Showing 147001 words to 150000 words out of 166068 words

Chapter 50 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25428

Abba tabbas da tuni wani zancen ake ba wannan ba musamman yanda ta kula shima Saddiku tunda ya dawo daga makaranta cikin girmamawa yake mu'amala da ita.


Suna fita ta kirawo Zahida ta sanar da ita yanda sukayi da Abban. Zahida tace


‘'To yanzu ya za ayi? Kinga fa ko Hajiya ba a gayawa halin da ake ciki ba.’


'Hmn! Da na gaya mata da yanzu ta tursasa ni na koma gidan ni kuma wallahi ba zan yi wannan rayuwar ba. In ya dawo kawai ya daga min hankalin gidan zan tafi sai ayi ta ta kare don ba zan zauna da wannan yarinyar ba. Ko yau ma baki ga wulakancin da tayi min ba da na shiga gidan, Ina kuma ga a ce kullum ina tare da ita.’


Cikin damuwa Zahidan tace


'Allah ya sauwake amma dai akwai kura, ba kadan ba.’


Sukayi sallama suka ajiye waya.


……….


Wajen karfe biyar Abba ya dawo daga aiki, gaba daya ya sakankance cewa zai tarar da Aisha a gidan. Yana shiga falon bayan ya amsa sannu da zuwan Yusra wadda ya tarar a falon kasan tana kallon TV ya karasa ya bude kofar dakin da aka gyarawa Aishan. Ga mamakinsa babu komai a dakin, ya janyo kofar ya juyo ya cewa Yusra


'Antinki bata dawo bane?’


'Eh, babu wanda ya zo.’


Bai amsa ba ya haye saman zuciyarsa tana dugunzuma. Me yasa Aisha take son ta saba umarninsa? Me take nufi da hakan? Idan bata rike masa yaran ba meye amfanin ta a rayuwarsa a daidai wannan lokacin? Bai taba zaton zai dawo ya tarar bata gidan ba amma gashi saboda raini bata dawo ba.


Jakarsa kawai ya ajiye a dakin ya fito ya wuce gidan Aishan.


Tana zaune a falo a kan kujerar zaman mutum daya tana ta faman dube-dube a waya. Bata ji alamar ya yi sallama ba don haka bata amsa ba, ta mike tsaye ta ajiye wayar ta nufo shi tana yi masa sannu da zuwa.


Bai amsa ba ya tsaya daga bayan kujerar yana mata wani kallo na takaici, ta karasa ta tsaya daga kusa da shi tana fadin


'Ga ab…’


Muryarshi ce ta katseta


'Aisha me nace miki? Me kike a gidan nan bayan ga inda nace ki koma kafin na dawo zaki bar min yara su kadai, zaman kansu zasu yi kenan saboda mahaifiyarsu ta rasu ko me?’


Ta sunkuyar da kai ta share kwalla a hankali tace


'Kayi hakuri ai na gaya maka ba zan iya komawa ba.’


A fusace ya nuna ta


'Idan dai zamana kike to yanzu ba tare da bata lokaci ba ki fito ki koma can gidan idan ba haka ba kuma to zaman kanki kike yi. Mun gama magana da maigidan nan next week zasu karbi mukullinsu idan kuma zaki kama hayar sai kiyi magana da su ki kama hayar tunda kin fi karfina.’


Ta bude baki zatayi magana ya dakatar da ita yana mata kallo mai cike da takaici, ya fice ya mako mata kofar.


Yana fita ta zagaya ta zauna a kan kujerar ta sa kuka. Ita kanta bata san kukan me takeyi ba tunda dama ta sa ran hakan zata faru. Sai da tayi mai isarta sannan ta share hawayenta, ta dubi agogon bangon da yake dakin taga karfe shida saura minti biyar. To zaman me takeyi a gidan mutane tunda ya gaya mata gida ya fita daga hannunsa kuma idan ta zauna zaman kanta takeyi. Ta mike a hankali ta shige dakinta.


Kafin magriba ta tattara kayanta na bukata da kuma duk wasu kaya masu mahimmanci wadanda motarta zata iya dauka. Ta fito ta zuba a motarta, ana kiran Magriba ta rufe gidan ta ja motarta ta nufi gidan Hajiya.


—-------


Abba yana fitowa daga gidan Aisha ya koma gida, kai tsaye dakinsa ya shige ya rufo kofa. Ya zauna a gefen gadonsa kamar wanda aka tunkuda, ya hada tafukan hannunsa guda biyun ya zuba fuskarsa a ciki yana fitar da wani huci na takaici; bai taba tsammanin taurin kan Aisha ya kai haka ba. To me Yusra tayi mata da zata ce ba zata zauna da ita ba? Ita Yusran ya zai yi da ita kenan? Babu yanda za ayi ace a rayuwarsa yanzu ya kara aure don wannan ba zai ma yiwu ba. Iya tsawon rayuwarsa abinda ya sani shine idan aka saki mace ko ta rasu to idan dai tana da abokiyar zama yaran wajen abokiyar zaman suke komawa ba tare ma da anyi wata magana ba.
Ita Aishan me yasa take jin cewa tana da zabi? Me Yusra tayi mata da har take jin a cikin yaran zata rike wasu wasu kuma ba zata zauna da su ba? Tabbas ya san da sa hannun Zahra a lokacin da ya manta da Aisha na wani lokaci to amma menene laifin Yusra a ciki?


Ya daga fuskarsa ya gyara zamansa; in dai Aisha tana son zama dashi dole ta zauna da yaransa gaba dayansu, kuma zai yi iya yinsa wajen ganin hakan ya faru. Ko babu komai yana son ta sosai kuma a iya tunaninsa ita kadai ce macen da zata zauna masa da yaran tsakanin da Allah babu cutarwar. Ya tabbatar bata da mugunta kuma bata da sharri, hasali ma zai iya cewa idan dai magana ake ta tarbiyyar yara ta fi Zahra iyawa saboda yanda yaga mu'amalarta da yaranta da kuma yanda take kula da Rukayya. Ba zai taba rabuwa da Aisha ba kuma ba zai kara aure ba, itace dai zata hakura ta zauna masa da yaran.


Yana nan zaune ya jiyo motsin su Sumayya suna shigowa sun dawo daga islamiyya. Yana matukar tausayin yaran kuma tabbas ya san suna bukatar uwa kamar Aisha, yana fatan kafin gari ya waye ta farka daga mafarkin da takeyi ta tattaro kayanta ta dawo gidan.


……..


A guje su Sumayya suka shiga gidan suna murna saboda sun zata zasu sami Aisha a gidan. Yusra ce kawai a falon, ba tare da ko sallama ba Sumayya ta dubeta tace


'Yaya Yusra Anti Aisha tana nan?’


A gajarce ta amsa


'Bata nan.’


A dai-dai nan Rukayya ta shigo falon bayan ta yiwa Yusra sallama ta sanar da ita sun dawo kai tsaye ta wuce dakin da aka gyarawa Aisha ta tura kofar. Babu komai a dakin don haka ta mayar da kofar ta rufe sannan ta wuce dakinsu na kasa. Yusra da take zaune a kan dining table ta bi bayanta da harara sannan tayi tsaki; wanda Rukayyan ta ji amma sai ta kawar da kanta.


Tana shiga dakin ta ajiye jakarta ta canza hijabinta, Ummi da take zaune a gefen gado bayan ta ajiye tata jakar tace


'Yaya Rukayya Antin bata dawo nan ba, gidanta zaki je?’


'Eh, zan je na gani idan ma ta shirya sai na tayata debo kaya.’


Ta mike ta nufi kwandon kayansu tana fadin


'Bari na sa hijabi muje, mu sulale mu bar Sumy naji ta haye wajen Abba.'


Sukayi dariya a tare.


A dai-dai nan Yusra ta shigo dakin, ta dubi Rukayyan tace


'Ku kuma Ina zaku je kuke wani gyara hijabai?’


A gajarce Rukayya ta bata amsa


'Gidan Anti Aisha.'


Dogon tsakin da Yusran ta ja shi ya sa Rukayyan ta dubeta, ita kuwa Ummi a take ta fara kokarin cire hijabinta don tana shakkar Yusran. Cikin izgilanci Yusran ta matsa gaba Rukayyan tace


'Babu inda zaku je wallahi. Ke wai wace irin marar tunani ce Rukayya, uwarki ta mutu amma ko sati biyu ba ayi ba kin fara karya dokokin da ta shinfida miki lokacin tana raye. Iya biyayyarki da Mommy kenan? dama jira kike ta mutu ki koma wajen makiyiyarta? To wallahi baki isa kije wajen wannan ma-sharranciyar matar ba yau. Ke kenan saboda tsabar ba kya kishin Mommy kullum ki kwashe mata yara ki kai su inda ta hanaki zuwa sai kace mai kwakwalwar kifi. To yau babu inda zaku tunda uwar taku nan zata dawo sai…’’


Cikin takaici idonta yana fitar da kwalla ta matsa kadan zata shige ta gefen Yusran amma Yusran ta tareta, ta sake matsawa Yusran ta sake tareta tana fadin


'Malama ki cire wannan hijabin ki zauna babu inda zaki je. Lallai yau da Mommy zata dawo duniya da tayi mamakin yanda kika manta da ita kike kokarin sake uwa….’


Kafin ta gama fadin abinda tayi niyya Rukayya ta dage iya karfinta ta tunkudata. Ta tafi taga-taga, saura kadan ta kai kasa ta dafe kofar dakin ta tsaya tana kallon Rukayyan da mamaki. Cikin kunan rai tace


‘Kan bala'i, wato saboda matar nan ta gama dake ni kike turewa saboda baki da kunya kuma kinga babu idon Mommy ko?’


A fusace ta nufo ta yayinda ita kuma Rukayya take tsaye ta nade hannuwanta a kirjinta tana fadin


'Babu ruwanki da ni Yusra, fita a harkata! Zan je na tambayi Abban idan yace kada naje sai na fasa amma ke baki is…’


Kafin ta rufe bakinta Yusran ta dauke ta da mari. A take ta dafe kumatunta tana huci, kafin tayi wani tunani ta zare hannu itama ta gaurawa Yusran mari.


Da gudu Ummi ta fice tana kuka ta haye sama don ta kirawo Abba.
Yusran ta cakumo wuyan hijabin Rukayya, cikin zafin nama Rukayyan ta fisge ta tunkede Yusran wadda ta fadi kasa, ba tare da bata lokaci ba Rukayyan ta bita kasa ta haye kan ruwan cikinta tana ta kai mata duka ko ta ina; duk wani bacin rai da Yusran ta dade tana cuzguna mata da shi tun kafin rasuwar Mommy ya dinga dawo mata don haka ta rufe ido tana ta faman kai mata duka. Ganin abun yayi yawa yasa Yusran ta fara ihu tana kokarin ture Rukayyan daga kan cikinta wanda ya gagara, kamar ma karawa Rukayyan karfi takeyi. A dai-dai nan Abba ya banko kofar ya shigo Ummi da Sumayya suna biye da shi. Da karfi ya fincike Rukayya daga kan Yusra wadda idonta ya rufe, ta fizge daga rikon da Abban yayi mata tana huci. Ba tare da bata lokaci ba ya gaura mata mari wanda ya dawo da ita hayyacinta ta dafe kumatun tana kallonsu shi da Yusran tana fitar da hawaye masu zafi.


Da gudu Sumayya ta fice ta nufi bayan gida inda Jummai da Nana suke wanki don ta kirawosu.


Abban ya tsuguna a kan Yusran ya kamata ta mike tsaye yana nuna Rukayya yana fadin


‘Wannan wane irin rashin hankali ne Rukayya, yayarki kikewa wannan dukan kamar kin sami wata jaka?’


Ta sunkuyar da kai hawayenta yana diga yayinda Abban ya tallafi kafadar Yusran yana kokarin zaunar da ita a kan gado yana duba fuskarta inda bakinta ya fashe yake fitar da jini.


'Baki da hankali Rukayya? Kalli yanda kika ji mata ciwo. Fice kije dakina ki jirani kuma ki daina wannan kukan don sai jikinki ya gaya miki.’


Ya zaunar da Yusran a gefen gado yana share mata hawaye yayinda Rukayya ta ja kafa ta fito daga dakin. Tana fitowa taci karo da Saddiku yana shirin shiga dakin wanda shigowarsa gidan kenan yana dauke da jakar computer dinsa. Ya sha gabanta ya dafa kafadarta da mamaki a fuskarsa yana tambaya


'Rukayya me ya sameki?’


A nan Jummai ta shigo da gudu Nana da Sumayya suna biye da da ita, suka tsaya a inda suka ga Saddikun yana tambaya. Sumayya ce ta bashi amsa tace


'Fada sukeyi ita da Yaya Yusra shine Yaya Rukayyan ta zane Yaya Yusran.’


A nan Rukayya ta fada jikin Saddikun ta fashe da kuka, ya dafa bayanta yana bata hakuri.


Jummai ta wuce shi ta shige dakin, ta tsuguna a gaban Abban tana fadin


'Subhanallahi. Muna can ni da Nana muna wankin uniform ashe fada suke yi haka. Yaya me kika gayawa kanwarki ya fusata ta haka? bari na samo ruwa a wanke bakin.’


Abban yace


'Yauwa wanke mata, ina zuwa.’


Yana fitowa yaci karo da Saddiku yana bawa Rukayya hakuri, ya dubesu yace


'Ba ce miki nayi kije dakina ki jirani ba, mara kunya fitsararriya?!


Ya maida dubansa ga Saddikun yace


'Ka kyaleni da ita ka shiga kaga yanda ta kama ‘yar uwarta da duka sai kace mara hankali.’


Cikin damuwa Saddikun yace


'Abba Yusra ce fa bata da gaskiya.’


Abban ya harareshi yace


'Gafara ka bani waje Malam, ka ga abinda ya faru ne zaka ce Yusra ce bata da gaskiya. Ka shiga ka ga yanda ta yiwa Yusran duka. Wuce kije ki jirani a saman.’


Ta ja kafa ta wuce saman tana shesshekar kuka, shi kuma Saddiku ya wuce dakinsa.


A hankali Abban ya ja kafa ya karasa kan dining a table din kasan ya zauna ya dafe kai, wannan wacce irin musiba ce? Yaran da basu taba yin wani fada irin wannan ba? Me yasa Aisha tayi masa haka? Da tana gidan nan ai da hakan ba zata faru ba. Jummai ta fito daga dakin ta sameshi a zaune, ta rage tsawo tace


'An wanke fuskar Alhaji, ciwon ma ai baiyi tsananin ba. Yarinta ce take damunsu, gashi Yaya ta iya tsokana. A yi hakuri a yiwa Rukayyan a hankali.’


Kai kawai ya daga mata ta tashi ta wuce kicin tana rike da hannun Sumayya. Jimawa kadan shima ya tashi ya haye saman zuciyarsa a jagule.
UWAR SADDIKU


Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)


43


Ba a jima da idar da sallar Magriba ba ta tsaya a bakin gate din gidan, ta matsa horn don ta san Abdallah yana nan. Kafin ta danna na biyun ya leko, yana ganinta ya koma da murna ya bude gate din. Ba tare da bata lokaci ba ta tura motar cikin farfajiyar gida, ta sami guri a cikin garejin gidan ta ajiye motar ta yanda duk wanda ya kalla ya san motar a nan zata kwana.


Tana fitowa daga motar ta mikawa Abdallah mukullin motar ta nuna masa akwati a bayan motar tace shi kadai zai dauko ya bar sauran kayan sai daga baya.


Kamar mara gaskiya ta shiga gidan da sallama, Hajiya, Anti Uwani da Farha suna zaune a falon. Da gudu Farha ta mike daga kusa da Anti Uwani ta rungume Mamanta tana mata sannu da zuwa. Kafin ta gama amsawa Abdallah ya shigo da akwatin ya nufi dakin Anti Uwani da shi. Itama Farha ta dubi Aishan tana murmushi tace


'Mama kwana zakiyi na kai miki jakar dakinmu ko?’


Ta daga mata kai a take ta bi bayan Abdallah.


Ta karasa cikin falon ta zauna a kan kafet daga gefen Hajiya wadda take zaune kafafunta a mike. Ta gaida Hajiya sannan ta juya ta gaida Anti Uwani. Hajiya ta dubeta fuskarta da alamar tambaya tace


'Lafiya dai da magribar nan kuma naga ana kwana zaki yi kina daga kai?’


Ta danyi murmushin yake ta kawar da kai saboda yanda kallon da su biyun suke binta da shi yake saka ta jin kamar wata mai laifi. Tace


'Kwana zan yi Hajiya, sai gobe zan tafi.’


Cike da mamaki Anti Uwani tace


'Ikon Allah! To wa kika barowa gidan da yaran?’


'Suna can Anti, ai akwai mutane a gidan.’


Ta mike da hanzari tana fadin


'Bari naje nayi sallah, ko magriba ban yi ba ga shi nan har an fara kiran isha'i.’


Ba tare da ta saurari abinda zasu fada ba ta bar wajen da sauri ta shige dakin da yaran suka shiga da kayanta.


Hajiya ta dubi Anti Uwani tace


'Kin ga yarinya don Allah, guduwa fa ta yi. Tabbas wannan zuwan nata akwai dalili.’


Anti Uwani tace


'Barni da ita, bari ta idar da sallar na ji abinda ya kawota.’


Har aka ci abinci akayi sallar isha'i tana daki, babu wanda ya nemeta. Sai dai Anti Uwani ta zuba abinci ta bawa Farha ta kai mata daki. Da yake tana tattare da yunwa ta dan taba tuwo, ta mayar ta rufe kwanukan ta wanke hannunta a bandakin da yake cikin dakin sannan ta dawo ta kashingide a gafen gadon Anti Uwani.


Bata dade da zama ba Anti Uwani ta turo kofa ta shigo dakin, bayan Aishan ta amsa sallamarta ta wuce ta zauna a gefen gadon yayinda Aishan ta gyara zama ta janye kafafunta. Bayan Anti Uwanin ta zauna ta dubi Aishan, suna hada ido ta sunkuyar da kanta yayinda Anti Uwani tayi murmushi. Tace


‘Kya ji kunya mana Shatu! To ya aka yi? Don dai wannan zuwan na san ba na lafiya bane.’


Sukayi shiru na dan lokaci, Anti Uwani tana sauraronta ita kuma tana kallon hannunta tana tunanin ta inda zata fara. Jimawa kadan ta gaji da yanda Anti Uwanin ke kallo da sauraronta ta bude baki da kyar tace


'Cewa yayi idan na zauna a gidan zaman kaina nakeyi, shine na taho.’


Mamakin Anti Uwani ya karu, ta gyara zama tace


'Ban fahimceki ba fa, Yusufan ne yace zaman kan ki kikeyi ko kuwa? Kiyi min bayani yanda zan gane.’


Ta dan muskuta ta fara yiwa Anti bayanin abinda ya faru a kan umarnin da ya bata ta koma gidan yaransa har zuwa inda yace idan bata koma ba zaman kanta takeyi ba zamansa ba. Ta kara da


'Shine na taho.’


Mamakin Anti Uwani ya sake karuwa, domin duk wannan bayanin da Aishan ta dauki lokaci tana yi kara kulle mata kai kawai tayi; ta kasa gane dalilin da ya sa ita Aishan ba zata koma wajen yaran nasa ba. Tace


‘A’a! To ai dole yace zaman kanki kikeyi Aisha, matar nan ta mutu fa me ya sa ba zaki bi umarninsa ki koma gidan ki kular masa da yaran ba? Wannan ai kowa ma ya san haka ce zata kasance.’


Nan ta fayyacewa Anti Uwani dalilan da suka saka ba zata rike masa Yusra da Nana ba, ta bata misalan wasu daga cikin abubuwan da Yusran ta yi mata.


Suka yi shiru na dan lokaci, Anti Uwani tace
'Kina da gaskiya Aisha, to amma fa gaskiya bana jin akwai wanda zai saurareki. Kowa cewa zai yi yarinya ce in an tsawatar mata zata daina; amma ni na fahimceki sosai. Rayuwa ce mutum zai yi ta yi rigima daga wannan sai wannan, kuma tsakaninki da miji kullum sai fitna.’


'To ai shine. Kuma ni Allah bai dora min zama da yaransa ba, ya kai su dangi uwarsu ko kuma ya auro wata ta rike masa su amma ba ni ba. Kinga ni uwarsu musamman take koya musu tsanata don haka zai yi wahala a sami wanda zai saukesu daga kan koyarwar uwarsu, amma kinga idan wata ya aura watakila su bata dama ta zauna da su.’


‘Hakane Shatu. Amma fa gaskiya duk bayanin nan naki babu wanda zai fahimceki fa don ina jin ko Hajiya ba zata saurareki ba. Ina ga gara kiyi hakuri ki koma in ya so a zauna da Yusufan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login