Showing 159001 words to 162000 words out of 166068 words

Chapter 54 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25393

zata rike min yaran nan amana. Kuma…’


Da hanzari ya katse shi


'Uhm! Abinda ka gani game da Zahra ai ya isa ya tabbatar maka dan Adam bashi da tabbas ko?’


'Da wannan Yaya, amma ka san dan Adam kowanne da dabi'arsa fa. Wallahi a zaman da nayi da su da ace Aisha ce ta rasu ta bar min yara ba zan iya bawa Zahra rikonsu ba don na san ba zata rike min amanarsu ba. Amma ka ga Aisha, bata da matsala. In dai ta amsa tace zata yi abu to tabbas zata yi kuma cikin aminci. Matsalarta daya kafiya da taurin kai, gashi ita ko dan wayon nan da ake yiwa mata a lallabasu idan dai bata son abu to baka isa kayi mata wayo a kansa ba idan kuma tana son abu to tana da kafiya a kansa.’


Yaya Bello ya gyada kai yace


'Hakane. To yanzu ya za ayi? Tunda ka ga da anyi sallar Magriba ya kamata mu wuce gidan nasu.’


'Wallahi Yaya ban sani ba, da ma za su dan kara mana lokaci na samu nayi tunani sosai. Ka ga fa ga dukkan alamu irin kulle-kullen da muka samu a dakin Zahra irinsu ake aika Yusran tana binnewa Aisha, kuma ai ka ga da cutarwa sosai.’


Nan ya bashi labarin yanda ya kusan shekara baya iya shiga gidan Aishan saboda wari da yanda aka hako abun warin a gidan Aishan, har ya gangaro kan sakonnin da yaji a wayar Zahran wadanda suke nuna cewa tana da hannu wajen barin cikin da Aishan ta yi har sau biyu. Cikin mamaki Yaya Bellon yace


'Ikon Allah! Lallai matar nan ta dade tana cutar da kanta, don tabbas wannan kanta ta cutar.’


Suka sake yin shiru na dan lokaci, sannan Abban ya cigaba


'Kaga yanzu ni so nake Aishan ta dawo nan da wani satin, kafin nan na gyara gidan. To amma ban san yanda zan yi da Yusran ba, duka wata dabara da nake da ita wadannan abubuwan da na ji na gani sun shafe min ita. Dama ace ita Yusran zata samu Aishan tayi mata magana ta nuna mata ba zata bata matsala ba to da tabbas na san Aishan zata yarda.’


'Haka kake gani?’


'Gaskiya Yaya haka nake gani?’


'To idan muka je wajen Baffan nata kawai ka amince musu a kan za ka dauke Yusra da Nana. In ya so ko nan wajena sai ka dawo min dasu daga baya sai ka sa Yusran a gaba ta bata hakuri. Kuma ko ma bata karbe su ba nan din sai muyi zamanmu in ya so ka barta da wadanda ta zaba.’


Ya jijjiga kai cikin damuwa


'Yaya ni bani da damuwa idan yarana suna wajenka na san lafiya za a rike min su, amma zan so ace suna cikin gidan a tare gaba daya.’


'To ya za ayi, kaga dai yanzu wadannan abubuwan da muka gani ya tabbatar maka da abinda Aishan take tsoro. Kaga ita kanta Yusran tana bukatar a tsawatar mata a sauketa daga kan waccan tarbiyyar da uwarta ta dorata a kai. Ka bari ayi hakan, idan aka kwana biyu sai a lallabi Aishan mu ga abinda hali zai yi.’


Kai kawai ya dagawa Yayan don shima bai hango wata mafita ba bayan wannan.


Yayan ne ya tsinke shirun da suka yi, yace


'Kuma idan ka koma gidan ka tara yaran gaba daya ka sanar da su cewa Aishan zata dawo gidan, ita kuma Yusra ka sanar da ita zata dawo nan saboda tana yiwa Aishan rashin kunya. Amma idan ta fi son zama a can din to ta nemi Aishan ko a wayane ta bata hakuri.’


‘In sha haka zan yi.’


Nan suka zauna suka cigaba da hirarrakinsu, sai gefin magriba ya yiwa Yayan sallama ya nufi gidan don ya shirya ya dawo su tafi wajen Baffan Aisha.


__
Lokacin da Yaya Abubakar ya sanar da su an fasa haduwa da su Abban Sadik sai da magriba Aishan da Anti Uwani har sun shirya don tafiya gidan Baffan. Da suka ji haka sai suka fasa shirin suka bari sai bayan la'asar sa je.


Can wajen azahar Zahida ta shigo gidan da yaranta. Bayan sun gaisa da Hajiya ta dawo falo inda ta zauna wajen Aisha. Kafin su gaisa ta zaro sabuwar waya a kwalinta ta mika mata tana fadin


'Ga wayarki inji Abban Afra, yace rasit din yana ciki kuma kina da canjin dubu daya da dari biyar don an dan sami ragi.’


Ta karba tana dariya


'Kai shima don Allah harda wani canji. Wallahi kamar kin san jiya saura kadan na fasa wayar nan don takaici, ko awa nawa zata yi tana caji da ka cire daga socket zata dawo babu caji, lallabata kawai nakeyi.’


Nan suka bude wayar suka kunna da yake ya riga yayi mata caji suka cigaba da dubawa. Jimawa kadan suka koma kusa da socket Aishan ta saka tsohuwar wayar tata tana duba abubuwan da suke ciki don Zahidan zata bawa ta kaiwa Abban Afra a sayar mata da ita. Ta tura hotunanta da videos wadanda take so zuwa sabuwar wayar, tana ta dube-dube tazo kan recording wanda wayar takeyi idan tana waya. Ta dubi Zahida tace


'Kinga yau naga inda wayar nan take tara min hira. Kin san nace miki kullum na gama waya sai naga an saka min recording saved amma ban san a ina ake saving ba.’


Suka fara budewa suna sauraro, wasu suna dariya don yawanci hirarrakinsu ne su biyun.


Recordings din suna da yawa sosai don haka suka dinga tsallake wasu suna bude wanda suke son ji. A hankali ta zo kan wani recording guda daya da lambar Zahra, tayi murmushi yake tace


'Ga na mutuniyarki.’


Tayi mamakin ganin recording din don a zamansu bata jin sun yi waya da Zahra ya kai sau biyar. Ta danna ta kunna suka fara sauraro kamar haka:


“‘Dama Abban Sadik ne bai shigo ba kuma na kirawo wayarsa bata shiga shine nace ko lafiya.’
‘Lafiya kalau, yayi bacci.’
‘Um, t….’
‘Kema ina baki shawara kije kiyi baccinki, idan dai mijinane Yusuf uban Sadiku to bazaki sake jin duriyarsa ba. Ya manta dake ya goge babinki a rayuwarsa, ko da me kike takama kuma ya fi karfinki, duk lokacin da kika gaji sai ki tattara kayanaki ki koma gidanku. Kuma don Allah kada ki sake kirana a irin wannan daren muna kwance da mijina.’”


Zahida tace


'Ta kafawa kanta hujja ta tafi ta bari a duniya, aikin banza.’


Aishan tace


'Uhm.'


'Kada ki goge tura a sabuwar wayar, kin san fa in an jima muka je su Baffa kokari zasuyi ki koma ki zauna da wannan muguwar yarinyar tata. Wannan zai iya zame miki hujja tunda duk abubuwan da tayi miki abubuwa ne da babu wanda ya gani.’


'Hakane.'


Ta tura sabuwar wayar suka cigaba da abinda sukeyi.


Sai can wajen karfe shida saura suka shirya ita da Zahida da Anti Uwani suka nufi gidan Baffan.


__


Dawowar su Rukayya kenan daga islamiyya don ko uniform basu gama cirewa ba.


Bayan ya amsa sannu da zuwan su ya nufi saman, har ya kusa shigewa sai kuma ya ga gara yayi magana da yaran ko zai fuskanci wani abu kafin suje wajen Baffan Aishan. Ya juyo ya dawo falon kasan, ya kwalawa Yusra kira, bayan ta fito daga dakin yace


'Yusra ku sameni a falon sama yanzu ke da kannenki da Saddiku.’


Ta amsa ta koma dakin.


Ba tare da bata lokaci ba suka fito gaba dayansu suka sameshi a falon ya a zaune. Kowa ya nemi waje ya zauna yayinda Sumayya ta wuce ta zauna a jikin Abban. Ya kare musu kallo sannan yayi gyaran murya yace


'Allah shine me rayuwa, dukanmu muna cikin bukatar Mommy Allah ya dauki ranta. Hakuri kawai zamu yi sannan kuma mu cigaba da yi mata addu'a. Zuwa next week in sha Allah za a fara aiki a gyara gidan gaba daya, idan aka gama Antinku zata dawo nan mu zauna gaba daya.’


Idonsa yana kan Yusra yana lura da yanda take ta faman murgude baki tana kau da kai. Ya dubeta yace


'Zata zauna ne ba don a sake muku uwa ba sai dai ita din ma uwarku ce don haka akwai bukatar kuyi mata biyayya kuma ku bata hadin kai mu zauna lafiya. Sai dai ke Yusra tace ke da Nana kuna yi mata rashin kunya sosai, me yasa.’


Yusran ta bude baki zata yi magana Nana tace


'Abba ni dai ba ni bace.’


Yusran ta kawar da kai tace
‘Abba ni babu wata rashin kunya da nake yi mata, ni da bana ma kulata yaushe nayi mata rashin kunya?’


Abban ya bude baki zai yi magana Saddiku yace


'Wallahi Abba tana yi mata rashin kunya sosai, ranar sadakar uku Mommy ma baka ga yanda ta bangajeta ba kuma Anti Aishan bata ce mata komai ba.’


Idon Abban yana kanta tana hararar Saddikun. Yayi gyaran murya yace


'To ka ga kenan ba za a sami zaman lafiya a gidan ba tunda abun ya kai da bangaza wataran za ta kamata da kokawa.’


Tace


'Wallahi Abba ba haka bane, ni yaushe ma na ganta balle na bangajeta?’


'Itama da kanta ta gaya min abubuwan da kike yi mata kuma kin san dai ba zata yi miki karya ba. Yanzu kina da kwana uku ki kirawota a waya ki bata hakuri ki sanar da ita kin daina yi mata duk wani abu na raini, idan kin kirawota zata gaya min. Kin ga shikenan sai muyi zamanmu lafiya babu wanda ya raina wani. Amma idan baki kirawota ba to Babanki Bello yace sai dai ki koma gidansa don wajensa ne ta kai kararki. Ki kirawota ki bata hakuri zata sanar da shi in ba haka ba gidansa zaki koma komai za ayi miki kamar a nan. Tunda kinga ni ba zan iya saba maganar Yayana ba don ban raina shi ba kamar yanda ke kika raina naki Yayan har kike murguda masa baki a gabana.’


Suka yi shiru na dan lokaci.


Babu wanda yayi magana, don haka Abban yace


'Shikenan, ga kiran magriba nan mu tashi muyi shirin sallah.'


Ya tsallake su ya nufi daki yayinda su kuma suka nufi benen da nufin saukowa.


Tun a kafar benen Yusra ta fara mita ita kadai


'Wallahi bata isa na bata hakuri ba, ni da gidan ubana na ga wanda zai koreni sai dai kowa ya koma gidan ubansa wallahi.’


Har ya murda kofar dakin zai shiga sai kuma ya fasa ya dawo ya samesu a kafar bene don haka duk abinda Yusra ta fada ya ji. Bai kula da ita ba yace


'Sadik idan ka shirya ka jira ni mu tafi masallacin tare.’


Suka wuce shi kuma ya koma dakin yana mamakin Yusra.


Bai taba sanin lalacewar Yusra ta kai haka ba, tun kafin ma aje ko ina ta sanar ba zata bi umarninsa ba. Lallai gara ya barta taje gidan Yaya Bello don ya san ba zai yi mata a hankali ba. Watakila idan ya cigaba da addu'a Allah ya sa ta canza hali.


Nan da nan ya shirya suka tafi masallaci tare da Saddikun, suna dawowa ya shirya ya wuce gidan Yaya Bello.


……….


Tun a hanya ya sanar da Yaya Bellon yanda suka yi da Yusra, nan suka yanke maganar cewa kawai Yusra da Nana su dawo gidan Yayan.


Suna isa suka tarar Baffa da Yaya Abubakar suna jiransu.


A falon Baffa suka zauna gaba daya; Aisha, Anti Uwani da Zahida suna gefe yayinda Baffa da Ya Abubakar suke gefe sai Abban da Yaya Bello da suma suke gefe.


Tunda ya zauna yake kallon Aishan; tayi kyau tayi fes kamar bata da wata damuwa. Yanda yaki ya dauke idonsa daga kallonta ya sa ta sunkuyar da kai. Yaya Bello ne ya kula da halin da ake ciki ya tabo Abban.


Gaba dayansu suka gaisa da su Baffa da Anti Uwani.


Baffa yayi gyaran murya yace


'Yusufa me ya hadakane da amaryar taka har ta taho gida, duk da tace ba kaine kace ta taho ba?’


Nan ya mayarwa da Baffan yanda sukayi kamar yanda Aishan ta fada.


Sukayi shiru na dan lokaci, Baffa yace


'To tazo da wasu dalilai wadanda suka sa take jin ba zata iya zama da yarinyar ba, amma gata nan sai tayi bayani a gabanka kaji.’


A nan Baffa ya bawa Aishan umarni tayi bayanin abubuwan da Yusran takeyi mata da ma wasu abubuwan na cutarwa da Zahran ta dinga yi mata. Ta dora da


'Duk abinda za ayi kuma ita ake turowa ta shigo min da shi gida. Sannan kuma kullum muka hadu da ita sai ta gaya min bakar magana don kawai ina kawar da kai ne.’


Baffa yace


'Wannan maganar zargi a barta tunda kinga malamai ma sun ce wasu abubuwan aljanu ke son cutar da kai sai su nuna maka cewa wani ne daka sani.’


Tace


'Baffa wasu abubuwan idan tayi min da kanta take gaya min ko ta aiko Yusran ta gaya min.’


Kafin suce wani abu ta zaro waya ta kunna recording din da suka tsinta dazu na muryar Zahra. Kowa yayi kasake yana sauraro. Abba ya sunkuyar da kai zuciyarsa tana kara kuntata, muguntar Zahra da jahilcinta har ya kai haka?


Suna gama ji Yaya Bello yayi gyaran murya yace
'To Baffa dama muma hakuri muka zo mu bayar, kana zaune da mutum ne bisa kyautatatwar zato baka gane lokacin da yake sauyawa. Wadannan matsololi duk mun ji kuma ita Yusra da kanwarta Nana da ake magana in sha Allahu gidana zasu koma in ya so sai suyi zamansu da sauran yaran. Yanzu dai ana gyara a cikin gidan nan da sati biyu za a gama in ya so ita Aishan sai ta koma.’


Cikin farin ciki Baffa yace


'To Alhamdulillah, hakan yayi. Allah ya shirya mana zuri'a da mu gaba daya.’


Ya dubi Aisha yace


'Shatu ki dinga hakuri kin ji, yaro ko naka ne wanda ka haifa wani sai dai kayi hakuri da shi a lallaba. Bana jin ki da yara sai dai mu raka ku da addu'a, tunda gashi ita da take baki matsala bata nan don Allah sauran kuyi zamanku lafiya. Kuma ku sani mutum yana barin mugun hali ya shiryu musamman wanda ake tsaye ana masa addu'a don haka idan ta canza hali ita din ma duk ki hadasu ki rungume.’


Tace


'To Baffa.'


Yaya Bello yace


‘Akwai kuma yaran wajen Aishan su biyu idan babu damuwa sai ta taho da su duk su hadu a nan suyi zamansu gaba daya.’


Yaya Abubakar yace


'Wadannan ma ba za ayi haka ba. 'yan uwan mahaifinsu suna so su karbesu tunda Farha da take karama yanzu shekarunta sha biyu, suna ganin ya kamata a basu yaransu. Kuma yaran sunyi na'ama don haka nan da wani dan lokaci zasu koma wajen kanin mahaifinsu.’


'To babu laifi hakan ma yayi.’


Suka yiwa su Baffan sallama suka fice.


Suna fita Yaya Uwani tace


'Tunda ya auri yarinyar yana kallon yaran bai taba cewa su zo su koma wajenta ba sai yanzu da yake so ya bata rikon nashi yaran, ko kunya babu wai su koma can. Hmmm!’


Baffa yayi gyaran murya yana murmushi yace


'Hajiya Uwani ayi mana afuwa dai, kin san wani lokacin son kan mu yana rufe mana ido da yawa.’


Itama tayi dariyar tace


'Allah ya bude muku ido to ko kwa ga gaskiya.’


Daga baya suka yi sallama kowa ya koma gida.


………..


Tun da suka fito Aisha ta kasa walwala sosai. Bata ji dadin yanda taga Abban ba; yayi wata rama gashi kamar ma bashi da lafiya. Ta ji haushin kanta da ta ki daukar wayarsa har ya gaji ya daina kiranta. A take tausayinsa ya kamata duk da bata san me yake damunsa ba. Bata da wata matsala da shi kuma zata koma kamar yanda ya fada, musamman da yake ya amince zai dauke Yusra.


Haka suka koma gida tana cike da damuwar halin da ta ga Abban. Tana son ta kirawoshi a waya to amma bata san me zata ce masa ba, don haka ta hakura ta kwanta bacci.


Wajen karfe sha daya da rabi wayarta tayi kara, lokacin bacci ya fara daukanta. Tayi firgigit ta farka ta dauki wayar tana dubawa, Abban Sadik ne yake kiranta don haka ta tashi a hankali ta fice daga dakin saboda kada ta tashi Anti Uwani da Farha daga bacci.


Ta amsa wayar ta kara a kunnenta dai-dai lokacin da ta karasa falon ta zauna a kan kujera.


Yanayin yanda ya kirawo sunanta sai da tsigar jikinta ta tashi. Ta gaisheshi sannan ta tambayeshi yaran, bayan ya gama amsa gaisuwar yace


'Aisha, me yasa kika ki daukan wayata?’


Bata da amsar da zata bashi don haka tayi shiru. Sai da ya gaji da shirun sannan ya cigaba


‘Kiyi hakuri ki daina fushi dani kin ji.’


'Ni ba fushi nake yi ba fa.’


'To me yasa kika daina kula ni?’


'Ni ban daina kula ka ba.’


Yayi murmushin da saida ta jiyo sautinsa yace


‘Gobe za a fara aiki, wane kalar fenti kike so?’


Itama murmushi tayi tace


'Ko wanne kala ma yayi.’


Sukayi shiru na dan lokaci jimawa kadan ya sake kiran sunanta, ta amsa murya kasa-kasa. Yace


'Ina son ganinki, ya za ayi?’


'Gobe kazo gida mana.’


'Ba a gida ba gaskiya, please idan kin tashi daga makaranta ki zo office mana.’


Sukayi shiru na dan lokaci bata amsa ba, ya gaji da shirun ya sake maimaita mata


'Ki zo office kin ji Aisha.’


Tace


'To, amma da ka zo gidan zamu fi samun time mu tattauna a nutse.’


'To kizo din sai mu wuce gidan daga nan.’


'Ok.'


Suka sake yin shiru na dan lokaci, jimawa kadan tace


'Wai baka da lafiya ne?’


Yace


'A'a. Me kika gani?’


'Na dai ga kamar baka da lafiya ne.’


Yayi murmushi mai sauti yace


'Tsabar damuwa ce kawai, mutum yana da mata biyu a wayi gari daya ta mutu dayar kuma ta gudu ai kin ga dole na shiga damuwa ko?’
'Ni fa ba guduwa nayu ba.’


Yayi dariya. Suka dan taba hira sannan sukayi sallama ta koma ta kwanta.


—----


Washegari ranar litinin tun kafin yara su tafi makaranta ya sanar da su idan sun dawo daga makaranta su hada kayansu zasu tafi gidan Yaya Bello sai an gama aiki a nan sannan zasu dawo. Itama Jummai ya sanar da ita an bata Hutu, idan yaran sun tafi gidan Yaya zata iya tafiya ta barwa Saddiku mukullin gidan idan an gama aiki zai kirawota. Ya kawo kudi naira dubu ashirin ya bata yace ta yi wata hidimar, ya fice ya barta tana godiya.


Tun kafin ya karasa office din ya kirawo Aisha don ya tabbatar bata fasa alkawarin da ta yi masa ba akan zasu hadu a office, inda ta tabbatar masa zata zo da karfe sha biyu da rabi.


………


A

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login