Showing 96001 words to 99000 words out of 166068 words
zan je na taya Anti kwana.’
Ta kara hade girar sama da kasa sannan tace
‘To.'
Ya mike suka fice tare da Rukayyan.
Yusra tana nan a inda suka barta, har sun kusa fita daga falon Rukayya cikin sanyin murya tace
‘Abba.’
Ya juyo yana sauraronta
‘Na dauko keken dinkina na tafi dashi, na gama holiday homework dina kuma kaga sai next week za a koma bani da aiki.’
‘To dauko muje.’
Ta ajiye jakar makarantar dake bayanta a kasa ta koma dakin kasa da gudu ta dauko keken a kwalinsa, yana jin lokacin da Yusra ta faki idonsa tayi tsaki yace
‘ba sabun ba..’
Tana zuwa kusa da shi ya karbar mata keken ita kuma ta dauki jakar suka fice.
Tunda aka shigo da keken take so a tayata ta hada amma kowa sai gwasaleta yake yi, Saddiku yana so ya hada mata amma kiri-kiri Mommy tace a dauke keken a ajiye ba za ayi amfani da shi ba sai an siyowa Yusra irinsa. Ita Yusra bata ma sha’awar dinki kwata-kwata, jaka da turaren da aka bawa Rukayyan ya fi tsaye mata a rai saboda tana jin itace babba ita ya kamata a fara bawa, amma da ta sami goyon bayan Mommy sai ta koma jin haushin keken ma. Don ta ciwa kanta alwashin idan dai ba a saya mata irinsa ba sai ta lalata shi.
Ko da suka fita da keken nan ba karamin dadi Rukayya taji ba; don dama tunda taga yanda Mommy take gwalewa ta yanke shawara gidan Antin zata mayar da shi idan ya so in tana can tayi dinki ko idan Amira ta zo.
Bayan ya kaita ya yiwa Aishan sallama kuwa yana fita suka saka keken a gaba ita da Aisha saida suka hada shi wajen dayan dare sannan suka kwanta.
--------
Duk yanda Mommy ta so morewa a wannan daren bata samu ba domin yana dawowa ya rufe gidan ya shige dakinsa ya kulle. Haka ta kwana tana takaicin yanda yake Raina mata hankali.
__
Duk wata tsaraba da Abban ya siyowa yara haka ya tattara ya kulle ya ajiye a gidan Aisha; tunda Zahra ta saka shi a gaba da maganganun nan yace ba zai bayar da tsarabar don haka har abinda ya siyo mata duk ajiyewa yayi. Wasu ma duk sai ya kwashe ya kaiwa mutan gidan Yaya Bello wadanda ba zai iya bayarwa ba kuma kamar computer da wayar da ya siyowa Yusra da niyyar in ta gama SS 3 ya bata duk ya tattara ya ajiye.
Saida sukayi sati da dawowa sanna Zahra ta samu ya dan fara sauraronta, don haka nan da nan ta samu ta sanar da shi ana biki a gidan su Amina zasu je. Ba tare da wata matsala ba ya bata dama.
…..
Kwanan su Abba goma sha uku da dawowa Zahra ta shirya ta fice ranar Alhamis da sunan ta tafi biki, karfe goma na safe suka kama hanyar Doguwa.
Sun ci sa’a wannan zuwan babu kowa a wajen don haka kai tsaye aka kaisu dakin da suka gurfane a gaban bokan.
Bayan sun gama yi masa bayani da sanar da shi Abban ya dawo yayi gyaran murya yace
‘Kudin aiki Naira dubu dari hudu.’
Ya tura musu bakar tasa Zahra ta juye kudin dake cikin jakarta wanda dubu dari biyar ne ta taho da su.
Dariya ta karade dakin. Daga baya bokan yace
‘Ranar Lahadi da daddare zamuyi aiki, ke kuma ki tabbatar ya kwana da janaba a wannan daren. Idan kikayi haka gari yana wayewa ba zai sake tuna wata mata ba.’
Dakin ya sake cika da dariya. Bayan dariyar ta lafa tace
‘Um ba a dakina zai kwana ba ranar Lahadi sai dai litinin.’
Ya saki wata kara wadda har ta firgita su, sannan yace
‘Ba ma aiki ranar litinin, Alhamis da Juma’a . Don haka ranar asabar da daddare ki tabbatar ya kwana da janaba mu kuma za muyi miki aiki.’
‘To hakan yayi.’
Ya ware tafi hannunsa sama, nan da an aka jefo masa wani mulmulallen farin gilas mai fasalin kwai. Ya turowa Zahran yana fadin
‘Ki saka wannan a wannan bakar robar ta gabanki ki rufe, ki nemi waje ko ina ne ki boyeta. Matukar ba a bude wannan robar ba to sai yanda kikayi da Yusuf, domin ko Sallah kika ce kada yayi to bazai yi ba balle wani aiki na duniya.’
Ta karba ta fara kici-kicin sakawa a robar da take gabanta yayinda dakin ya rude da dariya.
‘Ku tafi, ku tafi.’
Haka aka dinga nanata musu har suka fice daga dakin suka kamo hanya.
Abun ya dan so ya tsorata Zahra sai dai idan ta tuna zai manta da Aisha a rayuwarsa sai abun yayi mata dadi. Ta dai san ta kashe kudi da yawa, domin kusan miliyan guda kenan wancan zuwan da wannan. Gashi ragowar kudaden da take shirin karawa a business dinta duk tana ta facaka da su.
……….
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
31
A tsaye take a tsakar dakinta tana tunanin inda zata boye bakar robar nan da boka ya bata. Ta duba robar ba zata shiga bayan wardrobe din ba kuma bata so ta saka ta a cikin wardrobe din saboda waje ne da take yawan budewa. Kayan dakin nata irin Turkish Furniture din nan ne masu girma da nauyi don haka kusan ba a taba motsasu ba tunda aka kafa su. Nan take dabara ta fado mata.
Ta karasa ta ajiye robar a kan durowar gefen gadon sannan ta dage iya karfinta ta daga katifar daga daidai kan gadon, ta daga katakon ma sannan ta dauko robar a hankali ta ajiye a kasan katakon. Ta mayar da komai ta gyara gadonta; a nan kam tana da yakinin babu wanda zai motsa mata gado sai idan itace ta saka kuma babu mai duba mata.
Ta yiwa kanta murmushin jin dadi sannan ta fice daga dakin.
___
Ranar Juma’a ce don haka da yake Yaya Zainab bata zo wa Aisha sannu da zuwa ba sai yau ta zo. Gaba daya ita da su Amira suka zo da yake babu islamiyya.
Lokacin da direbansu ya saukesu a bakin gate din gidan Aisha yayi dai-dai da lokacin da Malam Ali ya kawo su Rukayya da makaranta.
Ummi ce ta tabo Rukayya tace
‘Yaya Rukayya ga kawarki can Amiro ta zo.’
Yusra ta balla musu harara duka su biyun, don haka sukayi shiru.
Har suka shiga gida Rukayya tana tunanin yanda zata samu ta je wajen Amira; tana son taje ta nuna mata keken dinkinta don ita Amiran tana da nata ta ma fi Rukayyan iya dinki, amma ta san ba za a barta taje ba.
Idan Abba ya rakata da daddare ta taya Aishan kwana, da safe idan ta fito suka tafi makaranta to Mommy ta haramta mata komawa gidan har sai wani daren idan Abban yayi magana. Idan bai yi magana ba to ita bata isa tace zata je gidan ba.
Yau din dai haka kawai take so taje gida su dan taba dinki kafin su Amira su tafi.
Ta riga ta fidda rai don in dai Yusra taga fitarta to ta san ko ba gidan Anti Aishan taje ba cewa Mommy zata yi can taje, kuma ta san tabbas sai Mommy ta ci mutuncinta.
Wajen karfe uku babu kowa a falon daga ita sai Ummi, ta mike ta dauki hijabinta. Ummi ma duk da bata san ina zata je ba ta mike tace
‘Yaya Rukayya zan raka ki.’
Don haka ta bita a baya suka wuce.
Suna shiga ta gaida su Anti Aishan a falo ta ja Amira suka kule a daki suna ta fama da keke, ita kuma Ummi ta zauna wajen su Hanan kannen Amira a falo suna wasa.
Nan sukayi la’asar sai wajen biyar na yamma sannan direban su Amira ya dawo ya kwashesu, suna tafiya Rukayya tayiwa Aisha sallama ta ja Ummi suka fice.
Ta san zata sha fadan Mommy don haka a hankali ta shiga gidan tana fatan Mommy bata nemeta ba.
Tana shiga falon taci karo da Mommy a zaune tare da Yusra da Nana, da sallama ta shiga amma babu wanda ya amsa sallamarta. Kallon da Mommy take mata ya tabbatar mata tana cikin matsala. Kafin ta gama tsara karyar da zata gayawa Mommy muryar Mommy din ta katse mata tunani
‘Zo nan Rukayya.’
Cikin sanyin jiki ta karasa ta tsuguna a gaban Mommy tace
‘Gani Mommy.’
‘Daga ina kike?’
‘Um Mommy gidan Anti Aisha daman naje wajen Amira, sun ma t…'
Kafin ta rufe baki ta dauketa da mari, ta dafe kumatun bakinta a bude ta sunkuyar da kai tana fitar da kwalla. Ummi da take tsaye ta raba ta wuce bayan kujera saboda kada a mareta itama. Cikin fushi Mommy ta cigaba
‘Ba na hanaki zuwa gidan matar nana ba? Itace ta haifar min ke ne ko me da zan ce kada ki fita ki saci jiki ki fice harda daukar ‘yar rakiya? Uban me take baki idan kin je da bazaki zauna cikin ‘yan uwanki ba? Wallahi ki shiga hankalinki Rukayya, idan ba haka ba zamu sa kafar wando daya dake a gidan nan. Tashi ki bace min da gani kafin na mangareki.’
Ta mike tana share hawaye ta nufi dakinsu na kasa.
‘Ummi.’
Mommy ta kirawota cikin tsawa, ta leko daga bayan kujera tana zare ido
‘Idan na sake ganin kin shiga wannan gidan sai na zaneki kuma na karya kafafunki.’
A sanyaye tace
‘Ba zan sake ba Mommy.’
Yusra tace
‘Mommy ba fa laifinta bane, waccan uwar shisshigin ce don ita kowa ma bata ki yaje gidan ba tunda bata gane mai sonta da mara sonta.’
‘To zanyi maganinta a cikin gidan nan.’
Ta tashi ta haye sama ta barsu a nan Yusra tana kara jawa Ummi kunne.
………….
Rukayya tana shiga dakin su ta wuce bandaki ta turo kofa, don ta san idan ta zauna a dakin ma yanzu Yusra zata biyota ta zo tana gaya mata maganganu.
A bushe bandakin yake don haka tana shiga ta zauna a kasa daga gefen bahon wanka ta hada kai da gwiwa ta kara rushewa da kuka.
Mommy bata dukansu, ba karamin laifi mutum zai yi a gidan nan ba Mommy ta dokeshi amma ita gashi yau Mommy ta mareta kawai saboda ta je gidan Anti Aishan. Ta san Mommy din ta hanata zuwa amma ai Abba ne yace ta dinga zuwa; ko kuwa Mommy kawai ya kamata ta dinga yiwa biyayya? Ta san Yusra ce zata zauna ta tsarawa Mommy karya da gaskiya kuma ita ta zuga akayi mata wannan marin; duk da haka kuma ta san Mommy din ta fi son Yusra a kanta. Tunda da bakinta mommy din tana fada Rukayyan ‘yar Abba ce, kuma duk wata mu’amalar da take yi da su yana nuna tana son duka yaran fiye da yanda take sonta. Don ita ko doguwar hira bata fiya hadasu da Mommy ba saboda da zarar ta fadi ra’ayinta sai Mommy din su hadu da Yusra suce bata da hankali bata san ciwon kanta ba, ko kuma idan tayi wani abun Mommy tace wai bata da wayo kamar Anti Murja ko tace halin Abbanta ta gado.
Ta sa hijabinta ta goge hawayenta, bata jin dadin yanda Mommy take mata; ta kasa fahimtar abinda ya sa Mommy take ganin kamar Anti Aisha cutar dasu zatayi don ita abubuwa da yawa na ‘yan mata a wajen Anti Aishan take koya saboda tana sauraronta tayi surutu son ranta. Ba zata iya kinta ba ko don Abbanta, sai dai kawai tana son Mommy ta so ta ko Yaya ne don a yanzu zata iya cewa Mommy bata sonta; duk da abu ne da ta sani tun kafin Abba ya auro Aisha.
Ta mike tsaye ta fara wanke fuska tana fatan Allah yasa kada Yusra ta kulata don yau idan ta kulata duk wani haushi da take ji sai ta huce a kanta.
Haka ta wuni cikin damuwa har dare yayi Abban ya rakata gidan Aisha, ita kanta Aishan tana ta faman tamabayarta ko bata da lafiya saboda yanda ta ganta; sai kawai tace mata cikinta ne yake ciwo amma ta sha magani. Haka ta kwana babu walwala.
___
Tunda suka dawo daga wajen boka take tunanin yanda zatayi ta sa Abban Sadiku ya kwana da janaba. A iya zaman aurensu da shi zata iya cewa idan banda satin amarcinsu na farko bai taba kwana da janaba ba, duk yanda ya kai ga shagala sai yayi wanka yayi alwala. Ko da zai sake dawowa to sai dai idan yayi wanka kuma yana gamawa zai sake yin wanka. Gaba daya tunaninta ya kare, gashi yau Juma’a ta rasa ta ina zata kama abun.
Tana zaune a dakinta a kan dadduma ta idar da sallar Magriba dabara ta fado mata, gara ta kirawo Amina don ta san ba zata rasa dabara ba.
Tana bugawa tayi sa’a, bugu daya Aminan ta dauka, bayan sun gaisa ta sanar da ita halin da ake ciki. Tace
‘Ai da kin gaya min tuntuni, kin manta ne da Hajja. Akwai wani yaji da zata baki da kuma turare, wallahi in kikayi amfani da shi to sai dai kawai nace kema ki shirya don zai yi ta aiki ne daga ya juye zai sake laluboki. Ba zai ma sami sukunin wanka ba. Bari nayi mata waya, ko da yake kema ki kirawota na san gobe da safe zata iya kawo miki.’
Nan take tayi mata sallama suka ajiye waya ta kirawo Hajja, tayi mata bayanin duk abinda take so ita kuma tayi mata alkawarin gobe kafin azahar zata kawo mata kayan aiki.
Ta ajiye wayar tana murmushi.
Sai yanzu ne ta sami natsuwa, fatanta kawai kada a sami wata matsala musamman idan Abban yaki bata hadin kai. Amma dole ne tayi iya yinta saboda ba zata yarda Aisha ta rabata da mijinta ba, gashi yanzu kiri-kiri ta fara janye mata hankalin yara. Tana mamakin abinda ya sa Rukayya take son matar nan duk da dai ta san karshenta a wajen kwanan da take zuwa tayawa za a bata abubuwan da zasu saka a mallaketa.
Tabbas dole ta mike tsaye ta raba Rukayya da matar nan.
Tana matukar son Rukayya tun lokacin da ta haifeta kuma har kawo yanzu, duk cikin yaranta babu wanda yake kama da mahaifiyrta kamar Rukayya, domin da ta haifi Rukayyan ma sunan mahaifiyar ta taso sakawa. Sai dai lokacin da aka haifi Rukayyan Abbanta ya tafi aikin Hajii don haka Yaya Bello ne a kan komai, shi kuma bai yi shawara da kowa ba ya saka mata Rukayya. Wanda Abban yace hakan yayi, don haka suna ya bita. Shine saida aka haifi Ummi aka sa sunan mahaifiyar tata.
Duk da haka Rukayyan tana fara girma dabi’unta suka koma kamar na babanta. Ga saukin kai da hakuri, komai zata ce ba komai bane, ga rashin wayo. Sai kuma ya zama ta fi shakuwa da Abban saboda ya fi sauraronta fiye da Mommy din.
Amma yanzu duk abinda ta gani a tattare da Rukayya gani take Aisha ce take sakata don haka ta yi shirin dole sai ta rabasu ko ta wane hali.
---------
Ranar asabar tun kafin azahar Hajja ta kawo mata abin da ta bukata; wani gari ne dan kadan wanda tace mata gaba daya zata juye masa a miya sannan kuma da wani turare wanda zata shafa a jikinta dai-dai inda zai dinga shakar kamshin saboda kamshin turaren zai dinga kara kunnashi koda ya gama biyan bukatarsa. Sannan kuma ita kanta aka bata kayan da zata yi amfani da su saboda kada ta gaji.
Yana matukar son couscous da miyar alaiyahu wanda ita kuma bata son couscous din, don haka ma bata yawan yin couscous. Amma yau da yake da akwai abinda ta shirya sai ta dafa masa couscous din da miyar alaiyahu wadda ta sha kifi da nama duk don ta badda kama.
Wajen karfe takwas da rabi na dare bayan ya dawo daga sallar isha’i ya raka Rukayya gidan Aisha don ta tayata kwana kamar yanda ya saba. Kafin ya dawo ta riga ta jera abincin a kan dining table. Bayan ya zauna ta zuba masa abincin ta ajiye sannan ta wuce kitchen ta zubo indomie din da ta dafa domin ta ci, ta zauna a kujerar da take gefen tasa. Ya dubeta yana dariya
‘Yanzu fa sai kice indomie ta fi couscous din nan dadi ko?’
Tayi dariya
‘Ai ko ban fada ba ma haka ne, wallahi ni ban san me kike ci na dadi ba a cikin couscous gara nayi ta cin indomie.’
‘Allah sarki, kin bar dadi fa.’
Haka ya cinye couscous din nan yana ta faman yi mata surutu har sai da ya kara.
Bayan ya rufe gidan ya dawo ya zauna a falon sama tare da ita suna hira yayinda Sumayya da Ummi suke wasanninsu.
A al’adarsa sai wajen sha daya na dare yake kwanciya amma yau tun wajen karfe tara ya fara neman dalili, sai dai Sumayya ta ki yin bacci. Don haka ya dubi Mommy yace
‘Bari naje idan kin shirya kya sameni a dakin, naga mutuniyar taki yau hira take ji.’
Yana shigewa ta bi bayansa da dariya domin ita ta fuskanci abinda ya tasheshi da wuri don tana kula da yanda yake ta wasu muzurai da wasu mutsu-mutsu.
Sai da ta gama yangarta ta gama nata yi lokacin wajen karfe sha daya, ya gama zakuwa ta yanda shi kansa mamakin abinda ya janyo masa hakan yakeyi sanna ta shigo dakin. Tana shiga dakin kuma ta yarda zaninta a gefen gadon da yake kwance ta tsiri wata kaiwa da kawowa. Ta shiga bandakinsa tayi brush, ta fito ta kama zarya kamar mai neman wani abu a daki. Sai da ta tabbatar ya gama zakuwa sannan ta kashe fitila ta kwanta a kusa da shi. Tana kwanciya ya fada mata kamar wani mayunwacin zaki.
Tun sha biyun dare suke abu daya amma ya kasa gamsuwa, ko da ya gamsu kafin ya