yace

‘Hajiya ku shiga nan Malam yana jiranku.’

Suka daga labule suka shige da sallama yayinda shi kuma almajirin Malam ya juya ya koma waje.

Da fara'a Malam ya taresu; su biyu ne a dakin shi da wani babban almajirinsa wanda shi yayi yawo da yawa don haka ya tara ilimi sosai musamman irin wannan na kauce hanya.
A kan dadduma suke zaune, yaron Malam ya nuna musu daya daddumar wadda take dama da Malam yace su zauna. Akwai ruwan roba daga gefe guda a dakin ya balle ledar ya dauko guda biyu ya ajiye musu a gabansu.

Suka gaisa da Malam, yayi gyaran murya ya dubi Zahra

‘Hajiya Allah ya nufa kin zo kenan?’

‘Wallahi Malam.’

‘To

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login