Showing 78001 words to 81000 words out of 166068 words

Chapter 27 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25409

wai ya tafi gidan matarsa kuma a chan zai kwana.’

Da tsananin mamaki tace

‘Kwana Yusra?’

‘Wallahi Mommy, har yanzu ma yana can don bai dawo nan ba.’

‘Um, ba zama ta barshi ya dinga kwana inda kuke ba tunda ba na nan, shine ta janye shi ta barku ku kadai? Ai shike nan.’

‘Wallahi Mommy, yana can abunshi.’

‘Babu komai, ki cigaba da kular min da gidan kiga zuwa lokacin da zai dawo. Duk wani abu da yayi zuwa na dawo ki kular min. Zan kirawo ki da safe.’

Suka yi sallama suka ajiye wayar.

Yusra ta sauko ta mayarwa Rahma wayarta suka cigaba da sahur dinsu.

Duk da Rahma bata san menene dalilin da ya sa Yusran ta kirawo Mommy ba amma ta zargi cewa zata gaya mata ne yau Abbansu ba a nan ya kwana ba; domin tana sane da yanda duk wani motsi da akayi a gidan Yusra sai ta sanar da uwarta.


Sallah takeyi a lokacin da ta sallame ta amsa kiran Yusra, sai dai zuwa lokacin da suka gama waya da Yusran ta ma manta me takeyi. Abinda Yusran ta gaya mata ya girgizata sosai.

Ya za ayi ace Abban ya tafi kwana gidan Aisha? Ita da a gaban idonta ta ga cewa ya kasa shiga gidan. Kuma yaron Malam ya tabbatar mata muddin wannan abun da ya bata yana binne a gidan Aishan to Abban ba zai taba iya shiga gidan ba, to yanzu me ya faru? Zuciyarta ta kara harbawa da sauri a daidai lokacin da tayi tunanin watakila fa Aishan ta saka an hake abun nan; lallai yarinyar nan hatsabibiya ce kamar yanda yaron Malam ya fada. Yanzu kenan Abban yana can wajen Aishan ya bar mata yaran yana jin dadi; anya kuwa Aisha ba so take ta raba Abba da iyalansa ba? Ai kuwa doke ta dauki duk wani mataki da ya dace don ba zata zauna wata banza tazo ta rabata da mijinta uban ‘yayanta ba.
Ta dauki wayarta ta fara laluben lambar yaron Malam, sai dai ta tuna a babbar wayarta kawai take da lambarsa wadda kuma a gida ta barta ta taho da karamar duk saboda kada tazo da babbar wayar ta hanata ibada yanda ya kamata.


Tayi tsaki a fili, Falmata wadda suke daki daya tace

‘Hajiya Zahra ya dai, lafiya dai yaran suke ko? Naga kina gama waya da Yusran kin shiga damuwa.’

‘Tsewww! Wata ‘yar matsala ce amma in Sha Allah babu damuwa.’

‘To ki barwa Allah, ai idan kana nan baka da matsala sai kawai kiyi ta roka kafin kije gidan komai ya daidaita.’

‘Umm.’

A nan Falmata ta barta ta wuce bandaki don tayo alwala ta wuce masallaci inda ragowar ‘yan dakin nasu a can suka kwana suna ibada.
__
Bayan ya dawo daga sallar asuba ya jiyo motsinsu ita da yara a kicin, bai leka ba ya wuce dakinsa ya kwanta. Bacci ne me nauyi ya kwasheshi saboda yanda ya kwana ba tare da yayi bacci ba.

Kafin karfe bakwai sun gama gyara gidan sun shirya tsaf ita da su Amira.

Bata ji motsinsa ba don haka ta san bacci yakeyi, ta dauki wayarta ta shiga kicin ta kirawo shi. Bugu daya ya dauki wayar, tana jin muryarsa ta san bacci yakeyi, tace

‘Sorry, na tasheka. Zamu je kitso ni da yara kada ka tashi kaga bama nan.’

‘Oh, to ku dan jirani ina zuwa.’

Suka tsaya a falon cikin shirinsu.

Baifi minti biyu ba ya fito falon, bayan ya amsa gaisuwar su yace

‘Kuma da sassafe zaku je kitson haka? Yanzu fa karfe bakwai tayi.’

‘Ka san na Sallah ne akwai layi, yanzu ma kada kayi mamaki mu sami wasu a wajen. Kuma sai an wanke kan an yi kitso sannan ayi kunshi, idan bamu tafi yanzu ba a can zamu sha ruwa.’

‘To sai kun dawo. Ai ban bayar da kudin kitson ba ma ko?’

Su Rukayya suka fice suka barsu. Tace

‘Babu komai dama na tanadi kudin kitson ai.’
‘To ku tafi, amma dai zan turo da kudin kitson yanzu.’

Tayi masa sallama ta wuce suka kama hanya yayinda shi kuma ya koma ya cigaba da baccinsa.

Kafin su isa wajen kitson sako ya shigo wayarta, tana dubawa taga shine ya turo mata naira dubu ashirin kudin kitsonsu ita da yaran.

Bai fi mutum biyu suka samu a wajen ba don haka nan da nan suka fara tunda sun riga sunyi booking. A da tace ba zata yi gyaran jiki ba sai bayan Sallah amma tunda taga ya turo kudi har dubu ashirin haka ta sa saida aka yi mata gyaran jiki sannan aka gyara gashin aka dandasa mata kunshi. Suma Rukayya da Amira kowacce an dandasa mata kunshi da kitso.

Sai wajen karfe hudu saura suka gama, suna fitowa suka biya ta gidan kawarta inda ta kai musu dinkinsu; leshi ne mai kyau ta siya yadi goma ta kai a dinkawa Amira, Rukayya da kuma Farha, a nan wajen kawar tata da ta bayar da dinki ta saya musu kowa jaka da takalmi sannan da mayafi. Bayan sun karba suka wuce gidan Hajiya suka ajiyewa Farha nata kayan.

Farha taso tayi bori a kan sai ta bi Mama, domin da Rukayyan da Amiran duk ta saba da su; cikin dabara Aisha ta lallabata a kan jibi ne sallah idan tayi kallon sarki ta gama Baba Abba zai zo ya kawota wajen Mommy.
Har sun zauna a mota Rukayya tace

‘Anti da ma mun taho da Farha.’

‘No, za mu bar wa Hajiya gidan ba hayaniyar Sallah. Bayan Sallah dai zasu zo in Sha Allah.’

Bayan sallar la’asar suka shiga gidan; Abba yana zaune a falo yana kallon TV tunda ranar Lahadi ce babu aiki duk da yaje gidan Zahra don ya dubo yaran sai dai bai dade ba ya dawo nan din ya zauna.

Bayan ya amsa gaisuwar su Amira suka shige dakinsu ita kuma Aisha ta shige nata dakin. Suna wucewa ya bi bayan Aisha.

Ta riga ta shiga bandakin don haka ya zauna a gefen gado yana jiranta. Bai dade da zama ba ta fito daga bandakin da alwalarta. Tana fitowa dakin ya mike tsaye

‘Aisha.’

Ta amsa yayinda ta dauki hijabinta ta fara kokarin sakawa.

‘Aisha fushi kikeyi da ni ko?’

Ya fada yayinda ya sha gabanta.

Tayi dan gajeran murmushi tace

‘A’a, ni ba fushi nake ba. Amma dai yanzu kaga ban yi la’asar ba gashi kuma an kusa shan ruwa ban dora komai ba.’

Ya bi fuskarta da kallo yayinda yanayin fuskarsa ya canza zuwa na damuwa.
Maganarta gaskiya ne, kuma ya san idan ya takura zai iya karya musu azumin ma don haka ya ja baya yana fadin

‘Hakane. Nima a nan zan sha ruwa ki ajiye min abinci na.’

‘To.’

Ya wuce ya koma dakinsa.

Nan da nan ta idar da sallah ta fito suka shiga kicin ita da su Rukayya.
……….

Duk yanda ya zata zai samu ganawa da Aisha abun ya ci tura, idan ta zuba abinci to sai ta zauna cikin yara ta ci nata. Da daddare kuma idan ya fita sallar tarawih duk saurinsa kafin ya dawo ta zuba yara a daki sun kwanta har ita.

Tabbas da Rukayya ce ita kadai da tuni yace ta koma gidansu, to amma Amira ma tana nan. Sun yi bake-bake sun hanashi sakat a gidan ita kuma Aishan taki ta bashi fuska. Lokutan da yake samunta ita kadai kuma yawanci da yamma na, ya san idan ya takura sai ya karya musu azumin don haka ya hakura wadannan kwana biyun tsakaninta da shi sai kallo daga nesa; gaba daya taki sauraronsa.
___

Ranar Talata aka tashi da sallah karama; tun asuba ita da su Rukayya suka fada kicin, da yake abincin ba mai yawa takeyi ba nan da nan suka hada tuwon shinkafa da miyar gyada, ga kuma funkaso da farfaesun kaji. Amira ta hada kunun aya suka zuba a firji.


Karfe takwas saura Abban ya fito a shirye, yayi mata sallama sannan ya wuce gidan Zahra.


Suma duk sun gama wani shirin Sallah sai tuwo wanda Jummai take karasa kwashewa. Sadiku kawai ya dauka suka wuce masallacin idi.

Bayan sun dawo daga idi ne kamar yanda aka saba duk shekara ya kirawo Sadiku ya bashi abincin sallar gidan Aisha ya hada da na gidan Mommy yace Ali direba ya kaishi tare da Nana da Ummi su kaiwa Hajiya.

A falon Aishan ya zauna ta kawo masa abinci; ta sha kwalliyar sallarta cikin leshinta me ruwan hoda, tayi kyau matuka sai dai kawai yanda take daure fuska ne yake gundurar dashi.

Yana zaune a falo yayinda Aishan take kwashe kwanukan da yaci abinci Rukayya da Amira suka fito daga daki, bayan sun gaisheshi yace

‘Iyye, anko kuka yi ne keda kawar taki Rukayya?’

‘Eh Abba Anti ce tayi mana wannan kayan.’

‘Iyye ‘yan man Anti. Bari ni kuma na baku barka da da sallah kada ayi ta yawo jakar ‘yan mata ba ko sisi.’

Ya zaro sabbin kudi 'yan Naira hamsin ya basu kowa dari biyar, sukayi godiya suka wuce kicin inda suka jiyo motsin Aishan.

Suna shiga Amira ta mariraice tace

‘Um Anti don Allah ki bamu kudin mota muje gidan Anti Hida, itama Rukayyan tana son zuwa wallahi.’

Ta kyalkyale da dariya

‘Lallai yaran nan, na baku kudin mota ku tafi a motar haya ko? To ba inda zaku je. In dai cikin gari ne na gaya muku ku shirya gobe sai muje ko kuma ku bari da yamma ma je tare.’

Amira ta sake mararaicewa

‘Anti don Allah, wallahi zamu gane ko Rukayya. Kinga Anti idan bamu je da wuri ba kafin muje duk su Farha sun je kuma Baban Anwar zai kai su cikin gidan sarki banda mu.’

‘To ke Amira duk shekara ai dake ake zuwa gidan sarkin menene idan yau daya baki je ba, kya je da Babbar sallah.’

‘Anti da Rukayya nake so na nunawa bata taba shiga gidan sarki ba ita.’

Kafin ta basu amsa Abba ya taso ya tsaya a bayan su, yace

‘Wai ina za aje ne ake ta magiya haka.’

Aishan ce ta amsa

‘Wai gidan Zahida suke son zuwa a motar haya don bazasu jirani muje gobe ba.’

‘A’a gidan Zahida ai ba matsala bane, bari na kirawo Aliko ya kai ku in ya so idan kuka gama sai kuyi waya na turo shi ya dauko ku.’

Gaba daya suka hada baki suna masa godiya, suka koma dakin da gudu suka fara shiri.

Ta ajiye kwanukan da take kifewa ta nufo kicin din da niyyar fita tana fadin

‘Bari na shirya sai mu tafi tare in ya so gobe na huta.’

Tana zuwa zata wuce ya dan matso ya takureta a bakin kofar ya kawo bakinsa kusa da kunnenta ya rada mata

‘Ban barki ba.’

Ya hura mata iska a kunnen nata har ta dan noke sannan ya wuce inda ya taso ya dauki wayarsa ya kirawo Aliko; wanda dama yana gidan Mommy.

Ta karasa ta ja kujerar dining table ta zauna ta dafe goshi tana tunani.

UWAR SADDIKU


Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)


27

Takaicinsa ne ya kuleta, tunda take aurensa bai taba cewa ya hanata fita unguwa ba sai yau. Ta san manufarsa amma bata jin zata iya bashi hadin kai; haka kawai matarsa ta dawo ya sake mantawa da ita.

Tana nan su Amira suka fito sukayi mata sallama suna ta jin dadi suka fice.

Ta mike ta shige dakinta ta turo kofar.

Tana jinsa yana nemanta bayan ya sallami direban. Sai da ya duba kichin da dakinsa sannan ya shigo dakin nata.

Tana kashingide a gefen gadonta ta jingine kanta jikin gadon; bata amsa sallamar da yayi ba haka ya karasa inda take.

‘Aisha.’

Ta share hawayen da yake fuskarta tana shesshekar kuka. Da sauri ya karasa ya zauna a gefenta cikin matsananciyar damuwa.

‘Aisha kukan me kike yi? Don na hanaki fita ne kike kuka? In dai wannan ne idan nayi sallar la’asar s na kaiki da kaina.’

Ta sake share hawaye ta muskuta ba tare da tace masa komai. Sukayi shiru na dan lokaci yana tunanin ta inda zai fara.


Ya gyara zama ya dafa cinyarta sannan yace

‘Don Allah ki daina kukan nan Aisha, kin san bana son damuwarki.’

Suka sake yin shiru ba tare da ta motsa ba, ya gaji da sauraron ta tayi magana batayi ba. Ya dawo gabanta ya tsuguna daga gaban gadon yanda zai dinga ganin fuskarta. Yace

‘Aisha don Allah kiyi hakuri, ki gaya min me ya saki kukan nan. Idan rashin zuwa wajenki ne da bana yi wallahi ba yin kaina bane, abun ne yafi karfina. Yanzu kuma da kika ganni Allah ya kawo karshen abun ne don malamin da ya warware abun ma yana tunanin aljanu ne ko tsafi, ai sai mu godewa Allah da abun ya tsaya haka ko? Kiyi hakuri Aisha, kin san ba zan taba gudunki ba.’

Suka sake yin shiru na dan lokaci.

‘Aisha, don Allah kiyi hakuri ki daina fushin nan kin san bana son kukan ki kuma bana son kina fushi da ni. Kiyi hakuri kin ji.’

Ta kalleshi yanda ya tsuguna a gabanta ta share ragowar hawayen fuskarta tace

‘Ni ba fushi nakeyi ba.’

‘To me yasa ki kuka? Um?’

Ya taso ya dawo kan gadon gefenta, ya kama hannunta, tana nokewa yana jan hannun yana fadin

‘Bana son kukan nan.’

So yake ta saki jiki ya janyota jikinsa amma ta ki, don haka ya kara dagewa ya janyota har saida ta dan fado jikinsa. Ya sa hannunsa yana goge mata hawayen, daya hannun kuma yana janyo kafadarta don ta kara kwantawa a jikinsa.

‘Shikenan, ni dama ba fushi nayi ba. Amma dai ina so ka koma can gidan idan Mommy din ta dawo sai ka fara rabon kwanan ta kanta sai a cigaba.’

Ya leka fuskarta suka hada ido, yace

‘No, ai ba sai an yi haka ba tunda dama kwanan a rabe yake ko?’

Ya dan muskuta ya kawo bakinsa daidai kunneta sannan yace a can kasan makoshinsa

‘Kin san fa nayi kewarki ba kadan ba…'

Ya cigaba da lalube jikinta sako da Loko, tun tana kokarin kwacewa har ta hakura ta bada kai bori ya hau.

Nan suka balbalce har aka fara kiran sallar la’asar; yana ta tsara mata dadadan kalamansa na lallashi da ban hakuri.

‘La’asar fa nake ji kamar, ko azahar fa bamuyi ba.’

Ta fada tana shirin mikewa, yayi murmushi yace

‘Subhanallah, kin san an fara kiran azahar lokacin da na shigo kuma sai na manta.’

Nan da nan suka fada wanka.

Sai da suka shirya suka yi Sallah sannan ya sanar da ita ta kirawo su Rukayya tace idan anyi sallar isha’i zai kaita ta su daukosu.

Ya san duk halin da aka shiga dole ‘yanuwanta sun sani don haka zai yi amfani da wannan damar ya nunawa ‘yan uwanta cewa komai ya dawo dai-dai.
__

Tun washegarin Sallah yara suke shirin taren Mommy, don ya zama saura kwana biyu kenan ta dawo. Ko ina an share an goge tsaf banda dakinta wanda ta bayar da umarni kada a bude mata.

Rukayya ta hada kayan hadi zata yiwa Mommy cake, ta so ace ita da Amira ne zasu yi cake din sai dai tana tsoron ta shiga da Amira gidan Yusra tayi mata wulakanci don ta san Amiran ma ba zata dauki raini ba musamman tunda kusan sa’ar Yusran ce. Tana hada kan kayan cake din Yusra tana mata dariya a kan bata iya wani cake ba ta bari kawai suyi order kada ta bawa Mommy kunya; ita dai ta kafe a kan lallai sai tayi cake.
Kuma daga karshe da tayi cake din kowa sai da ya yaba.
…………

Wunin ranar Sallah gaba daya tana ta faman kiran Abban yana gaya mata baya tare da yara, bai gaya mata inda yake ba amma ta san yana gidan Aisha. Ta gaji da wannan abun takaicin gashi bata taho da wayarta ba balle ta kirawo yaron Malam, don haka tun safe take faman kiran Amina amma bata dauka ba. Don haka kusan ba a hayyacinta ta wuni ba. Ya kamata ace taje ta karasa sayayya amma ta kasa zuwa; kudin ma duk da ta riga ta kashe mafi yawa amma dai tana jin ba zata sake kashe kudi ba don ta san idan ta dawo tana bukatar kudi sosai; a halin yanzu ma duk tunaninta yana kan yanda zata sami kudi ne don ta fara tunanin canza malami tunda shi yaron Malam kamar aikinsa baya nisan zango.

Sai dare ta sami Amina, tayi mata bayanin halin da ake ciki. Suna ajiye waya ta tura mata lambar yaron Malam.

Kauyen su yaron Malam babu network sosai don haka duk kokarinta na ganin ta sameshi basu iya magana ba; shi baya jinta kwata-kwata. Daga karshe dai ya gaji ya turo mata sako cewa suyi magana ta Whatsapp kawai. Kwana biyun nan jinta take kamar a kan kaya, don haka ba cikin nutsuwa ta karasa su ba.
-------

Ranar Juma’a itace ta kama kwana hudu ga Sallah kuma tayi dai-dai da ranar da Zahra Uwar Saddiku zata dawo daga kasa mai tsarki.

Tun dare ta kirawo Abban ta sanar da shi jirginsu zai sauka da misalin karfe biyar na yamma; ta so kwarai ya zo daukanta da kanshi a airport sai dai ya sanar da ita zai fita bayan la’asar don haka dai Malam Ali ne zai zo.

Tunda Abba ya kirawo Malam Ali direba yazo yayi aikin Sallah Malama Sule ya sami damar gujewa gidan; cikin dabara ya tsara Abban a kan a bar Malam Ali ya cigaba da kai yara makaranta yana daukosu. Don haka tun safe Abba ya sanar masa ya zama cikin shiri jirgin su Mommy ana sa rana saukarsa karfe biyar na yamma.


Lokacin yana yi Sadiku ya shige gaban mota Aliko ya ja suka kama hanyar airport.
………..

Alhaji Salihi Bello abokin Abban ne tun na kuruciya, tun cikin azumi aka yi masa ministan lafiya. Tun lokacin ya so shirya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login