Showing 99001 words to 102000 words out of 166068 words

Chapter 34 - UWAR SADIKU COMPLT BY SAKINA YAZID.txt

11 Jul 2024

25424

tashi sai kuma yaji yana bukatar kari. Tun yana jin dadi har ya fara mamaki saboda bai saba samun irin haka ba. Watakila dai zai iya tunawa ya sami shigen hakan lokacin da ya dinga kasa yin komai a kwanan Aisha, sai dai a wancan lokacin ba kasa gamsuwa yake ba sai bayan ya gamsu sai ita Zahran ta kara laluboshi. To ko dai yanzun ma wani abun Zahra ta bashi yaci a abincin dare. Haka ya cigaba da hidimar nan yana yi yana tunanin da safe tabbas sai ya binciki Zahra.
Sai can gefin asuba wani bacci mai nauyi ya dauke shi, tunda ta duba taga yayi bacci kuma ta tabbatar baccin nasa yayi nauyi sosai sai ta zare jikinta ta fice daga dakin; domin itama ta gaji duk jikinta ciwo yakeyi.

Sai da aka idar da sallar asuba a masallaci gari ya fara wayewa sannan ya farka daga bacci.


Firgigit ya tashi zaune, ya janyo wayarsa ya duba lokaci yaga shida saura kwata. Yace

‘Subhanallah.’

Ba zai iya tuna lokacin da ya makara sallar asuba ba koda kuwa bashi da lafiya, nan yayi addu’a ya sauko daga kan gadon ya fada bandaki.

Har ya idar da sallah yana mamaki, sai dai ya kasa tuna mamakin me yakeyi, ya kasa tuna abubuwan da suka faru a daren jiya. Yana nan zaune a kan daddumar har kwakwalwarsa ta fara gajiya da kokarin da yakeyi ya tuno me ya makarar da shi sallar asuba amma ya kasa. Bacci kawai yake ji don haka ya tashi lokacin ya fara jiyo hayaniyar yara suna shirin tafiya tahafiz, ya koma kan gadon ya kwanta bacci ya kwasheshi.

Sai wajen karfe goma sannan ya fito, zuwa lokacin ta riga ta jera abincin safe a tebur. Nan ya zauna ya gama cin abincin, bayan ya gama ya fice ya tafi gidan Hajiya.
--------

Tunda suka dawo daga Dubai sai yanzu ne ta huta ta dawo dai dai duk wata gajiya ta rabu da ita, don haka tun asuba da ta tashi ta sa Rukayya ta tayata suka gyara gidan tsaf, har inda ma bata gyara ba tunda ta dawo. Karfe tara saura kwata Rukayya tayi wanka ta shirya ta fice don tafiya tahfiz, tayi mata sallama a kan sai an kwana biyu tunda ta san yau Abba a nan zai kwana.


Ko da taga Bai shigo ba da rana ta san gidan Hajiya ya wuce duk da ya saba yi mata waya ya sanar mata in ya wuce Amma yau shiru. Ta dai San sai dare zai dawo.

Ragowar abincin da ta dafa da safe shi taci da rana, sai bayan la’asar sannan ta tuka tuwon shinkafa da miyar agushi. Tana saukewa ta ci ta koshi sannan ta zuba musu na dare a flask ta jera a table.


Ana yin sallar Magriba kamar yanda ta saba tayi wanka ta kunnawa gidan turaren wuta, nan da nan kamshi ya karade gidan. Ta shirya ta dawo falo ta zauna tana jiran shigowar maigidan.

Karfe tara daidai na dare NEPA suka kawo wuta don haka ta mike ta kunna TV, ta kalli agogon bangon taga lokaci. Tana mamakin abinda ya sa har yanzu Abba bai shigo ba; ya saba wuce karfe tara bai shigo ba amma indai zai yi haka to ana yi sallar isha’i yake kiranta ya sanar da ita ba zai shigo da wuri ba. Amma yau din bai shigo ba kuma bata son kiranshi musamman idan ta san yana gidan Zahra.


Ta zauna ta dauki remote ta fara canza channel tana laluben abinda zata kalla.

Ta cigaba da kallo duk da hankalinta ya kasa kwanciya kuma ta kasa kiransa. Wajen karfe goma saura yunwa ta fara damunta don haka ta tashi ta zubi tuwonta ta zauna ta fara ci. A hankali take cin abincin don haka ta dauki lokaci kafin ta gama. Bayan ta kai kwanon kicin ta hado shayi ta dawo ta zauna, ta dauki wayarta ta duba lokaci; karfe goma da minti goma.

Hankalinta bai kwanta da wannan rashin kiran nata da bai yi ba don haka ta daure ta danna masa kira. Haka ta dauki lokaci tana ta faman kiransa amma wayar bata shiga, kamar dai yana wajen da babu network.


Mamakinta ya tsananta don bai gaya mata zai tafi kauye ba ko wani waje da babu network. Haka ta hakura ta ajiye wayar ta zauna tana ta wasi-wasi.

Tana nan zaune har wajen karfe sha biyu saura bai shigo ba kuma bai kirawota ba gashi wayarsa ta ki shiga. Zabi daya ya rage mata taje gidan Zahra ta tambaya, to amma gaskiya bata son shiga gidan nan ko da rana balle kuma da tsohon daren nan. Tana da lambar wayar Zahra amma bata taba kiranta ta dauka ba, don haka ma ta hakura ta daina kiran.

To yanzu wanne zata yi?
Idan zuwan ne ma ita ba zata iya fita waje yanzu ba. To amma ai tabbas da da wani abu da zata ji; to kenan lafiya kalau zuwa gidan ne ba zai yi ba ko me?


Ta mike tsaye ta fara zarya a falon, sai da ta gajib ta zauna ta sake duba agogo; karfe sha biyu da rabi.

‘To me yake faruwa?’

Ta tambayi kanta a fili.
Cikin karfin hali ta sake kiran wayarsa, amma ko shiga bata yi ba kamar dazu.

Bata da wata mafita illa ta kirawo Zahra, a kalla ko da gaya mata tayi cewa yana lafiya shikenan sai ta kwantar da hankalinta ta rufe gidan ta kwanta.

Nan take ta lalubi lambar Zahran ta buga.
…………

A al’ada da rana yake canza gida idan ya gama kwanan mace, idan ya ci abincin safe shikenan kwanan sun kare sai an sake kwana biyu.


Ranar Lahadi a gidan Aishan ya kamata yaci abincin rana amma sai ta ga bayan ya dawo daga gidan Hajiya ya shigo yace mata ta sa masa abinci zai zo ya ci. Ya shige dakinsa ya barta tana neman taka rawa saboda murna. Ba ma ce mata yayi ta dafa masa abinci ba kawai yi yayi kamar dama a nan ya saba cin abincinsa kullum. Nan da nan ta shiga kicin ta zubi masa abinci ta sa a table.

Nan ya wuni bai sake fita ba kuma bai nuna alamar zai tafi gidan Aisha ba.


Dare nayi ta gabatar da abincin safe suka ci suka kwanta kamar yanda suka saba. Fari tas take jin zuciyarta saboda dama tana bakin cikin raba kwanan da yake musu da Aishan.

Shabiyun dare ta gota ta farka daga bacci, yana kwance a gefenta yana bacci. Bata son ta tasheshi don haka ta dauki wayarta ta haska don ta dubo yara. Ta shiga dakin su ta tashi Ummi ta sakata a fitsari, ta gyarawa Sumayya kwanciya da yake ita diaper ce a jikinta. Ta fito daga dakin kenan wayarta ta fara vibration, ta kalli screen din wayar tayi dariyar mugunta sannan ta amsa wayar ta shige dakinta.

A tsakiyar dakin ta tsaya don ba so take wayar ta dauki lokaci ba, bayan sun gaisa tace

‘Dama Abban Sadikne bai shigo ba kuma na kirawo wayarsa bata shiga shine nace ko lafiya.’

Tayi murmushi mai sauti ta bata amsa

‘Lafiya kalau, yayi bacci.’
‘Um, t….’

Bata saurari abinda zata fada ba ta cigaba

‘Kema ina baki shawara kije kiyi baccinki, idan dai mininane Yusuf uban Sadiku to bazaki sake jin duriyarsa ba. Ya manta dake ya goge babinki a rayuwarsa, ko da me kike takama kuma ya fi karfinki, duk lokacin da kika gaji sai ki tattara kayanaki ki koma gidanku. Kuma don Allah kada ki sake kirana a irin wannan daren muna kwance da mijina.’

Bata saurari amsarta ba ta katse wayar , ta kashe fitila ta koma dakin Abban tayi kwanciyarta zuciyarta cike da jin dadi.
………..

Mutuwar tsaye Aisha tayi a nan inda take, bata san me take ji ba; mamaki ne ko kuma takaici. Kafarta ta fara kasa daukarta don haka ta zagaya ta zauna a kan kujera ta dafe kai. To wannan maganganun na Zahra me suke nufi? ‘duk lokacin da kika gaji sai ki tattara kayanki ki koma gidanku’.

Ta muskuta tace

‘Ikon Allah!’

Kwakwalwarta ta kasa jeranta tunaninta, don haka kawai ta runtse idonta tana maimaita


‘hasbunallahu wa ni’imal wakil.’

Ta jima a haka kafin ta bude ido, ta kalli agogon bangon wanda ya nuna karfe dayan dare da minti biyar.

Duk da bata gane me yake faruwa ba amma dai ta san ba zai zo gidan ba, ko da zai zo to ta san tabbas ba yau ba. Don haka ta mike ta sakawa kofar gidan kwado ta rufe ta kashe fitilun ta shiga dakinsa da niyyar kwantawa. Har ta saka kayan bacci sai kuma ta koma bandaki ta dauro alwala; babu yanda za ayi tayi bacci bayan wadannan maganganun da Zahra ta gaya mata.
Sai da ta dauki lokaci tana Sallah sannan ta bi da addu’oi, tayi karatun kur’ani sannan ta kwanta.


UWAR SADDIKU


Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

32

Ko da gari ya waye ranar litinin ce don haka Aisha bata ma tsaya jiran wani abu ba ta shirya ta wuce makaranta; sai dai kawai wunin ranar a cikin wasi-wasi tayi shi. Haka ta wuni tana kiran layin Abban ko shiga wayar bata yi har ta gaji ta hakura. Bata san abinda zata yi ba bayan wannan don haka ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido wata kila zuwa kwana biyu a sami mafita.


Abu daya ne yake firgita ta idan ta tuno abubuwan da suka dinga faruwa a lokacin da yake kasa shiga gidanta; bata son ta yarda wani asirin aka sake yi yanzun amma dai tabbas biri yayi kama da mutum
………..

A hankali har gashi an wayi gari yau Juma’a, ko sau daya Aisha bata ji daga Abba ba kuma bata sa shi a idanunta ba.

Kamar yanda ta saba duk ranar Juma’a in ta tashi daga makaranta gidan Umma take wucewa don taje wajen yaranta to yau din ma haka tayi. Ana tashi ta wuce ta dauki su Abdallah a makaranta sannan suka wuce gidan Umma. Suka baje kayansu Anti Uwani ta shiga hidima da su.

Can bayan sallar la’asar sai ga Zahida itama sun zo da yaranta harda maigidanta wanda bayan ya gaida Umma ya fice ya barsu a can sai dare zai dawo ya daukesu.

Suna zaune a dakin Anti Uwani ita da Zahida suna hirarrakinsu Aishan tace

‘Kin san wani abu Zahida, ina jin fa mutuniyarki tayi sabon boka.’

Ta gyara zama tana zare ido

‘Kai Jama’ah wannan Yaya taki ba dai himma ba! Allah ya sa dai bata taba ki ba.’

‘Ni ai na rigata na ce Allah kuma Allah ya sani bani da niyyar cutar da ita don haka Allah ba zai bata iko a kaina ba in sha Allah, mijinta dai ta taba.’

Sukayi shiru na dan lokaci Zahida tana rike da bakinta tana kallon Aishan, jimawa kadan Aishan ta cigaba, ta bata labarin abinda ya faru sannan tace

‘Yanzu dai maganar da nake miki tun lokacin rabona da shi don ko waya nayi masa bata ma shiga ban san me yake faruwa ba.’

Zahida tace

‘Ke Yaya Aisha, to ke yanzu haka zakiyi ta zama? Kamar wata wadda take zaman kanta.’

‘Ina addu’a, kuma na gayawa malaminmu a islamiyya ya bani wasu addu’oin da na sihiri duk ina yi. Kawai dai shima Malam din ya gaya min sai na yi hakuri na cigaba da addu’ar kada na kosa.’

‘To ai sai ki dawo gida tunda kinga can kina zaune ne ke kadai, ki dawo nan in ya dawo hayyacinsa sai ki koma.’

Tayi gajeran murmushi tace

‘Kin san Allah Zahida, ba zan bar gidan nan ba ina nan a cikinsa. Abinda take so kenan ace na bar gidan, ina jin ta kasa sakashi ya sakeni shi yasa ta bullo da haka kinga idan na tafi ai daga nan sai na nemi saki ko da akotu ne. To wallahi ina nan ko da me take tsafi sai naga karshensa, ita halittar Allah kaskantaciyya ta rike ni kuwa Allah Azza wa Jalla shi kadai na rike don haka na san abun nata na lokaci ne. Da ni da ita shege ka fasa!’

‘Kai Aisha nifa wannan abubuwan sun fara bani tsoro, to ai sai a gayawa Umma ko addu’a nei ayi. Ni zaman ma nake ji ke kadai kamar wata mara gata.’

‘Na san dole zan fada amma na kara bawa abun lokaci tukunna, amma in sha Allahu sai na nuna mata karya fure take bata ‘yaya.’

Nan suka karasa wuninsu sai bayan magriba sannan Aisha ta tuko motarta ta dawo gida. Tana shiga ta mayar da gidan ta kulle don ta san babu wanda zai sake shigowa.
…………

Kwanci tashi har an yi sati biyu rabon da Abba ya nemeta, zaman gidan haka ita kadai ya fara damunta. Gashi anyi hutun makaranta don haka babu inda take zuwa sai dai kawai taje islamiyya ranar asabar da halidi sai gidan Hajiya.


Don haka taje ta tsara Yaya Zainab ta dauko Amira; tun da zuwa yanzu duk sun san matsalar da take ciki, Yaya Abubakar ne kawai basu gayawa ba. Babu yanda basuyi da ita ba a kan ta koma gidan Hajiya amma ta ki don haka ma aka kyaleta. Haka aka bata Amira tunda Amiran tayi candy yanzu sai jiran admission da takeyi wanda ko da ya fito Aisha zata iya daukar nauyin kaita makarantar da daukota.
Daga ita har Amiran ba fita suke a unguwar ba balle su hangi koda yaran ne, domin itama Amiran Aishan ce take kaita islamiyya a motar ta daukota.

A haka karshen wata ya kare tana ta sa rai taga an kawo mata cefane ba a kawo ba, don haka dole taje ta yiwo cefanenta da akayi albashi. Duk wani abu da suke bukata ita da Amira ta siyo ta ajiye musu.
_

Cikin farin ciki take gudanar da rayuwarta tunda taga aikinta ya kama, ko da wasa Abban Sadik bai sake maganar Aisha ba rayuwarsa kawai yakeyi kamar yanda ya saba kafin ya auro Aishan.

Idan akwai wanda take jin zai iya bata matsala to Rukayya ce; don haka ta ja mata kunne sosai kuma ta sanar da ‘yan uwan duk lokacin da aka ga Rukayyan ta shiga gidan Aishan ko kuma ta kula Aishan ko da a unguwar ne a gaya mata. Don haka ta san babu wanda zai yi maganar Aisha a gidan.
………..

Zuwa yanzu abu daya ta sa a gaba; mota take so Abban ya saya mata irin ta Aisha ko kuma wadda ta fi ta Aishan. Ta riga tayi masa magana kuma ya amsa, ya dai sanar da ita bashi da kudi amma ta bashi wata biyu zai samu sai a siya mata.

Gaba daya yanzu yanda ta tsara haka Abban yakeyi. Ta kula dai kamar bashi da cikakkiyar nutsuwa amma wannan bai dameta ba tunda yana yi mata yanda take so.

Hannun Sadiku tuni ya warke, yana nan yana zaman jiran jarrabawar da zai maimaita tare da ‘yan ajin su Yusra. Tun da hannunsa ya warke Abba ya saka shi a makarantar da zai koyi computer kuma ya saya masa computer, sai dai bai je makarantar nan ya kai na wata daya ba ya daina zuwa.

Idan ya fita sai kawai ya wuce gidan su abokinsa wanda suke kira Kolo su yi ta shaye-shayensu a can, da yamma sai ya dawo gida. Duk lokacin da yake bukatar kudi sai kawai ya cewa Abban zasu sayi wani abu a makarantar computer ko kuma ya gayawa Mommy ita sai ta karbo masa kudin ta bashi ba tare da wani bincike ba.

Halin da Saddiku yake ciki yana sosa zuciyar Jummai saboda yanda take kaunar Uwar Saddiku sai dai ta kasa gane abinda ya sa ita Uwar Saddiku bata ganin yanda yaron yake canzawa. Ta san abinda ya faru da Rahma don tun daga wannan lokacin ma Rahma ta ja jikinta don haka itama Jumman kawai sai ta kau da kai tana yi musu addu’a.
___

Ranar Lahadi ce don haka yana gida bai je aiki ba.

Yana zaune a falon sama wajen karfe uku na yamma yana kallon TV. Daga dakinta ta fito inda ta kwantar da Sumayya ta karaso ta zauna a kusa da shi. Ya dubeta yace

‘Yar rigimar ta kwanta.’

Tayi murmushi

‘Uhm, ta kwanta ai in sha Allahu idan akayi hutu islamiyya za a sakata tunda ko babu komai ta kai shekaru uku. Yanzu haka ma ta iya karatun kowa ga surutun tsiya.’

‘Hakane, in Allah ya kai mu next session sai a koma bokon ma da ita.’

‘Ai ko da an taimaka min, aje can a yiwa Anti ko Uncle.’

Suka yi shiru suka cigaba da kallon TV din kowa da abinda yake tunani.

Jimawa kadan tayi gyaran murya tace

‘Yallabi wai ya batun mota tane, na ji shiru fa.’

Cikin yanayi na kosawa yace

‘To ai na gaya miki bani da kudi amma in sha Allahu kada ki damu kwanan nan za a saya miki kota.’

Ta dan bata rai

‘To gani nayi ai saboda mota sai binka nake kana wani ja min rai, kullum sai kace karshen wata amma in watan ya zo kuma sai kayi shiru. Ya dai kamata a duba don na gaji da yawo a motar direba kawaye suna yi min dariya gaskiya.’

Cikin murya ta lallashi yace

‘Kiyi hakuri za a saya miki mota kwanan nan.’

Ta zumbura baki tana muskutawa

‘Kullum haka dai kake cewa, ai shike nan. Idan ma kudin ne naga ga dayar nan da ta lalace a tsakar gida nace a hada da ita a sayar sai ka cika ka sayi motar.’

‘To ai motar da kike so a saya ta fi haka tsada, kada ki damu za a sayi mota. Ke dai ki kara hakuri.’

Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan ta tashi ta fice ta nufi falon kasa.

Ya bi bayanta da kallo yana jijjiga kai.

Ta matsa sai ya siya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login